Showing 48001 words to 51000 words out of 78257 words

Chapter 17 - Tubali Book 3 Hausa Novel Complete

*KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida ku蓷i gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin za蓳inki, ko karin bayani, zaki tura ku蓷in ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

馃馃徎馃グ馃槝 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*


Hannunsa ya 蓷aga, tare da nuna masa Jannart da yatsarsa.
Murya na rawa hawaye na kwaranya yace.
鈥淕ata, itace abinda Zainab ta haifa, itace 拼ar Yah Abdulkarim鈥�. Sai kuma ya tallabe kansa da tafukan hannunsa duka biyu, yana sakin shesshe茩an kuka.

Ita kuwa Jannart idanu ta zazzaro ta zuba musu, tamkar wacce bata gayyacinta,
Shi kuwa Rayyern da sauri ya rumtse 茩wayar idanunsa da yaji tauna tsastsafo wasu azabebben hawayen tausayin Jannart domin tuni ya gano inda mgnar Barrister Kabeer ta dosa.
Tafin hannunsa yasa kan tafin hannunta ya ha蓷esu kib, yatsunsu ya sar茩afe dana juna.
Wani irin masifeffen rauni, tausayi, jin茩ai, Jannart ne suka rufe masa zuciya da jiki baki 蓷aya.
Haka yasa tuni hawaye suke kwaranyo masa.

Yayinda tuni Aunty Dijat ma take wani kuka mai sassayan sauti.

Abba Rayyern kuwa, kanshi ya kife a jikin kujerar, domin dama ya zaci haka.

Mammy kuwa wani irin tausayi da son Jannart ya lullu蓳e zuciyarta, a zahiri take ganin kamannin fuskar Zainab 蓷in kan fuskar Jannart, domin kamace ta ha茩i茩a.

Shi kuwa Baba Mau蓷o, dafa kafa蓷ar Barrister Kabeer yayi tare da cewa.
鈥淜ada ka cemin basa raye, kada ka cemin haka, bana son jin haka.
Amman batun Jannart yarsuce kam na gamsu, kuma na dade da tuna hakan tun randa naji sunanta, domin kamanceceniyarta da Zainab sun 茩azanta, kada ka cemin marainiyace.

Zuwa yanzu gaba 蓷aya falon babu wanda rauni bai rufesaba.

Mamy kam itama tuni hawaye takeyi.

Dr Sajo ma kife kansa yayi, bisa hannun kujerar yana zubda hawaye.

Alhaji Bala Tambari, kuwa rumtse idanunshi kawai yayi yana mai jin rauni.
Riyyam-nsra da Ramadan kuwa, idanu suka zubawa Barrister.

Shi kuwa Barrister cikin Muryar kuka yace.
鈥淢arainiyace, maraici mafi muni, marsicine da ban ta蓳a jin irinsa ba a duniya koda a littatafai da finafinai.
Domin maraicine da ita kanta bata saniba maraicine da aka hana ta amfani iyayenta bayan ransu, maraicine da ba'a bata 茩ofar yiwa iyayenta addu'a ba, sabida masifar son duniya. Yah Idi da hannunsa ya kashe 蓷an uwanmu 茩aninsa mai binsa ni kuma yayana da nakeki.鈥�

Zuwa yanzu wani irin tsuma jikin Jannart ya farayi tare da jin wani irin tashin hankali yana ziyartota.

Shi kuwa Barrister Kabeer cikin rauni yaci gaba da basu lbrin kamar haka.
鈥淢u uku kacal iyayenmu suka haifa, Yan Idi shine, Babba sai Yah Abdulkareem, kana nine karami.
Iyayenmu sun renemu cikin aminci da bamu Kekkyawar tarbiyya.
Har muka girma, Yah Idi ya fa蓷a kasuwanci, cike da zalamar ganin ya zama shahararren mai ku蓷i, shi kuwa Yah Abdulkareem ya bawa karatu mahimmanci, inda burinsa ne ya zama cikekken lawyer.
Allah kuwa ya cika masa burinsu.
To amman fa Yan Idi baya godewa Allah kan abinda ya basa, shiyasa kullum na wani yake hango, ya samu abokai masu irin zuciyarsa.
Haka yasa mugayen zu茩atansu ha蓷ewa.

Yah Idi yayi aure, matarsa Amina mahaifiyar Junaid kenan.
Kana bayan ita, ya auri Momynsu Azeez amman ita a 拼ar sokotoce kuma acan ya ajiyeta, shiyasa.
Basu wani san junaba.
Amina tunda ta aifi Junaid bata 茩ara haihuwaba sai bayan shekaru goma, Allah ya bata ciki.

Momynsu Azeez kuwa ta Haifi Azeez wanda shekara uku ya bawa Abdul.

A lokacin kuma Yah Abdulkareem ma yayi auren, da ya kasance ba zata, domin aurene da akayi komi, da komai cikin 茩an茩anin lokacin.
Ya auri Aunty Zee, daga ranar kuwa.
Yacewa, iyayenmu zai 蓷aukeni.
Zan dawo gidansa da zama.
Haka kuwa akayi basu hanaba.
A lokacin in secondary School.

A watan da akayi auren a watan Allah yayiwa iyayenmu rasu baki 蓷aya su.
Dama ba yawan dangine da muba.
Yah Abdulkareem mutum ne mai jin茩ai da tausayi da gsky.
Aunty Zee kuwa wata daya da aurenta ta fara laulayim cikin.
Wanda sam bata son taji duk wani abu na 茩amshin girki.
Toh dan lokacin mafi akasarin lokuta nikeyi mana girki.
Aunty Zee macece mai ha茩uri da sanyin hankali.

A haka taita rainon cikinta har ya cika watannin haihuwarsa.

Wata rana da yamma Yah Idi yazo.
A falon Yah Abdulkareem din suka zauna.
Ni kuwa ina falon Aunty Zee muna kallo, sai take cemin, inje in amshi ku蓷i in seyo mata, kifi, don lokacin cikin ya kai haihuwa Yau ko gobe amman bata iya cin komai sai kifi.

Da sauri na mi茩e, na nufi 茩ofar falon Yah Abdulkareem din.
Har nasa 茩afa zan shiga sai kuma na tsaya sabida jiyo muryar ya idi da abinda yake fa蓷a.
Abdulkareem ka bamu goyon baya, a kan wannan 茩udurin namu, domin shine ka蓷ai kwanciyar hankali ka, sabida shi kansa uban gidan naka, yace mana takardun suna hannunka ya baka ka dawo dasu, a soke aikin, dan haka ka bani su, tun muna shaida juna.
Shi kuwa Yah Abdulkareem sai naji yana mgnar cikin sanyi yace.
鈥淎mman ai cewa yayi kawai a tsaida aikine bawai in baku, takardunba, ya za'ayi in baku abinda ba nawaba Kuma ba nakuba, inci amanarsa kenan.

Gyara tsayuwata nayi a bakin 茩ofar jin Yah Idi na cewa.
Wallahi ina garga蓷inka Abdulkareem domin, shakka babu, zan iya yin komai a kanka, ba tare da duba ala茩armu ba, muddin zaka hanani cika burina.
Da sauri naja da baya jin Yah Abdulkareem na cewa.
鈥淣asan zaka aikata, kuma nasan duk abinda zakayi bazai wuce, ka kasheni ba, to wlh koda kasheni zakayi bazan bada suba.
Hakan da yace ya fusata Yah Idi sai ji nayi yace.
Zaka ko gani ganin idonka.
Sai nayi saurin barin wurin sabida jin yana fitowa.

Saida ya tafi, na shiga na samu Yah Abdulkareem yayi shiru, cikin sanyi nace masa Meta faru,? Bai 蓳oye min komaiba, kana ya 茩ara da cewa.
Nasan son zuciya da rashin tsoron Allah irin na Yah Idi wlh zai iya min komai fa Kabeeru.
Naji tsoro sosai.

Dan haka, zan baka takardun nan, ka ajeyimen su.
Dan Kada in ya turo su sani in basu.
Cikin yarda dani yamin wannan bayani.
Kana ya bani takardun.
Sannan na gaya mishi mishi aiken da akayi min.
Ya bani ku蓷i naje, na saya mata.

Muka dawo muka zauna a falon munata hira, tanacin kitinta.
Saida ta gama sannan na tattare Wurin Yah Abdulkareem na dariya wai ta medani kande.
Ita kuwa sai ta zuba mishi ido tare da cewa.
Shekaran jiya da zaka tafi Gembu naso in bika, muje, amman nasan hanyar gashi kuma yadda nake, sai nakeji dama na gaya munje nayi musu kallon karshe.
Da sauri yace mata.
Zainab kallon 茩arshe kuma?
Sai tayi murmushi tare da sunkuyar da kai, mu kuwa duk ido muka zuba mata, cikin sanyi tace.
Musamman Neena na, naso in ganta ta ganni. Amman ba komai Allah ya sadamu a darussalam.
Wannan kalma ta girgiza Yah Abdulkareem dan a take naga yana zubda hawaye.
Ita kuwa da sauri ta yun茩ura zata tashi.
Sai kuma ta koma ta zauna tare da ri茩e cikinta.
Wachhh Abban Jannart yau kam da alamun Jannart zata fito duniya.
Jin haka kuma ya samu murmushi domin haka take tanada, raha, shiyasa tun kafin ta haihu take cewa, in dai ya mace ta haihu Jannart za'a sa mata in kuwa na mijine Jalaladdeen. Haka yasa take kiran Yah Abdulkareem da Abban Jannart tana yawan cemin idan mace ta haifa dai to matar Rayyern ce, wai sabida tana son yaron ni kuwa a lokacin banma san waye Rayyern dinba.
Shi kuwa Yah Abdulkareem murmushi yayi tare da cewa.
Wai da gaskene Zainab? Kai ta jinjina masa tana matsa la蓳蓳anta kana zufa na tsastsafo mata tace.
Allah kuwa da gaskene.
Da sauri nace, bazaki jira in zama likita ba, in kar蓳i haihuwar da kaina. Dan a lokacin dani da Yah Abdulkareem duk burinmu in karanci likita, ita kuwa Zainba da sauri ta kamo hannun Yah Abdulkareem.
Ganin haka yasa muka tafi asibin Dr Lukman, duk da Dr Sajo abokinsa ne, to amman lokacin baya 茩asar.
Muna zuwa kuwa aka amsheta, ana dubawa ma, akace ai yanzun zata haihu.
Muko sabbin shiga dama bamuzo da kayan haihuwa ba, hakan yasa, nayi maza nace zan koma gida in 蓷auko.

Ina fita kuwa, tana haihuwa.
Dr Lukman kuwa da kansa ya amshi haihuwar sabida, a lokacin babu yawan likitoci mata.

Cikin 茩ankanin lokacin na dawo, ina dawowa, na samu.
Yah Abdulkareem a ki蓷imi, yana bin Dr Lukman yana masa Dr Lukman, ka taimaka asan abin yi, jinifa ya 蓳alle mata.
Shi kuwa Dr Lukman waya yakeyi, haka yasa sai hannu yake juya mishi alamun yana zuwa.

Ni kuwa sauri nayi na shiga, cikin 蓷akin da naga sun fito.
A kwance na sameta da alamun har an gyara baby, da sauri ta yafitoni da hannu, ina isa, tasa hannunta ta 蓷auko Jaririyar daga kwance cikin jan numfashin tace.
Kabeeru, ga Jannart ta samu, amman zata rayu marainiya, babu uwa, kuma ubanma babu tabbas, domin naji abinda Dr Lukman yake fa蓷awa Yah Idi a waya kafin ya fita, a zatonsa bana jin turanci tunda ni ba fulatar Gembu ce.
Jini nake zubarwa amman cewa takeyi bazai min allurar tsaida jininba, bazai kuma gayawa Abban Jannart ba sai yaga na kusan mutuwa, yace kuma yanzu zaiyi 茩o茩arin tura musu Abbab Jannart ya tafi gida, suje can su sameshi, wai in har bai basu takardun ba su kashesa kamar yadda sukasa aka kashe Alhaji Bashir Maigaskiya daren jiya,
Cikin tashin hankali nace. Yah Idi Kuma, to shi yana ina, cikin jan numfashin tacemin shima yana cikin asibitin nan ya kawo Aunty Amina itama haihuwa zatayi, kuma naji suna cewa, ta rasu, abinda ta haifama babu rai.
Kabeeru, nasan ni kam bazan rayuba, kuma inaji a jikina zasu kashe Abban Jannart, dan Allah ka zame mata Garkuwa bongo abin jingina, ka ji茩anta, ka bata dukkan kulawa, da Kekkyawar tarbiyya, in ta girma kayi mata zabi da miji na gari mumuni mai jin tausayin maraicinta, Dan Allah Kabeeru kada ka bari, rayuwarta ta taggayara ko ta wula茩anta, ina tsoron kada magautan mahaifinta su dawo kanta.
Dan girman Allah Kabeeru kayi min al茩awarin kare min ita daga dukkan abin cutarwa, ka gaya mata ina sonta mahaifinta na sonta, tun kafin zuwanta duniya, ita kuma ta somu bayan barinmu duniya, tayi mana addu'a, ta zame mana al'waladussaliha.
Hankalina bai tashiba sai lokacin da na amshi yarinyar daga hannunta domin da ka gani kasan 蓷iyarta ce.
Sai kuma 蓷an 茩aramin yatsarta na hannun hagu da farcensa yake kamar a tsage kuma kala biyu, wanda irin farcen yatsar Yah Abdulkareem ne sak da sak.
Sai kuma na sunkuyo zan kalli fuskar Aunty Zee.
Nayi masifar gigitaccewa lokacin da naga idanunta na kafewa sunayin sama numfashin ta nayi 茩asa.
Cikin tsananin tashin hankali na kwantar da yarinyar, tare da tallabo kanta ina cewa.
La ha ila ha illahu Muhammadu Rasulullahi sallahu alaihi Wasallama.
Nayi kamar shadarne sabida firgicin ganin kamar ranta na barin jikinta ne, ita kuwa cikin sassayan murya ta amshi kalmar shahadar tana nanatawa, kira na fara aunawa Yah Abdulkareem lokacin da takai karshen kalmar shahada na ukun da kuma fitan ranta.

Ya salam naga tashin hankali a wannan ranar.
Domin a ki蓷imi na fito, sai dai ina fita motar Yah Abdulkareem na barin wurin.
Ban san me Dr Lukman ya gaya mishi ba yasashi komawa gida.
Babur na hau a guje nabi bayansa.

Sai dai ya rigani shiga gidan,

Cikin ki蓷ima nabi, bayansa, bayan na sallami mai babu 蓷in.
To sai dai bai tafiba ganin yadda nake kuka sai ya tsaya yana kallona.
Koda na shiga sai ya biyoni sabida bani canjina.

Ni kuwa da sauri na nufi falon jin wani irin masifeffen ihu mai ha蓷e da salatin da Yah Abdulkareem yakeyi.
Ina isa bakin 茩ofar na hango Yah Idi ne ri茩e da wu茩a, yanata caccaka cikin Yah Abdulkareem dashi. Alhaji Abdu Tababa na gefensa yana she茩a dariya.
Ihu nasa da azaban 茩arfi zan shiga, cikin.
Cikin zafin nama mai Babur nan ya fincikoni tare da fara jawoni waje.

Su kuwa a cikin inaga ihun da salatin da Yah Abdulkareem yakeyi ne ya hanasu jiyo nawa ihun.

Shi kuwa mai Babur nan da yake babbane da 茩arfi ya jani ya hau kashin sani.
Bayan layinmu ya tsaya jikin wani kango.
Yana cewa.
Kada kaje zasu kasheka dan Allah kada ka shiga, zasu kasheka yadda suka kashe na cikin.
Ni dai daga nan ban kuma sanin ina nakeba na suma.

Lokacin dana farka kuwa Yah Idi na samu a kaina.
Ashe shi mai Babur din da yaga na suma asibitin 蓷aya daukoni ya maidani, yayi komai aka bani gado sai ya gudu, sabida yana tsoro.
Toh da Dr Lukman yaga nine sai ya sanarwar Yah Idi.
Ashe kwanana uku ban dawo hayyacina ba sai ranan.
Ina farka sai na bushe kawai ina kallon Yah Idi sabida yadda ya ruggume ni yana wani irin masifeffen kuka mai tada hankali yana cemin. Wayyo Kabeeru mun rasa Abdulkareem sabida rasuwar matarsa Zainab da 拼ar data haifa, shima zuciyarsa ta buga ya rasu, sannan Amina ma ta rasu, sai wurin haihuwa sai marainiyar 拼arta data bar mana, Kabir ina tsoron rasaka, in ka rasu bani da kowa nawa a duniya.
Tsoro mai tsanani ne da mamakin makircin Yah Idi ya rufeni ya hanani Koda motsi.
Wanda da haka ya yaudari mutane haka yasa ko jami'an tsaroma basu shiga mgnar ba.

A ranan aka sallameni dole gidansa muka koma, inda muna zuwa na samu ya 蓷auko Mammynsu Abdul daga Sokoto ta dawo da zama nan gidan sa, ya kuma dam茩a mata Jannart a hannunta, da cewar 拼ar da Amina ta haifane.

Tsoro da fargaba ne yasa dole na kasa yin komai gashi bani da wani hujja bare shaida ga yarinta.
Sai dai nasan tabbas 蓷an sa Aunty Amina ta haifa ya rasu dansu 蓷a na mijine ba, kamar yadda Aunty Zee ta gaya min,
Sannan na gane Jannart, duk kuma wanda yazo sai aita mamaki ana cewa.
Wannan kam kamar 拼ar Zainab, to wannan abinne yasani yin shiru domin nasan bani da 茩arfin da zanyin fa蓷a fito na fito dashi.
Haka yasa na shiga jikinsa na zauna a gidan ina kula da komai na Jannart da rainonta Junaid kuwa yana sonta sosai.
Sai dai tana girma daga shekarunta goma sha hu蓷u abin ya fara sauyawa.

Sai ya fara sha'awarta, ni kuwa a lokacin nayi aure babu yadda banyiba, Yah Idi ya bani ita amman sai ya茩i fir dole na ha茩ura Amman babu randa gari zai waye ban jeba.
Sai daga baya na fahimci ita kanta Jannart ya fara sha'awar kasheta sabida yaga sa hannunta irin na mahaifinta ne sak.
Toh sai yake rainonta dan ta cika shekara ashirun da biyu, tasa mishi hannu a dukkan takardun kadarorin mahaifinta, a matsayin ya mallaka masa su kafinma ya rasu, shiyasa ya rainentan kuma yake da gudurin kasheta.
Wannan dalilin ne yasa, na fara shirin neman inda zan boyeta.

Kwatsam ranar a wurin taron mu sai naga Rayyern, kamanninsa yasani tuno da Alhaji Bashir Maigaskiya, ashema mahaifinsa ne, ina kallonsa a lokacin tamkar wanda aka haifa dan 蓷aukar fansane.
Daga nan nayi ta bibiyar rayuwarsa, na kuma gane shi asalin 蓷an Alhaji Bashir Maigaskiya ne, saidai bani da hujja, da naga Baba Mau蓷o kuwa naso in gane da tafiyarsa.
To amman bai bada damaba.

Wannan mai Babur 蓷in kuwa yanzu haka yana cikin tawagar Yan Idi, shi Al茩ali Baba,
Muna tsara komai tare, da hakane muka samu cikakkun hujjojin da Yah Idi ya rin茩a fa蓷a mana dukkan abinda yayi. Yayinda kuma muke na蓷an hakan a video komai.
Sannan Al茩ali Baba babban al茩aline da akeji dashi.
Kama kuma ga Alhaji Bala Tambari shima duk tawagar mu 蓷aya.
Zuwa yanzu duk munada cikekkun hujjoji na musamman.

Da sauri duk falon suka juyo kan Jannart, da ta saki wani irin maraitaccen kuka mai cike da maraici da 茩unan rashin iyaye.
Fa蓷awa jikin Rayyern tayi tare da kife kanta bisa cinyarsa.
Wani irin masifeffen kuka mai tafiya da numfarfashi ta sake cikin shesshe茩an raunataccen kukan take cewa.
鈥淚nnalillahi wa innailaihi raji'un, Hasbunallahiwani'imanwakil, wayyoooooooo Allah na, niyi asarar rayuwata ta, tsowon shekaru ban amfani iyayena da komaiba, kuma wai ina raye, banyi musu amfani ba ko ka蓷an ban zame musu mai tunasu da addu'a ba, wayyoooooooo Naaaan zuciyata zata fashe,鈥�.
Ya Salam shima kansa Rayyern fashewa yayi da 茩a茩茩arfan kuka mai sauti, ya jawota jikinsa ya ruggumeta da karfi.

Barrister Kabeer ma kukan ya saki kamar zai shi蓷e,
Baba Mau蓷o ma kife kansa yayi bisa sawun Alhaji Bala Tambari dake gefensa yasani kuka mai rauni.
Aunty Dijat kuwa itama ruggume yaranta tayi tare da sakin kuka.

Abba kuwa shima kukan yakeyi yana 蓷an bubbuga kafa蓷ar Barrister Kabeer alamun yayi ha茩uri.

Riyyam-nsra, Ramadan, Mammy da Mamy kuwa tausayin Jannart ne yasasu kuka mai ciwo.

Shi kuwa Rayyern cikin kuka yace.
鈥淣ooo! Nooo!! A'a Janna bakiyi asarar rayuwaba kuma suma basu yi asarar haihuwar ki ba.
Tsinenne kuma la'annne Alhaji Idi Sale Dakata shine yayi asarar rayuwar duniya data 茩iyama.
Daya tauye miki maraicinki
Yabar azzalumi 蓷ansa yana cutar min da ke.
Baki da laifi domin a baibai ya barki kika rayu.鈥�

Cikin kuka mai tafiya da numfarfashi ta kara ruggume shi tare da cewa.
鈥淣aaan kaji fa Mamana ta bada ya茩ini akan zan rayu, har tana cewa acemin suna sona tun kafin zuwana duniya.
Sannan tana bada wasiyan a sanarmin in sosu bayan barinsu duniya in rin茩a tunasu da addu'a.
Amman aka hanani wannan damar, Naan dame na amfanesu, me ribar haihuwata da sukayi? in banda cikin watannin nan daka nusar dani dayi musu addu'a a cikin dukkanin sallolina鈥�.





By
*GARKUWAR MARUBUTA*
1/2/22, 16:17 - Auntyn: Ya salam kusan gaba 蓷aya falon 蓷ibkewa da kuka sukayi.
Shi kuwa Rayyern kukan yakeyi har yana jin kamar kanshi zai buga, cikin tsananin tashin hankali ya tallabo kanta ganin yadda take kuka tuni idanunta sun kumbura sunyi jazir.
Hancinta yayi ja, numfashin ta sai korar juna yakeyi, hakan ne yasa ya jawota jikinsa ya ruggumeta da samun dai-dai ton numfashin ta.

Cikin tsananin tashin hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login