Showing 1 words to 3000 words out of 31410 words

Chapter 1 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

145

GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 1
Posted by ANaM Dorayi on 07:51 PM, 29-Apr-15
Under: Gangarjikinsa ta Aura
GANGAR JIKINSA NA AURA JAMILA UMAR TANKO
{JUT} ⃣Wata kwarababbiyar mota kirar bus mai
kararfatattakekkiyar salansa ce ta tsaya a bakin
get dinmakarantar 'yan mata ta gwamnatin
tarayya dakegarin Kazaure, wato F.G.G.C.
Kazaure. Tana tsayawakondastan motar ya ja
kofar ya bude "Barararaa"saboda kwankwatsewar
da kofar motar ta yi sakamakon cin ruwa da
gafje-gafje da tsabar tsufa.Wani dattijo mai
kimanin shekaru saba'in da doriyane ya fito, da
wata *yar yarinya tana biye dashiwacce
shekarunta basu wuce shekaru goma shadaya ba,
Bayan sun furfito kondastan motar yazagaya baya
wato but ya dauko wata katuwar akwatin karfe
irin ta *yan makarantar wacce akadafka sunan
mai akwatin garza-garza da fenti bakiHANNE
HABU IMAMU. Ya ajiye gefe ya sake janyowata
karamar katifa wacce take daure ya doraakan
akwatin, sannan ya dauko wani bokitin karfesabo
dal yana sheki shima an fenteshi da sunan mai
bokitin wato HANNE HABU IMAMU. Daga karsheya
mayar da kofar but din ya rufe ya juyo ya
kallidattijon wato Malam Habu ya ce "Baba baka
fa cikamana kudin motarmu bafa, gashi har kun
sauka"Malam Habu ya sake marairaicewa ya ce
"Dana daAllah fa nake hadaka kuyi hakuri kudin
da yayi saura a aljihuna ko gida bazai mayar dani
ba, sai nanemi ciko kayi hakuri dan Allah, dan
haka nemanace ta zauna a maleji yanzu baza ka
tausayawatsoho ba, karbi arba'in din?" Kondasta
ya sakefusata ya ce "Dalla Baba kana bata mana
lokaci gafasinjoji har sun fara tsaki sun kagu
suma a kaisu inda zasu. Ka zauna kana mana
magiya tun dazumuma fa ba'a bati muke shan
man motar da mukejigilar nan bafa, da kasan
kudin motar taka bai cikaba me yasa ka hau? Har
zaka ce wai yarinyar amaleji ta zauna, maleji ba
cikin mota bane? Bakasan har a sittin muke
daukar na maleji ba daga inda muka dauko ku
zuwa nan nayi maka ragi nace kakawo hamsin
dinma gashi kaki biya sai wataarba'in ka bani, kai
wallahi Baba saika ciko managomarmu kaji ko?
Direban motar dake zaune awajen tuki wanda
yake jin duk abinda suke yi, saiyanzu ya waigo
inda suke yayi magana ya ce "K.b wai yane? K.b
ya ce "Har yanzu wannan tsohon baidaina magiya
ba wai shi ayi masa ragin goma kudinyarinyar
nan data zauna a maleji, Hamsin nace yabiya, ya
wani bani arba'in. Kuma ma dan raininhankali
harda cewa kudin aljihunsa bazai mayardashi gida
ba, wato yana da kudin, cikawa ne bazai yi
ba.din aljihunsa bazai mayar dashi gida ba,
watoyana da kudin, cikawa ne bazai yi ba. Malam
Habuya danji dadi ganin direban yayi magana ko
zaice abar masa amma sai yaji kalamansa
sabanintunaninsa gara ma abinda kondastan ya
fada masa,cewa yayi in har bazai biya ta dadin
rai ba to zasu farka aljihunsa su dauki gomarsu,
Malam Habu yarike baki don mamakin irin
wannan rashinmutunci, can ya nisa ya ce "Allah
Ya kyauta, bari nabaku kudinku abin duk bai kai
ga haka ba, yasahannu a alhihunsa na dama ya
dauko watacukurkudaddiyar naira biyar ya sake
saka hannu a aljihunsa na bangaren hagu ya
dauko gudar nairaashirin da kwandaloli guda
biyar, ya hadakwandalolin nan guda biyar da
cukurkudaddiyarnaira biyar din nan ya mikawa
kondosta ya ce"Gashi dana Allah Ya kiyaye. Ba
kunya ba tausayintsohon nan yasa hannu ya
karbe yana gunani "Daman kana dashi ka tsaya
kana bata mana lokaciduk fasinjoji sun kagu,
direba ya juyo ya ce "YayaK.b ya baka, sun cika?
K.b ya ce "Eh sun cika jamujeJ.J.C. Malam Habu
da *yarsa Hanne suka bi motar dakallo har ta
hau titi ta kure sannan hankalinsu yadawo kan
kayansu. Malam Habu ya kalli *yarsa Hanne
wacce hawaye ya gauraye idanuwanta
dakumatunta, abin ya bashi mamaki ganin Hanne
nakuka alhali kuma ita take son karatu take
murna dazasu taho, ya sake juyowa sosai ya
kalleta yagahawaye ne ke zubowa daga
idanuwanta dayanabin daya, ya ce "*Yar Baba,
kukan me kike yi? Karki cemin yanzu bakya son
makaranta bayan keaka kira fadar mai gari aka
tambayeki kika ce kinaso. Ba'a son raina ba nima
na kawo ki makarantarnan ke kika amsa musu.
Shine kuma yanzu kikekuka? Idan kinsan bakya
so to ni a wajena tafinono fari sai mu juya kafin
mu shiga ciki. Kansila da mai gari su suka
tilastamin in kawo ki amma badanhaka ba nima
bazan rabu dake ba na kawo ki nanuwa duniya,
babu wanda kika sani. Hanne tagirgiza kai cikin
shesshekar kuka ta ce "Baba bamakarantar bace
bana so, rashin kunyar da masumotar can suke yi
maka shine ya sani kuka. Malam Habu yaji
hawaye ya cika masa ido amma sai yajure yayi
murmushin karfin hali ya ce "Allah Sarki*yar
Baba, babu komai duniya ce. Duk wanda
yagagirman tsohon wani, za'a ga girman nasa.
Hakakuma duk wanda ya raina tsohon wani sai
an rainanasa, zamani ne ya canja babu sanin
girman Allah, ko an hada mutum da Allah kamar
an hadashi dasa'ansa, wani cewa zaiyi daina
hadani da Allahkarka cuceni Wa'iyazubillah. Ya ci
gaba da cewa"goge hawayenki 'yar Baba kizo in
dora mikiakwatin mu shiga ciki kada dare yayi
min kinga harla'asar tayi. Tasa gefen gyalen da
taci damara dashi ta goge idanuwanta kana ta
matso ya ciccibiakwatin karfen nan ya dora mata
a kai shi kuma yadauki bokiti da katifa a daya
hannun sa'annansuka juya suka doshi cikin
babbar kofar shigamakarantar, yaci gaba da yi
mata nasihohi masuratsa jiki yana nuna mata
wannan abin da aka yi masa a gabanta ya zama
darasi a wajenta duklalacewar tsoho koma ba
tsoho bane na gaba da itakada tayi masa fitsara.
Ta zamana ko a ina takekuma kome ta zama ta
girmama na gaba da ita.Ta zama mai taimakawa
mabukata, kasancewartasan talauci ta kuma
dandanashi tana kandandanashi. Masu gadi uku
suka iske a bakin kofarshiga cikin makarantar,
suna zazzaune, MalamHabu yayi musu sallama
gami da mimmika musuhannu, Hanne ma ta
duka ta gaishesu, bayan sun amsa, Malam Habu
ya ce "Yarinya na kawomakarantar nan, ta ina
zanbi mu shiga ciki? Dayadaga cikinsu ya ce
"Mikewa zakuyi sosai zaku tararda ofishin
Malamai dana shugaban makarantar.Malam Habu
yayi godiya suka wuce, har sun danyonisa suka ji
masu gadin nan sun kwalla musu kira bayan sun
dawo, sai daya daga cikinsu ya kallesusama da
kasa ya ce "Dan Allah Malam muna datambaya
sai bayan da ku ka wuce tambayar ta fadomana.
Malam Habu ya gyara kayan dake hannunsagami
da yin murmushi ya ce "To Allah Yasa na sani.Ya
ce "Wai shin me kake tambaya ne? *Yar
makaranta ka kawo daliba ko kuma mai aiki
kakawo gidan Malamai a nuna maka gidan
Malamai(staff quaters)? Malam Habu ya ce "A'a
daliba nakawo 'yar makaranta ce. Su duka suka
kyalkyaleda dariya suna tafawa wani harda buga
kafa akasa. Abun ya daurewa Hanne da
Mahaifinta kai. Menene abun dariya?Konan ba
ita bacemakarantar 'yan mata ta gwamnatin
tarayya dakeKazaure? Malam Habu ya tambaya
suka ce "Nan cemakarantar daka ambata amma
watakila kayibatan kai ko baka ji dai-daiba.
Malam Habu ya ce"Batan kai kamar yaya? Daya
ya ce "Nan makaranta ce ta 'ya'yan masu hannu
da shuni,'yan birnimasu kokari, ba haka kawai
dan ance 'yarka tacimakaranta ba kaje ka suyo
akwati da katifa kazoka zabi makarantar da ranka
yake so ka shiga kacega daliba. Daya ya ce "Ko
dai waccan makarantar ceta gwamnatin jiha suka
rasa suka shigo nan. Koda yake ko can dinma
dakyar su kwashi wannan.Sannan na karshe ya
ce "Ku dai ku tsaya babumamaki nan din taci
abun ai na Allah ne, Malam inatakardar shaidar
taci nan makarantar? Malam Habuya ce "Mu
babu wata takardar shaidar cinmakaranta a tare
damu, ni dai kansilan garinmu yazo har gida ya
ce jarabawar da *yata tayi a birnita fito kuma
duk karkararmu ita kadai taci, maigarinmu ma ya
turo inje ya shaida min ya ce lallai-lallai nan taci
in kawota, ya ce min makarantun'yan mata a
Kazaure guda biyu ne data gwamnatintarayya
data gwamnatin jiha, ta gwamnatin tarayya taci
in kawota. Amma ni babu wanda yayi minzancen
takarda. Suka sake kecewa da dariya. Dayaya ce
"Malam sai kuyi waje don baza ku shiga bababu
takardar shaida, ku koma ku sami kansila
komaigarin naku su baku takardar shaida sai
kuzo kununa sannan mu barku ku wuce. Yau
gashi kusan wata daya ke nan da aka riga aka
gamakawo yara har sunyi nisa da fara karatu, kai
saiyanzu kake kawo 'yarka. Malam Habu ya ja
'yarsaa sanyaye suka yi waje, zuciyarsu cike
damummunar damuwa.Hakika Nigeria muna cikin
wani hali lokacin da yake ajiye kayan dake
hannunsa a waje,yakamawa 'yarsa akwatin dake
kanta suka saukekasa. Suka tsaya suka yi cirko-
cirko suna kallon masu gadinnan,wadanda har
yanzu basu daina yabo musubakakenmaganganu
ba. Malam Habu ya nisa ya ce "AllahSarki
rayuwa, Allah Ka fimu sanin halin da muke ciki
kaizaka fitardamu, 'yar Baba zauna a gefen
akwatinki kinjikafin mugayadda Allah zai yi damu.
Isa kansila da maigarisuka ja mana wannan
wulakancin. Ni nasan a rina, shi yasa dafarko
nakifur da akace za'a kaiki birni daukar
jarabawa,kuma kema daakayi kiranki me yasa ki
amsa musu? Kika ce kinason karatun, ga irinta
nan ai. Hanne ta zauna a hankali jikintayayi
sanyi,wanda ko yatsanta wuyar dagawa yake yi
mata.Zuciyarta cikeda damuwa, babu abin da
take tunawa illakomawarta gida haduwarta da iya
Abu kishiyar uwarta da'ya'yanta.Irin tsananin
azabar da suke gallaza mata dabautar ta din
daake tamkar baiwa alokacin cinikin bayi. Ta ce
aranta "Da inamurna zanzo makaranta nabar
gidan da banahutawa kuma ban taba hutawa ba
sai yanzu. Gashi yanzumakarantar masun koro
mu dole mu koma gida. Taci gaba da
tunairintataburzar da aka sha da Mahaifinta kafin
Iya Abutabar su suka fito daga gida zuwa
makarantar nan. Wai itaidan Hanneta tafi babu
mai yi mata aikace-aikace su sharawanke-
wanke,debo ruwa a rafi ko tuka-tuka. Saboda
haka nemataki fur wai baza a kawo Hanne
makaranta ba. 'Ya'yantakuma garda-garda maza
da mata suna zaune ko tsinke basadaukewa
saiHanne wacce bata da uwa a gidan. Allah
Sarkihawaye ne ya kecewa Hanne yayi ta zuba
daga idanuwanta.Maganar dadaya daga cikin
masu gadin keyi ita ta katse tadaga tunanindata
dulmiya tana yi. Taji kamar daga sama yanacewa
"Kai kauyawa ma da rashin tunani suke dan
kawai ance'yarka tacimakaranta sai ka taho ka
zabi makarantar data yimaka kawaika sako kai,
dubi yarinyar daya kawo sai kace maizuwa tallar
kalwa riga a cukurkude, zanin daga kasa ya
nadekamar annade tabarma. Takalmin kafarta
harda leda tadaure waye zaice daliba ce. Daya ya
ce "Danmarar data ci kai kacedandali zata, ta
daure kugu tamau. Ina jin ma basu san
anadinkakayan makaranta ba (Uniform) balle
takalmikambas da safa.Hanne tayi ajiyar zuciya ta
hadiye yawun da ya cikamata bakinta tayi shiru,
kanta a sunkuye a kasa.Tace a ranta "Lallai ko
nafi maye kwakwa dole nahakura damakarantar
nan harda kayan makaranta akedinkawa. Wayezai
dinka min? Ta sake kallon kayan jikinta tace
aranta "Kayan sallar tawa shine suke cewa duk a
cukurkude? Niina ganinnayi ado kowa a garinmu
da muka zo wucewayana cewaHanne yau kuma
ina zaki kika ci ado haka? Su anankazan- kazan
suke ganina ashe, dole mu koma gida asheban
rabu dawahalar Iya Abu ba. Kuka ya sake kece
mata hardashessheka. Malam Habu ya kalleta
fuskarsa cike dadamuwa ya ce "Yi shiru 'yar Baba
bari zamu san yadda zamuyi mukoma gida. Ni
yanzu ke nake ji gashi kudin da yarage mun
aaljihuna saura Naira ashirin kacal. Da
niyyatainnakai ki makarantar in zan koma gida sai
in hau mota daganan zuwatashar Kazaure daga
can kuma sai in kama hanyada kafa harBabban-
mutum (garinsu) idan dare yayi mun insami waje
in kwanta washe gari na tashi naci gaba. Har dai
inkarasa kokwana nawa zanyi a hanya. To yanzu
ba zai yuwuba tundagaki, sai dai kawai mu shiga
mota muje tasharKazauren, ko a bakin tashar sai
in siyar da akwatin nan ko katifarkoma dukamu
samu muyi kudin motar komawa gida. Hanne
tazabura tace "Ka siyar da akwati da katifa fa
kace? Kansila aisai yasa a kamaka, cewa yayi fa
gwamnati ce ta siya ta bani.MalamHabu yayi
kasake yana tunani na wani lokaci maitsawo can
yace "To laifin waye? Shi kansila da maigari basu
sanda kudi za'a zo makarantar ba, babu wanda
ya bamu kosisinsa,kansila kullum yana min
alkawarin zai je ya karbokudin da zaayi miki
siyayya da kayan makaranta da komai dakomai,
har cewa yayi motar gwamnati ce zata zo ta
kawoki..Daga karshe ya zo ya fara hanya tun
dagagwangwarmarakwatin nan da katifa da bokiti
babu abunda yakara kawowa.Bansan wacce
shawara suka yi da maigari ba kumadaga karshe
suka ce inzo in kawoki haka za'a aiko
mikikayayyakindaga baya. To yanzu gashi
takardar makarantar cebabu aka yimana korar
kare ina ga idan muka shiga ciki aka cemu kawo
kudi, muka ce babu ai sai a rakomu da duka.
CikinsauriHanne ta ce "Lah Baba na tuna jiya
maigari ya aikoda watatakarda da yamma ya ce
ta makaranta tace, bakanan. Na karba nasa a
akwatina ko itace suke tambaya?Malam Habucike
da mamaki da zumudin dauko takardar ya
ce"Haba 'yarBaba kina 'yar karamarki kike
mantuwa, tun dazufa ake maganar takardar duk
baki tuna ba. Yi maza kidaukotakardar in nuna
musu ko itace takardar. Hanne tadagaakwatin da
sauri ta bude, babu komai a ciki saikayan
sawarta kala biyu a cukurkude suke kamar anyi
sukuwardoki a kansu.Ta binciko can kasan
akwatin ta dauko watadoguwar takardafara ta
mikawa Babanta. Malam Habu ya karba dasauri
ya doshi wajen masu gadin nan yana cewa "Ga
daiwata takarda a cikinakwatinta saiyanzu ta tuna
ashe mai gari ya aiko da ita jiya kudai ku duba
ku gani ko ita ce. A yatsune daya daga cikinsu
yakarba yaduba yana dubawa kuwa yaga
takardar shaidar andaukiHanne Habu Imamu a
F.G.G.C Kazaure ce wato(Admission letter) Sun
sha mamaki kwarai da ganin nanmakarantar
kuwataci ba batan kai suka yi ba. Cikin sakin
fuska sukayi musuizinin su kwaso kayansu suzo
su wuce. Cikinmurna Hanne da Mahaifinta suka
kwashi kayansu suka wuce izuwacikinmakaranta.
Basu tsaya a ko'ina ba sai a bakin
wanibabbangini wanda ya kunshi doguwar
baranda da ofishinMalamai.Babu kowa a wajen
hatta leburori masu share-share da goge-goge
duk basa nan, wajen tsit kamar babubil'adama.
Sukasami gindin wata bishiya suka sauke
kayansu.Hanne ta hau kan akwatinta ta zauna
Malam Habu ya ce "To fawannanshine ko in kula,
yanzu kuma ina zamu dosa kokuma wazamu
tambaya? Ni wallahi abun nan na
makarantarbokon nan ya ishe ni daga nan sai can
ana tsattsare ka datambayakamar a lahira mun
gama da masu gadi yanzukuma Allah nekadai Ya
san wa zamu hadu dashi, kai Allah Yakyauta,
wannan shine ake cewa ba shiga ba fita wai
anbawamahaukaci gadin kofa. Shigowar wata
dalleliyarmota ce Jeeplaunin koriya (dark green)
wacce ta tunkaro indasuke, ita ta katsewa Malam
Habu surutun da yake yi. Ta zo dafda su tatsaya
babu abinda yake tashi a cikinta sai sautinkida
dasanyin A.C maza ne samari guda biyu suka
fitodaga gani wa ne da kaninsa, kanin yana sanye
da kayan bautarkasa ajikinsa wato (N.Y.S.C)
Yayan kuwa wata tsadaddiyarshadda cefara sol a
jikinsa sai kamshin wani tsadadden turarene yake
tashi. Abunka da kauyawa sai kallo suke
dukkauba da *yar,kanin ya bude but din baya ya
dauko wata Jakarkaya, yamayar ya rufe ya ce da
wansa "Yaya Habib, na godesai dai nace maka
Allah Ya kiyaye hanya. Yaya Habib
yayimurmushiya ce "To madalla. Allah Ya bada
sa'a sai yaushekuma zaka zomana weekend? Ina
fatan dai wannan karan zakayi kamar wata baka
zo ba ko?Su duka biyun suka tuntsire da dariya,
kanin yace "Ai Yayaranar juma'ar nan zaka ganni
a gida ko ba'azodaukana ba mazanzo Kano, haba
ai sai jini na ya hau zama a kauyein ba dole ba
wa zai iya? Yayan yana dariya ya mikawakanin
hannusuka gaisa ya ce "To Allah Ya taimaka, ina
ganinranar juma'arda zaka zo may be baza mu
hadu ba saboda dasassafe zan tashi zuwa
america kai kuma nasan sai da yammazaka
tahosai an tashi *yan makaranta ko? Kanin ya ce
"Ehkuwa bazamu hadu ba Allah Ya kiyaye hanya
Ya dawomana da kai lafiya, Yaya akwatinan
auren da nawa da naka yazamo iridaya. Yaya
Habib ya ce "Insha Allahu, Yaya Habibya
shigamota har zai ja kofar motar ya rufe sai ya
juyo yakalli Hanne da Babanta ya ce "Salamu
alaikum" Malam Habu yaamsagami da daga
hannu, Yaya Habib yaja motarsa yajuya ya
nufikofar fita kanin na tsaye yana daga masa
hannu.ayan da motar Yaya Habib ta kure,
idanuwansuduka na kantasannan hankalin kowa
ya dawo jikinsa. TunaninHanne yakoma ga kallon
kyakkyawan ginin makarantarginin bulo da
bulo,yaune rana ta farko da take tunanin take
saran zatakwanta a dakin ginin bulo ba gidan
kasa ba rufinazara. Ta cea ranta "Cafdijan yau
kuwa zan iya bacci? Anyabazan ringa jin sanyi ba
a wannan dogayen gininnikan. Bata sansanda
tayimurmushi ba har hakoranta suka fito, sai
tawayence ta kifakanta akan cinyarta kada
Babanta ya ganemurmushin dadi take.
Kyakkyawan saurayin nan ya tunkaro indasuke
yanarataye da jakarsa a kafadarsa, ya yiwa
Malam Habusallamagami da dan dukawa kadan,
kana ya wuce su yajegindin wata bishiyar dake
kusa da tasu ya daga wani benci yazauna yaajiye
jakar kayansa a kusa dashi yaci gaba dakallon
Hanne daMahaifinta. Can Malam Habu yaje ya
same shi a indayake zaune ya ce "Dan Allah *yan
samari kai maka'aikacine ananko kaima bako ne?
Yayi murmushi ya ce "Yaya akayi Baba?Malam
Habu ya ce "Yarinya na kawo makaranta tundazu
banga kowa ba balle in tambayeshi hannun wa
yakamata indankata? Saurayin nan ya gyara zama
gami da cirehular dakekansa ya ce "Daliba, daliba
ce wannan? Malam Habuya ce "Eh nan aka ce na
kawota kuma gama takardar canbari ta mikogama
korarmu akayi dazu da babu takardar, yakwalla
kira yace "Hanne kawo takardar nan ta dazu.Cikin
sauri Hanne tasa hannu a cikin bokiti
dakegabanta tadauko takarda tazo ta mikawa
Babanta da hannubiyu ta dukahar kasa. Babu
abinda wannan saurayi yake saikallon Hanne
sama da kasa kayan jikinta yake kallo da
takalmindakekafarta wanda ta daure da leda
saboda ya tsinkekudin naninma aiki ne, wata
uwar danmara kai kace dambentsiya za'a kwasa,
wuyan, hannu da kafa tsakiyoyi. Saurayinnan ya
kulada lallai Hanne ita kanta tana jin kunyar
shigar nantata ganinkallon da yake yi mata, sai
yayi sauri ya fara dubatakardar da Malam Habu
ya mika masa. Ya karance tsaf, sannanya dagoya
ce "Hanne Habu Imamu ko? Tace "Eh, ya ce
"ToBaba saikun dan jira don nima nan Malamin
nake jira gashitakamaimai ma ni bansani ba ko
yana makarantar kobayanan don nima shigowata
kenan. Malam HabuyayiHamma gami da yin dan
siririn tsaki ya ce "Yaroyanzu bayadda za'ayi ka
karbi yarinyar nan, dole sai waccan din ya zo?
Saurayin ya ce "Ni Malami ne amma kuma
bapermanentteacher ba bautar kasa (service)
nazo yi, a ka'idarwannanmakarantar kuma senior
master ne ya kamata ya karbetamusamman ma
kasancewarta sabuwar daliba ce.Gashi yau lahadi,
dama litinin ce ko sauranranakun aiki lokacin
principal tana nan, da sauranpamanent teachers
duk sai su karbeta koda seniormaster baya nan,
amma yanzu ku jira kadan idannan da minti
talatin bai dawo ba, zan tashi nima nashiga staff
quaters din na gani ko yana ma cikin makarantar
dan nima shi nake so na gani zan karbimukullan
gidana. Malam Habu ya ce "To Allah Yakawoshi
lafiya bari nayi sallar la'asar, nasan biyartayi ko
sallar la'asar bamu yi ba. Yaro ina buta? Yanuna
masa wani fanfo can kusa dashi kuma
dazagayeyyen waje nan ne Masallaci. Malam
Habu ya ce "To madalla. Ya kalli Hanne wacce ke
tsaye agefe har yanzu ya ce "*Yar Baba koma
kanakwatinki ki zauna zanje nayi sallah kinji.
Cikinsanyin murya ta ce "To, ta juya ta doshi
wajenakwatin. Malam Habu ya bita da kallo
zuciyarta cikeda tausayinta ganin yininsu guda
babu abun da suka ci tun dan kokon safe da
suka dan kukkurbaa tsattsaye bala'in Iya Abu ya
hanasu su zauna susha sosai. Malam Habu ya
girgiza kai alamartausayawa kansu da kansu ya
ce "Allah Sarki *yarBaba hakuri dai za ki yi, ki
kuma ci gaba dayi.Sannan ya juya ya nufi wajen
fanfo. Kyakkyawan saurayin nan na zaune yana
kallonsu zuciyarsacike da alamomin tambaya da
tsananin tausayi. Canya nisa yayi ajiyar zuciya ya
zaro gilashin dakealjihunsa ya saka a idonsa gami
da cusa hular dakehannunsa a cikin aljihunsa na
wando yasahannunsa ya dafe habarsa yaci gaba
da kallon Hanne dake zaune kan akwatinta tayi
lamo tanatunani ba tare da tasan wani na nan
gefenta ta cikingilas yana kallonta ba. Ya ce a
ransa "Wadannandaga wanne kauye suke?Sun
kuwa karanta takardar dake hannunsusunsan me
ya kamata su tanada suzo dashi? Kaibasu san
dokar da aka rubuta ba a jikin joininginstruction
din nan ba. Lallai kuwa da sun san meaka rubuta
da baza taci uwar danmarar nan ba tashigo
makarantar nan haka ba. Bayan kamar tafiyar
Malam Habu da minti ashirin sai gashi yadawo.
Ya zo ya wuce ta gaban saurayin ya ce"Sannun
ka da hutawa, ya katse tunanin da yakeya ce
"Yauwa Baba. Malam Habu ya kara da cewa"Har
yanzu dai kaga shiru baizo ba ga rana nan
nashirin faduwa yau kuwa anya mai karbar yaran
nan zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login