Showing 6001 words to 9000 words out of 31410 words

Chapter 3 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

149

da itagidanki kamar
kwana biyu haka kafin na diko mata kayan
makaranta( uniform) da sauransiyayya sai tazo ta
koma hostel. Uwar biyu tace''allah sarki malam
haisam ai wannan ba wani aikibane babu komai
ai sai mu tafi daman na gamadaure ledata tafiya
kawai zamu yi'' haisam ya ce'' tona gode '' yasa
hannu a aljihu ya dauko kudi ba tare daya kirda
ba ya mikawa uwar biyu yace '' toga wannan don
ku samu ku saisayi dan abundababu'' uwar biyu
ta karba zuciyarta cike da farinciki da mamaki irin
wannan yawan kudin da koalbashinta na wata
baikai wannan haka ba, gashidaman wata yayi
nisa. Tayi ta godiya da da shi albarka har ya gaji
da amsawa. Ya kalli hanne yace'' hanne inaga
yau duk a wunin nan baki ci abinciba ko? Hanne
ta sunkuyar da kai tayi murmushitace'' na karya
da safe'' uwar biyu tayi caraf tacea.a.a tin karin
kumallon safe kuna ta tafiya ko?Haisam yace nisa
, don haka uwar niyu kuje ki bata abinci taci ta
koshi.Haisam yace ki siya mata tsiren nan na
bakintasha dan alla '' uwar biyu tace to in allah
ya yardayanzu kuwa'' haisam yaci gaba da cewa''
sannan kisai sabulun wanka da mai me kamshi ki
bata tayiwanka , karki barta ta sharba yanxu duk
fuskartata kwabe da kwalli. Hanne ki daina yin
wannan dige digen kinji ? Hanne tace to uwar
biyu tayidariya tace'' ai da haka suma zasu zamo
'yan matasu koyi yadda ake kwalliya me kyau irin
na yanboko ko hanne? Haisam yace'' ina ganin
har kantasai an wanke , anyi mata sabon kitso,
ko kinyi kitsomuga kan? Hanne ta zame
dankwalinta ta durkuso da kanta ta nuna musu
wayyo allah kowa ya kallikan hanne zai san bata
da uwa a gidan ko wanitsayayyen mafadi ko
kuma kazamar uwa allah yabata gashi ne irin
kanannadaddennan na fulani kobuzaye ko
larabawa mai laushi mai santsin gaskebaki wullik
mai tsawo sosai wanda yake taba doron bayanta.
Amma me ? Yayi datti. Kura, amosalikai kace
dambe tayi aka tumurmusa kan a cikinyashi . Sai
wani kitso tuma tuma guda biyu dagagani ita tayi
da kanta. Uwar biyu tace'' la la hannehaka kanki
yake ? Amma kinyi wasa a yashi ko ?Gaki da
gashi tubar kalla baki san yan mata yanzu ido
rufe suke neman gashi ba. Da kudinsu ma
siyasuke su kara yaya kika bar kanki haka
babugyara ? Hanne tayi shiru kanta a sunkuye a
kasatana kokarin daura dan kwalinta. Haisam
wandayake zaune yayi shiru sai girgiza kai
alamantausayi. Can ya nisa yace'' uwar biyu
yanzu dai abunda za.a yi ga wannan wasu kudi
ne ya sakecunkusowa daga aljihunsa ya mika
mata tace'' nameye wannan kuma? Ya ce'' ina
ganin hanne nabukatar abubuwa da yawa a
kwana biyu da zatayigidanki . Ki tsaya a aishalle
super market kitattambayi masu wajen irin man
wanke gashi, dana kitso da sabulun wanka,
wanki, abun goge kafa kisiya mata silifas. Ki duba
kan idan akwaikwarkwata ki sayi shaltos duk a
fesa su mutu. Kozaki taho aiki gobe to ki sami
wata ki biya ta waccezata gyara mata kannan tayi
mata kitso. Kai harmawanka kuyi mata da kanku
ai bata wuce ayi mata wankan bama'' uwar biyu
tace'' in allah yaso yaudin nan kafin mu kwanta
da kaina zan gyaratagobe kuma ko zan taho aiki
da diyata halima tananan auren ya mutu tana
gida sai in barta da ita.Kuma ta iya kitso kala
kala sana'arta kenan ki agarin da tayi aure''
haisam yace to nima gobe wajen karfe biyu idan
an tashi a makaranta akwai tela dazamu je dashi
can gidan naki ya auno ta zai dinkamata kayan
makaranta(uniform)sai ki kwatantamin gidanki
don naje. A kanti kike ko cikin gari ?Uwar biyu
tace'' ah a cikin gari nake. Idan kajefada, kofar
gidan sarki daga hannunkan a dama zaka ga titi
ya mike to kabi shi kace a nuna makagidan
dalhatun kazaure alhaji hamisu to lyngun mudaya
ko a gidan kace gidan uwar biyu kake nemayaro
karami zai nuna maka dan mu muke yi
mususurfe, katangar gidanmu daya'' haisam
yace'' toshike nan yanzu k dauki wannan kayan
ku kai store din kicin ki ajiye su sai nan da kwana
biyuidan anyo siyayya sai a dauko a zuba,
sannankuma abinda nake so dake bana son ki
gayawasauran abokan aikin ki ga dalilin da yasa
zata jegidanki da sauransu. Ko a cikin gari ma kiyi
gum dabakinki kinsan jama.a da surutu za.a yi ta
cewa an kawo yar kauye makaranta babu komai
sai dauwar biyu takai gidanta wani malami ne
yayi matasiyayya da dai sauransu. Ba wai nace
kin cikasurutu ba ko gulma a'a ko mutum daya
yaji saidubu sunji. Kuma ai akwai matan kicin da
yawa damuke gaisawa amma dana ga alamun
suna da yawan magana ai ban kira su na basu
amana bako ? To yadda tasa nace ta kira uwar
biyu'' uwarbiyu ta kyalkyale da dariya dadi ya
lullubeta '' tacehakane malam haisam ni dana ke
cikinsu yangulma ko sun tambayeni ni nasan me
zn fadamusu'' haisam yace'' yauwa ku dauki
akwati da bokiti da katifar kamar yadda nace akai
store aajiye, sai da safe'' suka ce allah ya
kaimu''uwar biyuta kama akwati ta dora akan
hanne ta dauki bokiti,da katifa a daya hannun
suka doshi store din kicininda suma suke boye
shirginsu . Malam haisamkuma ya rataya jakarsa
ya nufi gidajen malamai (staff qurters). Zuciyarsa
cike da tausayin yaddarayuwar hanne take. Kuma
da burin canza matanan gaba* * * * HAISAM
ABDULHAMID ZAKAR Sunanmahaifinsa ne
abdulhamid zakar. Mahaifiyarsakuma sunanta
NANA HAUWA'U Wacce a yanzu akafi saninta da
hajiya nana ko kuma barista nana kasancewarta
kwararriyar lauya ce. Mahaifinhaisam haifaffun
unguwar kwalli ne a kano. Kumasun fito daga
tushe daya yar kanwace aka hadasuaure a
lokacin alhaji abdulhamid ya gama karatumdigiri
dinsa a london yana da shekaru ashirin dabakwai
ita kuma hajiya nana ta gama karatun sakandire
tana da shekara goma sha shida.Dukkaninsu
iyayensu suna da matukar arziki. Donhaka an
sakar musu kudi yadda ya kamata antafka musu
kerarren gida, motoci an kuma bawaalhaji
abdulhamid jari mai tsoka yana juyawa itakuma
hajiya nana ta fara karatunta na law a jami'a
bayero ta kano. Allah ya albarkacesu da
ya'yahudu, uku maza mace daya itace autar.
Wacce ahalin yanxu ko yaye ta ba ayi ba karama
ce.Babban shine yaya habib yanzu yana da
shekaratalatin , mai binsa shine abdulhamid ake
kiransa dahaisam yanzu yana shekararsa ashirin
da shida mai binsa iziddeen shekarunsa ashirin
da uku. Sai daiziddeen ya gama sakandire ya
shiga jama'asannan aka yi masa kanwa mai
shekara daya anakiranta da amratu.Girma
yazowa alhaji abdulhamid da matarsaamma
kumakarfi ya tasamma ya'yansa zasu iya kula da
dimbindukiyarsada kamfanoninsa yaya habib ya
kammala digirinsaa jamia'ar a.b.u ya karanta
business admin a yanzu yana aikia
kamfaninbabansa shine kuma mai zurga zurga
zuwakasashe dabandaban na shige da fice da
kayan kamfanonin.Haisam wanda a shekarar nan
ya kammala karatun jami'a yakaranta
bscgeography yanzu yana bautar kasa a
f.g.g.ckazaure da zararya gama kujerarsa ta aiki
nanan na jiransa a dayadaga cikin kamfanonin
mahaifinsa. Na uku wato izziddenyana shekara
tauku (level 3)a jami'ar bayero ta kano yana
karatunlaw don yagaji mahaifiyarsa wato barista
nana wacce itacebabbar lauyar kamfanonin .
Tana kuma farin cikin ganin dayadaga
cikin'ya'yanta ya taso gadan gadan da karatun
lawwanda a cikin'yan shekaru kalilan zai gama ya
zama cikakkenlauya ya canjeta alhaji abdulhamid
ya dankawa yaya habibragamaraiki ya koma gida
ya zauna yana hutawa sai daiyajekamfanonin
fisha yaga yadda aiki yake tafiya yakoma
gida.Dan lelen abba da umma wato haisam shine
yafikowashagwaba a gidansu ko kuma nace shi
akafishagwabawa tunyana kankani. Amma ai
izidden ne yakamata yayishagwaba kasancewarsa
ya dade yana auta kafin ayi masakanwa ammashi
yana gefe tun suna yara haisam ne a
kancinyarsabodatsananin biyayya, ladabi , tausayi
da jinkai irin nahaisam shine ya kara masa fada a
wajen mahaifansa sunfisha'awarsu zauna suyi
hira da haisam sau dubu da suyi fayayansahabib
tun suna yara saboda haisam yake magana acikin
nutsuwa yake kalamansa masu muhimmanci
akoda yaushefuskarsa cike da annuri(fara'a),wasa
da dariya damanya dayara. Bashi da raini ga
hakuri , baya ga zunzurutunkokari da allah ya
bashi a bangaren karatunsa dukka akur'ani da
bokonyasan alkur'ani kamar me a kansa duk
gidansubabu maiiliminsa. Hatta mahaifinsa yakan
yi masa tambayoyiakan duk wata matsalarsu ta
addini ko ta zamani, yana datsananinhakuri sau
tari ana masa abu da yawa yayi
hakuri.Ammakuma duk gidansu babu mai zuciya
kamarsa idanaka kureshi, idan yayi fushi abin
babu kyau mai hakuri bai iyabacin rai ba.Da farko
a enugu state aka turashi bautar kasa(n.y.s.c)
kasancewar shakuwa da sabon da mahaifinsasuka
yi dashi basa so yayi musu nisa don haka alhaji
abdulhamidyasa adawo dashi kurkusa saboda
yasan manya manyakasar nandaga yan boko har
rukakkun yan kasuwa. Ammaduk da haka haisam
yana korafi shifa kazaure yayi nisa da kanoa
dawodashi cikin kano inda kullum zaina kwana
gida, dakyar dai akalallasheshi yayi hakuri duka
duka bazai yi shekaradaya ba zai gama ya dawo
gida gaba daya. Don haka dukjuma'a yaketafiya
gida wani lokaci ma a kanon yake yin sallarjuma'a
sailahadi da yamma ake dawo wa dashi. Gashi
yanzuma baifi saura wata uku ba ya kare bautar
kasa kwatakwata ma yakoma daya ke
muradi.Bayan tafiyar hanne gidan uwar biyu da
kwanauku wato ranar laraba da sassafe sai ga
wata mota an kawo hannemakarantahaisam ya
roki wani abokinsa safiyanu yaje cangidan
uwarbiyu ya dauko hanne da kayanta ya
kawotamakaranta. Haisam ya gama mata
siyayyarta kakaf ko yaranattajiranmakarantar
baza su fita kaya ba(provision)kayanmakarantarta
(uniform)suma har kala kala bibiyuyayi
matatakalma kuwa kala kala akwai kito, sandal ,
kambos fari dabaki tsadaddu, silifas dan madina
har biyu, ya suyomata dawasu yan kanti riga da
siket suma kala biyu. Yasuyo matajakar zuba
kaya mai kyan gaske yar madaidaiciya wato
(travelling bag)a ciki aka zubawa hanne
kayansawarta, nata nada kuwa yana gidan uwar
biyu, kayan tande tandedamakulashe kuwa abun
baya lissafuwa kama daga biskit kalakala, alewa
(chocolate)indomie, madara, milo,sugar
,complakes da dai sauransu ko gari babuballe
wanikanzo irin na yan makaranta makilin da
brushhadaddu, mayukan shafawa da sabulansu
masu kamshi gamayukangashi cike a akwatin
hanne hankar da kaya allahya taimaketasa
kansilansu ya tashi kawo maya akwatin yakawo
mata randimemiya, mai cin kaya da yawa.Hanne
sanye take da kayan makaranta(uniform)kafar ta
kumafarin kambos ne da farar safa an tufke
kitson kantada waniribom mai kyau mai fulawa,
duk wanda yaga hanne kwanakibiyu da suka
wuce a yau dai bazai gane taba tayifari kyalkamar
yar larabawa, ashe mai dangwali ya ba neda
bakinkwalli suka cabe mata fuska tayi baki kirin.
Safiyanu yazobakin offishin malamai ya tsaya da
motarsa sannanya fitodaga ciki ya juya ya kalli
hanne wacce ke zaune abaya tanakokawa da
murfin kofa ta kasa budewa abunka fa
bakauyiiya.Wannan ne karo na farko da hanne ta
taba hawadon hakabata san ina zata ja kofa ta
bude ba. Safiyanu yazagayo dasauri ya bude
mata, ta fito yace'' to dauko jakar litattafan
nakimana'' hanne tasa hannu ta jawo wata bakar
jaka(schoolbag)tsadadda mai kyan gaske, yar
madaidaiciyadaidaibayanta cike take da kitattafan
rubutu da litattafan karatu(textbook)duk dai
kamar yadda aka zano ajikintakardar babuwanda
haisam bai siya mata ba ga biruka da
fensirdamathematical set din su ya suya mata .
Safiyanu ya nunawahanne yadda zaya rinka
ratayawa a bayanta tarataya sukanufi cikin
ofishin. Suna shiga suka iske wani
malamibayansafiyanu ya mika masa hannu sun
gaisa sai yayi masa bayaninabunda ke tafe dasu
yace daliba ya kawo, sai yanuna masaofishin vice
principal yace nan zasu shiga.sukayi sallama suka
shiga suka iske viceprincipal yanaharhada wasu
takardu a gabansa, bayan syn gaisasafiyanu
yashaida masa cewa yarinya ya kawo yar aji daya
cesabuwar zuwa sai ya nemi daya bashi takardar
shaidar cewaita dalibarnan makarantar ce wato
(joining instruction)daman haisam yabashi ya
dauko ya mika masa ya duba yace''sunanta
hanne habu imamu daga babban mutum ko ?
Safiyanuyace ''eh,''vice principal din nan ya
kurawa hanne ido yanakallozuciyarsa cike da
mamaki ga yarinya kyakykyawakamar baturiya
gashin kanta har baya amma duk dama
antufkemata da ribon amma kuma sunnan
kauyawagareta gata kumadaa kauye. Ya ce a
ransa'' wata kila dai asalin garinsune babban
mutum din amma daga birni take, can yanisa
yace''babu komai,'' ya jawo wani littafin rasitai ya
budeyace dasafiyanu'' sai ku bibbiya kudaden in
baku rasitai dasauri don yanxu lokaacin assembly
ne, don taje ta shiga cikindalibai ayida ita. Vice
principal ya lissafawa safiyanu yawankudade
dazai kawo safiyanu ya dauko ya bashi, shi
kumayana rubuta rasitai har ya biya kudin komai
ya ce '' sannan yafadi sunandakin da zata je,
sannan zata je j.s.s. 1A ajin malamhaisamsunan
ajin, yanzu ka kaita hall ayi assembly da
ita,kayanta kuma a barsu a nan bakin staff room
ana tashi tazozamu samaigadi da prefect din
dakin suje ta bata gado.Safiyanu ya ce''to'' yayi
godiya suka fito yana sake yiwa hannebayani
akan abinda vice principal ya ce, yana kuma
karalallashinta ganinyadda nan da nan ta canja
hankalinta yayimummunan tashidaga shigar su
ofishin vice principal duk kwalla tacika mata ido
saura kiris ta fashe da kuka. Yace mata'' kar
kiyikuka nanmakaranta ce karatu kawai za.a koya
miki babumai zaginkiballe duka kinji. Gashi ajin
malam haisam za,a kai kidon haka baki da
matsala zai kula dake''suna tsaye a bakin
baranda yana yi mata nasihasaiga viceprincipal
ya fito daga ofishinsa zai tafi hall
wajenassemblyyace'' ah har yanzu bata tafi
assembly ba ai gara kuyi sallamata tafi,'' safiyanu
yace '' aima shikenan mun gamadaman halldin
zan tambaya don bamu ganshi ba,'' viceprincipal
t harcikin hall din yashige da hanne a lokacin
principal tana bayanihall din yayi tsit kowa yana
sauraro. Amma dagashigowarhanne da vice
principal sai kowa hankalinsa yakoma ga
kallonhanne. Hanne ta zama yarinya ''yar dagwas
'yar karama maikyan gaske akwai dubbunan
dalibai a makarantardaga jahohidaban daban
amma babu mai kyawun hanne watokamarwata
tauraruwa ce mai haske a cikin taurari. Sai sheki
take danfarar fatarta hanci har baka, dan
karamin baki,gazar gazargashin gira dana ido
fatar jikinta luwai luwai irintayan hutuamma ita
dai daga innallahi. Ga ido dara dara bata da
kibakuma bata cika tsaho sosai ba gata dirarriya
duk dadaikarama ce masassakin budurci bai fara
sassakataba. Wasukitso ne yiri yiri aka yarfa mata
kamar bada hannu aka yisuba. Hanne tayi kyau
kwarai da gaske a cikinkayanmakarantar nan ga
'yar jakar litattafanta a baya.Babu wandazai kalli
hanne bai sake juyowa ya kalli halittar ubangiji
ba.Dalibai manyansu da yaransu babu wacce
bata cedama nicewannan ba ko kuma ace 'yata
ce a ransu ba. Hattahaisamwanda ke tsaye a
bakin kofa bai gane hanne ba. Suka zo sukawuce
ta gabansa ya bita da kallo sai dai a
zuciyarsayaketambayar kansa da kansa ina nasan
wannanyarinyar?Tabbasa na santa a wani waje,
sai daga baya zuciya ta bashiamsar cewa wannan
itace hanne habu kenan. Yayimatukarmamaki
ganin yadda hanne ta koma haka a
kwanabiyu,hanne ta tsorata ta kuma rikirkice
ganin dubbunnan idanuwacaa a kanta, ta tsaya
cak, ta kasa tafiya tana shirinfashewa dakuka.Vice
principal yayi kiran wata prefect dake tsaye agefe
yace tazo ta kaita layin 'yan j,s,s 1A. Tazo ta
kamahannun hanne takaita layin ajinsu ana ci
gaba da assembly kamaryadda sukasaba. Bayan
principal ta gama jawabinta, viceprincipal ma ya
fadi albarkacin bakinsa sai aka nemi
sauranmalamai sucewani abu akan dokar
makaranta. Bayan sun gamaaka yinatsonal pledge
kowa ya kama gabansa, ya nufiajinsu. Hanne ta
tsaya cak a inda take tsaye tana kallon
dalibaikowa yanatafiya ajinsa ta rasa ina zata
nufa. Haisam ya matsokusa da itaya ce'' hanne
yaya kika tsaya bakya gani kowa yanufi ajinsu ke
kika tsaya idan baki sani ba, ba sai ki tambaya
ba.To nanmakaranta ce kowa ta kansa yake, gara
ki rinkatambayar dukabinda baki sani ba, muje in
nuna miki ajinnaku, hanne tace'' to'' ta bishi suka
doshi bangaren da ajujuwa sukeyaci gaba dayi
mata nasihohi akan kada ta sake ta
zamawawuya, idan bahaka ba sai sauran dalibai
su raina mata wayo tazama duk abunda bata
sani ba ta tambaya musamman idanmalamiyana
darasi idan bata ganeba tayi masa
tambaya.Hanne nasauraro da alama kuma
nasihohin suna shigarta.Haisam ya kalleta yayi
dariya ya ce'' hanne ince kin
zamacikakkiyardaliba babu wannan damarar?
Hanne ta kyalkyaleda dariyahaisam yace'' to
tunda kin zama yar birni 'yar bokomai aji to
yanzu komai naki yzai koma na aji, kin san
abundanake nufi?Hanne tace ''a'a'' yace to
sunanki zai tashi dagaHANNE HABUIMAMU ZAI
KOMA HANNAH ABUBAKAR IMAM.kowaya
tambayeki sunanki kice..'' kafin ya fada cikin
murnada farinciki tace '' hannah abubakar imam''
haisam yatuntsire dadariya yace harma kin rike
sunan kenan? Hannetace eh hannah yafi dadi
Allah'' a daidai wannan lokacisuka haubarandar
ajin haisam ya wuce gaba ya shiga ajinhannah
nabiye dashi a bayasuka shiga dukkan daliban
ajin suka mike dongirmama malaminsu suka
hada baki dukkansu''good morning sir'' haisam
yayi murmushi yace''morning how are you ? Suka
sake hada bakisuka ce'' we are fine sir'' yace
thank you sit down ''kowacce ta zauna akan
kujerarta. Haisam ya jawo hannah gaban aji
yace'' ga wata sabuwar dalibakun samu'' rauda
itace monita ta mike tace'' lah ,what is your
name ? Hannah ta daga ido tanakallon haisam''
ya harareta ma'ana ta bada amsa ,hannah tace''
my name is hannah abubakar imam''kama yadda
haisam yace ta dinga fada. Nusaiba wacce itace
mataimakiyan monita tace'' emh, nicename you
are welcome hannah'' haisam yayimurmushi ya
ce'' kun fara iyayin naku ko ? To mazaku saka
mata kujerarta a tsakiyar taku a gabakuma kunga
itama yar kucila ce kamar ku'' cikinsauri rauda
taje bayan aji ta dauko kujera ta kawo ta koma ta
dauko tebur yazo ta dasa a tsakiyar su ajere.
Dake duk ajin su duka ukun sune kanananajin
sunfi kowa kankanta kasancewar akwaidingin
dingin din yammata a ajin musammankabilun na
wata sai ka rantse uwa ce amma yar ajidaya ce
farin ciki ya lullube hannah da haisam
musamman ma haisam yaga hannah ta samu
shigaa wajen nusaiba da rauda wadanda su suka
fi dukyan ajin kokari dan rauda a america tayi
karatunnusery da primary dinta don haka tana
bala'inkokari ga turanci daya kama bakinta hausa
matana kokarin ta subuce mata.Kuma auwal
abokin haisam ne na kuttan kaibabanta alhaji
shitu abokin baban haisam nesannan ramla
yayarta ita haisam zai aura don hakanema aka
kawo rauda makarantar saboda haisamyana nan
tazo akayi mata jarabawa taci shikenanaka
dauketa, don haka nema take kiransa da yaya
haisam sabanin uncle haisam da sauran
dalibaisuke kiransa. Nusaiba ma wata
tsadaddiyarmakaranta ta gama a abuja, ita yanzu
hakaiyayenta suna abuja karatu ya kawota nan
ammasu haifaffun garin gwambe ne fulani, rauda
danusaiba sun zama kawaye tun ranan da suka
hadu ranar da aka kawosu makaranta, ajinsu
daya sukakuma ci sa.a dakinsu daya don haka ga
gadonrauda ga na nusaiba kuma sun hada
kayanakwatinsu. Haisam yace monita da
mataimakiyartaku biyoni waje ina da magana
daku rauda danusaiba suka mike suka bi haisam
wajen ajin. Hannah na zaune babu abunda take
sai kallonginin ajin da dalibai daya bayan daya
taga kowaccesanye da uniform dinta tsaf tsaf,
fararen takalmakambas da fararen safa kan
kowacce kitso ne tar.Hannah tace a ranta ashe da
na sha kunya da aceranar da baba ya kawo ni a
haka na shigo ajin nan da na fita daban, kai
wannan malami ya taimakeniallah yayi masa
albarka. Taci gaba da kallon gininajin da irin zane
zane da akayi a takarda duk anlillika a jikin bango
ga fankoki a jikin silin sunatafitar da sansanyar
iska suka , ginin bulo hannah tafada a fili ba tare
data san a baiyane ta fada ba, bayan fitarsu
haisam a bayan ajin suka tsaya yakalli rauda ya
juya ya kalli nusaiba yace raudanusaiba su duka
suka amsa yaci gaba da cewa gahannah nan ,
kamar rauda kike kawar nusaiba tohannah ta
zama kawarki itama, sannan kamaryadda ke
nusaiba kike kawar kawar rauda to ina son
hannah ta zama kawarki duk da ku biyudakinku
daya to hannah ma yar dakin kuce dakesafiyanu
ya fada masa sunan dakin hannah yacedon haka
ku uku dakinku daya ajinku daya. Kamaryadda a
ko ina kuna tare a hall ne, a ajine a daki neto
hannah ma ta zamana kuna tare itama kanwata
ce kunji ko ? Su dukka suka amsa. Nusaiba
tace''uncle haisam ko baka ce mu zama kawaye
badaman zamu zama tana burgemu'' haisam
yayidariya ya juya ya kalli rauda yace'' kanwata
ke bakice komai ba ke bata burgeki ? Rauda ta
tabe bakitace'' yaya haisam rannan fa kace nice
kadai kanwarka a makarantar nan yanzu kuma
kace itace'' haisam ya kyalkyale da dariya ya dafa
kantayace!! Rauda kenan, ai har yanzu kina nan
amatsayinki na kanwata itama hannah yar uwata
cekibga dole kanwatace, nusaiba ma kanwata ce
donhaka karki damu. Gata nan duk abunda bata
sani ba akan karatu ki koya mata. Haka kuma
maganada turanci ku rika tunasar da ita koda ta
manta tayihausa karku rubuta sunanta a masu
yin hausa sai ahankali zata saba itama ta rinka
yin turanci sosai.Haka a daki idan bata san yadda
zata yi amfani dawani abu ba kamar man gashi
in zata shafa a jiki ku nuna mata mata na gashi
ne ba ku ringa yi matadariya ba kuna gayawa
kawayenku kunji ?Musamman ke rauda kinga
rose suna yawan kawomun kararki wai kina yi
musu tsawa kar in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login