Showing 12001 words to 15000 words out of 31410 words

Chapter 5 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

148

suka je gida su
dinga taya iyayensu aikibanda yawo a gari gidan
kawaye balle kuma masu samari. Mataimakin
principal ma ya tofa albarkacinbakinsa. Ya jawa
daliban kunne akan su zamamasu da.a da ladabi
da biyayya a duk inda suke.Saura malamai ma
suka yi musu nasihohi akan suyiamfani da
abunda principal ta fada musu damataimakinta.
Sai kuma daga karshe malami uku da suka zo
bautar kasa suka yiwa dalibanmakaranta sallama
akan in sun tafi sun tafi kenanba zasu dawo ba.
Malaman yan bautar kasar suneuncle haisa, rose
iliya da hassan bawa. Dalibaimasamman ma yara
sunji ba dadi saboda sun sabada malaman.
Musamman haisam saboda kirkinsa da wasa da
dariyarsa yasa kowacce daliba tahi tanasonsa.
Musamman daliban da take koyarwa
sunamatukar bakin ciki da rabuwa da
malaminsuwanda ya kware wajen koyar musu da
geography.Nanfa dalibai suka rode da surutu
wasu na kukawasu na fadin'' we miss you ! We
miss you so much!! Uncle haisam, we miss you
more, stay don'tgo please. A haka dai principal
da sauran malamaisuka fice suka umarci daliban
suma su tafi dukwacce aka zo dauka. Hannah da
nusaiba a bakinbarandar hall din wajen
jakunkunansu suka zauna.Nusaiba tace'' allah
yasa dady na tun jiya yaxo kano daga abuja. Ya
kwana a kano yau da safennan ya kamo janyar
kazaure. Kar ace yau zai tahodaga abuja gaskiya
sai yamma zai karaso kazaurewallahi murna nake
yi kaman za'a sani a aljannah.Dama ace ina rufe
idona na ganni a gida'' hannahtayi murmushin
karfin hali don babu walwala a zuciyarta dama
ace duk wanda son zuwa gida yadaga hannu sai
tafi kowa daga hannu dan ta zaunaa makaranta.
Nusaiba ta kallo hannah wacce tunsafe bata
murna. Musamman ma yanzu da taji ancehutun
kwana arba'in da biyu za'ayi sai ranta yasake
baci. Ga kuma babban tashin hankali haisam zai
tafi. Nusaiba ta kula hannah ko irin dan
dokintafiya gida bata yi. Sai surutu take ita kadai
hannahbata sauraron ta sai wani tunani take
daban.Nusaiba ta dan zungureta da gefen hanni
tace''waike hannah meke damunki ko murna
bakya yigida fa yau zamu'' hannah ta nisa
sannan ta sake yin murmushin karfin hali tace''
me kika gani ?Wallahi nima ina murna dama na
bude ido in gannia gida yanzu'' nusaiba tahi dadi
da wannangudunmawar hira da hannah ta fara
bata tace'' nikuma ina zuwa gida fruit salad zansa
ayi min in ciwallahi shi nake marmari ''Nusaiba ta
zabura tace'' meye makani,kwatantamin yadda
yake nima idan naje gida incea soyamin'' hannah
tace'' ai shi makani dafa shi akeyi. Ba kisan
gwaza ba ? Nusaiba tace'' gwaza!gwaza!! Menene
ma gwaza ? Oh cocoam zaki cemun. Kai allah ya
sawake inci gwaza sai kace wata yar kauye ?
Hannah tayi shiru don tasan ita yarkauye ce
kuma acan su gwaza abun marmari ne.Nusaiba
tace. A ina kuke samun gwaza ni banaganin ta
ma ko a kasuwan abuja'' hannah tace mumuna
samu'' uncle haisam ne ya tunkaro wajen dasuke
zaune , su duka suka mimmike tsaye don
girmamawa gami da cewa , good morning sir''
yace'' morning hannah, good morning nusaiba.
Yauyammata sai gida naga nusaiba sai murna
kike yiko ? Nusaiba tace yaya haisam murna yau
nakelamar za'a sakani a aljanna. Haisam yayi
dariya yace '' hannah kefa, kema kina murna
kaman za a sakaki a aljannah ? Hannah tayi
murmushin karfinhali tace'' eh'' ina murna nima,
shigowar wata motakirar end of discussion ce ta
katse hirar da suketazo ta tsaya. Kafin mutumin
da yake ciki ya fitodaga motar nusaiba idris ta
daka tsalle mike dagudu ta nufi wajen motar nan
tana cewa babama oyoyo. Ya taho shima da
saurinsa ya rungume ta suduka murna suke yi.
Nusaiba ta ruko hannunmahaifinta ta nufo wajen
da malam haisam dahannah suke zaune su duka
suka mike dongirmamawa. Nusaiba tace, ga class
master mu danake baku labarinsa a wasika nace
shi yake kula damu uncle haisam sunansa. Alh
idris yayi dariyayace. Oh uncle haisam duk
wasikun nusaiba sai tarubuto mana labarinka da
kai da kawayentahannah da rauda. Haisam yayi
murmushi yace allahsarki ai ga kawarta hannah ,
hannah ta duka tagaishe shi ya mikawa haisam
hannu suka gaisa. Nusaiba tace'' baba daga
wannan hutun unclehaisam ba zai dawo ba.
Alhaji idris ya ce da haisam''ai dama teaching
practice kake yi ananmakarantar ? Haisam yace
''eh bautar kasa(N.Y.S.C)nayi kuma mun gama.
Alhaji idris yace badadi yara sun saba da kai
gashi zaka tafi, mun gode allah ya saka da alheri.
Haisam ya ce '' ba komai aikannena ne.nusaiba
ta ciro takarda daga jakarta dabiro ta mikawa
haisam tace ya rubuta mata lambarwayar sa. Ya
karba ya rubuta mata. Ta karba tamikawa
hannah tace '' hannah rubuta min lambarwayar
ki a kasan ta uncle haisam'' hannah tayi turus ita
bata taba taba wayar bama balle ta sanyadda
ake amfani da ita har ta san wata lamba.Haisam
yayi sauri ya ce a'a ke rubuta mata taki
zatakiraki. Nusaiba ta rubuta lambar wayarta ta
mikawahannah, hannah ta karba. Daga karshe
hannah takamawa nusaiba jakarta suka nufi
wajen mota. Alhaji idris ya bude but haisam ya
kama ya saka.Nusaiba ta rungume hannah su
duka sunahawaye. Nusaiba tace'' kina zuwa gida
ki kirani awaya kuma kullum zamu dinga waya
munagaisawa. Alhaji idris ya dafa kansu ya ce ''
ku dainakuka hutu za kuje yana karewa zaku
dawo ai baku rabu ba gaba daya. Nusaiba da
mahaifinta sukashiga mita ya ja suka tafi hannah
da haisam sunadaga musu hannu har suka kure
sannan sukakoma inda suke zaune da suka
zauna. Sai gacincirindon dalibai suka zo suka
zagaye haisamkowacce na baiyana rashin jin
dadinta game da barin makarantar da zai yi,
haisam ya baiyana musucewa in allah ya yarda
duk term zai dinga zuwayana ganin su. A haka
suka dai suka dinga wasada dariya kamar yadda
suka saba rauda ma takaraso wajen ta zauna a
hirar da ita basu lura dasanda motar gidan su ta
shigo ba, sai kawai suka hango auwal wan rauda
ya tinkaro su. Rauda tamike da gudu taje ta
rungume yayanta, yanakarasowa ya mikawa
haisam hannu suka kashe yace'' malam ,malam
haka kake sa daliban naka agaba kuna rera hira ?
Haisam yayi murmushi ya ce''bankwana muke yi
kasan daga yau shikenan bazan dawo ba'' auwal
ya ce wai har kun gamabautar kasar haisam yace
''kwarai kuwa ba famanake da kai ba kazo ka
dinga yi mana dan kwanabiyu ma kaki to gashi
nima allah yayi min komawagida gaba daya mun
zama daya. Ya ce'' lallaishekara kwana ce kamar
yaune muka kawoka kamar kayi kuka baka san
kauye. Haisam yatuntsire da dariya ya ce'' gashi
kuwa na saba yanzuhar bana jin dadi zamu rabu
da dalibaina, nan daiauwal ya sami kujera ya
zauna shima dake gwaninwasa da dariya ne da
mutane ya dinga hira dadaliban nan yana
zolayarsu dakyar haisam ya banbaro shi daga
wajen daliban nan, auwal dazolaya ya sami yara
yana ta zolayarsu musammanhannah, duk da ma
baisan yadda take da haisamba yana tayi mata
wasa wai ita balarabiya ce takoya masa yarensu
yana tambayarta me ake cewayaro da larabci?
Tayi dariya tace ban sani va shi a tunaninsa taki
fada be kawai baisan ita babalarabiya ba ce.
Auwal ya mike ya ce da daliban to ragowar
kwakida kanzo na tafi tunda kun zama yan
kwantai ba'azo daukar ku ba. Ya kallo hannah ya
ce'' ke yaryemen jirgin kasarku baizo ba kema
mun tafi munbarki sai kinfi kowa kwantai saboda
ke ba yar kasaba ce. Hannah ta kyalkyale da
dariya sauran dalibai suka ce'' mu bama cin
kwaki bamu san ma yaddakanzo yake ba
allahnya sawake kuma mumayanxun nan za'a zo
daukar mu. Haka wasa dadariya aka dinga yi da
auwal da su hannah haisamna gefe yana kallon
yana dariya yace'' da hannahkema dauko jakarki
kizo mu tafi na riga na muki signing ke da rauda
mu tafi kawai. Auwal ya ce dahannah ''ah ke da
nace sai kinfi kowa kwantai ashetare zamu tafi
dake ko a filin jirgi zamu ajiyeki ne akano ?
hannah tayi dariya tace ''oho ni dai banyikwantai
ba'' haisam ya dauki jakar rayda cimaksaboda
nauyi ba zata iya dauka va ya kai ya saka a
mota.Auwal ya ce da hannah'' kawo kema in taya
kitunda vaki da karfi don nasan a garinku bakwa
cintuwo sai yar gurasa da zuma ko ? Hannah
daimurna take kawai da ba gida za'a kaita ba
kanozasu wuce da yaya haisam. Rauda da
hannah sukaje suka shiga mota a gidan baya
suka zauna, yaya haisam da auwal suma suka
shiga motar yayahaisam ne yake yukawa auwal
yana zaune a gefe,suka nufi get din fita. Dalibai
na daga musu hannuhar suka tafi.rabon rauda
da ta yiwa hannah magana tunjiya yau ko
magana bata yi mata ba saboda tsabankishi da
ita wai saboda yaya haisam yana ji da itaitama
yace kanwarsa ce, yanzu taga yan uwantakarta
tabbata gata a motarsu yaya haisam zai wuce
daita gidansu ma. Ta kalli hannah ta yamutse
fuska tace'' kema kano zamu dake kenan, daman
a kanokike baki taba gaya mana garinku ba !
Hannah tayishiru ta rasa amsar da zata bata.
Haisam ya ce ''ehrauda da ita zamu kano a
gidanku ma zata zaunakinga sai ku dinga karatu
tare ko ? Rauda tace'' saikace basu da da gida ai
a gidansu a nemeta. Cikin rada hannah tace''
babu wanda zai nemeni, ni bazani gida ba. Ta
mudubi haisam na kallonta yayimurmushi kawai.
Haisam ya nufi cikin garinkazaure auwal ya dubi
haisam yace a'a haisam inazamuje mu da zamu
kama hanyar kano. Haisam yace'' cikin garin zani
akwai wacce zamu dauko. Basu tsaya a ko ina ba
sai kofar gidan uwar biyu damana shirye take
suna aika yaro yayi sallama ya ce injimalam
haisam sai ta fito da gyalanta daman a shiryetake
tsaf ta fito. Bayan sun gaisa haisam yace da
surauda su matsa mata ta zauna, suka matsa ta
shigata zauna a kujera baya sannan suka gaisheta
dukkaninsu. Haisam yaja mota suka tafi bai tsaya
ako ina ba sai a babbar tashar kazaure ya tsaya
yajuya ya kalli uwar biyu da hannah yace'' to
ananzaku hau mota ko ? Uwar biyu tace'' eh
akwai motahar babban mutum a nan'' uwar biyu
ta yunkurazata fita ta juya ta kalli hannah wacce
bata da niyyar fita bata ma san da ita za'a fita ba
a tunaninta uwarbiyu ce kawai zata sauka ita
kuma su kara gaba sutafi kano sai taji uwar biyu
tace'' to hannatu fito mutafi ko ? Cikin rudani
hannah ta juya ta kalli haisamdon jin abinda
zaice sai ya rasa me zai ce matakawai ya
sunkuyar da kansa kasa ya kasa magana, ya fito
daga motar ya bude but ya dauko jakarhannah.
Nan da nan kwandastocin mota suka zosuna
cewa'' babura zaku ne. Ko daura ? Uwar
biyu''motar babura zamu hau sai mu sauka a
babbanmutum. Haisam ya mikawa kwandasata
da zasubabbam mutum jakar hannah, uwar biyu
tace '' af har yanxu hannah bata fito daga motar
bane ?Haisam ya leka cikin motar ya tsaya yana
kallonhannah baice mata komai ba, ta sunkuyar
da kaicikin sanyi jiki ta jawo jakar litattafanta
(schoolbag)ta rataya ta juyo ta kalli rauda ta kalli
auwaltace'' na tafi sai anjimanku'' rauda tace au
har dake zaku shiga motar haya kin fasa zuwa
kanon ne ?Hannah ta gyada kai kawai sannan ta
fito. Yayaauwal yana yi mata wasa yana cewa, af
ashe yarkauye ce ma, motar babura zaku hau
ko? Hannahta fita ba tare da ta bashi amsa ba,.
Haisam dahannah suma suka nufi cikin tasha
dama uwar biyu da kwandasatan daya dauki
jakar sun shiga tasha.Motar bus ce wacce baifi
mutane hudu ba ta cikaba. Uwar biyu ta zauna a
kujerar baya aka sakajakar hannah a but hannah
ma taje kusa da uwarbiyu ta zauna, jikinya sanyi
kalau kamar marar lakahankalinta a tashe yake
kamar wacce za'a kaita lahira ba gidansu ba.
Haisam ya zaga ta wundon dauwar biyu ke zaune
ya danko kudi ya mika mata yace' ga wannan
kuyi kudin mota dan karku mastu kibiya kudin
kujerun bayan a barku ku kadai sannanki fito ki
shiga aishalle super market kafin mota tacika ki
siyowa hannah sabulun wanka, wanki man
shafawa dana gashi. Biskit da alewoyi ta yiwa
yangidansu tsaraba.?ya sake deno wasu kudi
masuyawa yace wannan kuma ki ajiye da zarar
hutu yakare ya rage kwana biyu kije ki taho da
ita kikawota gidanki zanzo in kara yi mata siyayya
namayar da ita makaranta. A cikin kudin ki bawa
mahaifinta dan na kashewa ki gaya masa lallai
lallaihutun kwana arba'in da biyu aka basu da
zararhutu yana karewa zaki zo ki dauke ta inji ni
zakice.Ki san dai kalaman da zaki gaya masa na
kwantarda hankali kada ya hanata dawowa
kinsantsofaffin nan namu, kice ke uwar dakin
tace a wajenki take a makaranta na hadaku, kice
inagaisheshi da kyau. Uwar biyu tayi godaya
tashialbarka kamar ita aka bawa kudin ko jikarta.
Yadauko wasu kudin ya mikawa uwar biyu yace''
kisayawa hannah sarka da dan kunne na jiyal
maikyau ki bata'' uwar biyu tace'' kai kudin ai
yayi yawa malam haisam duk a cikin wannan ya
isa nayimata siyayyar'' ya ce ''ba komai na gode
uwar biyuallah ya kiyaye hanya'' tace amin
malam mune dagodiya'' ya zagayo jikin wundon
da hannah kezaune tayi tagumi ta langwabar da
kai a jikinwundon mota jawaye ne yake sulalowa
daga idanuwanta daya bayan daya. Haisam ya
kalletayayin da yaji kamar zuciyarsa zata fashe
dontsananin tausayinta , yayi karfin hali yace''
hannahkukan meye kike don kawai anyi hutu zaki
tafigida ? Ai hutu na karewa uwar biyu zata je
tadaukoki kinji ko ? Zan zo inyi miki siyayya na
mayar dake makaranta, yanxu idan kika je gida
kinakuka baba zaice wahala kike sha a
makarantar yace ba zaki dawo ba. Amma ki
nunawa babamakarantar da dadi ga ladabi da
biyayyar da akekoya muku ga karatu da abinci a
wadace shi kansazaice ki dawo, kinji ko ? Hannah
ta gyada kai ta fara share hawayen idonta. Yace
gaba da cewa'' kiyihakuri da abun da iya abu
take yi miki hutu nakarewa uwar biyu zata zo ta
daukeki ta kawo kimakaranta. Sannan kullum ki
rika zuwamakarantar islamiyya kina kuma duba
litattafankina makarantar boko don karki manta
karatu kinji. Allah ya kiyaye hanya hannah. Ya
juya ya tafi,muryarta yaji ta rushe da kuka, ya
juyo ya tsaya cakyana kallonta sai ya rasa me ma
zai ce mata sai yajuya ya tafi da sauri. Yana mai
tsananin damuwa datakaici.kukan zuci kawai
yake. Ba tare da ya cewa suauwal komai ba, ya
ja mota ya fara tukawa. Canrauda ta nisa tace''
yaya haisam daman hannahfulanin daura ne, ko
ba daura zasu ba ? Haisam yayidan murmushi
kawai. Auwal yace'' haisam ka cikashige shige ina
ka samu wannan buzuwar har da kakarta kuma?
Haisam yacce'' wai shige shige ni dakai za'a san
me shige shige naga daga zuwa harkasan su
naja'at suleman ko banga sanda takebaka
adiredhinta ba balle ni dana shekara
amakarantar'' auwal yace to ya isa ga
wannanzabiyar a baya ta bude kunnuwa tana
daukar rahoto'' haka dai har suka isa kano jifa
jifa haisamyake magana babu abunda yake
tunawa sai halinda hannah zata kasance a
gidansu. Zuciyarsa cikeda tausayinta kulle kullen
yaya zaiyi yaci gaba dataimakonta yake gashi
kuma ya bar makarantar,har suka isa kano . A
nasarawa g.r,a suleman cresent gidan su haisam
yake, suka shiga cikinkatafaren get din gidan .
Bayan auwal da rauda sunshiga sun gaisa da
hajiyar haisam sai suka yi mususallama suka nufi
suma nasu gidan da yake lamidocresent basu da
nisa sosai. Alhaji shitu mukhtar sunan mahaifinsu
rauda,mahaifiyarsu kuma hajiya jamila sunanta
alh. Shitumuktar haifafen garin kano ne, dan
unguwankabara ne tare sukayi firamare da
sakandire damahaifin haisam abokaine tun suna
yara. Haj.Jamila kuwa mahaifiyar su rauda
mutumiyar chadi ce ya aureta. Allah ya
albarkacesu da 'ya'ya uku,yaya auwal shine
wanda ya kammala karatunlikitansa a america
yanzu cikakken likita ne. Sai antiramla wanda ta
gama sakandirenta a wannanshekaran tana jiran
sakamakon jarabawarta tawuce jami'a bayan an
cancara bikinta da angonta haisam, saita fara
karatu a gidanta, sai yar autarsurauda wacce
yanxu take ajin farko a sakandire.Tsantsar yan
boko ne yaya uku sun ishesurayuwar duniya suna
basu cikakkiyar kulawa datsantsarso da kauna.
Allaha yayi musu arziki maiyawa don haka a daula
suke ta ko ina hutu, ba su fi shekara biyu da
dawowa nijeriya ba kasancewaralh. Shitu muktar
yana aiki a embassy, shinejakadan nigeria a
america {ambassador} don hakaduk a can suka yi
karatunsu har mahaifiyarsu haj.Jamila acan tayi
digirinta.al'amarin hannah da uwar biyu kuwa,
bayan tafiyar haisam uwar biyu tayi sauri ta
sauka daga motartaje ta yiwa hannah siyayyar
kamar yadda malamhaisam ya umarceta da tayi.
Ta dawo cikin mota dasauri ta iske motar dai
bata cikaba , bayan mota tacika suka kama
hanyar tafiya. A hanya uwar biyu taci gaba da
lallashin hannah tana bata baki dakyar tayi shiru
da kukan da take yi. Ta dade daman tanaso taji
labarin hannah da dangantakarta da
malamhaisam, saboda tsananin kulawar data ga
yana yimata, cikin wayo da dubara irin na manya
uwarbiyu ta dinga bugun cikin hannah tana son
tajilabarina. Abunka da yarinya kuma mai neman
agaji da take yi ta ko ina hannah ta fayya cewa
uwarbiyu komai daga biri har wutsiya. Uwar biyu
tatausaya hannah ta sake jinjinawa malam
haisambisa jihadin da yayi saboda allah na
taimakonhannah. A garin babban mutum suka
sauka aka saukemusu jakarsu . Tun daga sauka
hannah ta farafaduwar gaba tazo garin da bawa
ya fita jin dadi.Uwar biyu ta lura da hakan sai
tayi ta bata baki tanakwantar mata da hankalinta.
Kawayen hannahmaza da mata yan garin suka
baibayeta suna kallonta wasu kuma suna
shishshige mata harrububin yi mata magana su
ke. Masu daukar matajaka suka dauka suka
dunguma zuwa gidan suhannah. Samarin garin
sai kallon hannah suke ganisuke kamar ba
hannar da bace da suka sani. Tayijawur da ita
tsaf tsaf. Babban mamakin kambas din da ta
dana a kafarta suke kallo wasu na cewatakalmin
yan ball tasa, wasu na cewa na faretinsojoji ne.
Mamaki ya ishesu yadda akayi hannah tazama
haka kamar baturiya a wata guda nan danan,
kyau na zuba duka cikar garin da
batsewarsababu mai kyawun hanne da
gogewarta. Nanfa samari kowa ya hau cewa
gaskiya tawace wannan.Wancan na cewa na
rigaka. Kawayenta da yawasun kudiri niyyar suma
sai sun tuburewa iyayensuan kaisu makarantar
kwana irin ta hannah donsuma su goge suyi
jawur haka. Kafin hanne takarasa gida labari ya
kai cikin gidansu ance ga hanne nan zuwa ta
zama fara kal kamar baturiya itada wata
tsohuwa. Farin ciki ya rufe mahaifinta yaiwuf ya
fito kofar gida ya tsaya yana murna yanajiran
isowar hannensa(yar boko). Budar bakin iyaabu
kuwa sai cewa tayi watakila ciki aka yi mata
amakarantar tayi haske don hanne ba fara ba ce
kal. Surutai dai na hassada da bakin ciki barkatai
tadinga yi.Hanne na doso kofar gida ta hango
mahaifintasai su duka murna ta lullubesu.
Hannah ta karisa dasauri taje ta rungumeshi
kamar yadda taga sunusaiba suna yima
mahaifansu sai hawaye suke itada mahaifinta. Iya
abu a tsakar gida ita da yayantababu wanda ya
amsawa uwar biyu sallamarta da tayi, sai malam
habu yace shigo kawai ai ba zasuamsa muki ba''
ya shiga daki ya dauko tabarma dasauri ya
shimafida mata ta zauna a sanyaye cike
damamaki irin wannan tsana da ake yiwa wannan
yarkaramar yarinya wanda ma yake sonta an
tsaneshi.Hannah taje gaban iya abu ta durkusa ta
gaisheta ko ta amsa ta juya ta gaishe da
yayyenta 'ya'yan iyaabu kenan suma suka kwata
abunda mahaifiyarsutayi. uwar biyu ta rike baki
tace ''oh ikon allah bayinallah me yayi zafi
hannah nawa take ? Don allahkuyi mata yar
fara'a mana ko taji dan sanyi yanzuko dokinta
bakwa yi kusan wata biyu bata nan, aidarajar
sabon idon ni bakuwa kwa raga mata harin tafi''
suka yo ca akan uwar biyu uwar biyu nayi yayan
nayi, ta mike tsaye ta juya ta kalli hannahwacce
ta kame a jikin katanga tana makyarkyatahawaye
ne ke zuba daga idanuwanta tasan yauduka da
zagi allah ne kadai yasan iyakarsa da zatasha.
Hawaye ya kecewa uwar biyu tace'' hannah
yihakuri wuya bata kisa ko anki ko anso gidan
ubanki ne duk inda kika je sai kinzo gidan
dole,''iya abu tace'' gidan uban nata ya gagareta
zamaidan naso ba. Malam habu shima yayi
jugum yakasa magana tashin hankali ya isheshi
sabodayana tausayin hannah yasan wahala zasu
ci gabada linka mata ganin allah ya rufa mata
asiri tayi kyau, uwar biyu ta fita malam habu ya
bita hannahma ta bisu da sauri, uwar biyu tasa
gefen gyale tashare hawaye tace'' allah yana nan,
malam ni yaraikece. Malam haisam malamin daya
karbeta ahannunka din nan. Malam habu ya
katseta yace ''ehna gane kiyi mana godiya da
kyau da kyau na gode madalla. Tasa hannu a dan
tofi ta dauko kudimai dan afki ta bawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login