Showing 21001 words to 24000 words out of 31410 words

Chapter 8 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

150

din
me da zaki yi min wulakanci? Sahabi ya tashiya
karbi reshen nan ya zazzabga mata sau biyar
dakarfi kuwa ya ce'' tashi saura ki ki zuwa nan
gabaidan muka aika kiranki prep'' tana tafe tana
rusakuka ta nufi ajinsu. Sahabi yana cewa '' bari
mugazata zo da prep din daren kuwa? Idan bata
zo ba wallahi doble din wannan zamu yi mata.
Haisamyayi tsaki ya mike ya nufi ajinsu hannah.
Zuciyarsacike da tsananin bakin ciki da tausayin
hannah.Yaje ajin ya tambaya aka ce hannah bata
shigo ba.Nan da nan hankalinsa ya sake tashi
yayi waje dasauri yana dube duben ko daji ta tafi
ta zauna tana kuka, yazo wucewa ta ajijuwan yan
aji shida yajinishi kamar wata tana tsallen kwado
ya leka tawundo da sauri yaga ashe a s.s.3a sun
taru kusandukkaninsu suna azabtar da hannah ta
jike dagumi sharkab saboda gwale gwale da
duka.Juwairiyya ce rike da dorina a hannunta
tana biye da hannah tana tsallen kwado tana
fyauda mata. Afusace haisam ya daka musu
tsawa duk sukawaigo wasu suka ruga ajijuwansu
suka zazzauna.Ya hango wani masinja ya kirashi
yace yaje daji yakaryo masa manya manyan
reshen bishiyar mainaya kawo masa. Ya zagaya
cikin ajijuwa ya ce dukkaninsu su firfito waje bai
rage kowa ba duks.s.3 din, sun dauka abin wasa
ne suna tafe sunarangwada suna tauna cingam,
juwairiya kenansuka firfito waje daga ajijuwan ya
ce'' su fara tsallenkwado suma, yaje cikin ajin ya
tarar hannahsharkab tayi gumi ga sawun bulala
nan duk jikinta lambar. Yasa hannu ya tasheta
tsaye yace ta daureta tafi daki ta kwanta. Tana
tafe tana layi tana rikebango ta nufi hostel.suna
tsallen kwadon a duk yadda suka gadama a
zatonsu zaice su koma aji su zauna sai
sukahango masinja dauke da himilin bulalai kai
kacejakuna za'a daka tafka tafka dasu. A fusace
haisamya karbi bulala suna tsallen kwadon yana
binsu dulwacce ta fadi kota tsaya a baya yana
tafka mata wani dogon waje ya nuna ya ce har
can zasu kaikuma sai su huyo. Haka suka dinga yi
suje su juyohar sai da ya tabbatar kowacce ta
jigata hawayenma ya kasa fitowa sannan ya ce su
biyo layikowacce ta kwanta flate sannan ya
shashsharbamata reshen nan sau gima sha biyu.
Bayan jikinsu yayi kaca kaca ya farfashe kuka
wiwi dankwalayensu a hannu ga kafa ta sage
babu damartafiya. Juwairiyya tafi kowa shan
wuya duka yayimata kamar allah ya ne ya aiko
shi ko kirgawa mabaya yi daa bulalai suka
karkarye yasa kafa yadinga ball da ita daman
yana ciki da ita. Kuka wiwi suke suna bashi
hakuri daga yau baza su sake ba.Sannan haisam
ya gyalesu anan a kwance wasu adurkushe.
Tunda haisam yazo makarantar nan baitaba zagin
wata ba balle duka yau sai ga haisam yacanja
fuskarsa babu digon rahama murtik da itakamar
zai kashesu haka yayi musu ligi ligi dukkan da
babu malamin daya taba irinsa a makarantar
kodispline master baya yin irin wannan dukan.
Labariya kai gidan principal , agigice ta fito ta
taho a bakinofishinta ta gamu da haisam. Ta
dube shi sai taga yacanja gaba daya sai taji ta
shiga tsoronsa tayi masamagana. Can
tace''haisam wannw irin duka kayiwa s.s.3 yau
me suka yi maka haka? Ya juyo a fusaceya ce''ki
tambayi kanki da kanki daman n fadarannan
tunda baza ki iya daukar mayaki ba akanabunda
su juwairiyya suka yiwa hannah to ni nadau
fansa , kuma zan iya tin haka akan kowa
dukwanda yake marmarin takurawa hannah a
makarantar na'' principal ta rike baki kawai
tanakallon haisam , ya wuce ya barta anan tsaye
ya nufigidansa. Yana jiyo malaman da suke
zazzaune awajen suna cewa'' ai kuwa yarinyar
nan sai zamanmakarantar nan ya gagareta don
sai mun zane ta,itama'' nan dai principal ta hau
fadace fadace tana cewa'' dole ne na kira
meeting da manyan yanfederal akan abun da
haisam yake yi min amakaranta. magaruba tayi
uncle yusuf da uncle sahabi sukanufo gidajensu
ta jikin gidan haisam suka zowucewa yana jin
abunda suke fada wai da prep dindare zasu kira
hannah suyi mata dukan tsiya .Shima haisam sin
yaji in da dadi. A haka suka rabukowanne ya nufi
gidansa. Haisam na idar da sallar magariba yayi
shigar wata yar riga mai gajerenhannu
damammiya(body hook) ya dora wata suitaka ya
fita ya nufi gidan sahabi. Ya kwankwasakofa,
sahabi yazo ya bude fuskar haisam ce ya
ganimurtik ta bashi tsoro. Yaja da baya da sauri.
Haisamyasa hannu biyu da karfi ya angaza shi ya
tafi taga taga ya fada kan kujerar dake falon.
Haisam yashigo cikin falon ya mayar da kofa ya
datse. Sahabiyayi tsuru tsuru a zaune haisam ya
karaso indayake zaune yasa kafarsa daya ya taka
kujerar dasahabi ke zaune ya duko dai dai fuskar
sahabisuna kallon kallo . Sahabi ya yatsune fuska
ya ce''meye haka haisam lafiya ko ka zama dan
taadda ne kazo har gidana ka angajeni'' ya
yunkurazai tashi taji haisam ya turashi karshen
kujerawannan karon hannu yasa ya danki wuyan
sahabi.Sai ido kuru kuru an shakeshi kai kace
mujiya ce tafada rami. Haisam yasa hannu a
aljihu ya ciro wata karamar wuka ta bude ta tana
walkiya tasansanawa sahabi a hancinsa ya ce ''
ka kula daabun fa nake so na fada maka idan ka
kiyaye kakubuta idan kuwa kaki to kaiconka kaga
wannanwukan zan iya lumata a cikinka ko na
yanka ta awuyanka ka fadi ka mutu ko? To ina da
niyyar aikata haka in har ka kuskura ka sakw
takurawahannah a makarantar nan. Zan iya
kashe ko wayeba kai kadai ba don haka ka
kiyaye. Sannanhaisam ya sake shi ya mayar da
wukarsa aljihu yajuya ya bude kofa ya fita yabar
sahabi nan zauneyana tunani kamar a mafarki
yau yaji kanshin mutuwa baro baro yana
fadin''lallai haisam dagaske yake zai iya kis a kan
yarinyar nan fa'' abayyane. haisam na fita gidan
uncle yusuf ya shigakasancewat duk yawancin
malaman samari nebabu mata a gidan. Daya
taba kofar yaji a bude saikawai yasa kai. Kicibus
suka yi yusuf ya fito dagawanka daure da dan
tawul a jikinsa. Yayi mamakidaya ga haisam a
tsakiyar falonsa ko sallama bai ji ba, murtik
haisam yake babu walwala. Shima sai jiyayi an
tunkudeshi kan kujera yayi masa gargadi,kamar
yadda ya yiwa sahabi ya firo ya barshi nanzaune
yana mamaki. Saboda tsabagen tsorata suyusuf
ko fitowa basu sake yi ba sai da safe . Balle suje
su daki hannah da daddare kamar yadda suka
shirya yi, haisam ma tunda ya ya shiga gida
baisake fitowa ba ba sai kashe gari da misalin
shadaya na rana yana da lesson a s.s.2b zai yi
musugeography yana doso ofishin principal ya
hangomotar yaya habib yana cikin ofishin
principal ,kuma yasan yau za'a yi tane ta kawai
donshi babu mai rabashi da makarantar nan. Ya
karaso da sauriya nufi ofishin principal tun daga
kan baranda yakejiyo kukan hannah ya shiga a
fusace gami fa yayelabulen kofar bazar ya tarar
da hanna a durkushega jakar kayanta nan a
gabanta, principal tanarubuta mata takardar kora
{dismisal letter} takardar kora daga makarantar
kwata kwata ga yaya habiba zaune yana cewa''ai
idan yaga tabar makarantarzai bari shima dole ''a
gigice haisam ya karaso yakalli yaya habib ya kalli
principal yaga da gaskesuke sun sha kunu.Haisam
ya wawuro wata adda a bayan kyaurenofishin
irinta yankan ciyawa ya dora akan kirjinyaya
habib. Wanda mamaki ya hana yaya habib
yinmotsi daga kan kujerar da yake zaine,
haisamyace''hakika zan iya kashe duk wanda
yake dakokarin jefa hannah a cikin tashin hankali
da wahala a rayuwarta. Ban dauka zan sameka
kanadaya daga cikin irin wadannan mutane ba,
ammaduk da haka ba zan karya alkawarina ba.
Kaiyayana ne uwa daya uba daya da irin soyayyar
damahaifanmu suke yi mana, ka duba kuma
irinsoyayyar da muke yiwa junanmu don haka
bana son na zama ajalinka . Ba kuma zan bar
makarantarnan ba har sai na cika burina dana
kudira akanhannah''hannun haisam rike da adda
akan kirjinyaya habib karkarwa duk jikinsa yake
hawaye neyake shatatowa daga idonsa haisam
gaba ki dayansa ya canja, yaya habib ya tabbata
haisam ya kai kololuwar bacin rai don shi yasan
yadda bacin ranhaisam yake abun babu kyau. Da
wuya dai yayifushi abu da yawa bai cika bacin rai
ba sai an kaishi bango idan ya hau to kowa sai ya
tsorata kumamai lallashinsa ya sauko sai an sha
wuya kumaidan ransa ya baci zai iya yin duk
abunda ya ce zaiyi. Hanna ta kwala kara tace''
yaya haisam kadaka kashe dan uwanka a kaina
na yarda ni zan barmakarantar dan allah yaya
haisam, dan allah kayihakuri''wani zazzafan
hawaye ne yaci gaba dazubowa daga idanuwan
haisam a tsaye yake kawaiya kurawa yaya habib
ido rike da wannan adda a wuyan yaya habib.
Principal kuwa tuni ta dagatsalle tayi lungu tana
jiran taga yadda haisam zaiyida yaa habib sannan
ya dawo kanta. A fusace yayahabib ya yinkura zai
tashi haisam yasa hannu yaturashi kan kujerar ya
koma ya zauna. Haisam ya ce''bani takardar
hannunka''yaya habib yace son hannah kake? Ya
sake fada cikin tsawa yace''tambayarka nake
sonta kake shi yasa ka kasabarin makarantar?
Haisam yace''burina ingahannah tana cikin farin
ciki a rayuwarta kuma inkwatar mata 'yancinta
kamar kowacce yarinyatunda ita ba baiwa bace
gatan hannah allah, sai kuma ni a duk duniyar
nan. cikin sanyin jiki habib ya mikawa haisam
takardar asanyaye sannan haisam ya dauke
addar daga kankirjinsa ya wurga bayan kyaure ya
dauki jakarkayan hannah ya ja hannunta suka
fice. Habib daprincipal suka bisu da kallo suna
fita principal tayiajiyar zuciya don da kyar
numfashinta yake fita saboda tsabar ta tsorata ta
tabbatar yadda haisamya harzuka yau zai iya
kashe yayansa balle kymaita. Bayan wani lokaci
mai tsawo suna zaune shirubabu wanda ya iya
magana suna tunani kawai,yaya habib ya nisa ya
kalli principal ya ce'' madamyaron nan da gaske
yake don jaka kada a kaishi bango ya zo ya kashe
wani a dinga kai kawo akotu, ina ganin a kyalesu
kawai don allah a dainadukan yarinyar balle har
ya harzuka yayi kisadomin haisam zai iya aikata
hakan tunda ya furtayana da zuciya sosai amma
fa sai an kaishi bangodan bai taba zai yi kisa ba
sai yau akan yarinyar nan, zanje in sanarwa da
mahaifanmu'' ya mike yafita, principal kuwa da
kyar take iya maganasaboda tsoron haisa tana
ganin zai iya binta gidacikin dare ya kasheta.
Daga karshe ta yankewakanta shawara gara taje
ta sami haisam ta bashihakuri suyi sulhu . Ta
kuma yi masa alkawarin baza ta sake yadda kowa
ya takurawa hannah ba. Hakakuwa tayi ta sami
haisam har gida cikin lumanasuka zauna ta bashi
hakuri suka yi sulhu. Tana fitahaisam ya tuntsire
da dariya dadi ya lullubeshoi yace HAISAM
HANNAH!! Kwanci tashi su hannah sun shiga aji
shida {s.s.3}sune manya . Cikin ikon allah da
hukuncin allahhannah tazo tafi kusan duk yan
makarantar kokarisaboda tun tana zuwa ta
takwas ta fara zuwa tabiyar daga nan ta kwacewa
pamella matin positiondinta ya zamana rauda ta
daya. Nusaiba ta biyu ita take zuwa ta uku. Tafi
tafiya saiga hannah tazo tadaya a ajinsu wani
lokaci rauda ta kwace kayantaidan nusaiba mata
hargistso sai ta kwance itama,haka dai ake ra
fafatawa amma yanzu da sukashiga aji shida har
malamai ma fada suke hannahtafi su rauda
kokartawa don sau da yawa ko tambaya aka yi a
aji hannah ce take amsawa sautari. Sannan a
class work da assignment tafi kowa ci. An basu
mukamai daban daban. Hannahabubakar imam
itace shugabar dalibai {head girl}nusaiba
mataimakiyarta. Rauda kuwa dake tayikaurin
suna a wajen iya rawa da wasanni {games}
harma ake mata lakabi da janet jacson sai aka
batasocial prefrct da games prefect mukami biyu
akahada mata kuma tayi murna da wannan
mukaminnata. Duk ranar social night har koyawa
yara rawardisco kala kala take yi. Hannah ma ta
dace damukamin saboda ana son head girl ta
zama mai kokari, wacce ta iya turanci sosai, mai
gaskiya,ladabi da biyayya, mai kamun kanta ba
ballagazaba, mai aji , da tausayi da kuma adalci
to dukwadannan hannah ta hada sun don haka
nema daaka tace aka zabeta. Domin a yanzu
hannah kohausa bata cika yiba turanci ya kama
bakinta sosai haisam har mamakinta yake idan
yaji tana zubaturanci. Tana da jan aji hannah ba
kasafai ta fiyeshiga cikin yan mate dinta ba suna
hayaniya. Gatada tausayi musamman ga yara
'yan kananan aji.Babu ruwanta da cin zali kyma
bata yardakawayenta suci zalin yara a gabanta.
Tunda itace shugabar dalibai tana da ikon hana
sauran prefect . wannan halaye na hannah ya
sake fito mata dakyakykyawar surarta hannah ta
sake gogewaabun har musaltuwa ta yi kyau kai
kace ba yarafrica bace . Yaya haisam yasan irin
mayukan dakayan sawar da suka dace da jikin
hannah.Haisam yasan irin mayukan da kayan
sawar dasuka dace da jikin hnnah . Tsadaddun
riga dawando da sket kala kala yaya haisam yake
hadawahannah sai dai kawai idan ta dawo hutu
ta tarar yaaje mata a gidan uwar biyu, daman
tun ba yaubabaya ga mahaifinta babu wani da
take ganin girmansa a duniya irin haisam. Amma
da yakehaisam mai wasa da dariya ne da dalibai
suna wasada dariyarsu a aji kamar yadda ya saba
yi musu tuna aji daya. A garin su hannah kuwa
hannah hargixo take yi musu. Gani suke kawai
baturiya tazotace itace hannah, duk ranar da
hannah zata dawo gida hutu samari har tsayawa
suke a hanyar dazata wuce suna kallonta mata
kuma ta katangasuke lekowa. Ana cewa hannah
ce fa yar malamhabu a garin turawa take karatu.
Hannah sai tayimurmushi kawai ta wuce. A gidan
su kuwa iya abuda yayanta daina magana suka
yiwa hannah sunga ci gaba na hannah daga allah
yake babu irin asirinda basu yi mata ba dan a
korota daga makarantarko kuma ma ta haukace
amma baici ba. Hannahtana dawowa da duk
kayayyakin amfani wadandazata yi amfani dashi
har hutu ya kare, ko ta bawasu iya abu da
yayanta sai suce basa so. Sai tayi hutunta kakaf
ta bar gidan iya abu bata bataabincin da suke
dafawa ba. Ita kuwa hannahdaman tafi sin haka
domin ita yanxu ta saba da cinmai maiko a
makaranta tuwon dawa miyar kukasai su iya abu.
Madara da biskit ne abincinta , alufge a jakarta a
dakinta. Sabulan wanki dana wanka masu kamshi
take amfani daus ita damahaifinta. Ta bashi yayi
wanka ta wanke masakayansa. Malam habu yana
jin dadi sosai dawannan abu da hannah take yi
masa. Yasan doleidan hannah ta zo zata kawo
masa kudi da abunduniya. Ga dinkuna da take
kawo masa tace inji yaya haisam. Silifas dan
madina dana gayu yanzumalam habu yake sawa.
Tsaf tsaf dashi na kashewaya daina gagararsa.
hannah ta zama tamkar wata tauraruwa mai
haskea cikin taurari a makarantarsy. Akwai
kungiyoyi{club} a makarantar da yawa, tun
hannah tana ajidaya ta shiga kungiyoyi daban
daban. Kuma dukwasannin kwaikwayo da za a yi
a kowaccekungiya sai an saka hannah ko tana so
ko bata so saboda kyawunta. Tun ana sata a
matsayin yarinyahar aka zo ake saka ta a
matsayin budurwa. Donhaka hannah ta kware
sosai wajen iya wasankwaikwayo suna fita suje
makarantu daban dabana fadin kasarnan, kamar
su f.g.g.c azare,f.g.g.cbauchi, f.g.g.c.
Kano,f,g,g,c, bakori da dai sauransu. Saboda
kyawun hannah da iya acting dinta
yajawowa.f.g.g. C kazaure suna da farin jini a
wajendaliban sauran makarantu. Kowa ya budi
baki saiyace kai a f.g.g.c. Kazaure da suka
zomakarantarmu akwai wata mai kyau
hannahabubakar ta iya wasa. A yau da yamma
su hannah ne suke gwaji{rahazal}din wani wasan
kwaikwayoda zasu he unity gwaram suyi sati mai
zuwa.Kungiyar yan hausa fulani ne suke yi,
malamhaisam shine shugaban 'yan hausa club,
shinemalamin kungiyar{club master}don kawai
yafarfado da al'adun hausawa a makarantar, ya
kuma hada kan musulmai yara da manya ya
zamana sunhadu a waje daya yare daya sunyi
raye raye fawake wake da wasannin kwaikwayo
tare. Hannah abubakar itace a mastayin yarinya
maisuna talatu cikin wasan kwaikwayo, maryam
tijjaniitace a matsayin saurayin ciki mai suna
abdul.Haisam ne ya rubuta labarin wasan
kwaikwayon. Ayadda wasan kwaikwayon yake
maryam tijjani{abdul}saurayin ciki shine ai yi
tafiya kasar libiya karatu sai yayi shekaru hudu
acan sannan zaidawo. Ga budurwarsa hannah
wato talatu a cikinwasan sunyi alkawarin zasu yi
aure daman saitafiya ta taso masa yazo zai tafi
ya barta. Damanhaisam ya gutsuro takarda ya
rubutawa kowacceabinda zata ce a wahen sai ta
rike tana karantowa harta rike da ka, kafin ranar
da zasu yi ba sai datakarda ba. A yau kusan yan
aji shida kakaf sunazaune a hall din nan wajen da
ake gwaji{rahazal}din nan da wasu da yawa daga
cikin yan aji biyar,hudu da uku yan kungiyar.
Maryam tijjani {abdul}itace ta taho da jakar kaya
katuwa a rataye a kafadarta tazo wucewa suka
hadu da hannah{talatu} dauke da kwarya a kanta
zata je kogi deboruwa. Abdul ya sakarwa talatu
wani lallausanmurmushi na so da kauna cikin
sassanyar muryahannah(talatu) tace''abdul ba
dai tafiya ba'' ya ce''tafiya zanyi talatu nazo ne
daman inyi miki sallama'' sai kawai kwaryar dake
kan talatu ta fado kasa dangigicewa. Ta rushe da
kuka. Abdul ya gigice yaajiye jakar dake
hannunsa, hannah ta fara karantotakardar da
haisam ya rubuta musu tace'' abdulkayi min
alkawari ba zaka yi aure ba a cam har saika dawo
ka aureni karka je can ka sami yar larabawa ka
aura ni ka manta dani'' haisam yasatafi sai duk
aka dau tafi a hall din. Haisam yacekunyi kokari
wajen yayi kyau kema maryam tijjaniki dage ki
bata amsa dan allah banda dariyar nanda kika
saba'' maryam tijjani tace to bazan yi dariyaba''
ta daga ido ta kalli hannah(talatu) wani kallom
soyayya da hannah take, tayi wani narai narai
daidanuwanta kai sai kace a gaban saurayinta
nagaske take. Sai dariya ta kwacewa maryam
tijjanisai kowa yasa dariya. Haisam yace
''maryamgaskiya kina bata mana lokaci kullum
muka zodariya kawai kike yi saura kwana uku fa
mu fita excusion idan kinsan ba zaki iya ba
nasawata''maryam tace''uncle allah hannah ce
take sanidariya baka ga kallon fa take yimin bafa
kamar tasami saurayinta da gaske sai kashe
idotake''haisam yayi dariya yace''tsabar tafiki
iyaacting kenan. Shi daman wasan kwaikwayo ana
son duk abunda aka baka kayi kokari ka
nunakamar da gaske ne. wajen kuka kayi kuka,
wajen murnakayi murna . Kema kiyi mata kallo
kamar kecesaurayin kin hadu da budurwar da
kika fi so a duniya. Wannan yana nuna kenan
hannah ta iyaacting sosai kamar da gaske. Kowa
ya hau dariyaana yiwa maryam tsiya ''kema ki yi
mata kallonsoyayyar mana ko baki iya bane?
Haisam ya tashi yaje ya karbi takardar
hannunmaryam ya ce''koma gefe ki dinga kallon
yaddazamu yi sosai don ki koya'' ya ce da
hannah''tokara karanto naki''babu kunya hannah
ta narkarda idanuwanta ta kashe murya lallausa
ta dubihaisam kallo ido cikin ido''abdul kayi min
alkawarin ba zaka yi aure ba a can har sai ka
dawo ka aurenikar kaje can ka sami yar larabawa
ka aura ni kamanta dani anan'' haisam ma ya
narairaice ido yakurawa hannah ido kawai
wannan kallo da haisamyake yiwa hannah ya
sosa mata wani waje axuciyarta, ya ce''talatu ba
zan yi aure ba, kuma ba zan manta dake ba. Ko
a ina nake, ko da gangarjikina bata tare dake
ruhina yana tare da ke.,soyayya baiwa ce,
hannah kina raina a kodayaushe . Ina sonki
hanna'' taji gabanta ya fadi donjin yaune rana ta
farko da hannah tasan ma'anarwakar nan da
take yi tayi shiru tana tunani tana kallon yaya
haisam ta san tabbas wannan wajen acikin wakar
nan da take yi masa ya dauko kamardaga sama
taji yaya haisam ya ci gaba da cewa''inasonki ina
sonki hannah! Ba zan manta dake bakina raina
har abada'' wannan karon bakarantowa ya ke a
takarda ba kuma ba talati yace ba, hannah sai ta
fara ja da baya taba tafiya ahankali tasa hannu
ta rufe idanuwanta tanamurmushi. Kunya ta ka
mata gaba daya yan kallonsun zubo mata ido
suna kallon sarautar allah, domin kowa ya san
wannan kallon kadai da sukeyiwa junan su yafi
karfin gwaji balle kalaman da yake fita daga
bakin haisam ba a jikin takardaryake ba. Sai yaja
wani dogon numfashi ya juya yakalli sauran
dalibai yace'' kuje ma karasa gwajin dadaddare''
ya fita ya nufi gidansa. Dalibai su ka firfitosuna
gulmammaki'' wannan anya hannah da
unclehaisam ba soyayya suke yi ba, ke kinga
kallon da suke yiwa junansu uncle haisam kamar
yarungumeta fa. Haka suka shiga
dakunansukowacce ta nufi bangaranta. Rauda ta
sami hannah a kwance akan gadonta tadora filo a
kanta babu abinda take tunanowa saiidanuwan
yaya haisam sai kuma tsananin mamakinyadda
ya rike baitukan wakar nan da take yi masatun
tana aji daya. Tace a ranta ashe ma'anar
wakarkenan banda yarinta nake kai kaicewa nake
rera masa ko da gangar jikina bata tare dakai
ruhinayana tare da kai. Har nusaiba take cewa
hannahmeye ruhi nace ina jin larabcine ashe ni
ban sanhausa ba ce tsaba a lokacin . Ruhina ,
ruhina'' tsakitaji anyi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login