Showing 27001 words to 30000 words out of 31410 words
Chapter 10 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete
sun gaisa ya ce da hannah''yau zaki
tafi gida ko sai kin sake hutawa kamar satidaya
anan sannan ki tafi ? Hannah tayi caraf tace''yaya
haisam yau zan tafi na dade banga babanaba''
haisam yayi dariya ya ce'' wato ke yanzu kin bar
kazaure kenan zaman kazaure sai mu ? Tayidariya
tace'' sai ku ai mun daku wannan hutun harna
daina sha'awar garin allah yaya haisam''
haisamya mike ya ce'' to ki shirya zanje nan
makwabtasafiyanu yana ciki wajen abokansa ana
wankemasa motar ana gamawa sai ku fito zan
aiko yaro yayi kiranku sai mu kaiku tasha ku tafi.
Da har cangarin zamu kaiku inyiwa baba godiya
ince masagaki na dawo masa dake lafiya na cika
alkawarishima ya cika to sai safiyanu ya ce kano
zai tafi dakakarsa in anjima'' hanna tayi dariya
tace'' kai yaahaisam ai babu komai yana gani na
yasan lafiya na dawo lallai kuwa ka cika alkawari''
ya juyo yakalleta yace ''ko? Tayi murmushi tace''
E'' sannan yafita yana murmushi. Bayan fitarsa
da dadewa sosaiyaro ya shigo ya ce wai uwar
biyu da hanna su fitoinji su safiyanu suna kofar
gidan dallatu'' daman ashirye suke tsaf sai
hannah ta dorawa yaron jifgegiyar jakar kayanta.
Jakunkuna uku ne. Yakaiya dawo ya dauki ta biyu
sannan yazo ya dauki takarshe sannan suka fito
uwar biyu ma da buhuntaa kanta, suka shiga
mota sai tashar kazaure.Hannah ta hado kayanta
kakaf na gidan uwar biyu.Katifa da bokiti kuwa
taba uwar biyu kyauta. Kaya masu kyau atamfofi
da shaddoji da yawa. Hanna tabawa uwar biyu
kyauta da 'yarta halima. Dake kayatsadaddu leshi
ma uku, shadda da atamfofobibbiyu yaya haisam
ya yiwa hannah na candy.Bayan takalma da yan
kunne, sarka da dan kunneharda gwal ya suyo
mata. Suna isa tasha a bakin tasha safiyanu ya
tsaya da motar. Ma'aikata nan'yan union su biyi
suka zo suka tambaye su inazasu da suka fada
sai suka ce babu motar babbanmutum yanzu
amma baza a dade ba zata zo. Haisamyace su
kwashe jakunkunan su kai cikin tasha,hanna da
uwar biyu suka shiga cikin tasha. Safiyanu da
haisam suna nan bakin mota a tsaye abakin
tasha. Can suna taye suna hira sai safiyanu
yakalli agogo ya ce yanzu fa muka yi da hajja
kakatazan dawo mu tafi kano tana can tana jira
na''haisam tace'' ai ba komai heka kawai nima
idannaga tafiyarsu acaba zam hau in koma cikin
makaranta.. Suka yi sallama safiyanu ya shiga
motaya tafi, haisam kuma ya shiga cikin tasha A
cikinwata yar rumfa ya iske hannah a zaune akan
jakarkayanta uwar biyu kuma akan wani benci
suna'yar hira suna jiran zuwan mota.Haisam ya
karasa cikin yar rumfar yanatambayar su''har
yanzu motar bata zoo bane? Uwarbiyu tace'' sun
dai ce yaznzu zata zo munzo da wurine wai
daman motar bata zuwa da wuri'' ta mike
dasauri daga kan bencin tace da haisam ya
zauna ,yace''lah babu komai yi zamanki mana'''
uwar biyu tace'' a'a ka tsaya'' ga kawayena acan
suna sayarda zogale bari inje wajensu mu gaisa
daman dankar na bar hannah ita kadai shine
yasa banje tundazu ba''uwar biyu ta tafi .haisam
ya zauna yanakallon matafiya da masu mota ana
ta hayaniya. Canya juya ya kalli hanna wacce ke
zaune akan jakarta tayi jugum kamar tunanin
wani abu take, ya kuramata ido kawai yana
tunani a ransa. Babu abundaya fara tunawa sai a
ranar da aka fara kawohannah makaranta ta ci
dammara ta hau ta zaunaakan akwatinta tayi
jugum tayi shiru a lokacin dababanta ya tafi ya
barta. Amma yanzu maimakon dammarar da taci
sai tayi shar da wani tsadaddenbakin leshi mai
duwatsu kala kala suna sheki ajikinta. Dinkin fitet
tsamammiyar riga da siket ta yafadan yalolon
gyale ta dana daurin dan kwali yayinda lallausan
gashin nan nata mai santsi baki datsawo ta tufke
da bakin ribon a keyarta. Hannah ta dago kai sai
taga yaya haisam kallonta yake yikawai a lokaci
guda sai kowannensu ya sakarwadayan
murmushi. Abunda itama ta fara tunawaranar da
babanta ya kawota makaranta ta hau
kanakwatinta ta zauna tayi shiru yaya haisam
yanazaune akan benci yana kallonta. Mai tallar
biredi ne yazo ya ishesu da a sayi buredi ga
gardi, zakibiredin tsaraba . Haisam ya kalli hanna
yace'' bazaki sayi abun tsaraba ba ne ki kaiwa
yara? Hannatace'' kyalesu yaya'' ya ce '' ban
gane kyalesu ba,haka zaki yi wata bakwai kije
musu hannurabbana, biscuit ko sweat zaki shiga
aishalle ki saye, ungo kudin ko ki aiki wani yaron?
Ya cirokudi a aljihunsa, hannah tayi dariya tace''
su fasunfi ganewa ayi musu tsarabar biredi''
haisam yace su sha tea da safe dashi ? Hannah
tace'' a.a surinka gutsira a haka'' su duka suka yi
dariya.Haisam ya ce da mai biredi ya sauke yaje
ya siyo jakar bacco ya dawo. Ba dadewa sai ga
mai biredidauke da jakar bacco. Haisam ya ce ya
juye buredinduka a ciki. Hannah ta rike baki
tace'' yaya haisamwadanna manya manyan
buredi har wajen takwasai suna da girma sunyi
yawa biyu ma sun isa''haisam ya ce a'a basuyi
yawa ba kowa yazo yayi miki sannu da zuwa sai
ki yago masa gayan birediki bashi kice tsaraba''
su dukkansu suka kyalkyaleda dariya harda mai
sayar da biredi dadi yakamashi ana masa ciniki.
Mai lemon fata ne yagarzayo da sauri yaga an
siye na abokinsa, shimaya bude muryarsa gaba
daya yana ''a sayi na tsaraba'' shima haisam
yace ya siyo bacco yazo yajiye duka farantin , yayi
kololo kuwa dan cika. Nada nan ya garzaya da
sauri ya siyo bacco ya juye saikudinsu tumus a
hannu. Sika jerawa hannabakkuna a gaba suka
tafi suna murna. Hanna tadago kai ta kallo
haisam fuskarta cike da murmushi gami da nuna
jin dadin kulawar da yake yi matatace'' yaya na
gode fa kwarai da gaske'' ya ce''babu komai
hanna'' hanna ta dago ta kalle shi sukahada ido
tace'' yaya haisam baka bani abin busanaba da
tsakiyoyina daka ce in baka zaka boyeminkada
malamai su kwace min din nan tun randa aka
kawoni aji daya.Haisam ya tuntsire da dariya
hanna ma hakayace'' bazan baki ba sai kinyi
wannan kwalliyar dakika yi a fuskarki mai digo
digo nan da wannandammarar da kike yi sannan
zan baki sarkokinki''suka sake tuntsirewa da
dariya ya ce'' busa nake yida abun busarki fa.
Kusan kullum da daddare kafin in kwanta zaki yi
mamaki idan aka ce yanzu na fikiiya busar da
wakar. Nafa rike yadda kuke wakarda amratu
kanwata zabje in kaiwa a gida ashe bakibani ba,
bari inje in dauko muki'' hannah tayi sauritace''
ban san kana so ba na bar maka, hartsakiyoyin
ma in so kake? Yace ''eh suma amratu zan bawa
ta dinga kwalliya dasu'' hannah tayidariya
tace''amratu baza tayi kwalliya dasu ba,komu yan
kauye mun daina saka irinsu'' motar dazata je
babban mutum ce ta shigo. Doguwar bus cenan
da na uwar biyu ta taso tace dasu'' hannah
gamota nan tazo daga jakar su zuba kayan a but''
kwandasta yazo ya debi jakunkunan kayanhannah
da tsarabar ya zuzzuba a but, hannah dauwar
biyu suka shiga kujerar baya su biyu kacalsauran
wajen haisam ne yake biya daman hakayake
musu in dai ya kawosu tasha to mutane
hudubasa zama a baya. Hannah da uwar biyu ne
kawai suke zama ya biya kudin sauran kujerun.
Matafiyasuna ta shiga mota haisam yazo ta jikin
wundonuwar biyu ya mika mata kudaden
motarsu dakuma wanda zata bawa mahaifin
hannah kamaryadda ya saba aika masa, uwar
biyu tana ta godiya.Haisam ya zaga ta wundon
hanna wacce jikinta yayi sanyi tana daf da
fashewa da kuka, ya mikamata wata ambulam fal
da kudi. Ya fara yi matanasihohi masu tsuma
zuciya kamar yadda ya sabayi mata amma
wannan karon nasihohin sunshabambam da na
kullum hade da bankwana yake yiyace'' hanna
alhamdulillah allah ya kawo mu ranar da kika
gama makaranta kin zana jarabawarkarshe allah
ubangiji ya baki sa!a. Hanna ki kula daaddininki
sosao daman can ke mai addini ce nasanda haka
amma ki kara . Kada ki damu a duk halinda kika
tsinci kanki. Na wahala kina jin dadi dukallah
yana sane dake kuma yana sonki ba wai ya
wareki bane don ya tsaneki yake hadaki da
masifuiri iri da bakin ciki. Allah {s.w.a}yana
jarababawansa ta duk inda yaso kiyi kokari
kicijarabawarki , ki kuma din ga gode masa a
dukrintsin da kike ciki. Idan kika gode masa a
dukyanayin da kika godewa allah to shi zai canja
miki, ina so ki kula cewar babu wani mutum a
duniya dazai zama shine matakin gatan kowa don
allah kirike wannan allah shiya halicce ki shi yake
ba dawakuma shi yake hanawa babu me miki
wani abubanda allah kici gaba da yin tawakkali
allah yanasane dake. Tsananin kukan da hannah
take rusawa shine ya dabartar da haisam ya
rasaabunda zai ce shima ji yayi kwalla ta cika
masa idotaf sai kawai ya juya ya tafi ya ce'' allah
ya kiyayehanya, sai anjima'' wani kululun bakin
cikin neyazo ya tokaresu dukkansu a wuya
tsananin bakincikin rabuwa da juna. Gagarumin
tashin hankali ya mamaye zukatansu kowanne na
fidda ran sakeganin dan uwansa kuma. To tayaya
hanna zata zokano tace tazo ta gaishe da
malaminta bayan ramlana nan na nemanta zata
halakata idon ta idon tatace sai taga bayanta. Shi
kuma yaya za'ayi haisamyaje garinsu hanna
bayan duk gari ya dauka sharrin da ramla tayi,
iya abu na yadawa hanna bakaratu take yi ba
soyayya take yi da wanimalaminta. Hanna tayi
zugum a zaune a mota ji takeduk duniyar babu
dadi. Yanzu zaman dindindinzata je suyi da iya
abu tasan ba karamin bakin cikizata hadu dashi
ba a gidan. Ga tsananin bakin cikin rabuwa da
yaya haisam saboda sun saba sosai dontafi jin
bakin cikin rabuwa dashi akan nusaibawacce suke
kwana tare su tashi komai tare hattabacci baya
rabasu. Uwar biyu ma sai duk jikintayayi sanyi shi
kenan idan ta kai hanna gida baza tadawo ta
dauketa ba kuma. Suka isa gidan su hannah,
hannah ta shiga gida da sauri tana murnazata ga
babanta. A shimfidarsa a zaure ta ganshikwance
sharkab babu lafiya ashe watansa wajenhudu a
haka. Ciwo kullum gaba yake sake yi saiakwantar
a tayar. Hannah ta gigice har tana nemanrasa
hankalinta yayin da taga mahaifinta ya zama
kashi a kwance kurket dashi kaninsa ne uwa
dayauba daya yazo yana jinyarsa . Dan ta iya abu
cewatayi ya mutu mana tace ta gaji da zaman
jinya tundayaki warkewa tayi na allah 'yan
uwansa kuma suzosuci gaba da kula dashi ita ta
huta. Hannah tasakuka taje ta tsugunna a
gabansa tace'' sannu baba'' yace'' yauwa sannu
'yar baba ashe da rabonkizo muyi magana ban
mutu ba nace aje a kirawomin ke a makarantar
kizo kiga gawar mahaifinkibasu je ba'' cikin
sheshshekar kuka hanna tace''baza ka mutu ba
baba daina fada ma'' uwar biyuma ta matso kusa
dashi tace'' sannu malam habu ya jikin ''yace''
jiki dai gashinan uwar biyu sai dai kuyimin addu'a
idan na mutu, allah ya saka miki daalheri ke da
haisam da gidan aljannah abundakuka yiwa
hanne na gode''uwar biyu ma hawayetake yi.
Hanna tayi kuka kamar ranta zai fita. Ananuwar
biyu ta yini sai da la'asar tace zata tafi suka yi
sallama da malam habu dake radai yana
maganatashi tsaye ne baya iya yi. Hannah ta
rakata hartasha.A hanya Uwar biyutakebawa
Hannah shawara ta ce "Tun da ke mai ilimice
kiyiamfani da iliminki, ki kai Mahaifinki asibitin
Baburatunda kudin da Haisam ya bawa
Mahaifinki dawandaya baki mai tsokane zai
isheku. Da abarshi a gidaanamasa jike-jike duk
wata cuta ake kara masa.Mutum akwance har
wata hudu ya kare sai kashi da fata. Atashar
Uwar biyu ta sami mai mota aka yi tsadazata
jegida a dauko marar lafiya a kaishi asibiti.
HannahdaUwar biyu suka shiga mota, dake itama
Uwar biyudaman motar Babura zata shiga daga
Babura zatahauta Gumel. Sai kawai su duk su tafi
tare. Motar tajeharkofar gidan, direban da
kwandasta da kanin MalamHabu suka ciccibeshi
suka sashi a mota sukashigasuma da *yan
kayayyakinsu suka nufi asibitinBabura.Iya Abu
nata yiwa Hannah surutu tana cewa gatananUwar
iya yi wai har tayi kilin din da zata
daukiMahaifinta ta kai asibiti wai har asibitin
Babura tazama *yar boko. Sai da Uwar biyu tayi
wata gudacur aGumel sannan ta dawo Kazaure
tana zuwa tananiyyarta shaidawa Haisam halin
da Mahaifin Hannah kecikisai aka ce mata ai
bayan tafiyar su Hannah da satibiyushima ya bar
koyarwar ya kwashe kayansa yakomaKano. Ta
nemi Safiyanu shima aka ce mata ai shitundayayi
aure a Kaduna ya tare da sabuwar
amaryarsaacan ya sami aiki, sai Uwar biyu ta
hakura dasanarwaHaisam don ita bata taba zuwa
Kano bama balleta tafinemansa. Su Hannah kuwa
sai da suka shafe wataguda da kwana shida
sannan aka sallamesu dagaasibiti. Kanin
Mahaifinta ne a wajensa amma itamatakan je tayi
kwana biyu uku acan har dai sukadawogida gaba
daya. Jiki da sauki tunda yana zama dakansa ba
sai an tallafo shi ba. Sai dai
kudadenhannunHannah sun kare kakat saboda
siyan magungunanasibiti.Nan fa balokokon Iya
Abu ya tashi akan tagaHannahbata da kudin da
zata sayi dan biskit da madarardatake sha idan
tazo hutu da, dole ta ci tuwan gidan.Hannah ce
shara, wanke-wanke da dafa abincitukatuwan
bakar dawa da miyar kuka a murhun kasa.Kwanci
tashi su Hannah sunyi wata biyar da
gamamakaranta. Hannah har ta fara zuwa
makarantarbokongarinsu tana koyarwa. Duk da
dai ba'a dauketa amatsayin Malama ba don
Jarabawarta bata fitoba.Amma a karshen wata
ana bata dan na batarwa.Ranarasabar babu
makaranta. Da sassafe bayan Hannahtagama
wanke-wanke tana kokarin daura tukunyartuwon
burabuskon gero miyar kuka na rana saikawaiIya
Abu tazo ta kashe wutar da ruwan tuwon. Tace
tacanja ra'ayi yau an fasa yin abincin ranar
sabodaunguwa zata ita da jikokinta don haka
meyeamfanintuwon. Ta dauke garin tuwon da
kukar kadin tasaadaki ta datse ta yafa mayafinta
zata fice. RanHannahya baci ta ce "To Baba fa,
me zai ci shi da bashidalafiya? Yau jikin nasa a
rikice yake tunda sassafeamaiyake. Iya Abu ta ce
"Sai yaci hakuri ko ki kwasheamanda yayi ki
dumama masa. Cikin fushi Hannah ta ce"Inaraye
a duniya Mahaifina ba zaici amai ba
inshaAllah"Mari tas Iya Abu ta sakar ma Hannah
akanlallasusankuncin nan nata ta ce "Ke kin isa
ina fada kinafadalalle wuyanki ya isa yanka.
Malam Habu da yakekwance sai jikinsa ya dau
kakkarwa tashin hankaliyadira a zuciyarsa yaji
marin da aka sakarwa Hannesaiya hau hawaye
yana kira "Yar Baba yi hakuri zonanwajena ki
zauna. Hannah tana hawaye ta je
gefenshinfidarsa ta zauna Iya Abu tana tsaye
akansutana tabalokokonta tayi har ta gaji ta
kama hannunjikokintasuka fice, da taji ba'a
kulata ba. Zuwa can wanilokacimai dan tsawo
Hannah da Mahaifinta sunyi zugumsuna tunani
sai ta jiyo mai tallar fura da nono tazotazo
wucewa, da sauran *ayan canji a jakarta tatashita
leka ta kirawota, ta dauko kwanon sha ta
saya.Tadama ta tashi Mahaifinta zaune ta bashi
yasha yakoshisannan ta gyara masa kwanciyar ya
kwanta takomagefensa ta zauna tayi lamo
zuciyarta cike datakaici gayunwa tana addabar
cikinta. Can Malam Habu yace"Yar Baba, ta ce
"Na'am Baba. Ya ce "Allah Yayimikialbarka ya
baki miji na gari mai sonki kamarHaisam,sai
Hannah tayi shiru tana tunani da mamaki
yaakayiMahaifinta yake hada mijinta da
Haisam.Malam Habu ya ce "Ya ba ki amsa ba? Ta
ce"Babakamar Haisam kuma? Ya ce "Eh kamar
yadda yakekuladake yake nuna miki kauna. Tayi
murmushi ta ce"Mutunci ne dashi da tausayi
amma ba soyayyabace.Malam Habu yayi dan tari
ya ce "*yar Baba matsokusadani kiji. Hannah ta
matso kusa dashi. Ya ce "YarBabababu mai sonki
a duniyar nan kamar Haisam, babumairikeki
tsakani da Allah irin Haisam, babu mai
rikekiamana ko bayan raina wanda ko dar bana
yi saishi*yar Baba. Haisam yana matukar sonki.
Hannah tace"Meka gani kake cewa haka? Ba sona
yake ba kokadanmutunci ne ai bai taba gaya mun
ba. Malam Habuyanisa ya ce "Yanzu tashi kije ki
nemi gidansu aKanokice na amince masa ya zo
zan bashi ke ya aureki.Hannah ta zabura ta ce
"A'a Baba ya za'ayi injekawaiince masa ka yarda
yazo ya aure ni bayan bai cezaiaureni ba. Malam
Habu ya ce bakya yimun musu,karkifara daga yau
bazan ce kiyi abunda zaki cutu bajekikawai ki
fada masa. Haisam ne zai rike mun keamana*yar
Baba duk duniyar nan shine kadai na
yaddayaaureki. Jeki ki shiryo ki tafi yi sauri *yar
Baba.Hannahta tashi a sanyaye zuciyarta cike da
zuluminwannanal'amari.Ta shiga cikin gida ta
sake salla wanka ta sakawanidandatsetsen sabon
leshinta kalar brown ta yafagyalenta a kusa da
Babanta ta ce "Na shirya zantafi,ya laluba
karkashin tabarmarsa ya dauko wasukudi yabata,
ya ce tayi kudin mota. Ta ce ya barshi
tanadakudin mota, ya ce ta karba shi mai zaiyi
da kudininbata karba bama kwashe su za'ayi,
kudin da yatattarane na *yan dubiya. Har
Hannah takai bakinkofazata fita sai ta tuno ai
bata san kwatancen gidansuHaisam ba gashi bata
taba zuwa Kano ba sai cantatuna akwai inda ya
rubuta mata kwatancengidansu ajikin littafinta
(slum book) da ta bashi ya cikemata. Takoma
daki da sauri ta binciko cikin littattafanta tadauko
sai kawai ta jefa littafin a jaka ta fito.MalamHabu
na kwance bacci ya fara daukarsa
yajimotsinmutum sai ya bude ido ya ce "Waye?
Hannah tace "Nice Baba, ya ce "Baki tafi ba ne,
*yar Baba kobakyasonzuwa ne? Ta durkusa a
gabansa ta ce "Baba bahakabane mantuwa nayi
na dawo amma yanzu zan tafizanbi ta gidan Iya
Salma(tsohuwar matarsa ta fari) koitatazo ta taya
ka zama kafin in dawo baza a barkakaikadai ba.
Malam Habu ya ce "To Allah Yayi mikialbarka.
Hannah ta ce "Amin Baba Allah Ya bakalafiyaya
ce "Amin *yar Baba, kuma ko bayan raina
adauraaurenki da Haisam ina fatan kema kina
sonsa?Hannahtayi dariya ta rufe ido, alamar
kunya Malam Habuyayidariya shima ya ce "Yar
Baba fada min gaskiyamana.Ta ce "Baba saboda
tsananin kyautatawa da kuladayake mun sune
suka sa nake ganin girman YayaHaisam har naji
babu wani mutum da nake so datsananin kauna
bayan kai Mahaifina sai kuma shi.Babaina son
Yaya Haisam sosai har nakan kasa
bacciyanzusaboda tunaninsa da kewar sa
musamman yanzudamuka rabu. To amma Baba
babu yadda zanyi sainagakamar shi ba haka yake
nufi a zuciyarsa ba.MalamHabu ya ce "Tashi kije
shima yana sonki fiye dayaddakike ji. Amma muyi
addu'a kafin ki tafi mu karanta salati goma
gaannabisuka karanta suka shafa. Hanna tadinga
kwararo addu'ai sannan daga karshe sukashafa.
Hannah ta sake yi masa sallama ta fita. Tanafita
gidan iya salmai ta nifa ta shaida mata abundake
tafe da ita. Nan da nan iya salmai ya zari
gyalenta ta nufi wajen tsohon mijinta dan uwanta
abunkaunarta wacce dole ce ta raba su don ta
kuladashi kafin hanna ta dawo. Hanna na isa
tasha tatarar da mota fijo zata je kano ta cika
saura wajenmutum daya tayi sauri ta fada sai
tafiya. Babuabunda hannah take ji a ranta yau
sai tsananin farin ciki, ji take kamar anyi mata
albishir da gidanaljannaj. Tana san yaya haisam
har ranta, to shimakuma yadda ta lura yana
sonta sosai kuwawadannan dara daran idanuwan
nasa ne takehangowa a zuciyarta idan yana
kallonta. Da wasufararan hakoransa tasa idan
yana mata nasiha wai waya ganni a kano yau a
kusa da yayana haisamkuma ma wai yazo muyi
aure an bashi ni'' hanna kefada a zuciyartaDadi
marar musali ya disu azuciyarta kowa yaga
hannah yasan tana farin ciki ayau. Sun isa kano
lafiya a tashar yan kura akasassauke su. Hanna
ta fito daga mota ta kalli gabas da yamma kudu
da arewa. Daga bil'adama neburjik a gaba da
bayanta. Tace a ranta''ikon allahkano mai mata
da maza, ta dawo tumbin giwa kodame kazo an
fika. Yanzu ina zan fara dosa gabas koyamma ?
Abunya bata mamaki ganin yadda akekallanta har
wasu mazan waiwayenta suke . Da farko ta dauka
kowa ya ganta yasan bakauyiya cebata taba zuwa
kano ba, ta fita daban da yan garisai da taji wasu
samari su biyu sunxo wucewasunce mata'' ke
kyakykyawa dan rufe fuskar nantaki kada kisa
wasu mazan suyi hatsari a garinkallonki. Sannan
ta yarda tsabagen farin da suka gani da
kyakykyawan fuskar da kirarta suke kallosai tayi
sauri ta dora gyalenta aka ta rufe
fuskartaidanuwanta kawai a bude, tace a ranta
dukkyawawan matan garin nan daman har wani
kyauzaus gani? Kwalelensu yaya haisam ya riga
su. Tabude jakarta ta dauko littafin da adireshin
gidansu haisam ke rubuce ta karanta sunan
unguearsuleman cresent, sai ta sami wani
kwandasta motatace malam don allah ina motar
suleman cresent ?Yace ''a'a gaskiya babu
takamaimai motar da takezuwa irin wadannan
manyan inguwanni, ammashawarar da zan baki
ki sami tasi ki dau shata ya kaiki har kofar gida.
Ga masu tasi nan a tsatstsayebabu kowa a ciki.
Ya nuna mata su, tayi godiya takarasa wajensu,
babu abunda ta fara hangowa saiwajen waya an
rubuta'' make your call here'' takarasa wajen
masu wayan tace'' anan ake yinwaya ? Mai waya
yace eh nan ne. Ta dauko littafinnan ta dubo
lambar nusaiba ta mika masa.Bugu daya wayar
ta shiga ta fara ringing. Watamata ce ta dauka
sannan ya mikawa hanna kanwayar hanna ta
karba tana kallon kan wayar donita