Showing 9001 words to 12000 words out of 31410 words
Chapter 4 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete
sakenaji kina yiwa hannah
kinji ko ? Rauda tace''yayaya za'ayi ta shafa man
gashi a jiki sai kace bakauyiya'' haisam ya ce a,a
wai a misalai nakenufi, koda ace zata manta ta
dauko man gashin''tafiyar wani malami ce tasa
duka hankalinsu yahuya baya don ganin mai
tahowa, haisam yace'' toshikenan ku koma aji ga
malam shaiya nan zaikaya muku maths an kada
firs period,'' suka ruga a guje, malam shaiya ya
mikawa haisam hannu sukagaisa sannan ya nufi
s.s.3c yana da period yanakoya musu
geograpykamar haisam yayi duba da yace idan ta
daukoman gashi zata shafa a jiki haka kuwa aka
yihannah babu abunda ta sani a kayan
akwatintadaga ta dauko man wanke gashi
[shamppoo] takwaba a jikinta sai ta dauko man
shafawa ta makaa kanta makilin ma wani lokaci a
tsagar kitso rauda tazo ta isketa tana sharbawa.
Suyi ta dariya har sugodewa allah daga karshe
dai suyi mata bayanidalla dalla , wannan ne na
kaza wannan kuma awaje kaza ake shafawa.
Babu laifi a sati biyuhannah ta waye ta gane duk
kayayyakin amfani nazamani sannan ta koyi cin
kayan gwangwani dana kwali, don da farko inda
suka dama comflask damadara cokali daya zatayi
sai ta fita a guje ta kelayaamai bata sanshi ba
haka sardine da gesha kifingwangwani sai taki ci
tace tsutsace amma dagabaya duk ta waye tana
ci. Hannah tana farin cikimatuka da wannan
sabuwar rayuwar data tsinci kanta. Abinci
lafiyayye a akwatinta na makaranta ,gashi tana
cikin yara sa'anninta suyi karatu taresuyi wasa
tare musamman nusaiba tana bala'inkaunar
hannah tafi rauda kirki don rauda ta cikanuna isa
da nuna tafi kowa kuma duk girmanka saita riga
daka tsawa.Ta fannin karatu kuwa. Ada hannah
dumama kujera take yi kawai saboda tsantsar
turanci ake yia makarantar amma sai nusaiba ta
lura hannahbata fahimta don haka a koda yaushe
bayanmalami ya gama darasinsa sai ta matso da
kujerartahar kusa da ta hannah tayi mata bayani
dalla dalla. Haka shima malam haisam kullum a
prep dinyamma yana zuwa ya kira hannah ya
koya mataabubuwa da dama. A wata daya
hannah ta faragane turanci fiye da yadda kuke
zato. Ranar wataasabar da daddare ranar ne ake
warewa dalibai sushakata su hole rayuwarsu
kamar a saka musu kidan disko su cashe wasu
kuma su kada tebur dakansu suna waka wasu na
rawa. Wasu kumatalabijin ake kunnawa da bidiyo
suyi kallon kasetduk dai abunda ransu keso shi
zasu yi. Daga 'yanj.s.s 1 har manyansu s.s.3
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 2
Posted by ANaM Dorayi on 02:02 PM, 30-Apr-15
Under: Gangarjikinsa ta Aura
Wannan rana ita ake kirada '' social night'' uncle
haisam kuma shine social master wato shine
malamin da yake kula da dalibaiyake kula da c.d
din da ake kunna disco da bidiyoda talabijin din
da ake kunnawa. A wannan dare anyarjewa
dalibai su saka kayansu na gida{persinal}kowane
iri ne kama daga leshi ko shadda riga daskit kai
har jeans da tea shirt duk zasu iya tsukewa.
Rauda sarkin rawa ita har tunanin wannan
asabardin wacce irin rawa zanyi don har fili ake
batakowa ya koma gefe yana kallonta rawa salo
salohar wasu suke kiranta janet jacson wai
kanwarmacheal jacson nusaiba kuwa ita da
hannaah babuabinda suka fi so irin kallon bidiyo
hausa fim masu kyau malam haisam yake
samowa ko nigerian fims.Social night din wannan
asabar din bata yiwahannah da nusaiba dadi ba
saboda bidiyo talalacebabu kallo sai dai c.d aka
kunna aka ware kida dukmai bukata yaje ya
cashe wasu na rawa wasukuma na gefe suna
kallo. Amma wasu suna kan barandar wajen hall
din a zazzaune basa sha'awaryin rawa ko kallon
masu rawa kungiya kunkiyakowanne da group
dinsu suna waje suna zazzaunesuna hirar duniya.
Hannah da nusaiba suna dayadaga cikin wadanda
basu shiga cikin hall din bawajen kida suna
zazzaune a can kan wata barandar ofishin
malami suna hirar duniya, hirarma ma jifa jifa
suke yi saboda duk rayukansu abace yake yau
babu kallo kuma wani hadaddenamerican film
mai suna''mr bones''uncle haisamyayi musu
alkawarin zai saka musu. Nusaiba tayiajiyar zuciya
tace anya kuwa yau zan iya bacci saboda bakin
ciki na kudiri niyar danin firm dinnan,wallahi fim
din akwai abin dariya muna dashi fa agidanmu.
Hannah tace na last week ma yayi kyauga abin
dariya osofia in london yaya haisam ya iyazabo
man films masu kyau. Wata murya ce abayansu
tace na kamaku kuna gulmata'' suka juya da
sauri sai suka ga yaya haisam ne su duka
sukatuntsire da dariya ya zagayo suka matsa
masa yashiga tsakiyarsu ya zauna yayi murmushi
ya cekuna gulma ta ko, dan ban kunna muku
kallo bako ? Nusaiba cikin shagwaba tace'' yaya
haisam harkwalla nayi fa wallahi yau duk ranmu
a bace yake. Haisam yayi dariya yace'' kai haba
harda kwalla ?Ke fa hannah kema kinyi kukan ?
Tayi murmushitace a.a banyi ba uncle haisam.
''yaci gaba da jansuda hira yana zolayarsu kamar
yadda ya saba wasada dariya da dukkanin
daliban makarantarmusamman da wadannan
ukun. Ya ce dasu '' ga rauda can a hall tana
cashewa kuje ku tayata manako kuma kuyi mata
liki. Suka danyi dariya suka ce ''mu bama rawa''
suka ci gaba da jugum , haisam yalura yau dai
nusaiba da hannah babu kanta basason magana
balle doguwar hira yace nusaiba,hannah yaya
haka kowacce tayi zugum babu nishadi kamar
yau ba ranar social night ba. Nusaibatace''yaya
haisam tsabar bakin cikin rashin kallonnan ne
yake damunmu.'' yace shi yasa baku fara'a?To
yanzu daya bayan daya sai kun yimin waka
darawa tunda yau social night dole kuyi murna''
cikinshagwaba nusaiba tace''yaya ni bana iya
waka ba sai dai hannah ta fara tunda itace
karama. Hannahtayi dariya tace to bari inyi muku
wakan sarkingarinmu,'' hannah ta fara tafi ta
fara rero waka.Haisam yace'' to tsaya tafi akeyi
muma mu dingatayaki muna muki amshi ? Tace''
ai da kwarya akekida dan dai babu kwaryar ne.
Yasa hannu a aljihunsa ya zaro wannan abun
busar daya karba awajenta ya ce zai ajiye mata
ya ce'' ga abun busarkima ki busa mana ki rero
mana wakar kiwo'' cikinfarin ciki hannah ta karbi
abun busarta ta haujujjuyashi tana cewa'' allah
sarki abun busata nadade ban busa kaba,''
nusaiba tace '' lah busa muji yadda akeyi''
hannah ta kaikaice ta fara busa abunbusarta
tana rera waka kamar haka. muyi kiwosamari.
Kuyi kiwo yan mata kiwo baiwa ne. Wakabaiwa
ce. Haka busa ma baiwa ce kuyi soyayyasamari.
Kuyi soyayya 'yan mata ke 'yar budurwaina naki
gwanin ? Ni nawa gwanin baya nan. Yayi tafiya
amma koda bana tare da gangar jikinsa.Ruhinsa
yana tare dani. Haisam yace '' hannahtsaya meye
koda gangar jikinsa bata tare daniruhinsa yana
tare dani ''? Tayi shiru can tace ohonima haka ya
mun wakar nusaiba tace meye ''ruhi ? Hannah
tace '' nima ban sani ba, ina jin larabci ne ,
haisam yayi dariya ya ce '' yarinta mai dadi.
Kwanci tashi yau kwanan hanna arba'in
amakaranta har an kafe musu tine table
dinjarabawa wato end of 1st teem
examinationkasancewar daman dalibai sai da
suka yi kimaninwata guda da dawowa makaranta
sannan akakawi hannah babu abunda yaya
haisam yake yi sai nasihohi da yake yiwa yan
ajinsa wato j.s.s 1a dakowacce ta cire wasa tasa
littafin karatu a gabantadon suci jarabawa. Haka
kuma wasu lokuta ya kankira kannansa rauda,
nusaiba da hannah yanakara musu fada dasu
dage sufi kowa cin jarabawaya sake xewa''
hannah bana jin fargabar su rauda kamar ke don
haka ki dage duk abunda ba ki saniba ki tambayi
nusaiba ko rauda idan sun sani sukoya muki,
idan kuwa basu sani ba to kuzo kutambayeni.
Haisam yayi musu rantsuwa da allah acikin su
ukun nan duk wanda ta fadi jarabawartasai yayi
mata bulala kuma daga ranar data fadi jarabawa
babu ruwansa da ita ya cireta a cikinkannansa
gaban hanna ya fadi rasa dajin bayaninyaya
haisam tace a ranta tace idan yaya haisa
yacebabu ruwansa dani aina shiga uku tunda
babu maiyimun siyayyar makaranta karshenta ma
karshenkaratuna yazo. Ta kudiri aniyar daga yau
babu ita babu cikakken bacci zata dage da karatu
don tacijarabawa kada haisam yayi fushi da ita. a
sati dayasu hannah suka gama
jarabawarsu,jarabawabibiyu suke a rana daya.
Don haka babu hutu badare ba rana kowacce ta
dukufa da karatu,musamman hannah sallah ce
da cin abinci tashinta daga kan littafin karatunta,
haka kuma ta zanajarabawar cikin sauki ma'ana
da an bata questionpaper sai taga tasan
amsoshin gaba daya, hakatake amsasu cikin sauki
saboda tsaban ta gamakarance litattafanta,
hannah tasan yaya haisamzayyi murna da
sakamakon jarabawarta tunda tayi karatu yadda
ya kamata. Hutu kuma sai juma.a donhaka dukka
wadannan ranakun babu abinda sukeyi sai
wasanni da raye raye da wasanninkwaikwayo na
kungiyoyi (club)din makarantarkasancewar akwai
kungiyoyi daban daban amakarantar kaar english
club, hausa club, jet club. Che,ical club,
geography club. Yoroba da igbo dadai sauransu,
kuma kowacce daliba daga yar ajidaya zuwa shida
tana da damar da zata shigakowanne club a
makarantar. Su kuwa malamaicikin satin nan suka
dukufa da aikin makinjarabawar dalibai, don
ganin kafin ranar hutu sun bawa kowacce daliba
sakamakon jarabawarta tatafi dashi gida iyayenta
su gani. Ranar alhamis anagobe hutu haisam ya
tara 'yan ajinsa a bakinbabban dakin taron dake
makaranatar wato halldon ya bawa kowacce
sakamakon jarabawarta(report card) 'yan ajin
malam haisam suna da dimbun yawa don dalibai
saba'in da shida ne a ajinhausawa da
yarbawa,igbo,musulmai da kiristocisma da talatin
ba hausawa bane kuma ba kiristocibane, wata ko
zo bata sani ba da hausa, tundadaga kudu suke
babu abunda suka sa a gaba saikaratun littafinsu
don shine abunda ya kawosu tun daga uwa
duniya zuwa nan arewa. Don haka babukoma
baya a ciki kowacce tayi iya kokarintamatuka a
wannan jarabawa. haisam ya kallifuskokinsu daya
bayan daya sannan ya kyalkyaleda dariya. Abun
mamaki babu wacce ta taya shidariya kamar
yadda suke wasa da dariya a aji yau kowacce
fargaban jin sakamakonta takemasamman ma
hanna. Tunanin maganar da yayahaisam ya fada
yayi musu ranstuwa yace dukwacce ta fadi
jarabawa sai yayi mata bulala kumababu ruwansa
da ita. Hakika bata fargabar bulalarsosai tafi
fargabar babu ruwansa da ita din daya fada, idan
haisam ya cire hannunsa akan hannahwaye kuma
ya tsaya mata a duniya yadda takekaunar
makarantar nan aiko hutu bata so ayi.
Watohannah na daya daga cikin yan kwaleji tafi
gidadadi, ga uwa uba kwanciyar hankali wasa
dadariya da kawayenta sabanin a gidansu sai
bauta. Anan makaranta akan sasu aiki ko aike
ammabamai wahala ba kasancewarsu kanana
'yan ajidaya dole seniors zasu aikesu. Haisam
yace ''oh''yau babu dariya duk kunyi cirko cirko
kuna jiransakamako to da yawa daga cikinku
kunyi kokariamma wasu basu yi kokari ba don
haka wadanda basuyi kokari ba sai sun dage idan
ba haka bakarshen shekara za'ayi musu
repeating kowa yawuce aji biyu a barku a aji
daya ku sake maimaitashekara,. Gaban hannah
ya sake fadi ras sai addu'atake sannan taji dan
saukin dukan da zuciyartatake yi mata. Haisam
yace'' yanxu zan fara kiran sunan wadanda suka
yi na daya zuwa uku sai atafa musu zan basu
kuma kyaututtuka sannan nakirawo na hudu
zuwa goma zuma zasu fito a tafamusu sune suka
fi yin kokari sauran kuma sai kudage nan gaba
''hadiyar yawu yake ji mukut mukutdakiban nayi
don faduwar gaba dariya ta sake kecewa malam
haisam ya girgiza kai , sannan yabude file din
dake hannunsa yace'' dalibar datayimatukat
kokari ta zo ta daya itace Rauda shitu muktar ta
kwalla kara don dadisauran suka sa tafi suka juyo
suna mata kallonsha'awa kowacce a ranta tana
dama nice raudashitu a ransu haisam ya ce taso''
fuskarta cike dafara'a zuciyarta cikw da farin ciki
tazo ta tsaya agefen haisam yaci gaba da cewa,
sai kuma wacce tazo na biyu itace nusaiba idris,''
farin ciki ya lullubenusaiba itama tazo kusa da
rauda shitu ta tsayadalibai nayi mata tafi raf raf,
ta uku kuma itacepamella matin benin,pamella ta
daka tsalle danmurna ana tafa mata itama ta fito
ta tsaya kusa danusaiba idris'' hannah na lungu
ta kankame guiwarta da hannayenta ta zura
kanata a matsematsin cinyoyinta yayin da kuka ya
kece mata.Taga kawayenta biyu rauda da nusaiba
wadandasuke karatu tare sun zo sun fita kokari .
Ta gamasaddakarwa yaya haisam ya cire
hannunsa dagakanta tinda batayi kokari ba.
Haisam ya rufe file din dake hannunsa ya kalli
sauran daliban da sukezazzaune a kasa yace''
kunda wadannan ukunsunfi kowa kokari a ajina
don haka zan basukyaututtuka da zasu je gida su
nunawa iyayensusuji dadi , bawai su daban suke
daku ba a.a kumakowacce a cikinku ta dage zata
iya zuwa na daya, biyu da uku. Don haka duk
wacce take so itamanext term taji sunanta a cikin
wadannan ukun to tadage da karatu. Don haka to
ku sake tafawarauda,nusaiba da kuma pamella.
Tafi raf raf raf yadinga tashi saida haisam yace
ya isa tukunna sukadaina. Ya dauko wata
katuwar anbulan wacce aka like ta da salataf an
yi rubutu da maka dara darakamar haka. FIRST
POSITION IN J.S.S 1A RAUDASHITU MUKTAR ya
mikawa rauda , daliban suna tafamata raf raf
yace taje ta zauna, ya sake dauko watawacce
girmanta bai kai girman na rauda va, itamaan
like jikinta da salataf an rubuta SECONG
POSITION IN J.S.S 1A NUSAIBA IDRIS Ya mikawa
nusaiba akatafa mata ta tafi ta zauna itama. Ya
dauki ta karshenitama girmanta bai kai ta
nusaiba ba, ajikinta anrubuta. THIRD POSITION
IN J.S.S 1A PAMELLAMARTINS BENIN Aka tafa ta
karba da murna ta tafita zauna, haisam yace''to
yanxu san kira na hudu zuwa goma suma su fito
nan su tsaya a tafa musudon suma sunyi kokari
matuka.'' fargaba ta sakedira a zuciyar hannah.
Tace a ranta' idan kumabana cikin mtane goman
nan ni kaina nasan banyikokari ba, shi kenan
karshen makaranta na yazodon nasan tunda
malam haisam ya rantse nasan da gaske yake sai
ya zaneni sannan ya korani gida, tarushe da kuka
dan ta tsani wannan kalman ta gidasaboda
tsananin da ake yi mata da azabtarwa .Baya ga
bautuwa ga horon yunwa, babu wankako tayi
wankan ma kusan daya ne da batayiba,don
wankan babu sabulu, sai wani lokacine idan tayi
wanke wanke dan omo yayi saura takeboyewa
tayi wankan dashi shima a sati baifi sodaya ba
anan kuwa sunkinan sabulu zesr haisamya siya
mata, ga mayukan shafawa iri iri ba kalarkitson
bane ko tayi kitsin kwana biyu ya farazamewa .
Amma yanzu da ta sami mayuka masu sashi yayi
laushi sai take wankewa da man wankegashi ta
mulke da man gashi tasa ribon ta dauretamkar
indiya baki sidik a kwance fatar jikinta tayiluf luf
sumul sumul ba ita ba, ita bata ki har
shekarashida ba'a yi hutu ba . Malam haisam
yaci gaba dakiran daliba ta hudu, ya kira ta biyar,
ta shida hannah bata ji sunanta ba, ya kira
bakwai da tatakwas. Sai kukan da take ya kara
tsananta har nakusa da ita suka fara jiyo
sheshshekar kukan datake yi suna juyowa suna
kallonta, haisam ya kirata tara sannan ta goma
yace '' hannah abubakarimam . Shima sai yayi
ajiyar zuciyar jin dadi hannah ta mike ta taho
idonta tamkar anyi wasan ruwakaca kaca da
hawaye. Haisam ya dafa kanta yacehannah kukan
meye kike shashsheka lafiya ? Yishiru goge
hawayenki kinzo na goma kinyi kokari''dadi da
kwanciyar hankali suka lullube hannahyasa aka
dinga tafa wa daliban da suka zo na hudu zuwa
na goma. Daga karshe yace su koma suzauna
yaci gaba da kiran dalibar data na goma shadaya
zuwa saba'in da shida ta karshen kenan
watagandamemiyar ajin ce tafi kowacce girma a
ajin maisuna eneka eddiward itace tazo musu ta
karshe, dayawan dalibai suka rushe da kuka jin
malam haisam ya furta repeating suna tunanin
shikenanza,ayi musu repeating haisam ya shiga
lallashinsuyana cewa kowa tayi kokari babu wacce
za.ayiwarepeating kasancewar da damar da zasu
iyadagewa nan gaba ba.ayi second term ba balle
thirdterm sannan suka ji dan sanyi a ransu suka
fara goge hawayen daya jika musu ido. Hannah
takoma gefe tana kallon jifgin mutanen data
kayaryayin da zuciyarta take jinjina mata ai kinyi
matukarkokari tunda kin wuce mutane sittin da
shida, farinciki ya lullube zuciyar hannah. Ta sake
sa randawowa makaranta idan hutunsu ya kare
kasancewar taji haisam ya yaba da
sakamakontadon haka zai sake yi mata siyayyar
makaranta dabiyan kudin makaranta da aka ce
duk term akebiya kuma dubunnan nerori. bayan
kowacce tayishiru da kukan da dayawa suke yi sai
haisam yace''duk kunyi kokari kasancewar 'yan
ajin babu marar kokari yace kowacce tazo ta
karshe anan ajin ne ab.c. Ko d ita zata zo musu
ta wajen goma sha waniabu, kunga kowacce tayi
kokari karku damu. Yadauko wata katuwar leda a
gefensa ya ce dai dai suringa tasowa suna
karba.Biscuit nemai dadi ya rarraba musu
kowacce daliba ta samutun daa kan rauda har
eneka eddiward kowacce tafara murnar tayi
kokari. Da haisam yaga duk sunware yana musu
wasa da dariya sai yace'' ina si na shaida muku
daga yau ko kuma ince daga dagagobe ranar
hutu idan na tafi hutunnan shikenan natafi
kenan. Gaban kowacce ya yanke ya fadi.
Bamugane ka tafi ba kenan uncle haisam '' su
duka sukatambaya . Haisam yayi murmushi yace
''kun san nicopper ne. Nazo ne yin bautar kasa
wannan makarantar(N.Y.S.C)KUMA yanxu lokaci
yayi damuka kare don haka idan na tafi hutun
nan bazandawo makarantar nan ba. Ina muku
fatan alherikuma shawara nake baku akan
kowacce ta dagetayi karatu banda wasa ''
kowacce jikinta yayi sanyifuskarsu alamar basu ji
dadin wannan batu na class master dinsu ba .
Suna son haisam saboda kula dasoyayya da yake
nuna musu wasa da dariya akoda yaushe sai
wasu dayawa daga cikinsu sukarushe da kuka.
Babu kamar rauda, nusaiba dahannah, ai kuma
gara rauda da nusaiba akanhannah wani sabon
tashin hankali ya rufta mata fiye dana dazu.
Haisam zai bar makarantar nan itakuma ina zata
dosa ?''.Haisam ma wani tsananin bakin ciki ne
yamamaye a zuciyarsa yana tsananin son yan
ajinsa.Baya so ya tafi ya barsu yana
tausayinsukasancewar yan yara babu kuma wani
malami komanyan daliban da zasu zauna suna
basushawarwari kamar hannah, wa zai kula da
hannah? A bar zancen kudin makaranta da
siyayya(provision )ita kanta tana bukatar a kula
da ita dakara karfafa mata gwiwa wajen idan ta
tafi hutugida ta dawo makaranta. Koda a gida an
ce baza tadawo ba tasa kuka har sai an dawo da
ita. Ga wasuabubuwa da suka yi mata nauyi a aji
ma'ana bata ganewa sai shi haisam da kansa
yake nunnunamata har sai ta gane. Allah sarki
hannah ya fada azuciyarsa ji yake kamar ya
rushe da kuka dantsananin bakin cikin rabuwa da
dalibansa. Ammaya daure ya dinga lallashinsu,
idan wadannnansuka yi shiru sai wadansu su
rushe da kuka. Haisam har ya gaji da lallashi
yace su tashi su tafidakunansu sai gobe zasu
hadu a wajen assemblyhutu, suka nufi
dakunansu kowacce na sharbehawaye. Haisam
kuma ya nufi gidansa dake staffqurters yana mai
matukar jin ba dadi a ransa. Kowayayi shiru ya
daina kuka amma banda hannah. Nusaiba da
rauda suka dinga lallashinta amma takidainawa
taki cin abinci sai tayi kamar tayi shiru tadaina sai
ta tuna ta rushe da kuka. Haka ta yini curtana
kuka. Rauda tace waini hannah kukan nan dakike
yi kinfi kowa son yaya haisam ne ? Ni fa
munfikusa da shi babana abokin babansa ne.
Kuma yayana auwal abokinsa ne. Haka kuma
yata ywadaya uba daya ramla budurwarsa ce
koma nacematarsa ce don har ansa musu raba,
sanda mukeamerica yan gidansu a gidanmu suke
sauka insunje kuma da muka dawo nan kasar
saboda yayahaisam ma aka kawoni makarantar
nan tunda yana malami yace da abbana
makarantar akwai karatu.To harni na hakura na
daina kuka ke ba za kihakura ba kamar kinfi
kowa sonsa. Ya ce dai kekanwarsa ce kuma ni a
sanina 'yan uwansa duk akano suke na sansu
kuma amma ni ban sanki ba.Kuma duk yan
uwansa babu masu kama dake ke kamar
balaraniya kike ko buzuwa ce ni ban saniba''
nusaiba tace'' haba rauda meye haka in ba
yaruwarsa bace zai fada ne ? Hannah ta sake
rushewada kuka. Daman abunda rauda take yi
mata yaisheta. Tunda aka kawo ta malam haisam
yacekanwarsa ce taga rauda tana kishi da ita. Wai
ya za ayi ace hannah kanwar yaya haisam ce
bayan itakadai ce kanwarsa a makarantar. washe
gari da sassafe dalibai suka shirya kayansutsaf na
tafiya gida suka saka kayan makaranatar(uniform)
suka dunguma babban dakin taro (hall)don yin
assembly hutu. Hannah nusaiba sukakinkimo
jakunkunan kayansu na sakawa sukakuma
rarrataya jakar litattafansu a baya. Akwatinsu
kuwa da katifu da bokitai a wani daki ake
lufgawaa rufe. Ba.a tafiya dasy gida. A bakin hall
din sukaajiye jakunkunan sannan suka shiga cikin
hall dindan yin assembly. Kallo daya haisam yayi
wahannah yasan tasha kuka kuma tana cikin
tashinhankali . Principal ta sanarwa dalibai cewa
an basu hutun kwana arba'in da biyu. Don haka
ranar dakwana arba'in da biyi ta cika kowacce
daliba kadata kara ko kwana daya. Idan ta kara
to za.a koratagida. Baza a karbeta ba. Sannan
tayi musu nasihohiakan idan