Showing 24001 words to 27000 words out of 31410 words
Chapter 9 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete
kanta ta bude ido sai taga
raudaamurtuke. Tayi furgigit ta tashi zaune tace''
rauda har kun dawo? Rauda ta kaste ta
tace''haka zaki cemana har mun dawo da acan
zamu kwana? Komuma son maso wani muke yi
da zamu bishigidansa? Yaya haisam dai yana da
wacce yake sokuma an gama magana gara
kowacce ta komakauyenta ta sami wani bakauyen
ta aura amma haisam sai ramla. Hannah tace''
rauda me ya faru ,wani abun akayi ? Nusaiba
tace'' ke rauda meyehaka wasan kwaikwayo ne fa
kowa yasan gwajine ba gaske bane. Wai ke rauda
me yasa bakya sona zauna lafiya ne ? Rauda tayi
tsaki ta fice tana cewa'' duk gulmace gulmacen
da ake ina sane. Dan iskan kauye yafi na burni
iya iskanci da rashinmutunci ai. Hannah ta fashe
da kuka, tayi kuka kamar ranta zaifita. Nusaiba
na lallashinta da kyar hanna tayi shirusuka je
suka yi alwalar magaruba. Bayan sallarisha'i
sunci abinci karfe takwas dai dai sai suka jesuka
kora dalibai kowacce ta fita ajinsu don yinprep
din dare, uncle haisam ya fito daga gidansa
takwas da rabi yazo ya kirawo yan hausa club
donsuzo su karasa gwajin wasan kwaikwayon da
sukeyi. Ta bayan wundo ya hango rauda tsaye
akanbencin hannah tana ta gurza mata rashin
mutuncihar cewa take da ba'asam asalin balbela
ba sai tacemadina ne garinsu. Yaga hanna zaune
tayi shiru tana hawaye, ran nusaiba ya baci ta
taso tashigarwa hannah kamar zasu daku da
rauda. Saihaisam ya leko ta wundo yayi musu
tsawa ya ce sufito waje yana son ganinsu. suna
zuwa gabansa kallo daya suka yi masa sukasan
babu wasa yau a murtike yake kasancewarsunsan
bacin ransa babu kyau sai kowacce ta fararawar
jiki. Ya daka tsawa yace kowacce tayi kneeldown
bayan sun yi ne ya tambayi nusaiba me yafaru.
Nusaiba ta zaiyana masa dukkan abunda ya faru
tsakanin rauda da hannah tun daga yammahar
na yanzu ya juya ya kallo rauda yace''
raudahakane ? Ta gyada kai gami da tabe baki
tace''haka ne kuma gaskiya na fada'' haisam ya
fusataya kaiwa rauda mari tayi sauri ta kwanta a
kasa baisameta ba. Tace' yaya haisam yau ni
zaka mara akan hannah? Haisa yayi shiru
hannayensa a cikinaljihu kansa a sunkuye a kasa.
Can ya dago yace danusaiba ta tashi ta shiga aji.
Ya dubi rauda wacce kedurkushe a kan gwiwarta
a gabansa rauda tarushe da kuka. Haisam yace''
rauda tun ba yau ba,tun kuna aji daya na lura
kin kafawa hanna karan zuka a makarantar nan.
Yanzu kece kadai kikarage a cikin masu takurawa
hanna zan iya daukankowanne irin mataki a kanki
muddin baki fitaharkar hannah ba ki kiyae, idan
kuma kin ki ni zanfiki farin ciki don zaki ga
abunda zan zartar a kanki.Ko amratu 'yar shekara
bakwai zan iya.hukuntata muddin ta nemi
takurawa hannawannan alkawari nayi wa allah
kuma sai na cika shidon hanna amana ce a
wajena'' kamar a mafarkirauda take jin kalaman
yaya haisam, tana fada aranta lallai abun nasa
babbane da gaske yake'' daga karshe ya ce ta
shiga aji tana sharbar kuka tamike a fusace ta
shiga aji. Ya shigo shima ajin yakalli hannah
wacce ido yayi mata jawur don kukayace hanna ki
kira sauran yan hausa club ku tahohall ku sameni
mu karasa rahazal din. Cikin ladabihannah ta
amsa masa. Ya fita ya nufi hall. Hannah cewa''
rauda muje hall yaya haisam na kira'' tadago ta
harari hannah tace'' bazan je ba kuma nafita
daga club din ko za'a sani dole ne? Hanna zatace
wani abu nusaiba taja hannunta tace ''kyaletamu
tafi mu kira sauran. Hutu ya kusa karewa har
ana shirye shiryen farafirst term examination.
Kowacce karatu takehaikan, sunyi jarabawa an
basu sakamako kafinranar hutu. Hannah ce tazo
ta daya a ajinsuwannan karon, rauda ta biyu
nusaiba ta uku ranarhutu bayan anyi assembly
hutu da wur wuri kafin kowa ya fara tafiya
haisam yazo ya sami hanna,rauda nusaiba da
wasu kawayensu a zazzaune akan barandar hall
suna ta hira. Bayan sun gaisheda shi sai ya ce''
hannah taso ga safiyanu yazodaukarki, idan muka
saukeki a gidan uwar biyuzamu wuce dashi dan
musa can jahar katsina acan yake neman aure
zamu kai kayan gaisuwarsurukai'' su duka suka
kyalkyale da dariya. Hannahtace ''oh yaya
safiyanu daman aure zai yi ko ya fadamana
sunanta ranar nida nusaiba muka ga hotontaa
motarsa muka ce budurwarsa ce ya ce wai shi
babudurwarsa bace'' nusaiba tace'' haka ne kuwa
a bayan hoton an rubuta dan musa har nake
cewadan musa kuma sunan mace dan musa ya
ce ehhaka sunanta. haisam yayi dariya , sannan
ya juya ya kallo raudatasha kunu ta kawar da kai
gefe daman tundaakayi wannan abun bata cika
yiwa hannahmagana musamman idan taga
haisam da hannah.Ga uwa uba hannah ta kwace
mata position tazo tadaya , sai take jin haushin
kamar ta kashe hannah. Haisam ya ce'' rauda ni
ba kano zanje ba sai mundawo daga danmusa
don gida ma nace kada aturomun da mota auwal
zaizo daukarki ko direba?Tace '' sai dai direba
yaya auwal yanamaiduguri''yace''oh haka ne fa,
to ki gaishe dasuhajiya sai wahen jibi zanzo
kanon. Idan muka tafi yau ba damar muyi tafiyar
dare dole mu kwanasannan washe gari mu dawo
kazaure wata kila inkwana a cikin gari jibi muje
kanon da safiyanu .Rauda tace zasu ji . Allah ya
kiyaye hanya. Hannahta kira wasu juniors suka
dauki jakunkunanta sukazuba mata a mota. Tayi
wa kawayenta sallama tana zolayarsu su tana
cewa yau itace farkon tafiya dukmakarantarn ta
barsu su yan kwantai ne. Rauda tatabe baki
tace'' yanxu wata kila har kowa ya isagida ke baki
isa gida ba, saboda hanyar garinkukwalta ce
sambel ba kasa ba'' hannah da nusaibane kawai
suka gane rauda bakar magana ta fada, wato
hannah bakauyiya cekenan take nufi saihannah
tayi murmushi kawai ta tafi ta shiga motatana
dagawa nusaiba hannu har suka fita get . a gidan
uwar biyu su haisam suka sauke hanna ,haisam
ya shiga cikin gidan bayan ya bawa uwarbiyu
kudaden motarsu da wanda zasu kaiwamahaifin
hannah suka yi godiya yayi musu sallamaya juya
ta tafi har yaje kofar fita ya juyo yace '' koyanzu
zaku tafi mu ajiyeku a tashe'' hannah tayi sauri
tace yaya haisam da yamma zamu tafi ina soinje
gidajen kawayena a nan cikin gari. Yayimurmushi
ya ce'' wato akuyar daure ta samu sake,su
hannah an iya yawo ko? Su duka suka yi
dariyasannan ya fita. Damisalin karfe biyar uwar
biyu dahannah suka isa babban mutum , suka je
suka iske gida a hargitse anyi tashin hankali.
Malam habumahaifin hannah kuka wiwi. Cikin
rikice da rudanihannah ta tambaya meya faru
babanta yake kuka.Iya abu ta tuntsire da dariya
tayi buda da shewatace'' tambayi ubanki.
Karshen tuka tiki tik yauallah ya nuna mana
gaskiya'' hankalin hannah da uwar biyu ya sake
tashi sosai, suna so suji me iyaabu take nufi da
wannan habaici nata. Malam habuya sharbe
hawaye da babbar riga ya ce''muje zaurein fada
muku abunda ya faru'' da yake damantsakar gida
suka iske su. Suka je zaure sukazazzauna
malamhabu ya nisa gami da langabar dakai yace''
idan ka haifa dole a jawo maka, damanance dan
kuka shi ke jawa uwarsa zagi. Uwar biyu
dahannah su dai sun kagu suji abunda ke
faruwayace'' yanzun nan babu dadewa watakila
kunhadu da wata bakar katuwar mota a hanyar
shigowa garin nan wata fitsararriyar yarinya
cetazo ta cimun mutunci a kofar gidan nan har ta
taramun mutane. Hannah tace''wacece baba?
Cikinrudani da fargaba ta tanbaya. Ya ce'' farko
da tazosai ta tsaya ta karemun kallo a wulakance
sannantace naji kunya wallahi yasa naji kunya.
Dama yarinyar yar talakawa ce yake bata mun
lokaciakanta to baba bari in fada maka ka jawa
yarkahanna kunne ta kiyayi mijina idan ba haka
ba nizan zamo ajalinta domin zan iya kashe duk
yarinyarda zata rabani da haisam abun sona.
Kuma ka cireyarka daga makarantar nan domin
idan bata bar makarantar va haisam ba zai bar
makarantar ba yarabu da ita. Muddin hanna ta
sake komawamakarantar to kuwa har makarantar
zan bita inzartar da abun da na yi niyya. Ba tana
takama itakyakykyawa bace to zan kwara mata
wani abuafuskarta {acid}fuskar ta sale ta
kwakwkwabe har makarantar zan tarar da ita in
yaso sai inga fuskarda zai sota. Don soyayya
hannah take yi da mijinava karatu ba. Har
sakamakon jarabawar kanwatayake dauka ya
bata tazo ta daya a ajinsu. To na gajiwannan
shine lokaci na karshe dana bawa hannahidan
taki ji ta koma makarantar to wallahi ta kuka da
kanta'' malam habu ya sharbe hawaye yaci
gabada cewa'' da wata kanwarta yar makaranta
tanasanye da kayan makaranta irin naki yar baba
itamatana taya ta suka yimin tas, iya abu na ihu
tanadariya tana cewa daman ta sani ba tun yau
bahanne karuwanci aka kaita tayi ba makaranta
ba yanzu gari duk ya dauka maganar ake yi don
agaban mutane aka yi haka. Tace hannah taci
sa'ada bam sameta ba da sai ta faffalla miki mari
sannansuka shiga mota suka tafi. Hannah bata
iya cewakomai ba sai ta sunkuyar da kai kasa
tana kukamalam habu ma kukan yake uwar biyu
ta matse hawaye tace'' kuyi shiru, ku daina kuka
wannanduk abune na shirme da karya ita
wannan yarinyardata zo ina tunanin matar da
malam haisam zai aurace take ganin son hanna
yake alhali kowa yasanhaisam a matsayin yaya
koma ince uba yake awajen hanna tun tana
karama fa inah, ai zancen so ma bai taso ba.
Hannah karatu take a makarantababu wata
soyayya daga wannan hutun ma bazasu sake
dawowa har sai sun gama makarantar makwata
kwata saura wata bakwai su gama. malam habu
ya zabura yace'' wacce komawa aihanne tazo
kenan baza ta koma ba ina wanizancen saura
wata bakwai hanne ta gama aikosaura kwana
bakwai ne hanne ta gama karatuntabayan a
gaban mutane aka ce ba karatu take yi
amakarantar soyayya take yi sannan in bar yata
ta koma ai sai a dinga cewa tana can tana iskanci
harwata bakwai ba ta komo gida hutu ba, ni
daiabunda zance muku uwar biyu ke da wannan
yarohaisam allah yayi muku albarka amma hanna
bazata sake koma wa ba karatun ya isa haka
dukkawayenta harma da kannanta duk sunyi
aure gara itama in hadata da wani a dangi tayi
aurentabaki alaikum kafin a kone mata fuska.
Damanabunda muke ji a redio gaskiya ne ace an
fesawawani ko wata wani ruwa a fuska ya
kwakwkwabogaske ne to ba zai faru akan hanne
ba. Karatun datayi na baya ya isa nagode
madalla'' cikin rudewa uwar biyu tace'' haba
malam habu yaya zaka yimana haka ? Baka
kyauta masa ba yarinyar nanduk zance take
haisam ba zai barta taje gurinhanna ba balle tayi
mata wani abu. Bama a barinkowa yaga dalibai in
ba ranar bisitin ba dokarmakarantar ce'' malam
habu ya mike ya shiga gida yana cewa'' nifa na
gama maganata uwar biyu kiyihakuri ki bar
maganan komawar hannemakaranta. Ai ko karan
hauka ya cije ni ba zan baryata taje inda za'a
halakata ba ina hanne ina kishida wadannan
gogaggun yan burnin masu kudi.Tunda tana
ganin mijinta son hanne yake ai sai a hakura da
taimakon na baya ma allah ya saka'' yashige ya
bar hannah tana matse hawayen dakeidanuwanta
da wani farin hankici dake hannuntatace uwar
biyu'' kyale shi ya tsorata ne kafin hutuya kare
zai yadda idan na wayar masa dakai ahankali na
lallabashi sai dai idan hutu ya rage sati guda kizo
don muji mai zai ce in yaki yadda sai daiyaya
haisam yazo ko kuma ya turo principal idankuma
yaki yarda na shiga uku karshen karatunaya zo.
Hannah ta rushe da kuka, uwar biyu tace ''yadda
za'ayi shine haisam zan turo yazo garin
nanmahaifinki ya kalli kwayar idonsa ya ce ya
hanaki ki koma makaranta, haisam zaizo da
kansa. A hakahannah da uwar biyu suka yi
sallama. Hanna tayitayi da uwar biyu ta shigo
cikin gida ta huta sannanta tafi uwar biyu tace
baza ta shigo ba ina zata iyashigowa wajen iya
abu masifaffiyar matar da zataiya kashe mutum
ma don rashin imani. Hannah ta raka ta har
tasha ta shiga mota sannan hanna tadawo gida.
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 4
Posted by ANaM Dorayi on 02:25 PM, 30-Apr-15
Under: Gangarjikinsa ta Aura
A zaure malam habu ya shimfida tabarmar kaba
dawani yagulallen filo da zanin gado irin na da da
dadinnan shekara aru aru da suka shude. Nan
neshimfidarsa da yake kwana nan ne dakinsa
danduk dare duk sanyi da damuna a nan yake
sabodaiya abu ta mamaye dakunan gidan.
Dakinsa din ya barwa hanna data girma ya dawo
zaure don da datana yarinya tare suke kwana a
dakin. Ko dayaushe hannah zaka ganta a zaune a
gefenbabanta tana lallashinsa tana wayar masa
dakaigame da makarantarsu. Tana nuna
masamuhimmancin karatu da kuma irin bacin ran
da haisam zaiji idan bata koma ba.Ta kwashe
labarun abubuwan da suka faru tuntana aji daya
har tazo aji shida yadda haisam yakekula da ita
da irin tataburzar da aka sha yi akantada dalibai
da malamai har ya kwatar mata yancintababu
mai dukanta ko zaginta yanzu, kuma yayialkawari
zai iya kashe ko waye yake son ya takura mata.
Malam habu ya gamsu sosai da bayananhanna
ya kuma san haisam ba zai yadda a cuce taba.
Hutu ya rage sati guda sai ga uwar biyu ta dira
agarin su hanna ta iske hanna da mahaifinta a
zaurea zaune zance daya dai suke ta nanatawa
kullumshine zancen ya barta ta koma makaranta.
Bayansun gaisa da uwarbiyu ta fadi abunda ke
tafe da itacewar tazo ne ta tafi da hanna hutu ya
kare sai malam habu ya kekashe idanuwansa ya
ce shifababu inda hanna zata je. Hanna tayi
mamaki da tajiya fadi haka yanzu bayan da ya
yarda da tayi masabayani sai kawai hanna ta
rushe da kuka, magiyarduniyar nan uwar biyu ta
dinga yiwa malam habuamma yaki yarda daga
karshe uwar biyu tayi musu sallama ta tafi. Tana
isa kazaure ta wuce gidan susafiyanu abokin
haisam bata sameshiba ance yanakano sai ta
koma gida ta zuba ido ko allah zai jehomata
haisam ko safiyanu idan zasu kawo
sayayyarhanna ta makaranta tunda sunsan hutu
ya karezasu kawo. Har ana gobe a koma
makaranta uwar biyu bata ga safiyanu ba balle
haisam. A can kuwahanna hankalinta ya gama
tashi taji shiru yayahaisam baizo ya taya ta rokar
babanta , sai ta daukashima yayi fushi ne yace to
a bar masa 'yarsa kartayi karatun mana. Da
la'asar likis hanna damahaifinta suna zaune akan
lintsimemiyar tabarmar kaba a zauren kasa da
rufin ciyawa hanna kukatake yau tun safe. Malam
habu lallashin duniyar nantayi shiru ta hakura
tama cirewa ranta makarantardon shi ya gama
magana bazata koma makarantaba . Taki ci taki
sha sai kuka take rafsawa. Kwatsamsuka ji
sallama daga idon na da hanna tayi sai tayi ido
hudu da yaya haisam , safiyanu da uwar
biyusuka yi sallama suka shigo. Da sauri hanna
tadauko musu tabarma ta shimfida musu
sukazazzauna ta koma ta dauko musu ruwa a
randacikin kwanan sha. Ta kawo ta durkusa kasa
tagaishe su ta koma gefe ta zauna. Murna ce ta
rufe malam habu yama rasa inda zaisa
wadannanmanyan baki, yan gayu, ya lalubo kudi
a aljihunsaya ce da hannah tayi maza taje bakin
kasuwa tasuyo musu fura da nono, su haisam
suka ce kaihaba ai su a koshe suke ya barshi
kawai. Bayansun gaggaisa malam habu ya gama
yi musu sannu da zuwab da tako kare sai
safiyanu ya nisayace''baba munzo ne mu ba da
hakuri akan dalilinda yasa ka hana hanna zuwa
makaranta. Shinemuka zo da kammu mu roke ka
baba duka dukasaura wata nawa ne yanzu hanna
zata gamakaratunta ta dawo gida'' nan da nan
malam habu ya canja fuskar fara'ar dayake ta
gushe yace''wai me yasa kuke sani inamuku kin
kyautatawa ne ? Bana so ku tambayeniabinda zan
kasa baku na gama magana don allahdon annabi
ku bar zancen karatun 'yar baba. Nayanke
shawara ba zata koma ba. Haisam kokarin da
yake yi allah ya saka maka hakan ma ya isa basai
ta kara yin wasu watannin ba. Nace uwar biyuta
yi maka godiya ka cika min alkawarin da kadauka
wallahi ko bata karasa ba ai ka cika alkawariba
laifinka bane. Alkawari da amana ai ba
karaminaiki bane cika su amma cikin yardar allah
ka cika dai dai ubangiji ya saka maka da gidan
aljanna.Amma hanna ba zan bari ta koma ba.
Haisam yayidan murmushi game da gyaran
murya ya ce'' aminbaba, amma idan baka manta
ba a ranar dana karbiamanar hanna nayi
alkawarin hanna zata yi karatuto kai ma a lokacin
kayi min alkawari,kaga alkawari girma ne de
dashi baka cika ba, kayi min alkawarinzaka bar
hanna tayi karatun don sai dama nasakayi
alkawarin zaka dinga turo hanna makarantabaza
ka hana ta ba wataran sannan nayi
makaalkawarina. Malam habu yayi shiru zuwa
wani danlokaci can ya nisa yace'' anyi haka yaro
haka akayi nayi maka alkawari to ammma ai
abinda yarinyarnan tace gargadi fa tayi min akan
kada in kara tura'yata makarantar nan kaga ai
kome tayi mata batada laifi nine ban ji ba kenan''
haisam ya katseshiyace'' kare lafiyar hanna da
duk wani abinda zaicuce ta yana daga cikin
amanar dana dauka in allah yaso babu mai yiwa
hanna wani abu. Ramla kuwata fada ne kawai a
cikin bacin rai amma babuabinda zata yiwa
hanna, a ina ma zata ganta balletayi mata wani
abu ? Ta dai fadi son ranta dontatsorataka kaga
baba kuma abinda ta fada ba hakabane hanna
karatu take haikan a makaranta, kanwa ce hanna
a wajena ni ne mai tsawatar matama misali da
ace tana soyayya da samari amakarantar . Baba
mu canfa akwai doka babuyadda za'ayi malami
yayi soyayya da daliba, babukuma yadda za'ayi
wata ya shigo cikin makarantardauke da wata
guba taje ta cuci dalibai don haka baba ka
kwantar da hankalinka ni da kai duk mucika
alkawuran da muka daukarwa allah''.Malam habu
yace ''to shikenan allah ya taya mucikawa. Hanna
dauko kayanki ku tafi allah yakiyaye hanya''suka
duka suka ce amin''sai murnata dira a zukatansu.
Cikin farin ciki da jin dadihanna ta shiga ta fara
hado kayanta ,iya abu tayicaraf ta fito daga
bayan kyauren da take labe ta hau malam habu
da fada'' au yarda kayi dawannan dadin bakin da
suka yi maka. Duk wannangaskiyar data baiyana
yarinya iskanci suke amakarantar don yana aiko
maka dana goro shinekaki fadar allah saboda
abun duniya ? Kallo dayahaisam yayi mata yaga
irin wadannan mutane ne masu abun haushi
masu kama da aljanu munanamasu bakin hali
yaji ya tsani iya abu har baya so yakara kallon
fuskar shegiya. Hannah ta ratayajakarta ta fito ko
kallon iya abu bata yi ba balle tayimata sallama.
Ta duka ta yiwa babanta godiya tayimasa sallama
ta wuce cikin mota. Haisam ya danko kudo mai
yawa ya ajiye a gaban malam habu.Safiyanu ma
haka ya debo kudi ta ajiye masa sukayi masa
sallama dukkaninsu yana godiya sunagodiya suka
shiga mota suka tafi. Ba safiyanu bahar haisam
yaji ya sake tausaya rayuwar hannasaboda ganin
yadda gidansu yake. Gidan kasa ne anyi masa
katanga da kara rufin azara abin dai abintausayi
talauci dai tsagwaransa. Babu abinda zakadaga a
gidan ka sayar dashi dari biyar komai ragaraga
kaico!hannah na komawa makaranta tasalittafinta
a gaba tahau karatu. Sune yanzu masushirin zana
s.s.c.e don haka babu wasa sai karatu. kwance
tashi su hannah sun fara jarabawarsu takarshe
[s.s.c.e} saboda daman tuni sun gamatsarge
karatu. Sai suka ga cin tuwo yafi jarabawarwuya
sai kawai suka hau fede ta. Geography dinmalam
haisam itace wacce suka yi ta karshe damisalin
karfe hudu na yamma suka gama daman
jakunkunansu su suna baki hall din da
sukejarabawar suna fitowa sai kowacce ta dauki
jakartasai tafiya daman kowacce ta kagu taje gida
taga'yan gidansu basu taba irin wannna dadewa
amakarantar ba har watanni bakwai a
makaranta.Hatta hanna da bata so ayi hutu
itama yanzu so taje gidq taga mahaifinta sai
mafarkinsa take kullum takwanta barci. Hanna da
kawayenta sun sha kukanrabuwa musamman ita
da nusaiba sun saba sosaigashi zasu rabu. Gashi
kuma babu waya a garinsuhanna balle su dinga
gaisawa a waya. Rauda ma tarungume hanna
tana kuka taji duk babu dadi yanzu da zasu rabu
kuka wiwi juniors suke yi narabuwa da seniors
dinsu zasu tafi su barsumusamman hanna basu ji
dadin rabuwa da ita basaboda tayi musu mutunci
samun shugabar dalibaiirin hanna sai an bincika.
Ta koya musu abubuwana cikin kungiyoyinsu
{club}na makarantar. A haka kowacce ta tafi gida
kuka wiwi. Safiyanu ne yazo yadauki hanna ya
kaita gidan uwar biyu. Yau haisamtun kafin su
shiga jarabawa yazo yayi musu sallamaya koma
gidansa ya rufe kansa kansa ko wajen daake
bankwana bai zo ba saboda tsananin bakincikin
rabuwa da yan ajinsa da yake matukar so. Gidan
uwar biyu ma sai washe gari yaje ya samuhanna
a can. Bayan