Showing 3001 words to 6000 words out of 31410 words
Chapter 2 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete
dawo? Yayi murmushi ya ce "Ina ganin
kakawo duk abubuwan da aka ce ta siya da
kudinmakaranta zan yi kasada na karbeta yanzu
in yasoranar litinin wato gobe idan mutum yazo
ya rubutarisitai yanzu sai nayi magana da masu
gadin get dinHostel su kirawo prefect din....
Malam Habu ya matso kusa dashi ya ce "Yaro
fadamin da Hausasosai na gane me kake cewa?
Har da wani abu dazan kawo nan gaba? Ya ce
"Eh Baba, ai a rubuce ajikin takardar aka rubuta
za'a dinka mata kayanmakaranta har kala hudu,
wanda zata sa idan zasuaji da wanda zata saka a
dakunansu, dana wasanni (sport) duk an rubuta
kuma lallai-lallai sai da kayanmakaranta za'a
karbeta ba zata ta saka kayan gidaba, sannan
daga karshe aka rubuta zata zo dakudin
makaranta (school fees) shi kuma dakesabuwar
zuwace sai kun biya sama da dubu.....Malam
Habu ya katse shi da sauri ya ce "Tsaya yaro
karma ka kirawomin wadannan dubunnai. Ta
faruta kare wai anyiwa mai dami daya sata, yaro
nagode madallah, sai anjima. Malam Habu ya
juya batare da ya jira amsa daga bakin saurayin
nan ba yadoshi inda Hanne ke zaune da saurinsa
kamar zaikifa cikin gaggawa, ya ce "*Yar Baba
tashi maza mu tafi ga magariba ta kawo kai. Cikin
sauri ta mike yaciccibi akwati ya dora mata akai
ya sungumi bokitida katifa suka kama hanyar get
din fita. Sunyi takudaya biyu sai sai suka ji
magana kamar daga samaance "A'a Baba ina
zaku kuma? Su duka suka juyadan ganin mai
maganar sai suka ga wannan kyakkyawan
saurayin ne ya taso yazo wajensu.Malam Habu ya
ce "To yaro me zamu yi in ba tafiyaba, dubunnan
kudi fa naji kana kira, kuma ka tsayacak ka
kalleni dani da dubu daya ma waye ya ajiyewani?
Daman kansilan garinmu ne da maigari sukasani
dole na kawo *yar nan makaranta, suka ce za'a
aiko da kudin, na tabbata har ga Allah basusan
kudin yakai dubunnai ba da suma basu tankaba.
Kuma kudin gwamnati ba'a bashi babu
yaddaza'ayi nazo na ajiye yarinya a makaranta
babukudin makaranta babu kayan makaranta na
ce abimu bashi zamu kawo ba. "Wannan ba zai
yiwuba, inji saurayin. Malam Habu ya ce "To ka
gani cewasuka yi na zo na kawo ta za'a aiko da
kudin kumayadda naji kalamansa shi kansilan a
tunaninsakudin makarantar bai wuce dari uku ba,
bai sandubunnai bane kuma koda shine yazo ya
kawotaaka kira dubunnan nan cewa zaiyi ta fasa
karatun. Don karamar hukuma baza ta biya
wadannanmakudan kudin ba.Saurayin nan yayi
murmushi ya girgiza kaiya ce "Amma Baba bai
kamata daga kirandubunnan nan ka kwasheta
haka da sauri kacezaku tafi ba. Malam Habu ya
fara jin haushinsaurayin nan, ya ce a ransa "Wai
shin wannan dukzancen nan da ake bai gane ba
ne? Makaranta sai da kudi kuma babu kudin jiran
me zanyi, ko shi baisan babu ba ne? Saurayin
nan yaci gaba da cewa"Baba kuzo ku ajiye kayan
nan bai kamata ka juyada yarinyar nan ba, ai bai
kamata ba. Ta cimakaranta har kun shigo cikin
makarantar sannanku kwasa ku tafi ka ce ka fasa,
babu fa abin da Uba zai yiwa *yarsa a duniya in
ba ya bata ilimi ba,yarinya kamar wannan ai
kamata yayi tanamakaranta tunda bata isa aure
ba, me zata yi agidan? Malam Habu ya sake jin
haushin saurayinnan kamar ya doke bakin da
yake masa wadannankalamai ya ajiye bokiti dake
hannunsa ya ce "Yaro, wai shin a harshen Hausa
idan akace babu me akenufi? Yayi murmushi ya
ce "Baba kenan, na gameduk dalilan da kake
nuna min yanzu, ni kuma abinda nake so na
rokeka shine ka fasa tafiya da itatunda ka kawota
har cikin makarantar ka kyaletatayi karatu. Abun
da ya kamata ka tambayeni shine tayaya zata yi
karatu tunda babu kayan makarantababu kudin
makaranta? Malam Habu ya ce "toyanzu nasan ka
gane babu,ta yaya zata yi karatubabu kudin
makaranta babu kayan makaranta?Kyakkyawan
saurayin nan ya ce "Yauwa Baba kayitambaya
mai kyau, amsar tambayar ita ce in Allah Yaso Ya
yarda Hanne zata yi karatu in har kaamince ka
yarda zaka ringa turo ta makaranta dazarar hutu
ya kare ba sai ta fara ba kace baza tadawo ba ka
cire ta.Idan kayimin alkawarin haka kuzo ku
ajiyekayan nan ka tafi ka barta. Malam Habu yayi
jigumyana tunani, a ransa ya ce "Wannan yaron
me yakenufi? Hanya zaiyi mana a dauki Hanne
babu kudinmakaranta babu kayan makaranta ko
kuma yayaza'ayi? Bana tunanin dai shi zai biya
mata kudin makaranta harda dubunnan da ko
karamarhukumar mu baza ta iya biya mata ba
yaddazamanin nan ya canja masu kudi basa
taimako,babu yadda za'ayi yaron nan ya zare
makudankudi ya baiwa yarinyar da bai santa ba
bai tabaganin ta ba bazan bar *yar Baba a
makarantar nan ba in tafi ta wulakanta ba, wacce
bata san hanyarda zata bi ta koma gida ba idan
an korota. Yanzuakan Naira goma masu mota
suke kokarin sudanneni su dauka ina ga
dubunnan kudade gakayan makaranta har kala
hudu waye zai dinkomata? Saurayin nan ya katse
Malam Habu daga tunanin da yake yi ya ce "Baba
tunanin me kake yine? Karka yi kokonto ba zaka
yi dana sanin barinHanne a makarantar nan ba in
Allah Ya yarda babuabin da zai sami Hanne sai
alheri da kwanciyarhankali ka tsarkake zuciyarka
ka danka Hanne gaAllah wanda a koda yaushe
Yana kallon halin da bayinsa suke ciki na kunci
kona farin ciki, sannanka danka Hanne amana ce
a wajena. Ni kuma namaka alkawarin zan karbi
amana na rike. Cikinsanyin zuciya da gamsuwa
da kalaman saurayinnan Malam Habu ya juya ya
kalle shi ya ce "AllahSarki duniya wani ya munana
maka wani kuma ya dadada maka. Yaro tunda ka
ce Allah na yadda kakuma ambaci amana, amana
kalmace mai girmamai wuyar rikewa kace zaka
rike tsakaninka daAllah, na gode yaro, Allah Yayi
maka albarka Yabiya maka bukatunka. Abin da
kayi min UbangijiAllah Yayi maka fiye da haka,
*yar Baba muje mu ajiye kayan. Suka juya harda
saurayin wajen bencinda yake, Malam Habu ya
kama akwatin dake kanHanne ya sauke mata ya
juyo ya kalli saurayin nandake zaune akan benci
ya ce "Yaro bazan gaji da yimaka godiya
ba.Madalla Allah Ya yi maka albarka zan tafi
nabarku lafiya, af kaga ko sunanka ban tambaya
ba.Saurayin nan yayi murmushi ya ce "Sunana
Haisam,Baba. Malam Habu ya ce "To madalla. Ya
juya yakalli Hanne wacce ke tsaye idonta ya ciko
da kwallaya ce "*Yar Baba zan tafi na barki ga
Allah na barki ga wannan bawan Allah. Sai ta
rushe da kuka takoma kan akwatinta ta zauna ta
kifa kai a gwiwatana kuka. Hawaye ya kecewa
Malam Habu ya ce"Nima ba'a san raina zan tafi
na barki ba Allah Yakaddara saduwarmu. Ya juya
ya kalli Haisam ya ce"Yaro mai wuyar suna har
na manta sunan(fatan Yayarmu ma Zee zata iya
rike sunan, kodayake ita 'yar birnice, loz) na tafi,
sai wata rana. Haisam ya ce "To Baba Allah
Yakiyaye. Malam Habu ya juya ya fara tafiya yana
facemajina yana goge hawaye da gefen babbar
rigarsa,sai yaji muryar Hanne ta ce "Baba ya juyo
ya ce"*Yar Baba. Ta taso da gudu ta karaso inda
yake takama gefen zaninta ta kwance sai ta
dauko wasu cukurkudaddun *yan Naira ashirin
guda hudu tace "Baba karka tafi da kafa gashi ka
hau mota.Haisam dake zaune har yanzu akan
benci yanakallonsu sai da yaji kwalla ta cika masa
ido dontausayin Uba da *yarsa. Malam Habu ya
ce "AllahuAkbar, *yar Baba Allah Yayi miki
albarka. Allah Ya baki ilimi mai amfani, kinji?
Waye ya baki harmurtala hudu? Hanne ta ce
"Dana shiga makwabtanayi musu sallama suka
babbani wasu, saurankuma kudina ne da nake
tarawa tun na yawonsalla. Malam Habu ya ce
"Kya bani duka ingomurtala biyu ni na dauki
murtala biyu, kema ki rika siyan *yar gyada kya
zauna haka kina ganin yarasuna siye-siye ke
bakya siyan komai? Hanne ta ce"A'a Baba
murtala biyu baza ta kai ka gida ba, banaso ka
shiga mota kudinka bai cika ba, kana rokonayi
maka ragi irin na dazu. Malam Habu ya
sakekecewa da kuka ya ce "To *yar Baba na gode
na tafi na barki ga Allah baki da kowa, baki da
komai,ba ki san kowa ba, Ya juya ya tafi. Hanne
na tsayehawaye yana zuba daga idanuwanta tana
kallonMahaifinta yana tafiya yana waiwayenta.Taji
wani kululun bakin ciki marar misali akirjinta da
mummunan tashin hankalin rabuwa
daMahaifinta, yaune ranar da ta taba rabuwa
daMahaifinta daidai da rana daya basu taba
rabuwaba. Gashi a yau ya kawota inda bata san
kowa baya juya ya tafi ya barta. Hawaye ne mai
radadi yake zubo mata har sai da ta daina hango
fararenkayansa ya kure, sannan ta yi ajiyar zuciya
tasagefen mayafinta ta goge idanuwanta ta juya
tadawo kan akwatinta ta zauna. Haisam na
zauneakan benci yana kallonsu zuciyarsa cike
datsananin tausayi ji yake wani abu yana yawo a
cikin kansa, saboda wani abu guda daya daya
bashimamaki ya bashi al'ajabi, shine ganin yadda
Hannetake da Mahaifinta suna cikin tsananin
talauci ammasuna da wadatar zuci. Haisam yaci
gaba da kallonHanne wacce take zaune akan
akwati a gabansa tasunkuyar da kanta kasa tayi
shiru kamar mai tunani, amma hawaye na
digowa daga ganintahankalinta a tashe yake tana
cikin damuwa. Yagyara zama gami da zare farin
gilashin da yakefuskarsa. Ya ce "Hanne, kukan
mai kike yi ne?Bakya so ki zauna a makaranta kiyi
karatu kamarsauran yara, kin fi so ki koma gida ki
zauna da Baba? Hanne ta girgiza kai alamar a'a,
ya ce "Tomeye kike kuka? In kinsan bakya son
makarantarnan yanzu nayi sauri na tsayar da
Babanki kafinyayi nisa sai ku koma gida. Hanne
tayi sauri ta ce"A'a bana so na koma gida, ya ce
"To ai kuka kikemeyasa kike kukan tunda kina son
makarantar? Bakya son ki koma gida inda zaki yi
wasa kuyiwake-wake da kawayenki a dandali?
Hanne tayidan murmushi ta sunkuyar da kai.
Haisam ya cigaba da cewa "Ni kuwa na dauka
danmarar nan dakika ci ta zuwa wake dandali ce.
Hanne tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka
ta ce "Ni ba'a barina naje dandali wasa. Kullum
aiki nake yi sai daiinzo in wuce su in zani debo
ruwa. Haisam ya sakegyara zama ya ce "Ban gane
ba sai dai ki zo ki wucesu in zaki debo ruwa? Ke
kullum a debo ruwa kikebakya zuwa wasa? Hanne
ta ce "Eh, sai dai suSaude Yayyena da kanne na
ne suke fita wasa.Haisam ya ce "Ina Mahaifiyarki
take? Hanne tasake saka gefen gyalenta ta share
hawaye ta ce"Tun ina shekara biyu ta rasu. Yaji
gabansa yayanke ya fadi ras, saboda yanzu ya
gane Hanne agidansu tana cikin halin wahala
kasancewarMahaifiyarta ta rasu da alama kishiyar
Uwa tana wahalar da ita. Allah Sarki Hanne ya
fada a ransayayin daya kura mata ido. Hanne ta
bashi tausayida, a yanzu kuma ta sake kara bashi
tausayi akantausayi wanda badan ya daure ba da
zai iyarushewa da kuka. Can bayan sun dauki
wani lokacimai dan tsawo babu wanda ya sake
cewa komai. Dukkaninsu kansu a sunkuye a kasa
suna tunani,Haisam ya rike kai da hannuwansa
guda biyu canya dago ya kalli Hanne ya ce
"Yanzu dai a gidankuke kadai Babarki ta haifa
kenan baki da Yayye ko?Hanne ta ce "Eh. Ya ce
"Shine kuma ake saki deboruwa kullum. Hanne ta
ce "Ba debo ruwa kawai ba kullum ni nake
wanke-wanke, shara, wankinsu, dakai dabbobi
kiwo daga can nayo musu ciyawa.Haisam ya buga
kafa a kasa ya ce "Kai wannanwanne rashin imani
ne haka? To ya akai kike zuwamakaranta? Hanne
ta ce "Sai wajen sha dayan ranakoma wataran
bana zuwa, tun ana min dukan makaranta har
suka daina su Malamai. Shine waniMalami ya je
ya sami mai gari ya ce a yiwa Babanamagana a
dinga turoni makaranta da wuri tundaina da
kokari, Haisam ya ce "Sai da maigari ya
kiraBabanki ya fada masa sannan ake
turakimakarantar da wuri? Hanne ta ce "Cafdijan
shima Baban ya isa? Ya ce "Kamar yaya bai isa
ba.Ta ce "Shima tsoron Iya Abu yake, matar
tasazaginsa take,*ya*yanta suyi masa, sai dai in
ana dukana inakuka shima yadinga yi. Hawaye ya
sake kece mata, shima ya jikwalla ta cika masa
ido, ya dauko wani hankici fari kal a aljihunsaya
gogeidanunsa ya mika mata, ya ce "Yi shiru
Hanne dainakukagoge hawayenki. Ta karba ta
goge. Haisam ya ce"Bari na danyi miki tambayoyi
naji kina kokari? What is yourname?Hanne ta ce
"My name is Hanne Habu,Ya ce "Howold areyou?
Ta ce "I'm eleben years old. Wich school areyou?
Ta ce "I'm in Babban-mutum special primary
school.Haisam yayidariya ya ce "Hanne Habu
haka kike da kokari? Toke da bakyazuwa
makarantar sosai ya aka yi kika koyi dukwannan?
Hanne tayi murmushi ta ce "Ai daga baya
maigariyasa akakirawo ita iya Abu da kanta taje
fada ya sakashaidu ya ce"Duk ranar data hanani
zuwa makaranta ko namakara sai ya kaita kara
local goverment. Sannan take barina
natafimakaranta da wuri sai dai idan na dawo
tayi tadukana tanacewa ga wanke-wankenta nan
harya bushe natsaya a hanya ina wasa. Haisam
yayi tsaki ya girgiza kai alamartausayawa.Yayi
gyaran murya ya ce "Hanne ina so kiyi
minalkawarin zakidage kiyi karatu duk rintsi duk
wuya. Kar ki zo kifara ayi hutu ki koma gida kiga
kawayenki da yayyanki sunagida basa
zuwamakaranta kema kiki dawowa. Hanne ta
ce"Kwarankwatsazan dawo.(hahah. Inkikayimata
dariya bazancigabarmikiba,'Eh' dake nake Zee )
Haisam ya kece da dariya (subhanallahi, tinda
shima yayi to kema danyi amma kadan),ya
ce"Kwarankwatsabarantsuwa bace wallahi Allah
za ki ce. Hanne tayidariya ta ce"Mantawa nayi
Malamin makarantar Islamiyya yahana mu cewa
kwarankwatsa. Haisam ya ce "Kina
zuwaIslamiyyakenan? Ta ce "Eh, ada makarantar
allo muke zuwadaga bayaaka bude makarantar
Islamiyya da yamma dakuma dare duka ina
zuwa. Haisam ya ce dakyau Hanne yanzuidan
anyihutu kin koma gida sai kici gaba da zuwa
taIslamiyya karkifasa zuwafa kinji? Hanne ta ce
"To. Haisam ya cigaba da kallonta har sai da
Hanne ta fara jin kunyar kallonda yakemata
sannan yayi murmushi ya ce "Hanne
dukwannankwalliya ce kika yi a fuskarki, ta zuwa
makarantace? Hanne tayi murmushi ta sunkuyar
da kai kasa tana rurrufefuska dahannu ta ce "A'a
ba kwalliya bace. Ya ce "Gashi nankinrambada
kwalli kinja wata doguwar jagira kinyifashin goshi
da kwalli kinyi digo-digo duk fuskarki kice
bakwalliya bace. Gawannan tsakiyoyi da kika jifga
a wuya da hannuhar kafarkima kin daura, Yana
dubanta yana dariya. Hannan tace "Eh sarkar
salla tace Baba ya siya mun. Ya ce
"Kingananmakarantar an hana sawa idan Malamai
suka ganizasu kwacesu tsittsinka miki, ciro su ki
bani in ajiye miki saianyi hutu in zaki tafi gida na
baki. Cikin sauri taji zancentsittsinkawa taciro ta
bashi, yadda take bala'in kaunar sarkokinnan
natabata son abun da zaisa ta rasa su. Haisam
ya karbayana jujjuyasu yaga wasu irin tsohon
wuri ne aka jera sucikin liloaka daura ya ce a
ransa "*Yan kauye suna gayu.Yayi murmushi ya
jawo jakar kayansa ya budewanikaramin zip ya
zuba ya mayar ya rufe. Ya juya yakalli Hanneya
ce "Kuma a cikin akwatin naki bude in gani
kokinzo da wani abunda dokar makaranta ta
hana. Hanne tatashi dagakan akwatin ta bude ya
karkato ya leka akwatinbabu abundaya hango sai
tsummokarai, cikin sauri ya ce "Hanneme wancan
nake hangowa kamar miciji a cikinakwatinki?
Hannetasa hannu ta zaro wani dan siririn gyale
baki yakanannadeya kudindine ta ce "Gyale ne ba
miciji bane. Haisamya kyalkyale da dariya ya ce
"Na dauka kofi kika yiminna miciji.Hanne ma tayi
dariya ta ce "Gyale na ne dan bansaruwa bana
kadeshi shiyasa ya cukuykuye, ya sake
lekaakwatin sai ya hango wani dan dogon karfe
mai huda huda ajikinsa, jikinsakamar farar azurfa
yana kyalli ya ce "Hannewannan fa,
karfenmenene? Dauko muga. Hanne ta yi
murmushi tadauko karfen ta mika masa ya karba
ya jujjuya bai san ko meyeba ya ce"Wannan
kuma na maye. Hanne ta ce "Idan najekiwo
nakeyiwa dabbobi busa dashi, abun busa ne.
Haisam yace abun busa kuma? Hanne ta ce "Eh
kawo ka gani. Ta karbikarfen tamayar da akwatin
ta rufe ta koma kan akwatinta tazauna takaikaice
ta fara busawa Haisam wannan karfen kaikace
Sarkin busar Sarki ne yake yi, karin busar mai
dadi daalama daiwaka ce, Haisam ya buda
kunnuwa yana sauraroya baza idoyana kallon
yadda take yi.Can ta kyalkyale da dariya ta ce
"Haka nake yi.Haisam yayimurmushi ya gyara
zama ya ce "To ni abunda bangane ba,kamar
yaya sai kinje kiwo kike yi? Daman a wajenkiwo
ake yin busa? Waye ya koya miki kuma? Nan da
nanHanne tacanja daga yanayin farin cikin da
fara'a da sakinjikin da takejikinta yayi sanyi ranta
ya baci. Haisam ya ce "Yakika canja nan da nan
daga tambayarki? Hanne ta rushe dakuka ta
kifakai da gwiwa, Haisam yayi matukar mamaki
daganin wannanhali da Hanne ta fada yanzu-
yanzun nan ya ce"Yaya kina dariya ki koma kuka,
Hanne dago kanki. Ta dagoya ce "Gogehawayenki.
Ta goge. Ya ce "Fada min meye nakukan?
Hanneta ce "Wani abu na tuna shine ya sani
kuka. Haisamya ce "Meye abun da kika tuna?
Hanne ta sa hannu tasake gogehawayen da ke
idonta ta dauko abun busar dakekan cinyartata
rike a hannunta tana jujjuya shi.Tace kullum
dasafe nake fita kiwo da raguna da akuyoyin iya
abucan dawa. Bana dawowa sai da yamma
musammanrabar asabar da lahadi. To awajan
kiwo ne nakehaduwa da wani tsoho mai suna
malam saleh. Wani lokaci sai yazo ya wuce ni ina
kuka idan yunwa tadameni don yini nake anan
kuma ba.a kawominabinci. Har dai rannan ya zo
ya sameni a gingininuwa ina kuka. Yayi ta
tambayata dakyar dai nagaya masa yunwa nake
ji. yace '' ba.a kawo minabinci daga gida ?nace
ba.a kawomun kuma bana zuwa dashi. Ya ce ''
ina babata? Nace ta rasu'' shineya ce min kullum
zai rinka bani abinci ina ci dakekullum da rana
daga gidansa ake kawo masaabinci nan wajen
kiwon rigarsu tana nan kusakusa da garinmu ,
shine kullum muke haduwadashi yana waka
harya koyamin nima nakoya. Sai ya ce ya barmin
abun busar tunda na iya, ko bayanransa dansa
zai ringa kawo shanunsa datumakinsa kiwo na
dinga yi musu busa. Bayan nannaga kwana biyu
naya zuwa kiwo bana ganinshanunsa kuma.
Hankalina ya tashi naji duk banajin dadin kiwon
ni kadai babu wanda muke zama muyi hira muyi
busa muyi waka tare. Sai da akadade naga
shanunsa da tumakansa an kawosuwajen kiwo
amma ba malam saleh bane wanisaurayi ne. Naji
gabana yana ta faduwa ko lafiyaina malam saleh
yake? Naje na tambayi yaron sai yace shi dansa
ne kuma babansa malam saleh satinsa biyu da
rasuwa shine a duk sanda naje kiwo
nagadabbobinsa sai suyi ta bani tausayi ina
kuka''hanne ta goge hawayen da yake zubo mata
haisamyayi ajiyar zuciya. Zuciyarsa cike da
tausayin hanneya ce a ransa'' hanne yarinya
karama tasan bacinrai, tasan tashin hankali ta
rasa kowa da zai tarairayeta wanda zata gani taji
dadi baya gamahaifinta. Allah sarki , na yiwa
allah alkawaribazan kyale yarinyarnan taci gaba d
tagaiyara ba''ya juyo ya kalli hanne wacce har
yanzu take rike daabun busarta a hannunta tana
jujjuyawa.Yacekawo abun busar shima na ajiye
miki, idan ba haka shima malamai zasu kwace''
hanne tayi murmushita mika masa ya karba ya
jujjuya ya bude zip dinjakarsa inda ya saka
tsakiyoyin nan nata ya saka yamayar da zip din
ya zuge ya ce'' yanzu abunda za.ayi kije kicin
gashi can ya nuna mata da hannunsaya ce kice
uwar biyu, tazo inji malam haisam kinji ku taho
tare'' hanne ta mike cikin ladabi tana maiamsawa
cikin ladabi ta nufi inda ya nuna mata tanatafe
tana kara tsuke damarar data ci da gyale
akugunta.Haisam ya bita da kallo har ta kure
yayimurmushi ya girgiza kai'' bayan tafiyarta da
kamarminti biyar sai ga hanne da uwar biyu sun
taho tare bayan uwar biyu ta gaishe da haisam
durkuso harkasa duk da ta haifeshi tama yi jika
dashi amma aidurkusama wada ba gajiyawa bace
irin abunalherin da haisam yake yi musu ita da
abokanaikinta na kicin sune masu dafawa yan
makarantaabinci. Duk ranar da yake duty idan
yazo kicin duk sai ya bisu da kudi dukkaninsu don
haka allahallah suke malam haisam yazo kicin
bayan sungaisa ya ce'' uwar biyu wata alfarma
nake si kiyimin idan baza ki takura ba '' uwar
biyu ta sakegyara gwiwoyinta da ta durkusa tace''
haba malamhaisam menene ni kuwa a duniya
zaka nema ina dashi na takura ai babu sai dai
ma nayi murna yauharka nemi wani abu a
wajena , mai yi maka kansada kafarsa. Kana yi
mana alheri allah ne zai sakamaka da alherinsa''
haisam yace '' amin na gode .Ba wani abu bane
daman wannan yarinyar da kikagani kanwatace
amma daga kauyenmu taci makarantar nan
babanta ya kawota dazu. Tokasancewar acan
basu iya karatuba basu san ancea diko kayan
makaranta ba da sauran saye saye .To shine
naga dasu koma gida gashi garinbakusaba shine
nace zan baki ita ki tafi