Showing 15001 words to 18000 words out of 31410 words

Chapter 6 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

154

malam
habu'' inji malamhaisam ya ce a bashi nasa ne
na kashin kansa banamakarantar hannah bane.
Da zarar hutu ya kare itada kanta zata zo ta
dauketa, malam habu yayi shiruyana sauraron
uwar biyu sai girgiza kai yake kawai yana
mamakin wannan tara ta arziki da haisamyake yi
musu yana fadin ashe akwai masu halinsahabba
a duniyar nan masu kyautar da dukiyarsuga
mabukata irin malam haisam. Malam habu
yadago ya kalli uwar biyu yace'' kema daya
aikokikika rike amana allah ya saka miki da gidan
aljannah dashi da yake mana hidima allah ya
bashida mai yi masa haka munji dadi mun gode.
Ni inanan wata rana na gaza barci ina tunanin ko
yayayar baba, kome take ci a makarabntar na
bartababu abinci? Ashe tana cam ta fini koshi,
kalliyadda tayi bul bul ah alhamdulillah. Maigari
ya aiko da garin kwaki kwano biyu da suga rabin
kwanosai kudin motar zuwa kazaure ya ce in kai
matamakaranta wallahi matar nan tawa data ga
garinnan da kudin mota sai ta sulalo ina bacci ta
sacekudin motar ta tilla ledar garin ya dinga
tsiyayewa akasa, da naje na shaidawa mai gari
ba kiga cin mutuncin da suka yimin ba wai
daman talauci yaisheni na sami kayan gwamnati
ina wadaka dashi,su babu ruwansu ya dai ya ta
ce in barta yunwar takasheta. Nayi kuka da
hawaye nazo na zauna nahakura sai addu'a na
dinga aikamata daga na allahya hadata da mai
bata. Allah ya amsa addu.ata gashi bamu girbe
amfanin gona ba shine yasa kotaro nakan tashi
babu a aljihuna. Uwar biyu tace,kaico haka kake
rayuwa ta malam ? To ni daishawarar dazan baka
dan allah dan annabi(S.A.W)duk runtsi duk wuya
ka toshe kunnankakome za'ace game da karatun
hannah karka cire ta daga makaranta. Babu
sisinka. Ba kai zaka dauketaba. Bakai zaka mayar
da ita va nice zan dingakawota ina zuwa ina
daukarta sai dai ka bata izinikarka hanata saboda
karatu ne kawai zai farfadoda hannah ta sami
yancinta da jin dadin rayuwartaanan gaba, amma
azabar tayi yawa. Malam habu ya ce da gudu
kuwa zan barta, aini badan za'ace nasiyar da
yata ba, ko ace na kaita birni tana iskancida ko
hutu ma sai ince ta dinga yi a gidanki
ammayanzu kowa yaji a rediyo an yiwa 'yan
makarantahutu ba aga hannah ba za'a fara
titsiyeni datambaya a fada. Uwar biyu tace allah
ya kyauta ni zan koma, ga sabulai can a jakanta
da mayukanshafawa malama haisam ce don allah
a dinga bartatana wanka da wanki da kitso ba
kamar yadda akakawota ba, kazan kazan ina
amfanin kazanta ?Uwar biyu ta fara tafiya bayan
sunyi sallama damalam habu yana ta godiya,
hannah ta rushe da kuka ta bi uwar biyu da gudu
ta rungumeta suduka kuka suke rusawa hannah
tace''uwar biyu karki tafi ki barni wuya bake sha
ni zanbiki gidanki in zauna a can. Daya daga cikin
'yayaniya abu musbahu shine ya fito daga cikin
gidan aguje uwarsa ta turo shi yazo ya dauko
mata hannah aka dake suna labe a zaure suna jin
dukmaganganun da suke yi. Ya dauko ta aka ya
mikata cikin gida ya rufo kofar zaure sai kukan
hannahne yake tashi ya cika unguwar kai kace rai
ake zaremata saboda irin karar kukan daga ji ba
karaminbudu ake yi mata ba, malam habu nata
kokarin bude kofar yana bugun kofar kamar zai
balla yanaso yaje ya ceci 'yarsa uwar biyu ta juya
ta tafi tanarusa kuka kamar ranta zai fita,
tsananin bakin cikida tausayin hannah ne ya cika
mata zuciya. Tana jinsamarin dake zazzaune akan
benci suna jiyo kukanhannah suke cewa''to
baiwar iya abu tazo har an fara nada mata dukar
kai wannan yarinya allah daiya rayata kar itama
wuya ta kasheta kamar uwarta.Haka hannah tayi
ta zama cikin wahala da kuncida azabtarwan iya
abu har hutun makaranta yakare. Ana saura
kwana biyu a koma sai ga uwarbiyu tazo daukan
hanne. Tunda iya abu ta ganka tahau fada ta
inda take shiga ba ta nan take fita ba,anan ne
malam habu yake fada mata , kinsan cewa tayi
indai da ranta hanne ta daina karatu tundawata
gulma aka hada na kaita gidan yan gayubabu
wata makaranta. Wuf iya abu tayi tayo wajedaga
cikin daki tazo ta tsaya a dokin kofa tanagirgiza ta
kama kugu tana kallon uwar biyu ayatsune. Babu
abunda uwar biyu take sai kallon wuyan iya abu
galleliyar sarkar jiyal din da tasiyawa hanne ce a
wuyanta. Muhajana 'yarta kuwariga da siket 'yar
kanti ta hanne ce a jikinta, saigamusbahu shima
yazo ya wuce da jakar hanne arataye a bayansa
(school bag)wai daga kasuwayake. Iya abu tace''
bai gaya miki ba na hana karatun hanne ko bai
fada miki ba ne ? Iwar biyutace '' shine
mahaifinta shine kuma mai iko da'yarsa bake ba.
Ni kuma akan kin barin yarinyarnan ta tafi zan iya
cin dammara mu daku da kowakuma daga na
har gaban mai gari zamu je dakeidan kika
kwatanta hakan. Iya abu tayi shiru tasan idan aka
kaita kara wajen maigari tasan bazai bibayanta ba
kasancewar sun sha gogawa akan zatahana
hanne karatu bata ci nasara va. Iya abu tanisa
tace to kije dawan da kanki ki kirawo hanne'yata
ba zata ba. Taja hannun 'yarta mahajana
sukashige cikin gida.malam habu ya leka kofar
gida ya kira musa dan makwabtansu ya ce yaje
dawa yaceda hanne tazo yanzunnan ta koro
kiwan su dawogida. Uwar biyu ta tabe baki gami
dayin ajiyarzuciya tace'' rabon gado akayi da
kayan hannetunda ranta ba'a jira ta mutu ba.
Caraf iya abu ta fitoashe a labe take tace'' an
raba kayan hannen ko hannen naga dama zan
iya rabata balle kayanta.Duk gulmace gulmacen
da kuke hadawa ya kare akanku babu wata
makaranta da ake kai hanneyawon bariki kawai
ake koyawa yarinya ta samoabin duniya'' uwar
biyu tayi dariya shekeke tace''wannan yawon
bariki na hanne don ke da yayanki take yi irin
wannan bushasha da kayan yarinya. Dayake
itama uwar biyu badaganan ba wajen iyamasifa
da yaba magana suka yi tayi dakyar malamhabu
ya hana uwar biyu magana ya ce ta yi shiru
takyaleta, iya abu tayi fada tana shiga da fice
bakinciki ya lullube mata zuciya kamar zata fashe
ganin anzo za'a dauki hanne a tafi da ita wajen
da takehutawa. hannah ta shigo a sanyaye tana
fargaba tanatunanin me tayi kuma aka ce ta koro
kiwo ta dawogida yanzu. Tana shigowa sai taga
uwar biyu damahaifinta a zaure a zaune ta daka
tsalle tarungume uwar biyu tana mai tsananin
murna dafarin ciki tace. Iya daukata kika zo yi
mu tafi'' uwar biyu tace'' yanzu kuwa shiga ki
dauko kayanki mutafi. Hannah tayi kasake a tsaye
murna ta koma cikitayi kamar zata fashe fa kuka.
Uwar biyu ta kalletatace'' hannatu lafiya meya
faru kuma kika zamahaka lokaci daya kamar mai
shirin rushewa dakuka ? Uban yace da kika ce
taje ta dauko kayanta shine jikinta yayi sanyi ai
babu kayan duk sunkwashe. Harda litattafan
makarantar sun yayyagasun siyarwa da mai kosai
wasu'' uwar biyu takwada salati tana cewa''
harda manyan litattafankaratu masu tsada suka
yayyaga mata ? Iya abutayi wuf ta fito tace da
uwar biyu !! Ki kiyayeni don kin zake dawa, karfa
ki kuskura ki cika min cikiba'aja dani an yayyaga
littafin kyi abinda zakiyikuje ku saya mata wasu ta
kawo na sakeyayyagawa muje duk inda zamu je
aikin banza.Uwar biyu ta mike tsaye ta juya ta
kalli malam habuwanda yayi tsuru abin duniya ya
isheshi ya kasa magana tace '' malam na tafi da
hanne allah yanabayan mai gaskiya kuma duk
dan hakin da karaina shike tsone maka ido
zakaran da allah yanufa da cara ko ana muzuru
ana shaho sai yayi.Hanne mu tafi garin da ake
kaunarki. ''iya abu tarako su har kofar gida tana
zagi tasa hannu ta fallawa hanne duka a baya
gami da angazata ta tafitaga taga zata fadi uwar
biyu ta riketa tajahannunta suka tafi. Hanne ta
rushe da kuka uwarbiyu fadi dake. Duk abinda
zaki yiwa hannah bakiisa ki hanata numfashi a
duniya ba tunda bake kikahalicceta ba'' suka
kama hanya suka tafi, suna ji iya abu ta koma
kan mahaifin hannah tana zazzagamasa masifa
yayi shiru kamar bada shi take ba. A tasha uwar
biyu ta siyawa hanna sabon silifasdomin na
kafanta wari da wari ne, suna zaune amota uwar
biyu take tambayar hanne abubuwanda ake yi
mata. Hannah ta zaiyana mata tsaf tacekusan
kullum sai an lakada mata duka an kwacekayan
sawarta da jakunkunanta, sabulan ma da
mayukan shafawa ko sau daya ba'a barta
tayiwanka da suba. Tana dai barinta taje
makarantarislamiyya kullum shima saboda tana
tsoron maigarine. Hanne ta sake dagulewa kamar
ba itace tayikyau din na ba das da ita gwanin
sha'awa, yanzu tadawo furtutunta, yagulallun
kaya uwar biyu tace'' yanzu har kayan
makarantar taki(uniform)duksakawa suke ? Tace
eh ta rarrabawa jikokintawasu, wasu kuwa ta
sayarwa 'yan jagorar makafi.Bani da sauran kaya
sai wannan na jikina, uwarbiyu ta nisa tace allah
ya saka miki, kuma wannanyaro haisam shima an
sake ja masa sabon aiki'' zugum suka yi su duka
kowacce tana tunani harsuka isa tashr kazaure
babu wacce ta sake yinmagana suna isa gida
uwar biyu ta shirgowahanna abinci mai yawa da
mamakinta hanna tatashi dashi tasha ruwa.
Bayan sun huta uwar biyutasa 'yarta halima ta
wanke mata cukurkudeden gashinta , hannah ta
sallah wanka. Kafin magarubahar an gama
rangadawa hannah kitso,Sai suka ji ana rangada
sallama uwar biyu tacehanne ta leka zaure taga
waye yake sallama . Tanalekawa sai taga safiyanu
ne abokin yaya haisam,rike da wata katuwar
jakar bacco babbar ta karshea girma. Hannah tayi
dariya '' tace lala yaya safiyanusannu da zuwa .
Ya ce yauwa har kinzo ,hutu ya kare ko ? Hannah
tace'' eh ka shigo mana'' dakyaryake jan buhun a
kasa saboda a shake yake damda kaya. Suka iske
uwar biyu a tsakar gida. Lalemar haban, uwar
biyu take cewa hannah tayi saurita shimfida
tabarma ya zauna. Bayan sun gaisa da uwar biyu
ya fara zazzagekayan dake cikin wannan katuwar
jaka siyayyarhannah ce ta makaranta (provision)
kaya ne abunbaya lissafuwa komai akwai kai kace
kanti za,abude uwar biyu ta rike baki kawai tana
kallon ikonallah, tace '' safiyanu wannan kaya ai
ya yiwa hannah yawa. Safiyanu yayi murmushi ya
ce aikudin da haisam ya bani ne masu yawa ne
ya ceduk ayi mata siyayya a wadace. Nima da
kainanaga ya dace na bar siyayyar nan haka ba
donkudin sun kare ba . Uwar biyu tace ai gara da
karago kudin don sai an sake siyan sababbin
uniform da litattafai. Safiyanu ya ce ina nata
nada , ko dukterm ake sake wa ? Uwar biyu ta
gyara zama ta farabawa safiyanu labari duk
abunda ya faru da kayanhannah tun daga biri
har wutsiya. Safiyanu yatausayawa rayuwar
hannah duk da yake damahaisam ya gaya masa
kadab daga ciki. Ya nisa ya ce'' abun babba ne
kudin da yawa musamman nasayan litattafan
karatun(text book)masu tsada negashi haisam din
bama ya kasar. Uwar biyu tacebaya kasar ina
yaje ? Nifa tun ranan hutu ban sakesashi a idona
ba. Safiyanu ya ce'' ai kuwa bai dadeda tafiya ba
shi da mahaifiyarsa suka tafi london kinsan shirye
shiryen bikinsa ake yi shi da yayansawatakila nan
da wata uku za'ayi don haka damanzaiyi wuya
haisam ya sake dawowa kazaure tundabautar
kasa daman yazo kuma sun kare. Nima dayake
daman a kano na sanshi a can muke haduwa.A
can kuma ya ce zai dinga kawo min kudin
siyayyar hanna. Yanzu dai abunda za'yi duk
abindaya tashi na game da makarantar hannah a
gayamin zanyi ko nawa ne zan ranta masa nasan
zaibiya ni don haka daga yau zuwa gobe zanyi
kokarina saisayo mata uniform din da takalmi da
kumalitattafan. Zuwa gibe telan daya dinka mata
wancan zai dinka mata da wuri . Jibi dai zasu
komamakarantar kafinnan insha allahu komai
yakammala. Uwar biyu tayi murna dajin
bayanansafiyanu tayi ta godiya. Amma hanna ta
fita yinmurna da farin ciki don ita da a tunaninta
za'acekarshen karatunta yazo tunda yaya haisam
baya nigeria to sai taji safiyanu ya ce zai ranta a
dinkamata. Suka yi sallama da safiyanu su duka
suna yimasa godiya ya tafi, akan jibi hannah ta
kwana dashiri zai kawo mata kayan ya kuma
mayar da itamakaranta. Haka kuwa aka yi
hannah tana dayadaga cikin wadanda suka fara
dawowa makaranta tun karfe sha biyun rana,
kafin yamma makarantata cika makil kowacce ta
dawo tana tsoro sabodaprincipal tace duk wacce
ta kara kwana dayabaza'a karbeta ba. yaya
haisam baya nan kishin da rauda take yi
dahannah ya kau yanzu suna zaune lafiya wasa
dadariya, sai dai su dukkansu basa jin
dadinmakarantar sosao saboda babu yayansu.
Haka dukyan ajin uncle haisam basa jin dadin
sabon classmaster dinsu saboda baya
tarairayarsu kamar haisam. Kowacce bata manta
da nasihohin da unclehaisam yayi musu ba akan
suyi karatu sucijarabawa idan ba haka ba za'ayi
musu repeating .Kowacce ta dage da karatu ba
dare ba rana donhaka j.s.s 1a is the best class in
f.g.g.c kazaureyawanci a wajen assembly
malamai suna fadar haka principal tasa a tafa
musu, tana kuma alfaharida su tana yabawa
tsohon class master dinsuhaisam saboda tasan
shi ya gyara ajin haka. Tanakuma nunawa sauran
malamai dasuyi koyi dashidon ire iren su haisam
a makarantar.Bayandawowar daliban makaranta
da kamar wata guda. Ranar wata litinin da safe
ana assembly sai kuwaprincipal tayi musu albishir
da cewa.kwararrenmalamin nan uncle haisam ya
dawo makarantar amatsayin permanent teacher.
Tasa wani malami yaleka waje ya shigo da
haisam saboda a waje la labekada su ganshi suki
tsayawa ayi assembly suyi taife ife don haka ya
tsaya daga waje. Malam haisam na shigowa
dalibai gaba dayansu yara da manyasuka hau ihu
da tafi murna kuwa ba'a cewa komaimusamman
a wajen hanna. Wai! Yau da za'a budezucoyar
hannah aga irin farin cikin da yake cikinzuciyarta
da abun da yawa. Dakyar dai dalibansuka dan
tsagaita da ihu aka karasa assembly kowacce ta
tafi ajinta. Yan ajin su rauda kuwa hadabaki suka
yi suka yi kungiya suka nufi ofishinprincipal dauke
da manya manyan takardu sunrubuta kamar
haka '' we want our former classmaster uncle
haisam back.'' waisu zanga zanganlumana suke yi
principal da sauran malamai suka sha dariya
sannan ta basu amsat cewa za'a dawoda haisam
dinsu, su koma aji. Sannan suka tafi sunamurna.
Haisam ya dawo yaci gaba da rike
ragamarshugabancin ajinsa j.s.s. 1A. Hutu yana
zuwa karshe jarabawa na karatowahaisam naci
gaba da yiw dalibai nasiha dasu dageda karatu
musamman ma hannah yana ci gaba danunnuna
mata duk abunda bata gane ba. Ba laifihannah
tana sake kokartawa fiye da waccan termdin. Ta
fara gane ayyukan makarantar sosai tana kuma
gane turanci tana yi kuma. Wannan termdinma
kamar wancan sunyi jarabawa sun gamasannan
malamai sun yi kokarin sun kammala fitarda
sakamako. Haisam ya tara yan ajinsa ana
gobehutu ya bawa kowacce sakamakon
jarabawarta.Wannan ma kamar waccan bata sake
zani ba rauda shitu muktar itace tazo ta farko.
Nusaiba ta biyu,pamella matin benin ta uku.
Hannah ce dai ta samici gaba maimakon tazo ta
goma data zo wancankaron yanzu sai tazo na
takwas.Hannah tayi murnahaisam har ya fita
murna ganin ba kudin banzayake kashewa ba, da
bata lokacinsa a banza ba. Kamar wancan hutun,
ranar hutu principal ta yiwadalibai assembly,
hutunne bashi da yawa sosaikwana ashirin da
takwas ne kawai zasu yi a gida.Amma wannan
karan direban gidansu rauda yazodaukar rauda
sai haisam ya ce ta tafi shima dagagidansu za'a
aiko da direbansa yazo ya daukeshi. Bayan tafiyar
rauda babu dadewa sai ga dalleliyarmotar haisam
kirar jeep da mahaifinsa ya bashibayan ya gama
bautar kasa, muntari sunan direbanhaisam, yazo
ya duka ya gaishe da haisam, haisamya nuna
masa jakar hannah ya ce ya dauka ya sakaa but.
Bayan ya saka hannah ta shiga baya, haisam na
gaba direba mutari yana tukawa suka fita
dagamakarantar. Haisam na nunawa mutari
hanya hargidan uwar biyu kamar waccan lokacin
suka iskeuwar biyu a shirye tsaf. Ta fito daga gida
bayan sungaisa, haisam yace da uwar biyu su
dauki jakarkayan su shifa cikin gida a ajiye, kaya
kala biyu kawai za'a bawa hannah da silifas faya
amma duksauran a ajiye da litattafanta. Da yake
safiyanu yabashi labarin duk yadda uwat biyu ta
gaya masaabunda ya faru da kayan hannah.
mutari direba ne ya taya su da shiga da kayan
cikingida. Uwar biyu ta zaba ma hannah kayan da
zatasaka ta cire uniform da kambas aka bata
silifas dawani kala daya a leda wanda zata tafi
dashi. Bayansun fito daga gida sai suka shiga
mota suka tafi,basu tsaya a ko'ina ba sai a tasha.
Wannan karan ma har bakin mota haisam ya
raka su hannah yadauki kudi mai yawa ya bawa
uwar biyu yacr suyikudin mota na zuwa can tayin
na dawowarta,sannan a ciki taba mahaifin
hannah na kashewa taajiye wanda zata je ta
daukota idan hutu ya kar
e.Yayi wa hannah nasihohi ya bata hakuri game
da halin da take ciki a gidansu.Daga karshe yayi
musu fatan allah ya sauke sulafiya. Ya juya ya
tafi uwar biyu na tayi masa godiyadashi masa
albarka hannah na rusa kuka

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100



GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 3
Posted by ANaM Dorayi on 02:12 PM, 30-Apr-15
Under: Gangarjikinsa ta Aura
Haka daiuwar biyu da hannah suka kasance idan
hutu yarage yan kwanaki sai uwar biyu taje ta
daukohannah. Haisam kuma baya gajiya da yi
mata siyayya duk abunda za'a bukata na
rayuwarmakaranta. Ko yayan masu hannu da
shuni na makarantarbaza su nunawa hannah
gata ba. Idan aka yi hutuhaisam yana kaisu tasha
ya sasu a mota uwar biyuta kaita gida. Amma
kuma kaya kadan uwar biyutake bawa hannah ta
tafi dashi garinsu kadandinma bata dawo
dasu,iya abu ta kwace tabawa yayanta ga bakar
wahala da ake bata, wujigawujiga hannah take
dawowa hutu kamar ba ita ba.Saboda wahalar da
take sha tayi duk sai tayi duhu.Amma daga ta
dawo makaranta kafin hutu ta sakefes da ita.
Kwanci tashi wannan ne hutun dasu hannah in
sundawo makarantar zasu shiga senior class wato
s.s1. Don haka duk uniform dinsu sai an sake
musuna seniors daban na junior class daban.
Don hakatun kafin uwar biyu taje ta dauketa
haisam yakawowa uwar biyu uniform din hannah
ta ajiye har ya dinka mata ya canja mata school
bag tsaleliyairin ta manyan dalibai, akwati
maitaya biyu yasayamata babba da karama.
Babbar ta zubaprovision karamar ta kayan
sawarta, kamar yaddayaga yayan attajirai ana yi
musu idan suka shigaajin manya. Ranar da aka
dawo makaranta safiyanu ya dawo da hannah. A
duk lokacindasafiyanu ya kawo ta makaranta
takan kirawokawayenta su zo su gaisa, yayan ta
take cewakamar yadda taga kowacce tana kiran
kawayentata gaisa da 'yan gidansu. Duk 'yan
makarantar sunayiwa hannah kallon wata 'yar
gidan gawurtaccen attajiri ko nusaiba da rauda
basu san ba dagagidansu ake yi mta siyayyar nan
ba saboda haisamyayi mata gargadi kada
tagayawa kowa labarintata rike surrinta. Rauda
da nusaiba sun dauka uwarbiyu kakarta ce kuma
babban mutum din da suketafiya duk hutu garin
kakanninta take zuwa. Ko a hira hannah bata cika
bada labarin yan gidansu basai dai tayi ta
sauraron na mutane. Masassakin budurci ya fara
sassaka hannah ma'anata zama budurwa kyau ya
sake fitowa. A gaskiyakyan hannah bazai iya
suffantuwa ba, farinta yasake haskawa, gashin
kanta ya kara tsawo sabidatayi wayon gyarashi ga
mayukan gashi kala kalada haisam yake siya
mata. Ranar wata social night da daddare ne
haisam ya hango hanna, nusaiba darauda sun
sha wandunan jeans da teasirt sun nufikatafaran
kantin siyar da kayayyaki kala kala dakecikin
makarantar. Suna tsaye suna siyayya saidariya
suke suna tafi, cikin sanda ya karasa kantindon
yaga me suke siya haka suna dariya. Wai ashe
rigar nono zasu fara sawa 'yan kanana. To shine
yakawo musu guda dai dai suke jin kunyar
siyakyma. Hannah tace'' ni dai ba don kunce a
siyobireziyar na dani ba da bazan siya ba, yanzu
fa dolebazan dinga sakewa ba zan dinga gani
kamar anaganin shatinsa ko hannuna yana fitowa
ta riga kowa yana gani'' rauda tace'' caf aini da
ganganzan dinga sakin hannun rigata don ta fito''
nusaibabata ce komai ba ashe ta hango uncle
haisam abayansu a tsaye tana ta kifta musu ido
basu ganiba. hannah tace'' ko da yake mun zama
senior har 'yanj.s.s 1 ma naga wasu suna sawa
fa, nusaiba zabi.Hannah na daddagawa, nusaiba
tayi gyaran muryataga dai basu san uncle haisam
na bayansu ba. Saitace '' ba ruwana ga yaa
haisam nan yana kinku''.Haisam ya kyalkyale da
dariya. Sai su duka suka juyo nan fa hannah ta
wurgar data hannunta taruga a guje, nusaiba da
rauda kuwa suka cusa tasua riga suma suka arce.
Haisam yazo ya dauki waccehannah ta wurgar shi
da mai kanti suka dingadariya. Haisam yace su
hannah yan mata Haisam ya dada kyau sosai
hankalinsa ya kwantaya zama mai kudi baya ga
albashinsa accountmahaifinsa ya bude masa yana
zuba masa ribar dasuka ci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login