Showing 30001 words to 31410 words out of 31410 words

Chapter 11 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

156

baya san
yaya zata yiba'' mai waya yace kudinkiyana tafiya
an dauka fa kisa a kunnenki kiyi magana. Sannan
hanna ta tuna yadda taga ana yibayan ta gaishe
da matar sai tace'' hanna kawarnusaiba ce.
Nusaiba nake nema'' matar tayi dariyatace'' oh
hannah ce ? Nice mami mahaifiyar aiyanusaiba ai
tana london har ma an samar mataaddmision
tana jiran sakamakon jarabawarta ne ta fara
karatu. Hanna tayi bakin cikin rashin
samunnusaiba a waya sai suka yi sallama ta
mikawa maiwaya kan wayar. Yace''minti uku kika
yi. Tace nawane? Ya fada ta dauko ta bashi
sannan ta juya ta tafimurna take kawai a
zuciyarta yau gata a kano tanawadaka da komai
irin na yan burni har kan waya yau ta rike lallai.
Wani mai tasi inyamuri baya jinhausa ta samu sai
suka fara yarawa da turanci .Tace suleman
cresent zai kaita ya fadi kudin ko ragibata nema
ba ita a tunaninta komai a burni a kaideyake ba'a
neman ragi kuma ita burinta kawaiyakaita taga
haisam. Suna shiga unguwar saita dauko littafin
ta duba lambar gidan ta gayawadireban ashema
a kofar gidan suke sai yace to ai gagidan ta zaro
kudinsa ta bashi ta fito daga motar yaja motars
ya tafi. Tsantsari, wani tsalelen gida negidan su
haisam yafi duka gidajen layin tsaruwahanna tayi
matukar mamakin ganin gidan su haisam saboda
bata taba zaton haisam dan gidangawurtaccen
mai kudi bane irin wannan .wasutsala tsalan
motoci tagani a wajen get din gidan sundosho
goma. Ta tafi kofar gidan makwabtansu tazauna
akan wata kwalbati tana tunanin yaddaza'ayi yau
taga haisam,Wani buzu mai gadi ne ya leko ta
jikin get yahango hanna a kofar gidan da yake
gadi sai yayiwuf ya fito yace'' kai me kana yi
anan ? Tace''waninake nema ''yace waye wani,
ba zaka tambaya bazaka zo ka zauna anan!
Hanna tace''haisam nacangidan. Yace''kace na
can gidan me yasa kazo nan ka zauna kuma,
kaima bakauye ne ko? Don kayikama da yan
garinmu masu yalalo yalalo gashi'' saisu duka
suka yi dariya shi da hanna'' mai gadin yaleka
kofar gidan su haisam yaji hayaniyar mutanesai
ya ce mata'' yauwa ga haisam din can sun fito
itada abokanayenta''hannah yace'' dan allah dan
garinmu kirawo min shi akwai maza bazan
iyazuwa ba. Buzu ya karasa wajen haisam ya
shaidamasa wata na kiransa. Haisam cike da
mamaki yatunkaro wajen da hanna ke tsaye sai
tasa gyale tarufe fuskarta. Ya karaso inda take a
tsaye yayi matasallama ta make murya ta amsa.
Yace wacece? Hanna ta sake make murya tace
bakuwa ce''haisam ya hada girar sama data kasa
yace'' wai kewacece in ba zaki fada ba zan koma
ina da abunyi''hanna ta yaye mayafin a hankali
ta bude fuskarta.Wai, kamar wanii hasken walkiya
ne ya haskewahaisam ido da yaga fuskar hanna
,cikin fara'a da mamaki haisam yace hanna!
hanna! Kece!! Tayilallausan murmushi tace'' yaya
haisam nice'' taduka ta gaisheshi. Taga haisam
ya caba ado dawata babbar riga mai aiki a wata
tsadaddiyarshadda fara sol yasa bakin takalmi da
bakar hulayayi matukar kyau. Tayi dariya
tace''yaya haisam yau kaine da babbar riga ? Har
kafi kyau haka'.Yace haba? Tace allah'' yace yaya
su baba. Dasauran yan gidanku? Tace sunanan
lafiya sunce nagaisheku. Yace to zaki shiga cikin
gida ku gaisadasu hajiya'' hanna ta dan yatsune
fuska tace'' kaisai dai watarab bi kunya nake ji
kuma sauri nake sai dai idan na dawo. Yace
daman ba nan kikazobane? Hanna tace ''ni kuwa
wa gareni a kanoidan ba kai ba? Gurinka nazo
baba ya aikonihaisam yace to gani fada min
aiken. Zumudin yajiabunda aka aiko ta ya kama
haisam. Tayi shiru tahau rufe fuska. Cikin zumudi
haisam yace'' haba hanna ki fada mun mana
kunyar me kike ji ne?Tace'' baba ne yace inzo in
fada maka cewar kazoka nemi aurena ta bakani.
Tu kafin ta karasa saitaga haisam ya fara dariya
da alama farin ciki yacika zuciyarsa. Ya kurawa
hannah ido na wani danlokaci yqce'' abunda kika
kasa fada daman? Ya sake yin dariya ya tsaya
kallan hanna wacce takerufe idanuwanta saboda
kunya ga tsananin farinciki.Haisam ya nisa
yace''yanzu baba da kansa yacekizo ki cemun ya
bani ke! Hanna ta amsa da''eh''yace yanzu ya
bani ke kacokan a matsayinmatata? Yanzu baba
ya yarda ki zama uwar yayanamun zama daya
dangina sun zama danginki,iyayena sun zama
iyayenki? Yanzu baba ya yarda na zama abokin
rayuwarki na dindindan har abada? Yanzuhanna
kin amince zaki zama abokiyar zamana harabada?
Hanna cike da fara.a da murmushi takeamsawa
haisam tambayoyinsa da ''eh'' haisam
yayimurmushi ya sunkuyar da kai na dan wani
lokacican ya dago ya kurawa hanna ido yayin da
kowannensu yake sakarwa dan uwansa
murmushida wasu masun kauna da suke firfitowa
dagaidanuwan kowannensu suna yiwa junansu
wanikallo mai kunshe da so, kauna muradi ganin
juna.Haisam yayi ajiyar zuciya ya nisa ya ce
alhamdulillahhanna na daukarwa allah alkawari
ba xika , sannan na cika burina dana kudira
akanki na ingakin kammala karatunki. Kuma
yanzu na dawo gidazan cika wani tsohon alkawari
dana dauka. Nan danan hanna ta kurawa haisam
ido ta dainamurmushin da take alamar bata gane
abundahaisam yake cewa ba. Haisam ya ce''
hanna na gode madalla , ki yimun godiya a wajen
mahaifinki .Good bye, good bye hanna. Ya fara
jada baya yanadaga mata hannu yana yi mata
murmushi . Bakintaya hau rawa tana so tayi
magana ta kasa . Gabadaya jikinta ya hau
karkarwa inda jakar dakerataye a kafadrta ta
sulmiyo wasu marokane suka wayar mata dakai
akan abunda haisam yake nufisuna cewa'' ango
haisam kasha kamshi fari maifarar aniya kagaa
ango na ramla, yan boko bayinnasara a daura
aure lafiya akai maka amarya gidalafiya. Wani
abokinsa ne ya taho da sauri yace dahaisam
''ana ta yin waya daga wajen daurin aure ance
waje ya cika kai ango kawai ake jira.muje ka
shiga nota mu tafi mana. Haisam daabokansa
suka shiga tsala tsalan motocinsu sukazo suka
wuce hannah anan a tsaye tana karkarwaido da
ido suke hadawa da haisam har suka wucesuka
tafi. Ta juya tabi motar da kallo har suka hautiti
suka kure. Sai hanna ta tsugunna a wajen ta
rushe da wana azababben kuka mai radadin
fita.Dakyar buzu mai gadin nan ya dinga bata
hakuri tadauki jakarta dankwalinta a hannu sai
gyalenta tayafa a kai ta tafi. Acaba ta hau har
tashar yan kurawannan karon ma taci sa.a tana
shiga mota ta cika .Kallo daya zaka yiwa hanna
kasan hankalinta a tashe yake matuka don
kwandasta sai da yayimagana sau uku yana cewa
ta bada kudin motartabata jiba, hankalinta yana
can tana tunanin damanhaisam ba sonta take ba.
Ramla yake so shine ita damahaifinta suke
yaudarar kansu . Yaya haisam meyasa kayi min
haka me yasa baka fahimci son dana ke yi maka
ba ? Ta nisa tace'' ko da yake bashi dalaifi bai
yaudare ni ba, ya taimakkamin ne sabodaallah ni
na dorawa rai sonsa. Bai san ina yi bakuma,
amma na rabu da farin cikin rayuwa na
rasamutum na farko dana taba hi inaso a
rayuwata,gashi tun bayan gama makarantarmu
ko bacci ma neman gagarata yake na kwallafa
raina datunaninsa da tsananin sonsa'' sai da
wata mata takusa da ita ta tattabta sannan
hannah ta farfadodaga tunaninda take yi.
Kwandasta yace kudinmota nake tambayarki kinyi
shiru kina tunani''sannan hanna ta zabura ta
dauko kudin mota ta mika. Mota ta bar cikin kano
ta kama hanya fetal saibabban mutum. suna isa
babban mutum tun dagatasha hanna ta dinga jin
faduwar gaba kafartakamar bazata iya daukar ta
ba dakyar take jefakafar burinta kawai ta isa gida
taje ta fada jikinmahaifinta ta sharbi kukanta son
ranta tunda duk duniya shine kadai ya rage mata
gaba dabaya.kamar yadda data shiga kano taga
mutanengarin suna ta kallonta har da waiwaye
yanzu ma agarinsu haka ta gani sai kallonta ake
tana tafiya harda masu nunata kamar basu santa
daba, hanna tayimamakin irin wannan kallo da
ake yi mat tace a ranta'' to ko sun san son maso
wani nake ? Wandanake so yayi aurensa da
wacce yake so'' kallon nandai da ake yi mata ya
daure mata kai. Haka daihanna taci gaba da
tafiya tana sauri ta karasa wajenmahaifinta shine
kadai mai lallashinta, mai gayamata kalaman da
zata ji dan sanyi a ranta. Ta kusa kofar gidansu,
kwatsam taga wata kungiyar mazadauke da gawa
sun yi gabas ana hailala. Tajigabanta ya fadi ta
dubi kofar gidansu sai taga taronwadansu maza
da yara a zazzaune ana jan carbitace a ranta'' ba
dai gawar babana bace waccan?Sai ta zubar da
takalmanta da jakarta ta shiga gida da gudu don
ta duba zaure shinfidar babanta yananan kuwa.
Tana shiga sai taga shimfidar wayambaya na ga
silifas dinsa da butarsa a gefe babandaki ya zaga
ba. Ga wannan furarsa gefesauran wacce ta
dama masa yasha ya rage. Nan danan taga su
iya salmai sun fito daga cikin gida suna rusa kuka
idonsu yayi jawur suna riketa suna cewasannu
hanna wannan ke aka yiwa mutuwa allah yajikan
mahaifinki da sunanki a bakinsa har ya mutu.sai
wani jiri ta kwashi hanna ta fada kanshimfidarsa
ta rirrike filonsa ta kudindine ta runtseido ji take
dama kasa ta bude ta fada da ita bakin cikin
rayuwa ya isheta. Ta kwalla kara tana karacewa''
innalillahi waina ilaihi raju'un allah kanasane
dani, allah ka san halin dana ke ciki. Allahbaka
tsaneniba, baka kuma manta dani ba. Bani
dakowa a duniya, babu wanda ya ragemin
kumaallah kaine gatana kai ka halicceni, ka halicci
mahaifina kuma ka halicci haisam. Ka hadani
dasumuka saba kuma kai ka raba ni dasu allah.
Allahkaine abun godiya. Allah na gode maka.
Allahkaine jagorana, allah kar ka barni na
dauwama acikin bakin ciki. Allahu akbar sai kowa
ya rushe dakuka. Hatta iya abu data tsani hanna
yau hanna ta bata tausayi matuka. Sai ta rushe
da kuka ta dingarike hanna.....Muhadu 2
dancigaban labarin


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login