Showing 18001 words to 21000 words out of 31410 words

Chapter 7 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

152

a kamfaninsu duk
wata yake warewa'ya'yansa, ga hannah ba laifi
ta girma wahalar datake sha a gida ta ragu
abubuwa da yawa ta fara takawa iya abu da
'ya'yanta burki tana kwatarkanta dole wasu
abubuwan suke raga mata. Donhaka kallo daya
zaka yiwa haisam kasan dan gidanwani
gawurtaccen mai kudi ne saboda suffarsa
ta'ya'yan hutu ce, fari ne sol fatarsa mai haske,
yanada dara daran ido da dogon hanci, mai
yawan gashin?idon dana gira gazar gazar . Wani
dan siriringemu ne ya zagaye dan madaidaicin
bakinsa(kautar million)gashi dogo mai dan
madaidaiciyarkiba. Haisam yana daya daga cikin
irin da kowacce'ya mace take mafarkin samun
irinshi. Gashi amakarantar yan mata masu ji da
kudi da kyau ga gayu. Don haka kusan kullum
haisam sai ya samiwasikun 'yan mata akan
teburinsa a ofis dinsa sunjefa masa. Wai suna
sonsa soyayya mai tsananikuwa sai kawai yayi
dariya ya yaga ya zubr kodakuma ya hadu dasu
bazai nuna musu yagasakonsu ba. Yan aji shida
ne suka fi yi masa wasikun amma wasu 'yan aji
biyar din suna rubutomasa shi gani yake suk
suna duk hauka suke zasugaji su daina. Gasu
kyawawa dasu amma bayaganin kyawun, 'ya'yan
attajirai amma shi baidameshiba, shi dai kawai
yazo ya cika burin da yakudira ya tafi. senior
juwairiyya itace shugaban dalibai (headgirl)
juwairiyya kyakykyawan gaske ce fara solharma
akan ce suna kama da hannah. Gatamahaifinta
wani babban manager ne a wani bankia lagos
tana ji da gata da dukiya ga tsananin kokaritafi
kowa kokari a shekararsu. Amma sai allah ya
jarrabeta da tsananin son uncle haisam tun ba
yauba gashi da yawa daga cikin malaman sun
mato a sontaita bata son su ta fi son haisam. Ta
aika masa dawasiku sunfi a kirga amma shiru ko
alama haisambaya nuna mata na yaga wasikarta
. Da ta gaji daaika masa da wasikun saita dinga
aika masakawayenta baro baro suke tarar sa su
gaya masa amsar daya basu cewa yayi duk
yarinyar data saketarar sa da maganan juwairiyya
saiya sabar mata.Don haka juwairiyya ta rasa
yadda zata yi ta shawokan wanda take so . Ranar
litinin da daddare an fitodaga (prep) juwairiyya ta
sami kan wata baranda tazauna tana tunani don
ita son haisam har ya fara dasa mata wani ciwo
da yake damunta a zuciya hartake kasa karatu
sosai gashi kuwa tafi duk yanmakarantar kokari,
don haka nema aka nada tashugabar dalibai.
Zaman da tayi wucewar haisamkawai take son ta
gani sannan ta iya bacci. Salahanura itace babbar
aminiyar juwairiyya tazi giftawa zata tafi ajinsu
taga kawarta a zaune a baranda itakadai, taje
wajen ta dade a tsaye a kanta juwairiyyabata sani
ba. Ta dafata sannan tayi firgigi ta dago .Salaha
nura ta zauna a kusa da juwairiyya
tace''juwairiyya tunanin meye kike, ke kadai kowa
yanaaji ? Juwairiyya ta nisa tace allah salaha
inasan uncle maikayu sosai har kamar zan zautu''
salaha tatuntsire da dariya tace'' uncle haisam
wai? Shegusunan da kuka saka masa kuma, to
juwairiyya yayazamuyi kin rubuta a rubuce yaki
kin aikemu yazazzagemu ko ke kika je da kanki ba
zai yadda ba.Kwarjini yake mun ba zan iya tarar
saba'' inji juwairiyya salaha tace'' to meye abun
yi? Juwairiyyata zunguri salaha ta nuna mata
haisam ne yatunkaro inda suke daga staff qurters
ya karasoinda suke su duka suka gaisheshi cikin
ladabi. Yace ''oh shugabar dalibaice da labour
prefect ? Sukace mune si'' yace ''wato kun kora
yara aji ku kunzo kun zauna kuna hira ko?
Kamata yayi kufi kowakaratu yanzu tunda kune
masu shirin yin waec daneco da jamb ko? suka
amsa eh ba hira muke bawani muke jira''
juwairiyya ta marairaice muryatace'' amma na
ganshi yanzu zamu tafi damanfatana in ganshi
kawai ''haisam ya gane abunda take nufi sai
kawai yayi sauri ya katseta ya ce'' idanzaku tafi
gashi kuje j.s.s. 1a science class ku bawahannah
abubakar imam. Ya mika mata wata leda adaure
ya juya ya nufi ofishinsa ya shiga sannan yarufo
kofar. Juwairiyya tace da salaha''kinga abunda
nakegudu ko shariya ce da wannan mutumin ko
fuskabaya bani da zan gaya masa abunda yake
damuna.Salaha nura tace'' to wai ni na lura
meye yaketsakanin uncle haisam da hannah
abubakar imamne ? Kamar duk makarantar nan
yafi kulata komai hannah zaka ji yana ambata
kamar shi ya radamata sunan. Juwairiyya tace''
ance abokin wantane wai, kuma saboda rauda
shitu kawar hannah itaai kanwarsa ce. Salaha
nura tace'' to kanwarabokinsa ai zai iya sonta.
Salaha ta karbi ledar da yabawa juwairiyya ta
kwance sai suka ga magunguna na ruwa da
kwaya ne , na zazzabidana tari ya saya mata.
Salaha ta tabe baki tace.Lallai magunguna ya
sayo mata tafi karfin ma tashana clinic din
makaranta kenan'' juwairiyya tace'' zomuje nasan
abunda zan hadawa yarinyar na''salaha ta taso
suna tafe suna zancen suka nufi ajin su hannah.
Juwairiyya tace'' ba uncle haisam yacekada wata
ta kuskura ta kara kai masa sakona bato ni kuma
hannar da yake ji da ita daga yau ita zandinga
aike wajensa. Salaha tace'' kwarai kuwahaka za'a
yi muga ko itama zai korota din'' tawundo
juwairiyya ta leka tace'' ina hannah abubakar ?
Yan ajin suka ce'' gata can a sit dinta akwance
bata da lafiya'' tace ''ko ciwon ajalo take tataso ta
zagayo tazo ina kiranta'' nusaiba ce tatasheta tace
'' hannah kije senior juwairiyya nakiranki'' hannah
ta daga ido dakyar tace'' bazan iyatashi ba bani
da lafiya'' jikinta zafi kyau kamar wuta. Jijiyoyinta
kanta sunyi rudu rudu don ciwonda yake yi mata.
Juwairiyya ta daka mata tsawatace da hannah ta
taso allah yasa asibiti ne a kantaba jinya ba.
Nusaiba da rauda suka rirrikota sukatasheta
tsaye. Juwairiyya ta daka musu tsawa tacemusu
munafukai su saketa tazo da kanta. Haka hannah
ta fara tafiya tana rirrike bango ta fita tazagaya
bayan aji inda suke. Juwairiyya ta mikamata ledar
da haisam ya bayar a bata suka ce''gashi inji
saurayinki. Hannah tayi jugum tanamamaki can
tace waye'' waye kuma saurayina?Salaha tace''
zaki sashi munafuka. Juwairiyya ta mika mata
wata takarda tace'' ki kaiwa unclehaisam kice ina
jiran amsa yanzu kice nace mikikarki sake ki dawo
min babu amsa'' hannah ta faratafiya jiri yana
daukarta ji take kamar ta fadi sabodayini cur a
kwance babu ko dan tea a cikinta. Ta isaofishinsa
ta kwankwasa yayi mamaki da yaji ana
kwankwasa masa kofa yanzu, ya tashi ya bude
saiga hannah a tsaye. Mamaki ya kamashi
yace''hannah lafiya ? Keda baki da lafiya kika
iyatahowa? Hannah ta cije baki gami da rike
bangokamar zata fadi tace'' aikoni wajenka aka
yi'' yace''aike kuma, waye ya aikoki? Ta mika
masa wasika tace ''inji senior juwairiyya da senior
salaha suncedole in taho musu da amsa kar inzo
babu amsa yabata rai ya karbi wasikar ya bude
ya karanta.Wasika ce irin ta kullum daga
juwairiyya ya cecirayuwarta tana sonsa.Haisam ya
cikuikuye ya wurgar ya ce'' sun
bakimagungunanki'' tace''ah ina ji sune anan'' ya
karbaya bubbude yana tsiyaya mata a murfi yana
mikamata sai ta karba tasha. Sai da ya tabbatar
ta shadukka sannan ya daure ledar ya mika mata
ya ce tawuce daki ta kwanta gibe idan taga baza
ta iya fitowa aji ba tayi kwanciyarta zai sanarwa
da dutymaster. Daga karshe ya ce'' sai da safe
allah ya bakilafiya hannah. Tace amin '' har ta
juya zata tafi sai tatuna ta juyo tace masa'' me
zan cewa seniorjuwairiyya ? Ya ce'' kice nace tazo
ta karbi amsar dakanta. Hannah ta amsa da to
sannan ta tafi. Daman su juwairiyya na zaune a
wata baranda suna hangosu. Hannah tazo
wucewa suka kirata tace musu takai masa ya ce
amsar taje da kanta ta karba. Salahatace'' jeki
to'' juwairiyya ta nisa tace'' kinga haisamko
wallahi wulakanci yake shirin yimin tunda ya
ceinje da kaina ni nasan ba wata maganar
amincewa zaiyi min ba. Saboda ai nagani
cukuikuye wasikartawa yayi ya yar a kasa, ya
buge da bata magani aidole ma son hannah
yake'' salaha tace'' ammakuwa sunan yarinyar na
gawa don sai taci ubanta amakarantar nan , mu
'yan s.s.3 muce muna sonsayaki ya so junior mu
ai bazai yuba. Jeki kiji abinda zai fada muki don
muci uwarta da hujja'' juwairiyyata mike ta nufi
ofishin haisam tana wani karkaderiga tana gyara
fuska. Tayi sallama gami da turakofar zata shiga
ya dakatar da ita da hannu yace''tsaya daga nan
baranda kiji abunda zan fada miki.Don me kika
sake yimin aiken wasika bayan nace kada wanda
ya sake zomin da wasikarki. Kumawanne rashin
tausayi ne da zaki taso yarinya mararlafiya ki
aikota, duk daliban makarantar nan, saihannah ?
Me yasa sai ita zaki aiko juwairiyya ?Juwairiyya ta
tsuke fuska tace'' amma uncle haisamduk aiken
dana keyi baka taba kirawoni kace meya sa nake
aiko kawayena ba sai dai kacewayan aiken duk
wacce ta sake zuwa zaka sabarmata. Meya sa
baka fadawa yar aiken ba a wannankaron sai ni
ka kira ? Haisam ya fusata ya dakamata tsawa
yace'' ina tambayarki kina tambayata ?To kar kiji
yauce rana ta karshe da zaki yimin haka. Ki rike
darajarki da mutuncinki a matsayinki na yamace
budurwa. Idan sai kinyi soyayya a makarantaba
karatu ya kawo kiba to ga sauran malaman
dasuke rubibin sonki amma ni bani da
ra'ayinsoyayya, this is the last warninng bana son
na sakeganin sako daga wajen ki sai anjima kije.
Wani jiri jiri juwairiyya take ji ta juya ta tafi tana
kwafa.Salaha tazo ta tare ta a hanya tana cewa''
meyenake hangoki a baranda ofishinsa ma ya
hanakishiga ? Juwairiyya tace'' ke dai muje in baki
labarinyadda muka yi'' daman lokacin tashi daga
prepyayi duka dalibai sun dungumo daga
ajijuwansu sun doshi dakunansu. Don haka
juwairiyya dasalaha nura sai suka nufi hostel a
hanya ta zaiyanamata duk yadda suka yi da uncle
mai kyau watohaisam. washegari talata da
sassafe bakwai da rabia lokacin dalibai suke
firfitowa daga dakunansuzuwa ajijuwansu domin
daukar darussa. Uncle haisam a tsaye yake kem a
bakin get din hostelyana kallon masu fitowa daga
ciki, mamaki yakama dalibai ganin sabon al'amari
meye unclehaisam yazo ya tsaya anan da sassafe
haka bashine da duty ba, ba ranar inspection ba
kuma.Kowacce idan ta ganshi sai ta duka ta mika
gaisuwa ta wuce'' good morning sir'' can ya
hangorauda da nusaiba da pamella suna tahowa
daganesa ya dauka hannah ce sai da suka karaso
yagababu hannah a cikinsu. Bayan sun gaisheshi
ya ce''yau kuma ina hannah ko jikin ne ? Rauda
ta waigagaba da baya taga babu kowa sai ta
matso kusa dashi tace'' hannah ba lafiya tana
clinic a kwanceacan ta kwana'' gabansa ya yanke
ya fadi ya ce''zazzabin ne ya rufeta ? Nusaiba
tace'' wannan yafizazzabi yaya'' rauda tace'' su
senior juwairiyya nesuka yi mata duka da tsakar
dare kusan dukkan s.s3 sai da kowacce ta doki
hannah jiya ina ji a sume ta fadi da kyar matron
suka zo suka hana su. Mumabamu san me tayi
musu ba. Kuka mu ma mukakwana muna nan da
nan haisam ya canja ido yakada yayi jawur gashin
jikinsa ya mimmike kai kacemuku mukun sanyi
ake amma duk da sanyin safiyazufa yake yi. . Ba
tare daya ce tak ba ya juya ya nufi clinic inda
hannah take a kwance ya same ta rikkicifbata
sanma inda hayyacinta yake ba. Abinka dafarar
fata sai sabun bulalan suka mata jawur a jiki ,har
wuyanta da fuskarta shatin bulala ne lambar.Ya
dade a tsaye yana kallonta kawai yasa hannu
yacire mata wani ganyen maina daya makale
mata a wuya a sanadiyar duka sai yaji jikinta zafi
kaukamar wuta, yaja mayafin dake kan gadon
yalullubeta. Babu kowa a clinic din nurse din ma
batanan. Ya juya ya fita a fusace ya nufi ofishin
principal.Ya shiga ofishin gami da yin sallama ya
sami wajeya zauna bayan sun gaisa ta dubi
haisam tace''haisam lafiya yau na ganka ranka a
bace dukwannan fara'ar taka ? Ya ce''dole raina
ya bacisaboda kusan kashe wata yarinya akayi a
daren jiya a makarantar nan 'yan aji shida ne
suka dakiwata yar aji hudu da tsakar dare kamar
zasukasheta tana clinic a kwance'' principal ta
zaburatace'' subhanallah'' ta danna kararrawa
masinja yashigo tace maza yaje aji shida ya kira
matajuwairiyya. Haisam da principal na zaune
sunyi jugun kowa yana tunani a zuciyarsa. Can
saigajuwairiyya ta karaso ita da wani malami mai
sunasahabi tazo ta dutkusa a kasa ta gaishe
daprincipal. Principal ko amsawa bata yiba ta
rufejuwairiyya da fada tana cewa'' in har ba zaki
iyahana a aikata laifi ba a makarantata banga
amfaninki ba a matsayinki na shugabar
dalibai''haisam yace'' madam ai itace ta gaiyato
sauran yanaji shidan suka hadu sukayi dukan''
principal tace''oh har da ke head girl kuka hadu
aka kusa kasheyarinya, kiyi kneel down yau sai
kun yabawa ayazakinta'' uncle sahabi yayi carab
ya ce'' madam tsaya kiji, juwairiyya ta fadamun
duk abunda yafaru daman zamu taho wajenki
muka hadu damasinja a hanya a gaskiya yarinyar
ce bata dakunya wai cewa tayi zata yi dambe da
head girlshine juwairiyya ta danyi mata bulala
uku labourprefecr tayi mata biyu. Ga yarinyar can
ma a aji tana daukar darasi babu wani zancen
kisa'' haisam yafusata yayi kan sahabi da fada
yana cewa'' karyazanyi musu? Yarinyar da duk
makarantar nan babumai shirunta da ladabi
yaushe zata ce zatayi fada dahead girl ? Kawai
baza ka tsaya kayi bincike ba donsun gaya maka
karya da gaskiya shine zaka yarda, kaje clinic
kaga jikinta a farfashe bata san ma
indahaiyacinta yake ba . Sahabi ya ce '' madam
donallah ki raba mana rigima ki aika clinic a dubo
idanakwai wata marar lafiya. Babu kowa ta warke
tamike ba'a gabanmu hannah tazo ta wuce ba
dazuko ba hannah ba ce wacce kake cewa an
kusa kasheta ? Kuma kai duk wannan hakilon da
kakecewa akan hannah saboda kai saurayinta ne
fa shiyasa kake wannan sauran da ake duka ka
tabamagana ? Principal ta lura maganar babba ce
saimanya sai tace da juwairiyya ta tashi ta tafi
zata aikoayi kiranta. Fuskar juwairiyya cike da
murmushi ta fice principal ta kalli haisam tace''
kwarai tun ba yauba ansha fada mun kana
soyayya da hannah.Dokar makarantar nan an
hana daliba da malamiyin soyayya . Yanxu na
gane manufarka don andaki budurwarka shi yasa
kayi magana ko? Dagayau zan sa c.i.d kada ka
kuskura in sake jin ance kana soyayya'' haisam ya
fusata, ransa ya bacizuciyarsa ta hau tafarfasa.
Ya dakawa sahabi tsawayaje har gabansa yana
nuna shi da hannu ya ce''kai sahabi karya kake
yi ni nafi karfin ka yi minsharri kai da juwairiyya
zaku gane kuranku amakarabtar nan. Ni kake
cewa ina son hannah ko ? Bayan da bakinka kazo
ka sameni kana rokona inhadaka da kanwata
hannah kana sonta naki nacekabarta tayi karatu
ashe kana kullace dani kasaaka yi mata wannan
dukkan ko ? Ke kumaprincipak kin goyi bayansu
sun daki yar mutabe abanza ko ? To ni sai na
daukarwa hannah fansa da kaina'' ya kada kai ya
fice. Sahabi ya juya ya kalliprincipal yace'' kinji
kuma inda ya lauya maganako ?tace ''kyaleshi
bayan kai ma mr.ojo ya fadamun cewa son
hannah yake don haka kaci gabada kula dasu.
Haisam ya nufi staff qurters ya shigagidansa ya
zauna a falon yana huci kamar ya kashe kansa
yake ji saboda tsananin bakin ciki yau kodarasi
ba zai je yayi ba. Yini yayi cur a gida ya
kudiriniyyar zai dauki fansa akan duk mai hannu
a cikinwannan al'amari , wai sahabi ne zaiyi masa
hakasahabin da ke zuwa har gida yace ya
taimakeshi yashawo masa kan hannah wai
juwairiyya da kanta take cewa rashin kunya
hanna tayi mata zata yidambe da ita wai shine
tayi mata bulala uku itakuma principal da kanta
take bin bayansu bayantasan hannah tasan
halinta tasha yin kwatance daita a wajen
assembly akan tafi kowa da'a da ladabishine har
ta yarda da kintsin da suka yi mata ko da kyau,
haka haisam ta dinga nanatawa a zuciyarsa
.Haisam ya dinga nanatawa a zuciyarsa. Haisam
baifita daga gida ba sai da yamma misalin karfe
biyarya shigo cikin makaranta a lokacin dalibai
sunaprep din yamma ya wuce kai tsaye ajinsa
don yagajikin hannah, a zaune ya ganta a kan
kujerarta ba laifi jikin burdin bulalan ya dan
warware zazzabinya sauka sai dai bata iya bude
idanuwanta sosai. Yace da ita'' hannah ya
jikinki ? Cikin sanyin muryatace'' da sauki'' yace
kinsha magungunan naki?Tace eh nasha'' wani
masinja ya leko ajin yacemalam haisam kazo inji
principal. A fusace haisam yace meye kuma? Dan
aiken ya ce'' waya aka bugomaka zaka dauka a
ofishinta'' ya ce gani nan zuwahaisam ya juyo ya
dubi rauda da nusaiba ya ce'' kudinga kula da
hannah ku tabbatar tana cin abincikunji ko ? Suka
amsa da'' to zamu kula da ita.Sannan ya fita
daga ajin ya nufi ofishin principal yana isa ofishin
yayi sallama ya shiga ya gaisheta amurtike. Tace''
yayanka ne habibu yake son yayimagana dakai
nace ya kira nan da minti biyar za.akira....'' kafin
ta rufe bakinta wayar ta fara karahaisam yasa
hannu ya dauka ya gaishe fa yayahabibu yaji da
kyar habibu yake amsa wa rai a bace habib yace
kai haisam mu fa ba yara bane kananakana ji ko?
Saboda me zaka dinga yi mana wasa dahankaki ?
Kace shekara uku zakayi a makarantarnan sannan
ka bari yanxu shekara uku sun cika,Saboda me
zaka dinga yi mana wasa dahankali ? Kace
shekara uku zakayi a makarantarnan sannan ka
baru yanzu shekara uku sun cika,last week da
kazo aka gaya maka cewar ka barteaching dinnan
ka dawo gida da kamfanoninbaba aiki yayi mana
yawa muna neman ma'aikata, kace da zarar ka
koma kafin karshen watannanzaka dawo gida
kabar koyarwa gashi munji kashiru. Kujerarka na
nan na jiranka ga ramla nan najiranka itama. Har
anyi bikina da jidda har ta haihu'yar mutane na
zaman jiranka kazo ayi bikinku. Waishin me ka
zamar da mune, har nawa kake da zaka dinga
juya mu ? Don haka karka sake nazomakarantar
nan da kaina ka rubuta takardar barinaiki kabar
koyarwa nan ka dawo gida muna nanmuna
jiranka. Kai baka kishin dukiyar ubanka
saigwamnati zata baka da kake mata wannan
wahala,me kake nema ka samu wanda a gidanku
baza a baka ba ? Haisam ya fusata yace'' ka
gamamaganarka ? To bari in fada maka gaskiya
ba zanbar koyarwa ba ina nan bazan dawo gidan
ba'' yakifa kan wayar ya fice. Principal ta bishi da
kallo harya fice. Wayar ce ta sake yin kara tasa
hannu tadauka taji habib ya ce''ina haisam din?
Tace ''ya fice'' ranki ya dade kema harda laifinki
tun rannanbaba ya kiraki har gida ya ce kiyi
murda murda kisaa koreshi daga makarantarki
zai biya ki ko nawane. Kika ce bazai yu ba.
Wannan yaron ko kasheshiza ayi bazai bar
makarantar nan ba. Wanne irinlallashine ba'ayi
masa a gida ba yaki ya bar koyarwa'' principal ta
nisa tace'' habib tunda kajinace bazan iya sawa a
kori haisam ba to babuyadda zanyi saboda
wannan makarantar tagwamnatin taraiya ce daga
kololuwa aka daukihaisam haka kuma korarsa sai
daga can abuja.Dana bincika ma babban director
na federal shine ya dauke shi aiki alh.sabi'u
auwal abokinbabankune ko? To babu kuwa yadda
za'ayi nahada baki dashi a koro haisam daga
makarantarnan habib ya ce''zanzo makarantar
watakila nan dasati biyu, idan na dawo daga
tafiya dole ne ma yabar makarantar donyaga ana
yi masa sakwa sakwa ya dauka tsoronsa ake yi
don ni banga uwar dayake samu ba a
makarantar'' a haka suka yisallama suka ajiye
kan wayoyin. BAYAN SATI asheda sahabi ba kadai
akwai malamai da yawa dasuke son hannah. Sai
yanzu suka dinga baiyana.Ranar talata data
zagayo haisam da sauran malamai uncle sahabi
da uncle yusuf suna zaune a gindinbishiya da
prep din yamma sai uncle yusuf ya aikawata
yarinya ya ce taje s.s. 1a ta kira masa
hannahabubakar . Haisam na zaune yana
tunanin lafiyayake kiran hannah. Hannah ta
karaso tazo tasurkusa ta gaishe su uncle yusuf
bai amsa ba yace'' hannah yau zan nuna miki
karshen taurin kai,girman kai daji da kai. Don
haka kije ki karyo bulalakatuwa mai kauri dai dai
tsawanki ki kawo min''haisam na zaune yana
kallonsu hannah ta tashijikinta a sanyaye ta nufi
dawa, can ba dadewa tataho dauke da wata
zabgegiyar bulala. Tazo ta durkusa ta mikawa
incle yusuf ya ce tayi kneeldown ta daga hannu
ya kuwa tashi ya farazabgawa hannah wannan
reshen. Haisam ya kauda kai gefe kawai yayi
shiru, yusuf yayi mata bulalakamar sau takwas
sannan yace ''kin san me kika yimin? Cikin
sheshshekar kuka hanne tace'' ban sani ba '' ya
sake daddagewa ya sakar mata wanidukkan
yace'' kin tuna yanxu? Cikin gigicewahannah tace
na tuna''ya ce'' to me kika min? Tacejiya daka
aiko kace inzo in sameka a lambu banzoba'' ya
ce'' yauwa ashe dai kin gane yau sai nalahira ya
fiki jin dadi don kin samu ma ana sonki , ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login