Showing 27001 words to 30000 words out of 30449 words
wears and accessories) a lokacin duniya na kwance, kasuwanci yanada albarka. Sai Allah ya hada Yohan da Mukhlis duk da bambancin addini sakamakon son da yake yiwa tilon kanwarshi.
Shi Yohan bai taba haihuwa ba da matarshi Marye, shi yasa yake son kanwarshi Anita kamar shi ya haifeta, gata da hazaka a makaranta, ita ma Marye tana son Anita saboda yarinya ce kyakkyawa mai shiga rai. Har yau Yohan bai musulunta ba, sai dai ya bar Anita (Asma’u) ta yi addinin da ta zaba shi kam banda shi.
Kuma fa Hausawa ne, Hausa rangadadau a bakinsu kamar jakan Kano, amma basu yarda da addini ba, Neither Islam nor Christianity, Budduism, Hinduism, Jainism, Sikhism Paganism, Rastafari, Taosim ko kowanne ma.
Ta wannan kasuwancin Mukhlis da Yohan suka yi kudi na ban mamaki. Mukhlis ya sayi gida a Jos, kawai don Yohan ya yarda ya aura masa Anita. Suka ci gaba da kasuwancinsu Anita na girma. Mukhlis ya sayi kadarori da yawa a Jos don a nan yake son kafa tubalin iyalinsa.
A lokacin kasar Egypt na fama da matsin durkushewar tattalin arziki kamar Sudan. Larabawan Egypt da yawa sun warwatsu a duniya don neman halalinsu. Garin Hurghada a can matsin yafi yawa. A Larabce ana kiran Hurghada da El-Ghardaqah).
Da yawa sun shigo cikin Cairo suna leburanci masu ilimi sun tsallaka kasashe irin Saudiyyah, Dubai, Bahrain, Kuwait, Taiwan, Dammam Qatar da sauransu. Wasu sunyo Africa irin su Mukhlis kenan.
Duk dimbin iliminsa a kan Geography ya fi ganewa kasuwanci, kuma Allah ya sanya mishi albarka a ciki. Har ya soma tsallakawa kasashen da suka ci gaba yana kawo kayan daga can, musamman Saudiyyah, akwai wani shago a Madina wai shi Majma’al Qimmah da ya shahara wajen kayan yara, Mukhlis na daya daga cikin manyan dilolinsu.
Sanda Anita ta shiga aji shida na sakandire shekarunta goma sha biyar, sai tsahon kafa kawai. A lokacin ne ya nemi Yohan da bukatarsa na neman iri a wajensa.
A lokacin shi Yohan yana shirye-shiryen komawa kasar Ireland shi da Marye, inda harkokinsa suka fi yawa. Shi abin ma dariya ya bashi, wai Mukhlis ya yiwa Anita tsufa duk da bai taba aure ba. Sai dai shi kansa ya san bai isa ya hana Mukhlis Anita ba, ba don su basu da addini ba su, sai don shakuwar da ke tsakaninsu ta tsayin shekaru masu yawa.
Tun Anita na ‘yar shekara biyar Mukhlis yake kula da ita da daukar nauyoyin rayuwarta. Da dora ta a kan hanyar tarbiyya kamar diyar Musulmi. Ya dora Asma’u a kan turbar yin shigar da ba ta fidda tsaraici ba, sun sha yin sallah shi da ita a boye.
Haka ya taka rawa wajen kara mata karfin gwiwa a kan ilimin zamani. Har abada Asma’u ba za ta manta da Mukhlis ba, har abada hoton wannan ranar ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba. Wato ranar da Mukhlis ya danka sadakinta a hannun Yayanta Yohan, ‘yan’uwa da abokan arziki suka shaida.
Bai kuma taba ta a ranar ba sai da ya lakana mata LA’ILAHA ILALLAHU, MUHAMMADUR-RASULULLAHI a bisa ra’ayi da yardarta. Don zuwa lokacin Anita ta yarda su dabbobi ne kawai sakamakon cakudo da musulmi a makarantu da take yi da kuma tarayyarta da Mukhlis, tana ganin yadda yake tafiyar da ibadar addininshi yana burgeta, su haka nan suke kara zube, kamar katakwaye da duwatsu. Babu direction.
Mukhlis shi ya sanya mata suna Asma’u, sunan mahaifiyarsa bayan yin shahadarta. Wata da watanni Mukhlis na koyar da Asma’u hukunce-hukuncen addinin gaskiya. A karatun Alkur’ani da yake koya mata sun zo izfi ashirin ya kuma dauketa ya sanya a Islamiyya, kasancewar shi ba mazauni ba.
Sai da ya tabbatar ta ilmantu ta zama cikakkiyar Musulma sannan ya fara mu’amalar aure da ita. Rayuwar auren Asma’u da Mukhlis rayuwa ce mai dadi amma takaitacciya. A lokacin Yohan da Marye suna Ireland sun tafi sun barta da mijinta, wanda ke tattara komai nasa a Nigeria cikin nutsuwa domin ya koma gida tare da matarsa. Allah ya aiko da mummunan hatsarin jirgin ‘Egypt Air’ wanda ya taso daga Cairo zuwa Nigeria har da Mukhlis a ciki.
Asma’u dai sakamakon wannan labari sai nakuda ta tashi, ciki wata takwas sai fedeta aka yi don ta kasa haihuwa. Aka fidda yaro namiji mai kama da ita, amma kalar mahaifinsa.
Bayan takaba da zuwan dangin Mukhlis suka sai da duk wata kadara tasa suka auna suka yi gaba, sun ki sauraren kowa a kan matar da Dan. A lokacin Yohan na Ireland kuma babu hanyoyin sadarwa irin na yanzu.
Asma’u gidan Yohan ta koma ita kadai ta ci gaba da rainon yaronta wanda take yiwa wani irin masifaffen so kamar yadda take son Mukhlis Abu-Arab, tana amfani da ajiyarta ta banki da Mukhlis ke zuba mata duk wata tun aurensu da sunan asusun ajiyar ko-ta-kwana.
Yau da gobe ba ta bar komai ba, kudin banki suka kare. Ko kudin da za a saiwa yaro madara babu, saboda tana da karancin ruwan nono. Haka nan ta yi ta fadi-tashi har da wanke-wanke da shara gidan masu akwai don kawai ta samu abin da za ta sanyawa Abdullahi a baki. Ba ta damu da kanta ba, she only want to save his life..... Asma’u har kosai da fanke ta sayar, a kofar gidansu take soyawa safe da yamma da kuruciyarta da komai, duk saboda Khalipha. Khalipha na da shekara daya Allah ya jefo Yohan gida.
Kuka na duniya Yohan ya yi shi da ganin yadda tilon kanwarsa wanke-hannu ka taba ta koma rufe hannunka sannan ka taba. Amma fa yaronta bul-bul very energetic, diety.
Ita dai ce cikin tsummokara, amma danta tsaf cikin napkin mai tsafta da riga mai kyau har kamshi yake. Rasuwar Mukhlis da abin da danginsa suka yiwa Asma’u da danta ya taba zuciyar Yohan. Abin da ya kai shi ga yin alkawarin har Khalipha ya mutu ba zai kai musu shi ba, zai rike. A satin suka daga Dublin.
Abin da Yohan ya fara yi domin inganta rayuwar Asma’u da danta shine samar mata gurbi a Jami’ar Trinity, ta fara karatun medicine cikin himma. Ba ta yi nisa da karatu ba Khalipha ya soma wani rashin lafiya, sai hankalinta ya rabu biyu, don ma Marye tana taimaka mata da hidimarsa.
Zama a Turai bai sa Asma’u ta canza daga addinin da ta karba da zuciya daya ba, ba ta son barin danta hannun Marye don ta san ba ta da tsarki. Ta fi so ta kula da danta da kanta, ko ina zata tura shi take cikin keken zaman yara, sai dai dole lokutan daukar darasi take barinsa da Marye.
Likitoci sun sha bincike a kan dalilin da ya hana yaro Khalipha barci kullum cikin dare sai kuka, inda suka gano cewa ciwon hanta ne (Hypertitis B). Allah ne ya yi kawai Khalipha rayayye ne ba maganin asibiti da kwakule-kwakulen likitoci ba.
Asma’u ta ji jiki ta sha wahala da danta Khalipha, Yohan da Marye sun taimaka. Ta yi ta yi su Musulunta sun ki. Rashin lafiyar Khalipha ne yasa ta dauki bangaren likitancin yara paedatric don kawai ta kula da lafiyar Khaliphanta.
Haduwarta da Mansur Balarabe Sardauna, ta samo asali ne a matsayinsa na daya daga cikin malamansu, a lokacin shi ya yi graduating yana aikin da ya zamewa duk wani foreigner dole bayan kammala karatu kamin ya koma kasarsu.
Ya lura in ana darasi tana yawan fita ta je ta shayar da baby a hannun wata dattijiyar Balarabiya da take aikin leburanci a Jami’ar, take rike mata dan saboda Allah, don ta lura Asma’u ce kadai Musulma a bangaren da take kula da shi. Amma abinda yake daukar hankalin Mansur da Khalisah (dattijuwar), basu taba ganin uban dan ba, ga shi Balarabe ziryan ita kuma da ganinta ka ga ‘yar Nigeria.
A al’ada irin ta Bature, mace mai aure kusan koyaushe tare take da mijinta duk inda za su je, balle idan akwai karamin yaro kusan uban ne ke da wannan alhaki na kula da yaron a lokacin zirga-zirga, shi zai tura shi zai dauka, basa barin matansu su sha wahala.
Hazakarta a karatu na ba shi mamaki yadda take yin zarra da manyan maki (marks) a cikin Turawa. Ya damu da al’amarin ta, gata yarinya karama da ko ashirin ba ta rufa ba. Idan yana lacca kusan rabin hankalinsa a kanta yake, idan tambaya ce ita yake jefawa, ba ta yin kasa a gwiwa wajen farke masa zare da abawa.
Tafi-tafi Mansur ya kasa sukuni da tunanin Asma’u da begenta dare da rana. Uncle Yohan shi yake daukar nauyin karatun Asma’u, ba yadda bai yi ba don ya samo mata Nanny din da za ta dinga kula mata da Khalipha a gida ta je ta dawo tunda ba ta son shi a hannun Marye. Asma’u ta ki.
Ya ce, zai dinga kai shi gidan raino na Turawa shima ta ki. Don haka ya yi fushi ya rabu da ita kamar akan ta aka soma haihuwa. Ga shi Allah ya jarrabi zuciyarsa da son Khalipha kasancewar shi Allah bai ba shi haihuwa ba.
Daga shi har Marye kyamarsu take, ko abincinsu ba kowanne take ci ba. Don a Jos Marye murde kan kaza take da ranta ta cizge ta cillar ta fige ta dafa. Ire-iren wadannan yasa Asma’u ta gwammace Yohan ya ba ta kudi ta sayi ‘halaal’ ta dafa da kanta ko ta yi take away daga makaranta a wajen larabawa musulmi ko Pakistani mazauna turai.
Asma’u bata takurawa Yohan da cewa lallai sai ya Musulunta ba, don ta lura tana tufka ne Marye na warware mata, ko yaso ya saduda zigar Marye ke hana shi. Tana nuna masa cewa addinin Musulunci addini ne na takurawa kawai, sannan Musulmin da ya zama kasurgumin Musulmi shine yake zama terrorist (dan ta-adda).
To Allah shi ke hukunta al’amura yadda yaso, idan ya so bawanshi da shiriya ruwa da iska basu isa su hana ba. Marye ta yi mutuwar wulakanci a Dublin inda wani ginin bene ya rubza da ita da jama’a masu dimbin yawa, ko gawarta sai part-part aka tattara, sauran namanta ya zama na ungulu da tsuntsaye.
Asma’u ta ja dan’uwanta a jiki, dare da rana, yini da safiya tana kwadaita masa dadin addini musamman na Islam. Ta kan ce, “Shi Musulunci haske ne kuma guidance ne, wanda zai sada dan Adam ga nutsuwa da kwanciyar hankali, hanya ce kawai dake nuna maka yadda za ka rayu a kan tafarki madaidaici. Tsani ne mai mika mutum kusa da Ubangijinsa yaje ya iske sakamakon abin da ya shuka a rayuwarsa ta duniya.
Ba abin da addinin musulunci bai koya mana ba, hatta shiga bandaki, tsarki, wanka, cin abinci duk Islam ya kawo su a kan hanya sahihiya (to the heaven)” Haka dai, yau da gobe har Allah ya taimaketa ta yi galaba a kan Yohan, ta kai shi wajen Limamai suka musuluntar da shi ya mai da sunanshi Yahya. Hakan bai hana har yau jama’ar da suka san shi kiranshi da Yohan ba.
Yohan (Yahya) ya shiga Islam ne da zuciya daya. A wannan lokacin Yohan ya yi karfi na ban mamaki cikin kasuwancin da yake yi tsakanin Ireland da Nigeria. Ta hanyar Asma’u ya auri wata mutuniyar Somali zaunannun Dublin wai ita Aasiya. Ba ta taba yin aure ba amma ta manyanta domin cikakkiyar likitar mata ce.
Shekara ba ta kai ga fita ba Dr. Aasiya ta haihu da namiji. Ashe matsalar daga Marye ne ita din ta sani likitoci sun gaya mata, wannan ne yasa ta san duk hanyar da ta bi ta hana Yohan zuwa asibiti a bincike su sai karyar bari (miscarriage) take masa.
Har lokacin Asma’u na jinyar Khalipha dake fama da hypertitis B. Zuwan Aasiya gidansu ya kawo sauki mai yawa cikin rayuwarta duk da ita ma Aasiyar ma’aikaciya ce a babban asibitin kasa amma tana taimaka mata sosai wajen rainon Khalipha har Allah ya raya shi, ta kai shi wata Islamic school a London (Al-Muntada Islamic Pri. Sch.) boarding, ita kuma ta koma Dublin. Duka cikin aljihun Uncle Yohan.
A shekarar Dr. Aasiya ta kara haihuwar diya mace, a wannan lokacin shekarun da Mansur zai yi yana aikin wucin-gadi da jami’ar Trinity sun kusa cika, zuwa lokacin ya yi duk binciken da zai iya a kan Asma’u, ya tadda komai, wato ba ta da aure, uban dan ya rasu.
A matsayinshi na Bahaushe Ba-Kano kuma wanda ya fito daga jinin sarautar Takai abin ya zo a karkace, saurayi da auren bazawara mai da. Duk da addininmu bai hana ba, karewa ma hakan sunnah ce, kuma ya san yayansa Abdulkadir ba zai taba ki ba. Shi a kaunar da yakewa Asma’u ma, ko kantin kwari ta haife zai rike mata, kuma in ta amince zai aureta.
Kai tsaye bai doshi Asma’u ba, domin ba fuska, kullum suturce take cikin yalwatacciyar suttura da karamin hijabi iya kafadunta. Sai ya bi ta hanyar da kowacce UWA ba za ta iya kaucewa ba.
Wato yaje ya yi kawance da dattijuwar lebura Khalisa, yake tayata hidimar Khalipha kafin Mamanshi ta kai shi makarantar kwana. In ba shi da lacca wajen Khalipha da Khalisa yake lalacewa. Siyo wannan, siyo wancan duk na Khalipha.
Har Asma’u ta fara mamaki saboda ta san ko shi wane ne a Trinity da tarin iliminsa. A hankali suka soma gaisawa, tunda an ce mai Da wawa. Wani irin so Mansur kewa Khalipha wanda ko shi ya haife shi sai haka, ba kuma don komi ba sai don kamanninsa da mahaifiyarsa. So na hakika shine ka so uwa tare da dan ta.
Sai ga Asma’u na gayar da Mansur Takai kullum, har in ba ta ganshi ba ta hau tambayar Khalisa yau Baban Khalipha bai zo bane? Khalisa kan ce, ya zo ya sumbace shi ya ba shi chaculates ya tafi. Sai Asma’u ta yi murmushi har ta kai Khalipha London a bisa shawarar Mansur a haka suke.
Mansur shi ya lalubo mata makarantar kasancewar ya zauna England kafin Ireland inda ya yi karatun share fagen shiga jami’a. Ya fita sanin UK da Islamic Schools masu yawa dake cikin ta. Sai kuma aka koma kawance har cin abinci take gayyatarsa gidansu wajen Uncle da Dr. Aasiya. Ta kai ta kawo duk wani wanda ya rabi Asma’u, to ya saba da Mansur mai yi mata son kan-uwa-da-wabi, wato sonta yake tare da dukkan ahalinta da duk wanda take tare da shi.
Tare suke zuwa London dubo Khalipha duk wata. Lokacin komawar Mansur gida ya cika, amma ya kara neman visar aiki ya shantake ya ki tafiya saboda Asma’u. Su kuwa gwamnatin Dublin ai gaba ta kai su don dama irin Mansur din suke so su suke gudunsu domin kishin kasa (Patriotism). Irin na ‘yan bokon nijeriyar jiya ba na yau ba.
Sai suka shiga jika shi da kudi, gida cikin gidajen malaman Jami’ar Trinity da Insurance, accommodation and allowances. Da Hakimi ya bi ba’asin fasa dawowar tasa bai boye masa ba, “He cannot live without Asma’uuuuu!!!”
“Wace ce ita?”
Hakimi ya tambaya.
Bai boye komai ba ya warware masa zare da abawa. Satin bai cinye ba, sai ga Hakimi Abdulkadir Balarabe Sardauna da mai dakinsa Kareema a Dublin. Suka karbi auren Asma’u da amincewarta hannun Yohan, suka danganata da dakin mijinta da alkawarin suma din su koma gida. Suka yi musu alkawarin hakan, wato da zarar ita Asma’un ta kare Khalipha ya gama primary.
Mansur da Asma’u cinye junansu ne kawai basu yi ba, saboda so da kauna, a shekararsu ta biyu da aure ne ta haifi IBRAHEEM. Ba ta kara haihuwa ba, ba kuma dalilin tsarin iyali ba, Allah ne bai bata ba, don in ta Asma’u da Mansur ne, duk shekara su haife, suna da halin da za su kula da abinsu, kuma suna so, kamar su hadiye su.
Sanda Khalipha ya gama primary, Ibraheem na primary 3 a Al-Falah Islamic Children School in London. Asma’u ta karbi kwalinta suka tattaro suka dawo gida Nigeria da ‘ya’yansu biyu maza, baki da fari duk kyawawa, kowanne da irin kyan shi mai daukar hankali.
Tun kan su zauna sosai su huta federal ta karbesu aka cillasu asibitin koyarwa na UNILAG Dr. Mansur na aiki yana kuma koyar da medical student. Basu kara haihuwa ba har aka mai dasu Ibadan Teaching Hospital duka tare suke aikin shi da Asma’u.
A can ne Allah ya basu Jawahir, aka mai dasu Jos suka haifi Abida a can bayan shekaru uku. Daga nan haihuwa ta kara dauke mata dif! Har suka dawo Kano, lokacin Gwamna Kabiru Gaya, shi ya dauki kujerar kwamishinan lafiya ya baiwa Dr. Mansur a dalilin wani aiki na koyarwar sa-kai (voluntary) da ya yiwa jami’ar Abdullahi Bayero, wanda shi gwamnan ya neme shi da ya yi.
Wannan ne mafarin zamansu a gidan da suke ciki yanzu a Lamido Crescent, Gwamnatin ce ta bashi ya zauna har ya yi kokarin da ya mallake shi bayan barinsu Gwamnati da komawarsu bakin aiki. A nan ne kuma ta haifi auta Azizah.
Shima Uncle Yohan ya baro Dublin tuni da iyalinsa suna zaune a Jos. Shakuwar dake tsakanin Khalipha da Uncle Yohan ta wuce tunani, don haka yau abin da ta gani ya tabbatar mata da sanya hannun Yohan Khalipha ya nemo dangin ubansa har ya auro jininsa ba da izininta ba.
Ta riga ta yi fushi mai tsanani da dangin Mukhlis shi yasa ko da wasa ba ta taba gaya masa cewa ba Dacta Mansur ne ya haife shi ba kada ya ce zai je ya nemo su. Da ta kawo nan a tunanin da take yi a tsaye a bakin kofa sai hawaye suka tsinke mata.
Yohan da Baba Dacta basu kyauta mata ba, ta fassara hakan da cewa Baba Dacta ya yi hakan ne don ya rama abinda ta yi masa na hana Khalipha auren gallafirar ‘yarsa, me ta yi da zafi, da ta cancanci hakan???!
****
MURFIN LITTAFI NA BIYU!
Tana shirin juyawa ta fita ta ji hannayensu sun rungumeta, sun hanata fitar. Khalipha da Mimtaaz, ke hawayen suma, suna rokonta ta shigo gidansu, ta sa musu albarka, in sun bata mata ne abisa rashin sani ta yafe musu. Domin dukkansu sun tsorata da dogon tunanin da ta afka a tsaye a bakin kofa. Mimtaaz hannun Radhiyyah ta kamo suka shigo dasu cikin falon..
Ita dai Radhiyyah jikinta ya yi sanyi,