Showing 6001 words to 9000 words out of 30449 words
ya dawo ya samu wannan labari da bai taba samun mai dadi kamar shi ba, wato warkewar Rayhanah. Daki ya shiga ya gabatar da sallar nafila raka’a biyu ya yiwa Ubangiji godiya, ya yiwa Baba Dacta addu’a, ya roki Allah ya ba shi karfin zuciyar fuskantar iyayensa a wannan lokacin a kan bukatarsa.
Sai dai abin da ke bakanta mishi rai kwarai shine, sabuwar mu’amalar da Mami ta tsiri yi da Rahane, na rashin sakar mata fuska, haka ko magana take yi da Khalipha idan Rahane ta shigo wajen sai ta yi shiru.
Sannan idan Rahanen ta gaisheta ko ta yi mata magana, amsawa take a ciki kamar ba ta so. A sati daya da Khalipha ya yi cikin gidan yana hutawa kamin ya koma ofis Monday ya lura da hakan.
Ba ta da zancen da take yi masa sai na Radhiyyah, and he is not interested at all. Ta kasa ta tsare ta hana shi kebewa da Rahane da yake tana cikin hutu.
Ko yaushe tana tare da shi, abinci tare suke ci, fita ma in ta kamata sai ta ce shi zai kaita, a haka dai har ya cinye satin shi da Rahane sai dai ya hango ta daga nesa ko in sun fito cin abinci.
Ranar Lahadi da yamma ya koma Abuja ya shiga sabon ofis dinsa, wanda bai sa shi farin ciki ba ko kadan, don tunaninsa da zuciyarsa basa kai, sun yi nisa cikin zuzzurfar soyayya marar misali.
Khalipha baya da zabi banda ya kara kauracewa gidan su, baya son bayyana abin da ke zuciyarshi yanzu, amma zuciyar ta ki jurewa. Ya kan kira iyayen a waya su gaisa a kai a kai ya kuma ba da uzirin rashin samun zuwa da aiki ya yi yawa.
A wata Seminar likitoci na federal govt. da Dr. Mansur ya je Abuja ya yi tunanin bari ya kai ma Khalipha ziyara gida tunda Asabar ce baya zowa ofis. Gidan Khalipha da ma’aikatar su ta ba shi yana nan a (Maitama). Daddy ya yi horn maigadin ya bude mishi yana barka da zuwa. Daddy ya tambaye shi ko maigidana yana nan?
Ya ce, “Eh, yana nan, amma gaskiya a tsukin nan baya ganin kowa, ya kuma yi umarni gare shi cewa ko waye ya zo neman shi ya ce baya nan ko ya same shi a ofis. Yanzun ma don ya ga Daddy ne shi yasa ya bude”.
Daddy ya faka motarshi a gefe cikin rumfar adana motoci a kalla guda uku, ga ta Khalipha nan guda daya kirar (Cadillac Srx) da canzo daga Morocco, daga ita ba wata.
Ya fito ya doshi (door-bell) ta falon yana dannawa. Jibril da ke wankin kayan Khaliphan a bayan gidan ya zo ya gaida shi, sannan ya ce,
“Oga bai da lafiya Alhaji, kuma ya ki yarda cewa ba shi da lafiyar balle ya je asibiti, ni dai na yarda ba shi da lafiyar ko abinci ban yi zaton yana ci ba, don ya hanani yi mishi girki sai dai kullum ya yi ta aikena siyen abinci, kuma yadda na kawo haka nake fiddashi abin da ya taba ba yawa. Ba zai bude ba, da dai ka kira shi a waya”.
Da sauri Daddy ya dauko wayar yana kiran Khalipha sannan ya yiwa Jibril inkiya da hannunshi alamar ya tafi.
Anyi sa’a wayar Khalipha tana kunne, kuma ya sanyata a caji nesa da shi kadan, yana kwance gefen gadonshi da ruwan tokan (pjs) a jikinshi, ya tasa kwamfuta a gaba yana shigar da sakonni.
Sarai ya ji kararrawar amma bai yi niyyar budewa ba, sai kuma ga kiran waya dole ya mike zuwa gareta, ga mamakinsa kiran Daddy ne. Da sauri ya amsa wayar.
Daddy ya ce, “Ina kofar falonka”.
Cikin rashin kuzari ya bude kofar. Daddy ya tokare hannayenshi jikin kofar falon yana kallon shi. Gaba daya ya zube ya yi jajir, idanuwansa manya masu sheki sun zurma ciki, hakan bai hana shi bayyana a kyakkyawansa ba.
Yana shirin russunawa Daddy ya yi saurin kama hannunshi suka idasa shiga cikin falon, ya zaunar da shi a gefensa cikin bakaken (leather seats) din da suka yiwa falon kawanya.
Kafin Khalipha ya furta gaisuwa Daddy ya katse shi da cewa........ “Me ya faru? Me ya same ka, ka kulle kanka kai kadai cikin gida? Me ya zabgar da kai haka? Mece ce damuwarka Khalipha? Gaya min maza, wannan ba Khaliphana da na sani bane”.
Sai ya fada jikin mahaifinsa shi kuma ya rungume shi sosai, ba kuka yake yi ba, ajiyar zuciya yake yi. Ji ya yi zuciyar tana sanyi daga zafi da suyar da take yi.
Wani bangare na zuciyarsa na karfafa shi da cewa, ka yi amfani da wannan damar da Allah ya kawo, ka fadawa Daddy abin da ke neman kwantar da kai ya salwantar da ci gaban rayuwarka.
Daddy uba ne mai fahimta, da akida daban da ta Mami. Babu haufi zai fahimceka, ya mallaka maka abin da rai da zuciyarka ke so. Walwalarka da kuzarinka su dawo, ka dauko Rayhanah ku rayu tare har abada, ku haifi ‘ya’ya masu albarka har zuwa karshen rayuwarku.
Duka wannan tunani Khalipha ya yi shi ne cikin ‘yan dakikan da basu wuce goma ba. Daddy bai katse shi ba, ido ya zuba masa yana sauraren amsar bakinsa.
Khalipha ya dago ya kalli Daddy idanunshi sun kada sun koma brown dinsu masu sheki dake cike taf, da kwalla, wadda babu alamun za a ba ta damar zubowa saboda dauriya irin ta namiji da rashin son nuna karaya.
Ya maida kai ya sunkuyar, sakamakon kwarjinin da idanun mahaifin nasa suka yi masa. Amma fa wani bangare na zuciyarsa na cewa da shi, “A kul! Ka bari wannan damar ta subuce maka...”
Cikin rawar murya da sarkewar harshe ya ce,
“Daddy… Rayhanah…. Rayhanah nake so ka aura mini”.
Dr. Mansur bai tambaye shi wace Rayhanah ba, tunda Rayhanah daya suka sani a duniya dukkansu, basu san wata mai wannan sunan bayan ita ba.
Dr. Mansur bai yi mamaki ba, shi kansa jikinshi na ba shi akwai wani boyayyen al’amari game da Rayhanah a kanshi da ‘ya’yansa tun ranar da ya fara ganinta jikinshi ya ba shi hakan.
Wannan yarinyar rayuwarta cikinsu na nuna al’amura da dama wanda Allah kadai ya sani. Sai dai kuma kash!
A inda ya yi fatan al’amarin ya kasance ba a can ya kasance ba. Anyway a hakan ma baya da ja, kuma yayi farin ciki, amma yadda yasan yunwar cikin sa haka yasan cewa Mami ba za ta taba amincewa ba, musamman da yake ta fishi power a kan Khalipha.
Tabbas Khalipha ba wani abu ke damun shi ba sai soyayya, irin soyayyar da ya yiwa Mami mai azabtarwa, wadda ba a lokaci daya take faruwa ba, a hankali take shigar mutum ta yi masa kisan gilla batareda ya sani ba, tayi masa babakare a zuciya da gangar jiki. Ta hana shi sukuni da nutsuwa har sai ya mallaki abin da take so.
Wannan shirun da Daddy ya yi ba karamin kada Khalipha ya yi ba, tsoron shi Allah, tsoron shi kada Daddy ya ce ba zai ba shi Rayhanah ba ko ba zai yi mata aure yanzu ba. At 34, yana cikin wani mataki na tsananin bukatar diya mace, amma fa Rayhanah kadai.
Ga dimbin mamakinshi Daddy murmushi ya yi ya dafa kafadarsa ya ce, “Wannan shine abin damuwa Babana? Har a sanya zuciya cikin takura? Baka tsoron hypertension kake wasa da aiki da lafiyarka?
Rayhanah ai ‘yata ce kamar yadda kake Da a gareni. Idan har kana so ita ma tana so me zai hana in mallaka muku juna? Ni ai abin farin ciki ne a gareni in aurar da Rayhanah a hannun da na tabbatar ko bayan raina ba za ta wulakanta ba.
A da, na yi niyyar ba zan aurar da Rayha da su Abida ba sai sunyi zurfin karatu, amma tunda har haka ta faru, bani da ja da yin Allah. Abdallah jeka nemi so wajen Rayhanah, idan ta baka ni mai daura aure ko gobe ne. Alas! Babu sauran damuwa ko?”
Hawayen farin ciki suka zubowa Khalipha, ya rungume Daddy yana kuka sosai. Daddyn na share masa da hankicinsa yana cewa,
“Haba Babana, tsakanin uba da dansa ai ba godiya. Duty na ne as a father in tabbatar da farin cikinku in har bai sabawa addini ba. Hakkina ne in yi muku aure, saboda kun kai munzali, amma sabgogin neman duniya suka sha’afar dani ga yin hakan, har sai da ka ankarar dani. Nima na gode Babana. Ya isa kukan nan bana son shi, ya isa!”
Haka ya ci gaba da share mai hawayen har kunya ta kama Khalipha. Daddy da kansa ya je kitchen ya dauki tray ya bude firij ya debo tuffah, inibi, fresh milk da cake da sandwitch ya dawo falon, ya ja tebir a tsakiyarsu ya daura tray din, ya dau tambulan mai garai-garai yana tsiyaya tatacciyar madarar Oldenburger mai sanyi yana cewa,
“Ni bako ba a tareni da komai ba, to bari in yiwa kaina maraba. You donno how hungry I’m”.
Dariya Khalipha ya yi, shima wata azababbiyar yunwa ya ji ta taso masa. Ya karbi tambulan din da Daddy ke mika masa cike da madara mai sanyi ya shanye, ya sake cika masa ya kwankwade. Zai karo masa yana dariya ya daga masa hannu. Sai shi ya cika ya shanye.
Khalipha ya mike ya je kicin din, ya debo dambun nama mai yawa da Mami ke ba shi in zai taho da coconut-cake mai yawa da ta ke sawa ayi mishi da kwalin Exotic ya zo ya kara musu a kan tray din, suka yi shiru dukkansu sai ci suke, da alama kowannen su tsohuwar yunwa ce a jikinsa.
Daddy na bai wa Khalipha labarin zuwansu (Braemar Village), da yadda komai ya wakana, a lokacin shi Khalipha yana Morocco. A nan ne Khalipha yake gayawa Daddy shima ya taba yin wannan tunanin, amma sai ya ga cewa tafiyarsu shi da ita ba za ta yiwu ba. Shi yasa ya bari a ransa sai sunyi aure.
Daddy murmushi ya yi yana tuno artabunshi da Mami a kan tafiyar, amma bai gayawa Khalipha ba kada mutuncin mahaifiyarsa ya zube a idonsa.
Shima ya dade yana mamakin wai Mami ce ta yi masa haka? Zargi a kan shirme? To dai ya yi mata uziri da matantaka. Ai mace ce ita ma. Tunaninsu ragagge ne. A wani fannin kuma yana cikin damuwar yadda za su karke da ita a karo na biyu idan ta ji bukatar Khalipha, sannan in ya tuna alkawarin da ya yi mata kafin ta yarda ta karbi yarinyar.
Amma ai ba ta fi karfin addu’a ba, Allah ya sanyaya zuciyarta don ya san ba ta iya fushi ba, shima bai iya ba. Musamman a kan Rayhanah.
Khalipha wanda ke cikin farin cikin da Daddy bai taba ganinsa cikin kwatankwacinsa ba ya katse tunanin shi da cewa,
“Daddy zan iya kiran Rayhanah a waya da amincewar ka? Daddy zan iya ba ta waya?”
A sanda ya fadi hakan kansa na sunkuye ne. Daddy sai ya mika masa hannu ya ce,
“Bani in kai mata. Amma da wajewar cewa za a bani salalar kaiwar, ka san ba a aikin banza a Kano”.
Dariya Khalipha ya yi, ya zaro wayarsa ya cire layin (MTN) wanda kowa ya san shi da shi ya sanya sabo na Etisalat ya mikawa Daddy.
Daddy ya karba ya zura a aljihun coat dinsa, ya sake mika masa hannu ya ce, “To bani salalar”.
Ba yadda Khalipha ya iya don tsananin farin cikin da yake ciki ya fi gaban biro ya rubuta, ya dauko credit card na layin da Daddy ke amfani da shi na naira dubu daya ya dauki wayar Daddy ya loda a ciki. Daddyn ya karba ya mike yana cewa, “To ai kaga haka ya fi, yanzu zan san na zama dan aiken soyayyah da hujjah”.
****
[12/24/2019, 21:47] Takori: Daddy na gudu a kan titi zuciyarsa kamar takarda don haske, Allah yana cika masa burirrika tun gabanin ya yi furuci a kansu.
Addu’ar da yake yiwa Rayhanah a kullum shine, Allah ya ba ta miji na gari, bai taba yin zabi ba sai kiyasi. Wato dama a ce..... sai ga shi kiyasin ya fada a inda bai zata ba.
Baya tsoron Mami da rigimarta godiya yake yiwa Allah da ya ba wa Rayhana miji irin wanda yake yi mata addu’ar samu dare da rana, fiye ma da kintacensa.
Daddy bai iso Kano ba sai karfe goma sha daya na dare. Sai dai tun kafin ya yi parking wayarsa ta hau tsuwwa, da ya daga sai ya ga Dr. Abubakar ne wani likita dake karkashinsa.
“Dr. it is urgent......a fatal accident at emergency.....”
Abin da ya fada kawai kenan. Bai yi la’akari da gajiyarsa ba da baccin dake cin idanunsa ya karya kan motar Mal. Dahiru ya kara bude mishi ya fita aguje don ba abin da ya fi ceton rai muhimmanci a wurin Dr. Mansur. Shine on-call ko ba shine ba, muddin aka samu mummunan hatsari sai ya tsaya a kai muddin an gaya masa.
Don haka bai samu dawowa gida cikin iyalinsa ba sai da Asubahi. Zuciyarsa cike da wani irin sabon Imani. Bai taba ganin mummunan accident irin wannan ba, kafa ta fita, hannu daya ya fita, ‘yan yatsu sun gutsire. Don haka he is not in the mood ko Mami bai nema ba yana dakinsa, ya yi wanka ya sha coffee ya koma ni’imtaccen gadonsa ya nade bayan ya karo karfin na’urar sanyaya daki don ya samu nutsuwa.
Mami ba ta san Dr. na cikin gidan ba ma sai da ta shigo dakinsa don ta gyara, wannan aikinta ne ba ta sanya kowa. Nan ta ganshi yana ta barci, sai ta hakura da gyaran don kada ta tada shi, ta koma kicin don ta hado masa karin kumallo mai kyau, don ga dukkan alamu a jigace yake.
Dr. bai fito ba sai karfe daya na rana ya fito a kintse, lokacin Mami na shirin fita ita kuma har ta ratayo (handbag), sai suka yiwa juna murmushi.
Ta ce, “Dactana.......”
Ya ce, “Maminaah!”
Su Abida duk suka fito, Rayhanah na bayansu suna gaida Daddyn don tun shekaran jiya basu sa shi a idonsu ba. Fuskarshi da fara’a sosai yake amsawa, idonshi a kan Rahane ya ce,
“Yammatan Mami duk za su tafi makaranta su barki ke kadai, don ke sai shekara mai zuwa, don haka maimakon zaman kadaicin gara a ribaci lokacin, na nema miki gurbi a Informatics dake Kazaure za ki yi International Diploma a Cyber Security (Computing) tsayin watanni takwas”.
Har kasa ta zube tana yiwa Daddy godiya. Abida na huci da zumbura baki, don dai tun farko ita ta kawo zancen shiga Informatics kafin result dinsu ya fito, amma Daddy ya ki amincewa da barinta ta tafin, a cewarsa rawar kanta ya yi yawa ba zai yarda ta je inda babu mai sa ido a kanta ba.
Ita kuma ta so tafiyar ne saboda kawayenta da yawa ‘ya’yan manyan gwamnati suna Informatics. Amma ga shi ya ce makiyarta ce za ta je. Duk duniya Rahane ba ta da burin da ya wuce karantar na’ura mai kwakwalwa, tana sha’awar taganta da ita tana sarrafa ta, me za ta ce da Daddy a duniya ban da ta yi mishi biyayya da addu’a?
Mami ko a kwalarta hankalinta ya yi gaba, domin kauye za su je da Dr. Halima a kan maganar Khalipha da Radhiyyah. Ta daina nuna adawa da Rahane a kan idon Daddy da ita Rahanen.
Dr. Halima ta ce ta yi hakan, ta ruwan sanyi za ta raba iyalinta da Raihar da ta zo ta zame mata karfen kafa, saboda take-taken Khalipha a kanta.
Jawahir ta taya Rayhanah godiya a wajen Daddy. Ya ce babu komai su je su fara shiri. Abida da Jawahir duk sun samu gurbi ne a Jami’ar Bayero. Abida a Zoology, Jawahir a Microbiology, Azizah an samu wucewa SS I a Nigerian Turkish dake Tarauni (Boarding).
Abida bata son kwas din da aka bata don ba shi ta zaba ba, amma da aka yi post UME suka cillata can saboda makinta bai kai ba, medicine ta zaba.
Wannan ya bakanta ran Abida ba kadan ba, ta yi kuka har ta gode Allah, ta ce ba za ta yi ba, za ta jira shekara ta zagayo ta kara nema. Daddy ya ce sai ta yi, ba za ta zauna a gida kowa yana makaranta ba.
Don haka ne ta kawo masa zancen Informatics ya ga ba ta dace da kowa ba sai Rayhanah. Ita kuma a bisa dole ta hakura za ta yi Zoology din don Mami ta tausheta da cewa ta yi din, ta kuma sake neman Medicine din shekara mai zuwa.
Litinin, Jawahir da Abida suka fara registration a Bayero, Azizah aka kaita Turkish, Rahane Dr. da kansa ya sata a gaban mota ya kaita Kazaure.
Duk wasu cike-ciken takardu da ya kamata ya yi mata, aka ba ta daki da sauransu. Rahane ta kudire a ranta da yardar Ubangiji ba za ta bawa Baba Dacta kunya ba.
Da ya karya kan mota zai tafi, hawaye ne suka zubo mata. Ba na bakin cikin an kawota inda za ta zauna ita kadai ba, a’a, na kauna ne da farin ciki.
Ganin tana kuka sai ya yi ribas ya dawo dai-dai inda take tsaye ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro dalleliyar wayar (sony xperia) yana cewa,
“Af! Kinga Rayhanatu na sha’afa, ungo wannan taki ce, zan dinga kiranki, Yayanki zai dinga kiranki, kema in kina cikin matsala za ki iya kiranmu na zuba miki duk lambobinmu, maimakon duk sati ki zo gida, ki yi hakuri sai bayan wata-wata zan ke zuwa da kaina in tafi dake a duk Asabar din karshen wata”.
Tana share ido da gefen gyalenta ta ce, “To Daddy”.
Ya ce, “Kukan na mene ne?”
Da sauri ta ce, “Ba na komai bane Daddy....... is just that I will miss my Daddy so much....”
Murmushi ya yi ya ce, “Daddy will miss you too. Sai dai hakan ba zai hana neman ilimi ba, duk matakin da muke a yau, albarkacin ilimin ne, wanda iyayenmu suka tsaya mana muka yi. Don haka dole ki yi hakuri da komai ki mai da hankali a kan abin da na kawo ki ki yi, ki manta da komai da kowa! Ki kawo min sakamakon da nake tsammani daga gareki”.
Da sassarfa ta daga kafa ta nufi hanyar hostel. Shi kuma ya ja motar a hankali