Showing 21001 words to 24000 words out of 30449 words
ke cike da sauyin rayuwa a gareta.
Ta tashi ne ta jita cikin wata irin nutsuwa da ba ta taba ji ba a kafatanin rayuwarta, ta daga kai tana kallon dakin barcin nata. Fentin dakin fari tas, haka marbles din tsakar dakin. Ga wasu ubansu English-Furnished Funiture bakake da ratsin silba, labulen ma silba ne da ratsin baki, split na aiki. Katifar gadon ta ruwa ce kamar kana kan gajimare.
Ba ta kara tsinkewa ba sai da ta shiga bandaki domin dauro alwala da wanka, inda ta ga bakonta ya iso (period). Don haka wankan ta yi, cikin lokokin saman da aka yi a bandakin ta samu pad da pantis ta gyara kanta, bayan ta yi wanka.
Ba ta da yawan ado, Pakistan ruwan toka kawai ta zura, ta fesa spray ko lotion ba ta shafa ba kasancewar zafi ake yi. Ta yi tattaki ta fito falo. Duniyar Turawan da Daddy ya shirya mata ko ‘yar gwamna sai haka, komai cool ba harbatsiya, abin kayatarwa a ido, kujerun kansu yatsu ta kai tana latsasu, domin kyansu da santsinsu ya isa (Leather Francaise) maroon da ratsin makuba, haka labulayen ma kalarsu kenan.
Dakunan barci uku ne a falon, na Inna Juma yana falon kasa, shigifar duk da ta shiga kalar kayan dakin daban ne. Musamman Baba Dacta ya taho da decorators din da suka gina gidan daga Ireland, sune kuma suka shirya gidan.
Ta shiga nan ta fita can har ta jefa kanta dakin da Gwaggo Juma take, tana kan darduma tana lazimi da carbinta mai ‘ya’ya dubu cunkus a gabanta. Ba ta katseta ba bayan sallamar da ta yi, Juma ta daga kai alamar amsawa, sai ta fada gadon Juman kawai ba ta san sanda barcin gajiya ya sake yina won gaba da ita ba. Tunda aka fara al’amarin nan ba ta samu isasshen barci irin wanda ta samu yau ba.
Da Juma ta gama laziminta, kicin ta fada tana yi musu abin da za su karya da shi. Duk na’urori ne fal da yawa ba ta san amfanin su ba. Amma ta san yadda ake amfani da Gass Cooker.
Nan ta bude store babu abin da ba a zuba ba ta fannin kayan abinci. Haka firij babu nau’in nama ko kifin da babu dankare cikin kankara a freezer. Ta debi dankali (potatoes) ta soya musu da kwai, ta dafa musu shayi a filas, kayan shayin ma duk gasu nan a cikin irin kwandon nan mai tayoyi, ta hado komai ta dawo dakin nata.
Har zuwa lokacin Rahane na barci. Sai ta ci gaba da ‘yan kintse-kintsen tsummokaranta cikin kwabar jikin bango. Ba ita ta tashi ba sai karfe goma da rabi, ta koma dakinta ta yi brush ta dawo suka fara karyawa.
Haka suka ci gaba da zamansu cikin kwanciyar hankali. Alal hakika Rahane ba ta iya komai da ya shafi girki ba, domin Mami ba ta sa su girki, ita take yi in tana gida ko kuku.
Haka Iya Bilki Allah ya ji kan rai ba ta bata tukin tuwo sai kwashewa da rabawa. Don haka Juma ta fuskanci hakan, sai ta dage wajen koya mata girki, mafi yawa na gargajiya don ita ma ba ta iya na zamani ba. Ta koya mata kunun tsamiya, na kanwa da na gyada dana farar shinkafa. Ta koya mata tuwo na alkama, na semo da na shinkafa. Ta koya mata sinasir da miyar ganye, waina da taushe, fankaso, dambun shinkafa, moi-moi (Alala), gashin kaza cikin oven da soya ta, dambun nama and much more. Yau ga shi har sun kwashi wajen watanni uku.
Daddy kan zo wani zubin in ya taso aiki su gaisa, ya ji ko suna da damuwa ta kudi ko ta cefane, kuma ka’ida ne muddin ya zo sai ya ba ta kudi ko tana bukata ko ba ta bukata, bai taba yi mata zancen angon ba, ita ma ba ta tambaya ba, sai dai ta fuskanci Daddy cikin damuwa yake yana dai yin kokari ne na boyewa amma har ya rame shi bai san ya rame din ba.
Kamar dai yau da ya zo ya kawo mata computers sabbi gal har guda biyu, laptop da Ipad, da conecction dinsu da komai, tana ta godiya duk da bai bata waya ba. Tata a can gidan Mami ta barota ba ta dauko ba tun ranar da Mamin ta kore ta. Ba ta damu ba, farin cikin wadannan computers yasa ta manta da komai.
Haka ya tafi babu kuzari a jikinshi. Damuwar Dr. Mansur kuwa shine, Ibraheem na neman ba shi kunya. Tun maganar farko da suka yi, inda ya ce mishi ya zaba masa matar aure ba tare da ya gaya mishi ko wace ce ba, ya ce dai wadda hankalinsa ya kwanta da ita.
Ya tattaro ya dawo gida Najeriya haka, ya bar aikin da yake yi a Chicago kasarmu ta fisu bukatar Nephrologists, Jami’ar ta rike shi yana part-time lecturing, haka yana aiki a babban asibitin koyarwa na Chicago (Illinois Teaching Hospital).
Abinda Ibraheem ya cewa Daddy shine, kowacece ya zaba mishi din ya karba, in dai ba auren zumunci bane. Zai duba bukatar mahaifin nasa ta dawowa gida cikin satin ko da bai dawo gaba daya ba.
Tun daga wannan maganar da suka yi, bai kara samun wayar Ibraheem ba. Idan ya kira ba ta shiga, babu shi a social network don shi dama baya sanya kansa cikin wannan abubuwan na asarar lokaci. Daddy ya buga ya buga ya kasa samun Ibraheem wata da watanni. Ga yarinya ya ajiye babu future plan na ci gabanta.
Mami da ta gaji da ajiyar amaryar Khalipha sai tasa ta a gaban mota ta bishi da ita Abuja. Anyi sa’a ya dawo daga Hurghada inda ya yi sa’ar samun kakanshi mahaifin Mukhlis da ‘yan’uwanshi.
An tafka shari’a a kotun Muslunci ta Hurghada tsakanin Khalipha da dangin mahaifinsa, inda ya yi kararsu a kan sun sheganta shi, ba dukiyar da suka lamushe ba ce a gabansa, a’a, tabbatuwar identity dinsa.
Madaura auren Mukhlis da Asma’u a Jos duk sun bayyana a babbar kotun Hurghada, inda sarkin Jos ya ba da shaidar komai, hotunan da aka yi da Mukhlis ranar daurin aurensa da Asma’u, har (vedio casette) da aka yi a lokacin da Mukhlis an kunna a kotun kowa ya gani.
Likitoci sun debi jini sun tabbatar. Shima Abu-Arab kakan Khalipha ya bada diary na marigayin wanda ke rubuce da bayanin aurensa da Asma’u da niyyarshi ta kawota Hurghada cikin shekarar. Ga hotunansu nan kala-kala shi da Asma’u da zungureren cikinta, dole dangin suka yi saranda suka karbi diyaucin Khalipha.
Amma sun nemi da ya yafe musu dukiya kam babu, sama ko kasa sun lamusheta. To dama haka cin dukiyar maraya yake kamar cin wutar auduga. Allah ka kara mana imani da arziki na halali ameen.
Khalipha ya yafe musu, ya kuma tabbatar musu shi ba dalilin neman shi dasu kenan ba. Abu-Arab ya hana shi tahowa sam-sam sai da ma’aikatar Foreign Affairs ta tsoma baki sannan kakan ya yarda ya koma bakin aikinsa.
Sai dai kuma tare da santaleliyar Balarabiyar amarya (Mimtaaz) ‘yar kanin mahaifinsa. Khalipha yaso ya turje, suka ce bai isa ba. Ya gaya musu Mamanshi ta yi mishi wani auren ko tarewa ba ayi ba, suka ce ai al’adarshi ta yarda ya zauna da mata hudu ma ba biyu ba, duk bayanin da ya yi kokarin yi musu mai nuni da cewa zai shiga matsala da mahaifiyarshi kakansa ya ki yi masa uziri.
A karshe ma kuka yasa masa, ya ce a yanzu shi yake gani kamar Mukhlis, zamanshi tare da ‘yar’uwarshi Mimtaz shine kawai alfarmar da yake so ya yi mishi kafin Allah ya dau ransa, ya tsufa sosai, amma hakan bai hanashi hada kan iyalinsa ba, ta hanyar kulla auratayya a tsakanin matasan jikokinsa.
Don haka Khalipha ya yi tubus, ya kara neman alfarmar Mimtaaz din ta zauna a Hurghada ya je ya yiwa mahaifiyarshi bayani tukunna ya dawo ya tafi da ita, zai dauki nauyinta.
Nan ma tsoho ya ki yarda, ya ce kafarshi-kafarta in yaso uwar tasa ta yi gunduwa-gunduwa da ita tasa a miya. Rigimar wannan tsoho da yawa take...... in ji Khalipha. Sai ya sako sullubebiyar matarshi a gaba suka sauka a gidan shi na Abuja.
Rayuwar Khalipha da Mimtaaz ta watanni biyu kacal sai ta zamo abar alfahari a zuciyar kowannensu. Mimtaaz ta ci sunanta Mimtaaz wato (excellent). Kaunar jini mai karfi ta haifar da tasirin da ya fi soyayya karfi. Yarinya danya shataf mai tarin baiwarwaki da falaloli da yawa daga indallahi.
Sai ga Khalipha yasa Mimtaz dinsa a barin damansa sun cilla Birnin Manzo yin umarah, daga nan suka wuce Sweden suka kwashi sati biyu suna (honey-mooning). Sai ga bakin cikin dake zuciyar Khalipha yana yayewa, haske ya cika shi farin ciki ya maye gurbin bakin ciki.
Sai dai kullum ya kan tuna Rayha, ko wane hali take ciki? Addu’a yake mata ba dare ba rana Allah ya zama gatanta kamar yadda ya yi mishi gata ba don ba shi da shi ba. Sai don ya dubi zuciyarsa mai kyau ce a kan kowa, mai son farantawa uwa mahaifiya don gamawa da duniya lafiya. Haka yake kyautata zato a kan ita ma Rayhanah.
Kwanansu biyu kenan da dawowa daga Sweden Mami ta iso da amarya Radhiyyah a gaban motar ta, maigadi bai hana Mami shiga ba don ya santa. Ma’auratan na falo Khalipha na karantawa Mimtaz wani novel mai suna (Surgeon’s Wife) na Azizah Idris Gombe, kasancewarta mai son labaru.
Haka yake bata lokaci ya yi ta karanta mata in ya dawo ofis, da yake tana jin Turanci sosai don a jami’ar Coventry take karatu aka tsigeta aka yi mata auren. Witness to Tears ma na Abubakar Gimba duk ya karanta mata tun a Sweden, The Burden of Memory na Wole Soyinka da wasu daga cikin na Babansu William Shakespear da yake Literature take karanta, ita kuma tana kusa da shi tana fifita masa shayin da yaji suga da na’a-na’a, daga shi sai singlet da wando short-nicker Mami ta yi sallama a falon, hannun Radhiyyah cikin nata.
Sai ta tsaya kawai kamar an dasa ta ana kallon-kallo tsakaninta da Mimtaaz, ba fuskar kowa take gani a fuskar Mimtaaz ba face fuskar Mukhlis (mijinta na fari), Balaraben Hurghada Mukhlis Abu-Arab. Don haka ta tsaya stand still ta kasa gaba ta kasa baya, amma bakinta ya mutu ta kasa yin ihun da da farko taso ta yi na ganin Khalipha da macen da ba tashi ba.
Duk da haka ba komai bane kuma ba abin mamaki ba a wurin matasan yanzu, musamman wadanda ke jike cikin naira suke kuma jan ragamar rayuwarsu irin su Khalipha. Sai dai tana da yaqinin nata dan, ba zai taba yin hakan ba tunda ita dai bata taba yin zina ba a rayuwarta ko kafin ta Musulunta.
Shekaru talatin da biyar a baya suka shiga dawowa suna giftawa a idanunnta tamkar majigi.
****
[12/24/2019, 21:47] Takori: RESHE YA JUYE DA MUJIYA!
“Anzo Takai, ina na Takai ku sakko!”
Kwandastan yake ta fadi, yana bubbuga kofar motar.
Rahane ta daga ido tana kallon mahaifarta wadda har gobe ba ta canza a idanunta ba, duk da dadewar da ta yi ba ta zo ba tun rasuwar Babanta.
Ga tafasa ta nuna, gero da masara sunyi yabanya kore sharr dasu, da yake lokacin na damuna ne. Da kyar ta cira kafa da ta yi mata tsamin gaske ta fito daga motar.
To gata ta dawo gida, amma wajen wa za ta a Takai? Ba uwa, ba uba balle dangi. Ko gidan gado ba ta da shi, balle ta je ta share ta zauna.
Wata zuciyar ta ce, “Ki tafi gidan Hakimi”. Wata kuma ta kalubalance ta da cewa, “A sanadin wa kika san Hakimi da iyalansa? In kika je gidan Hakimi kin je rokon a mayar dake gidan Dr. Mansur ne, a hada Mami da Daddy fada a kan gaskiyarta, ba ta yi isar da za ta hada mu’amalar jini da ita ba. Don haka ba ta ga laifin Mami ba don ta raba danta da ita, sai ma laifin ita kanta da ta gani, da ta bari zuciya ta rudeta ta mance da reality na rayuwa na dai-dai ruwa dai-dai tsaki ta amince da soyayyar Khalipha.
Har zuwa yanzun kuma babu abin da ya canza daga soyayyar da take yiwa Khalipha, domin soyayyar ba shigar sauri ta yi mata ba, balle ta fita fit! Farat daya. Circulating ta yi a hankali cikin jini da tsoka har ta huda kashi ta shiga cikin bargonta. Sai dai ta amincewa kanta ko soyayyar za ta kasheta, har abada ita da Yaya Khalipha.
Ta kai gefen hijabinta ta share hawayen da suka zubo mata a wannan lokacin. Ba wanda ta tuna a wannan lokacin sai Zinaru kanwar mahaifiyarta Yalwati da Malam Rashidu ya aura ya saki, rabonta da Zinaru tun ranar da ta bar gidansu.
Ta sani cewa duka kakanninta na wajen uwa sun rasu, amma Zinaru tana raye, za kuma ta iya sadata da wasu daga cikin dangin Yalwati in akwai, idan ita ba za ta zauna da ita ba har zuwa lokacin da Allah zai ba ta miji a nan Takai dai-dai da rayuwarta, wanda ba zai kalli tushenta, asalinta da tsohuwar lalurarta ababen kyama ba, tunda tushe da asalinsu daya.
To yanzu ina za ta nufa neman Zinaru? Shekarun da yawa, Takai da girma. Abin da ya kara ruruta wutar kukan da take yi kenan.
Ta bi gefen titi ta soma tafiya tana kukan, amma ta toshe bakinta da hijabin. Tafiya take cikin zafin nama ba tare da ta san inda take jefa kafafunta ba.
Horn din mota ta ji a bayanta ba kakkautawa, amma ba ta juyo ba ta ci gaba da tafiyarta, tunda ta san ita dai ba a tsakiyar titi take tafiya ba balle a ce ta matsa. Sai ma ta kara azama ta soma shigewa cikin gonakin masara.
Fakin din motar aka yi a gefe aka biyota da kafafu. Muryar da ta ji na kiran sunanta da karfi ya sata juyowa cikin razana da firgici. Baba Dacta ne da Sha’aban dan wajen Hakimi. Ya fi karfin ta kalle shi ta wuce, yana da kimar da babu mai ita a idanunta a duniya idan ka dauke iyayenta.
Don haka ta ja ta tsaya idonta cike da hawayen da suka kasa tsagaitawa. Har Baba Dacta ya iso inda take ya kama hannunta idanunsa shima sun kada sunyi jawur, amma ba hawaye a cikinsu.
Sha’aban ya koma ya matso da motar har inda suke. Baba Dacta ya bude kofar baya ya shigar da ita ya rufe, shi kuma ya zauna wajen mai zaman banza, Sha’aban ya ja motar suka hau titi.
Cikowar da ta ga kofar gidan Hakimi ta yi da bil-adama bai zamo bako a gareta ba, domin an saba yin bukukuwa da daurin aure a gidan Hakimin.
Sha’aban ya yi parking, wannan karon ma hannunta cikin na Baban suka shiga gidan. A dakin Hajiya Karima ta tadda Hakimi da kansa da sauran ‘ya’yansa wadanda suke kusa ba na nesa irin su Hibbah ba, har da Nabilah, da sauran iyayensu mata.
Ga Nabilah na suma ana yayyafa mata ruwa kamar mai iskokai, idan ta farfado ta yi surutai sai ta kara sumewa. Fuskar marikiyarta Inna Indo kamar hadari ta dubi Rahanen da Dacta ya shigo da ita shekeke!. Sai Haj. Karima Maman Nabilan ta asali ce ta nuna mata wajen zama, ta zauna a darare tana ta kuka.
Dacta yake gayawa dan’uwansa a bakin titi suka ganta dama ya kintaci lokacin tahowarsu ne da awoyin da za su dauka kamin su iso, ya je tashar ya daukota sai ya hangota bisa titi.
Hakimi ya ce, “Sannu Rayhanatu kin ji, insha Allahu kin yi sallama da rayuwar maraici, tunda kin samu uba irin MANSUR da nagartaccen miji irin IBRAHEEM da kuma ni surukinki Abdulkadir. Share hawayen nan Rahane, daga yau na tabbatar miki haka kawai ba za su kara zuba ba. Sai ko a kan wata kaddarar daban ba ta maraici da rashin dangi ba.
Muna yi miki barka da zuwa cikin zuri’armu ta alfarma wadda kudurinta shine kiyaye martaba da mutuncin talakawanta. Sannan muna farin cikin shaida miki cewa, mun samu kanwar mahaifiyarki Zinaru wadda ta hanyarta aka samu dangin mahaifiyarki. Sha’aban jeka shigo dasu”.
Ya mike da kansa ya iso har gabanta, ya dora mata warawaren farin zinare (bangles) a kan cinyarta.
“Ga sadakinki, mun daura aurenki da IBRAHEEM MANSUR TAKAI. Babanki ya karbi waliccin ki, na karbi na Da na Ibraheemu. Shaidar da Babanki Mansur ya yi miki ta kyawawan halaye, tarbiyya, biyayya da hakuri, ina fatan ta dore har a gidan aurenki.
Yadda Ibraheem ya karbi zabin da mahaifinsa ya yi masa hannu bibbiyu, muke fatan kema ki karba. Ki yarda cewa baka auren mijin da ba naka ba, kamar yadda baka auren macen da ba taka ba. Komai na rayuwar Dan Adam tun fil’azal rubutacce ne a (Lauhul-Mahfouz). Muna son jin ta bakinki Rayhanah, shin kin amince da zabin Babanki ko kina da uzirin da zai hana ki yin hakan?”
Girgiza kai take cikin kidima da gigicewa. Wannan fa shi ake kira reshe ya juye da mujiya…. Ana bikin duniya ake na kiyama….. Abinda ta samu harshenta na fadi ba tareda ta shirya kalaman daga kwakwalwarta ba kawai shine,
“Idan ni din ban yi biyayya ga zabin Baba Dacta ba…., idan shi bai ji kyamar hadani da Dan da ya fito daga jikinsa ba, duk da kauyancin da talaucin nawa, da lalurar dana samu kaina ciki a baya…. ai ni ba zan ki karbar zabinsa ba ko da tura kaina cikin dakin Zakuna ne.
Yadda Allah zai tambayeni idan ban yiwa iyayen da suka tsugunna suka haifeni biyayya ba, na tabbata haka zai tambaye ni idan ban yiwa Baba Dacta ba.......!” Ta ci gaba da kukan da bata san dalilinsa ba. Ta barsu suna juya tasirin kalamanta a zukatan su.
Daidai lokacin da ta ji sallamar jama’a, ta daga kai a hankali tana kallon su. Wasu harbatsattsun kauyawa ne babu wadda za a ce “gara ita”. Da kyar ta gane Zinaru a cikinsu saboda cindon dake gefen hancinta.
Ji ta yi kamar anyi mata gafara ta mike tsaye tana kallon su idanu a warwaje. Zinaru ta karaso ta rungumeta, wani hamami na baki da hammata ya