Showing 3001 words to 6000 words out of 30449 words

Chapter 2 - Rayuwar Rayhana Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

28 Dec 2024

88

al’ummar kauyen, kewaye da wannan mahadar akwai kimanin tsaunuka ashirin wanda sun kai tsahon kafa 3,000.
Braemar ya shahara saboda wasanni da ake gabatarwa a garin duk shekara. Wanda ake musu lakani da wasnanin tsaunuka. Shi wannan gagarumin biki ya samo asali ne tun shekarar 1832, wato zamanin sarauniyar Ingila Victoria wadda ta albarkaci wannan bukukuwa.
Har zuwa yau ‘ya’yan gidan Sarautar Ingila suna halartar wadannan wasanni wanda a yanzu Sarauniya Elizabeth ita ce babbar uwa ta wadannan wasanni.
Ana gabatar da wannan bikin ne a Asabar din farko ta watan Satumba, inda ake bushe-bushe da kada-kaden gargajiya masu dimbin tarihi wanda in ba a irin wannan wajen ba da wuya ka ji irinsu.
Wannan wasa ya kunshi gasar busa sarewa da ganga tare da raye-raye irin na da, sannan wasannin gargajiya. Braemar cike yake da dadadden tarihi domin a nan ne aka yi boren Jacobite a shekarar (1715) wanda ya komar da ‘Stuart’ kan gadon sarautar Birtaniya. Dai-dai wajen da aka gudanar da wannan bore shine a yanzu gurbin masaukin baki na ‘Invercauds Arms Hotel’ wanda su Dr. Mansur suka so sauka a can.
Wani marubuci Robert Louis Stevenson ya fara rubuta bangaren farko na tsibirin taska (treasure Island) a garin Braemar a watan Agusta na shekarar 1881. A yau guraben da suke dauke da tarihi sun zama wajen saukar baki. Fadoji biyu sun kara ma garin Breamar armashi, wato fadar ‘Kindrochit’ wadda aka gina a shekarar 1390, tana tsakiyar wannan kauyen. Sai kuma fadar Braemar wadda ke tsahon rabin mil (mile) daga garin Braemar.
Wani wajen kuma mai dadadden tarihi shine cibiyar tarihi da ake wa lakabi da ‘Highland Heritage Center. Wannan cibiya tana dauke da bayanai masu kayatarwa da suka shafi tarihin garin Braemar. Bayanan sun hada da bayanin bukukuwan tuddai, da bayanin Sarauniya Victoria, da fadar Balmoral da sauraansu.

Dr. Philips ke bai wa su Daddy wannan tarihi na kauyensa a kwanakin su biyu da zuwa, suna zaune cikin ‘hut’ suna shan coffee.
Su Daddy suka girgiza kai cikin gamsuwa da samun karin sani. Dr. Philips ya aje dan kankanin kofinsa a dan teburin dake tsakiyarsu. Ya dubi Daddy ya ce ya yi masa karin bayani kan wanda ya turo masa ta yanar gizo kan sanadin matsalar yarinyarsu.
Tiryan-tiryan Daddy ya zayyano masa komai. Ya ce, “To bayan hakan wane mataki aka dauka na gaggawa?”
Dacta Imam ya mika masa komai a rubuce cikin ‘Ipad’ dinsa.
Da shi da su gaba daya suka shiga Laboratory, dake cikin private asibitinsa. Bayan sun biya duka payment din duka ta yanar gizo, sunan asibitin Spire Little Aston. Dr. Philips ya shigar da Rahane ya soma gudanar da CT Scan and MRI Scan. Tsayin sati biyu kafin sakamako ya fito. A daren ranar ya sanya su gaban kwamfuta yana yi musu bayani kamar haka;

Abin da ke faruwa wajen karbar sako a kunnen bil Adama shine, da farko sauti kan biyo ne wajen kunne sai ya bigi gangar kunne wanda hakan kan jawo gangar kunnen ta girgiza, inda wannan kadawar ta gangar kunne za ta isar da sakon ga kananan kasusuwan guda uku dake a tsakiyar kunne, inda su kuma za su mika wannan sauti ga can cikin kunne, wanda shine zai mai da wannan kadawar ta gangar kunne zuwa sauti, ya kuma tura shi zuwa kwakwalwa, ta haka sai mutum ya ji sauti ko magana.
Yarinyarku na fama da cutar amosanin kunne wato (Otosclerosis). Shi wannan amosani ya kan kama wasu kananan kasusuwan dake a tsakiyar kunne, kuma dama sune suke taimakawa Dan Adam wajen ji tar-tar.
Ita wannan cuta kan rage motsuwar wadannan kananan kasusuwan, wanda da sannu sai ya jawo mummunan lahani a kunnen mai wannan cuta.
Amma a wani sa’in wannan cuta kan tsananta, inda ta kan kai har ga ta lahanta kwayoyin halittar kunne da masu kai sako wanda ke hade da kwakwalwa, in har cutar ta kai wannan matsayi to fa mai dauke da wannan cuta zai daina ji dungurungum..”
Cike da fargaba Dr. Mansur ya katse Philips “To ita Rayhanatu meye matsayin nata?”
[12/24/2019, 21:47] Takori: Dacta Philips ya yi murmushi ya juya yana wanke hannunshi cikin sink, ya gama ya tsane shi da dan karamin tawul, ya juyo yana kallonsu idanunsu a warwaje, Rayha kuma kanta na sunkuye cikin dan dakin da ke cike da na’urorin gwaji. Tsaurin turancin yafi karfinta bata fahimtar komi. Sai da ya huta ya nisa ya ci gaba da cewa.
“Wannan cuta kan kama kunne biyu, amma in aka yi sa’a a wasu lokutan kunne daya kawai take kamawa”.
Wannan karon ma Dr. Mansur tambaya ya jefo, “Mene ne kan jawo wannan cuta mai hana ji ta Otosclerosis?”
“Kai tsaye ba za a iya cewa ga abin da ke kawo wannan cuta ba. Bincike ya nuna cewa a cikin mutane uku, to biyu sun gajeta ne. Amma ana samun wadanda su basu gada ba, amma suna haduwa da ita ta wani sanadin daban kamar yarinyar ku.
Wasu masana na ganin akwai wasu kwayoyin cuta dake jawowa dan Adam ya kamu da wannan rashin lafiya kamar kyanda, sankarau. Ana kuma ganin cewa sinadarin fluoride na daga cikin abin da zai iya tunzura wannan cuta ta (Otosclerosis).
Babba alamar cutar ita ce rashin ji, shine alamar cutar na farko. Ya kan iya kasancewa ba mai tsanani ba amma a hankali sai ya tsananta, a mafi yawan lokuta ya kan shafi kunnuwan ne guda biyu. A wasu mutane rashin jin kan dau lokaci har tsahon shekaru kafin rashin jin ya tabarbare, amma wasu kuwa dan da nan da cutar ta kama su kafin wani lokaci sai ya tsananta.
A mafi yawan lokuta ya kan shafi kunnuwan ne guda biyu. A wasu mutane rashin jin kan dauki lokaci har tsahon shekaru kafin rashin jin ya tabarbare, amma wasu kuwa dan da nan da cutar ta kama su kafin wani lokaci sai su daina ji.
In har ba a nemi magani da wuri ba, yana hana kunnen da ya kama ji. Bayan rashin ji mai dauke da wannan cuta kan ringa yin magana kasa-kasa, (ta yadda in har baka saurara bama ko ka saba da shi bazaka ji shi ba), sannan ga juwa da hajijiya”.
Dr. Mansur ya ce, “Duk wadananan alamomi Rayhanah na fuskantarsu. Sau tari sai na saurara sosai nake jin me take cewa, to amma Dr. ta wace hanya jin Rayhanah zai dawo daidai ta daina amfani da hearing aid?
Likitocinmu sunyi iya kokarinsu amma abin da suka tsaya a kai dukkaninsu shine babu wata mafita sai ta amfani da na’ura mai kara karfin ji (hearing Aid)”.
Dr. Philips ya nisa ya ce, “Da farko in jin mutum ya fara raguwa, ba lallai ne sai an dau wani mataki ba, na ba da magani ko wani abu makamancin haka. Amma in cutar ta tsananta, na’urar kara ji ta kan taimaka kwarai da gaske. Amma kuma a kan kai matakin da cutar kan yi tsananin dama na’urar kara karfin ji ba za ta iya taimakawa mai matsalar ba.
A wannan matakin a kan yi aikin fida. Fidar da aka fi yi ita ce wadda ake canza dodon kunnen dan Adam da wani kashi da ake yi da dafaffiyar roba ko karfe. A kan kira wannan fida a Turance ‘Stapedotomi’.
A mafi yawan lokuta a kan ci nasara, inda matsalar ji kan kau. Mutum ya dinga ji rangadadau, ya kuma ba da kariya ga can cikin kunnen mutum.
Amma fa wannan aikin fida yana bukatar taka-tsan-tsan, don idan aka yi rashin dace, to fa jin mutum kan dauke dungurungum a kunnen da aka yi aikin. Bugu da kari akwai hadari na lalata jijiyoyi masu kawo sako da gurbata jin sauti.
Don haka kafin a yiwa mutum mai wannan lalura wannan aikin, a sanya zuciya karbar kaddarar samu ko rashi. Duk da a mafi yawan lokaci a kan dace da yin nasara a wannan aikin fidar kunne, amma akwai wahala wajen yanke hukuncin yinsa farat daya da matsalolin da ake samu idan aka yi rashin dace.
Saboda haka ne yasa wasu ke gwammacewa da yin amfani da na’ura mai kara ji cikin kwanciyar hankali har jinsu ya zo ya zama ya tabarbare, inda wannaan na’uraa kan daina yi musu aiki kwata-kwata.
Hakan yasa wasu kan zabi ayi musu aiki tunda wuri, wanda hakan zai sa su zama basu da bukatar wannan na’ura in an zabi yin aiki, ka ga in aiki ya yi nasara to an samu waraka kenan, in kuma an sami matsala ka ga ya zama cewa kunnen da yake da kyau sai mutum ya ci gaba da amfani da shi. Wato an jefi tsuntsu biyu da dutse daya.
Masana a fannin ENT (Ear, Nose & Throat) sunyi muhawara a kan cewa ko da nan gaba a iya yiwa wancan kunnen da ya rage. Wasu daga cikin su sun yarda kan cewa gara mutum ya hakura ya ci gaba da amfani da na’urar kara ji saboda risk hatsarin dake tattare da yin aikin na samu ko karasa kashe kunnen gaba daya.
Madallah da kuka kawo yarinyarku tun kafin na’urar kara karfin ji ta daina yi mata amfani, wato kafin lalurar ta tabarbare da yawa. Akwai shaida takaitacciya wadda ke da’awar cewa kwayoyin magani na flouride za su iya hana ji, kuma za su iya taimakawa wajen kyautata jin. Da ragewa mai lalurar juwa da hajijiya. Amma dai a nan Sikotilan ba’a cika amfani da kwayoyin maganin na flouride ba.
Don haka zabi yana gareku, ci gaba da amfani da na’ura, fida ko kwayoyin magani. Akwai bukatar in baku lokaci zuwa gobe don ku yi tunani da kyau ku yi zabi cikin ukun don samun lafiyar Rayhanah.......”
Har suna hada baki wajen katse shi da cewa, “Babu wani tunani da zamu yi mun dogara ga mahaliccinu, wanda ya saukar da kowacce irin cuta tare da maganinta. A yiwa Rayhanah fida a dukkan kunnuwan guda biyu. Sauran al’amarin (nasara ko rashin ta) mun barwa Ubangijinmu”.
Murmushi Dr. Philips ya yi, yana gyada kai cike da gamsuwa, haka nan shima ya ji ya samu kwarin gwiwa. Ya tura musu takardu cikin folder suka sanya hannu.
Zunzurutun kudin aikin Dr. Mansur ya tura masa cikin jakar dake gefensa (in cash) ba ta banki ba, kamar yadda Philips ya bukata. A yayin da ya dauki biro don rattaba sa-hannu cewa ya yi.
“TAWAKKALTU ALAL-LAH!
LA’ILAHA ILLALLAH!!!”
Wato
“Da Allah muka dogara! Babu sarki sai Allah!!!”

Bai yi barci ba, kwana ya yi nafila, zikirin Ubangiji da neman dacewa daga Allah. Tun Dr. Imam na jan carbi a gefe, har bacci ya kwashe shi a kan sallayarsa bai san tsahon lokacin da Dr. Mansur ya dauka yana sallolinsa da ambaton Ubangijinsa ba.
Yana mamaki cikin ransa, wane irin so Dr. Mansur ke yiwa patient dinsa haka? Da ba shi ya haifa ba? ‘Yan boko da yawa basu da wannan akidar. A wajen gogaggen dan Arewa a boko kowa ya yi ta kansa. Naka shine naka, basu da irin wannan zuciyar. A ganin Dr. Imam mutane irin Mansur, tsiraru ne a cikin al’ummah. Wannan haka yake (Takori)

****

ALKAWARIN ALLAH YA CIKA......
Kamar daga nesa take jiyo kiran sallah, don haka ta yi hanzarin kai hannunta ta shafo na’urarta, don dai ta san bata kwanciya da ita, kuma gabanin alluran da Philips ya yi mata ta tabbata ta cire su.
Da gaske babu su a tare da ita, hakan kuma bai hanata jin kiran sallar Asubar ba. Ta yi saurin juyawa don ganin ta inda sautin ke fitowa. ‘Yar rediyon Dr. Mansur ce dake kan dirowar gadonta ke fitar da sautin kiran sallar. Daga masallacin Qubah.
Wata sassanyar iska kuma ta ji tana ratsawa ta cikin kunnuwanta zuwa cikin kwakwalwarta. Ba ta ko haufi jinta ne ya dawo! Rasss!! Kuma rangadadau!!!.
Sai ta yunkuro da karfi daga kwancen da take, sai Daddy ya yi saurin maidata kwancen sakamakon na’urorin dake lullube da kanta.
“Rayhanahtu aikin bai yi ba ko???” Dr. Mansur ya fada muryarsa na dan rawa jikinsa na dan karkarwa.
Ta dago ido a hankali ta dube shi sai kwallar farin ciki ta ciko idanunta. Ta kurawa Daddy ido kawai ta kasa cewa komai. Ko uban da ya haifeta iyakar kaunar da zai yi mata kenan. Ita kuwa da me za ta sakawa Daddy a fadin duniyar nan? Babu, ba ta da shi ban da ta yi masa addu’a a bayan kowacce sallar farillah kamar yadda take yiwa iyayenta da Iya.
Dr. Mansur ya gaji da kallon da Rahane ke masa babu ko kiftawa hawaye na zuba a idonta, ya karaso jikin gadonta yana tambaya “Rayhanatu........Rahane.......Rayhanah.......kina jina???”
Cikin kukan farin cikin da ya kwace mata ta ce, “Ina jinka Daddy, sosai, ba tare da hearing aid ba!”.
Sai ya juya baya ya yiwa Allah Sujjadah. Dai-dai lokacin da Dr. Philips da Dr. Imam suka shigo. Suka nufeta da azama suna ciccire na’urorin domin allon kwamfutar dake makale a sama ya nuna komai na Rayhanah ya dawo normal.
Kwanaki bakwai suka kara bayan nan duk cikin treatments din ne, da shan magani, sai da komai ya zama dai-dai sannan suka taho. Suka sauka da asubahin safiyar Litinin mai albarka a filin jirgin Malam Aminu Kano.
Daddy bai yi mamakin ganin cewa Mami ba ta zo taryarsa ba, ya san ba ta sani ba, kuma ko ta sani ba za ta zo din ba. Don ko sallamar kirki basu yi ba, wannan ne ya hanashi kiranta a waya har suka je suka dawo.
Matar Dr. Imam ta zo ta dauke su, suka aje Daddy da iyalinsa a gidansa dake Lamido Crescent sannan suka wuce nasu gidan a Badawa lowcost.
Malam Dahiru maigadi shi ya biyo su da kayansu. Daddy ya yi amfani da mukullin shi ya bude kofar reception suka bi matattakala zuwa sama.
Jawahir da Abida na barci Zizah ta fada musu a kai tana ihun murna, “Tashi Yaya Jawahir, Yaya Abida tashi, Rayhanah na ji (with out aid), it is successful...... ku tashii ku gani....”
A gigice Jawahir ta mike da gudu ta rungume Rayhanah, sai ga kwallar farin ciki. Abida kanta ta mamakantu, ta kasa komawa barcinta ta rasa cikin yanayin da take ciki, tana taya masoyan Rayhanah murna ko tana bakin ciki ne ba ta sani ba. Abin da ta sani shine jikinta ya yi sanyi, ta kasa hassala komai.
Rayha wanka ta yi, ta dauro alwala ta bada faralin Asubahi, ta yi addu’o’i na godiya ga Gafurun-Rahimun, neman Rahamar Allah ga iyayenta da Baba Dacta ba don ya mutu ba. Duk hirarrakin da Azizah ke zuba musu labarin kauyen Braemar ne da basu sani ba.

****




Sanda Daddy ya shiga bed room dinsa, ga mamakinsa sai ga Mami ta biyoshi fuskarta a sake kamar ba abinda ya faru.
“Maraba da bakin Scotland, duk da dai tafiyar da dawowar duka babu waya..... da fatan an samu nasarar abin da aka je nema”.
Ta fada tana loosing tie din wuyansa. Bai ce komi ba kawai kallon ta yake. Sai ta fada jikinshi tana kuka a hankali tana ba shi hakuri da cewa, ta zauna ta yi tunani ta ga cewa abin da ta yi bai kamata ba, kishi ne da sharrin shaidan, wanda baya so a zauna lafiya.
Tsakanin mace da mijinta sai Allah. Balle Asma’u da Mansur, wadanda suka gina rayuwarsu a kan soyayya, kauna da fahimtar juna.
Ya ce, “Ni me za ki ce min kuma Mamina, tunda kin daukeni dattijon banza, wannan furfurar da ta fara baibaye kaina duk ta banza ce. Ban taba zato ba Asma’u, ban taba zaton za ki iya zargina a kan komai ba balle Rayhanah! Zan dauki komai, amma ban da a taba mutuncina da gemuna da furfurata.
Zan iya rabuwa da komai a kan hakan Asma’u.......... Rayhanah ‘yata ce, ki sa wannan a ranki, ina jin wani abu daban game da ita a jikina da zuciyata mai kama da kaunar jini a kanta. Allah shi ya fi kowa sani. Amma kin bani mamaki Mami, mamaki sosai, wanda ya sanya ni cikin kokonton anya ke ce? Asma’u ina hankalinki ina tunaninki? Ina yardarm da muka yiwa juna........”
Ta yi saurin kai hannunta ta rufe mishi baki tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta.
“Na tuba Dactana, na tuba likitan zuciyata. Tun ranar da wannan al’amari ya faru ban kara samun nutsuwar zuciyata ba, bana isasshen barci saboda nadama. Na yarda lallai lokacin hankalina ya tafi, ka yi hakuri Dactana, don Allah ka yafe mini.......”
Irin rikon da ya yi mata kadai ya isa amsar cewa ya yafe mata ko bai yafe mata ba. Tabbacin shima ya jigata da rashinta.
Da safe ne yake gaya mata duk abin da ya faru a Braemar da nasarar da aka samu. Ta mamakantu kwarai, kuma a lokacin ta tafi dakin su Rahanen.
Fuskarta da murmushi ta dubi Rayhanah ta ce, “Congratulation Rayhanah, Allah ya kara lafiya”.
A sanyaye ta ce, “Amin”. Tana son ta yi kuka zuciyarta cike da kaunar Mami da tsoron kada ta komo irin Mamin da ta koma mata a baya.

To haka rayuwar Rayhana ke tafiya a gidan Dr. Mansur, cikin dadi ko akasin sa. Dama rayuwar ta gaji haka. Watarana zuma, watarana madaci. Mami ta daina kyararta, amma fa bata shiga sha’aninta kamar da. Girman da yake bayyana a tare da Rahanen yana bata tsoro, yarinya ta koma kamar black American, kirar jikinta da yanayin tsayinta mai sa maza su kasa dauke ido a kanta ne.
Ga zigar Dr. Halima wadda ta fi komai yamutsa mata lissafi. Ta kan ce idan ba ta raba yarinyar nan da gidanata ba, to kuwa ta shirya shan mamaki a gaba. Asiri kuma ko ta ina Halima bankawa Khalipha take don ya yarda da maganar Radhiyyah, shi da ma kwata-kwata babu wanda ya san halin da yake ciki.
Su ba kudi ne basu da shi ba, ba kuma wani abin hannun Khalipha ko iyayensa suke hange ba, kawai tana son samawa ‘yarta abin da take so ne, don ta samu kwanciyar hankalinta.
Cikin wannan tsukin Khalipha ya dawo Morocco, ya kammala kwas din da aka tura shi, ya samu karin girma a ofis dinsu. Kowa ya sha tsaraba amma ta Rayhanah (is special).
Kaya ne na matan Morocco zabga-zabga, wasu lafiyayyun dogayen riguna kala-kala guda goma sha biyu, da Pakistan da Abayat suma kowanne dozen guda. Ya yin da kannensa suka tashi da guda shida-shida, doguwar riga biyu, Pakistan biyu da Abayoyi guda biyu.
Wannan karon kam Mami ta kara karfafa zarginta, ta kuma sa ido sosai a mu’amalar Rahane da Khalipha.
Da Khalipha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login