Showing 12001 words to 15000 words out of 30449 words
dan Adam.
Bai yi da niyya ba, bai hadasu ba su suka hada kansu. Shi dan bin umarnin Allah ne kawai da sunnar ma’aiki da ya ce idan ‘ya’yanku sun nuna suna son aure, to ku yi musu cikin umarnin Ubangiji.
Ban da haka shi bai taba hasaso Khalipha zai taba cewa yana son Rayhanah ba, yana dai da nashi burin a kan Rayhanan amma tunda Khalipha ya riga ya furta to ya kashe waccan kudirin nasa ya karbi wanda Allah ya bayyana.
Duk sati Khalipha na tafe, baya Abuja baya Kano, baya Kazaure. Wata muguwar shakuwa da fahimtar juna ta wanzu tsakaninsa da Rayhanah. Duk da cewa kullum shine mai nuna son, kalamanta tsada suke masa saboda kunyarta, in yana so ya ji furucin bakinta, to sai ya kirata da Rahane, ko ya ce matar Audu, a nan kam ba ta jurewa sai ta bayyana masa kyawawan hakoranta guda talatin da biyu.
Ba soyayya ce kadai tsakanin Khalipha da Rahane ba, akwai wani abu wai shi yarda da juna, kusancin zuciya da zuciya da amincin da ya zarta soyayya.
Ko Baba Dacta bai san Rahane yadda Khalipha ya yi mata kyakkyawan sani ba ciki da bai dinta. Ya san halinta, ya san abin da take so da wanda ba ta so. Ba ta da yawan ado, kuma ba ta cika kwalliya a jikinta, she is smart, and simple. Yana son Rayhanah har yadda ba zai iya kwatantawa ba. Yana son Rayhanah yadda shi kansa bai san adadin ba.
Yadda kwanaki ke gudu suna juyawa tamkar gare-gare abin wasan yara a wannan zamanin, don haka bai zamo abin mamaki ba idan aka ce har ga watanni takwas sun cika. Rahane ta fito da kwalin (International Diploma in Cyber Security) tare da admission na daukar ta degree a babban reshensu dake kasar Singapore, a matsayinta na (overall student).
Fadin irin farin cikin da Baba Dacta ya yi ba zai fadu ba, a take ya yiwa Khalipha waya yake sanar masa ita ma Mami ya sanar da ita tun kafin su iso Kano daga Kazaure.
Mami ta dade zaune a bakin gadonta tana mamaki, don dai akwai ‘ya’yan kawayenta da dama a Informatics fin shekaru uku sun kasa fita daga makarantar. A karshe sai bari suka yi aka yi asarar dubunnai. Da gaske Dr. Halima take idan har ba ta raba yarinyar nan da gidanta ba, ba ta gama shan mamaki ba.
A take ta bugawa Dr. Halima take sanar mata. Ta ce da ita kada ta damu komai ya zo karshe, amma ta shirya gobe su wuce Plateau (Jos) tushen Mami kenan, komai ya kammala karbowa kawai za suyi.
Don haka da suka iso ba ta yi wani action negatively a kan nasarar Rayhanan ba. Sai dai shi a can Khalipha ya shiga damuwa, yana tsoron kada Daddy ya yarda da batun tafiya yin digirin ba tare da anyi aurensu ba.
Don haka ranar Juma’a ya baro dukkan ayyyukansa ya taho Kano, abin haushin Daddy baya gari ya je Ireland wani taron karawa juna sani a kan cutar Otosclerosis a matsayinsa na ganau ba jiyau ba a kan fidarta, da aka yi aka kuma ci nasara a yankin Braemar.
Khalipha ya yi sallama a bedroom din Mami ba ta ji ba tana waya, kuma da yake ta bai wa kofa baya ba ta ga shigowar shi ba. Hirar da take yi a wayar bai fahimceta ba, amma kawai jikinshi ya ji ya yi sanyi da ya ji Mami na cewa, “Ko zan yi yawo tsirara haihuwar uwa da uba na Khalipha ba zai auri yarinyar nan ba”.
Ta ajiye wayar tana huci, a lokacin ne ta ankara da shigowarsa. Ta kasa saisaita fushinta ta kasa boye anger din da ta taso mata. Don haka kallon sa kawai ta yi ba ta ce masa komai ba.
A salube ya zauna a kusa da ita gwiwoyinsa babu kwari, duk da bai san wace yarinyar ake nufi ba tunda Allah bai nufe shi da jin an kama suna ba.
Khalipha ya san iya rayuwar Mami ba ta da makiyi, ba ta da mugun hali. To a kan wa take cin mugun alwashi haka? Ta dago idanunta jajir ta dube shi.
Cikin kakkausar murya ta ce, “ABDALLAH!”
A firgice ya dubeta saboda shi dai tsawon rayuwarsa bai taba ji ko da kuskure ta ambaci sunansa na ainihi ba, sai ko ranar da ta je gidansa a Abuja ta kama shi da babban laifi. Fargaba bata barshi ya amsa ba.
Ta ci gaba da cewa, “Duk abin da kuke ciki kai da ubanka na sani, tunda ban yi kama da wadda ba ta je makarantar boko ba. Amma ina so in ji sahihiyar amsa daga bakin ka, tunda Allah ya hana hukunci a kan zargi”.
Ya girgiza mata kai alamar yana sauraronta. Kafin ta jefo masa tambayar tata da ta shafe taraddadinsa.
“Wace ce yarinyar da kake so ka aura?”
Ba tare da nuku-nuku ba kai tsaye ya ce, “Rayhanah!’
Ta sake cewa, “Wane ne mijin da Dacta yake so ya aura mata?”
Ya nuna kirjinshi ba tare da ya yi magana ba wato “Shine”.
Mami ta girgiza kai, “Kai tsaye abin da zan iya cewa shine, ban amince ba! Watakila bai gaya maka alkawarin da muka yi da shi ba kamin in yarda da zaman yarinyar nan tare da mu. Kai kuma da fari ka munafunce ni, tunda har Abuja na taka na je saboda kai da damuwa da halin da kake ciki, amma ka ninke ni a bai-bai, saboda ka raina min hankali.
Me ka gani a jikin wannan yarinyar Khalipha ban da son zubar mana da kima da mutunci? Kaskantaccen asali, ragowar cuta, babu iyaye babu dangi, an ce ‘yar Takai ce uwarta da ubanta da kakarta sun rasu, to su daga sama suka fado kenan tunda basu da dangi?” Ta fidda manyan idanunta.
Khalipha tun daga kansa har yatsar kafarsa gumi yake, duk da sanyin split dake neman daskarar da mutanen dakin. Tunda ta fara magana bai ce mata komai ba, haka da ta dire tana sauraron jin ta bakinsa amma ya gaza ce mata komai.
Ta nuna shi da dan-alinta cikin matsanancin fushi ta ci gaba da magana, “Idan kana son zaman lafiya dani, to ka bar maganar nan, ka kai wa ubanka maganar Radhiyyah, idan fa har ni na haifeka na yi nakudarka bayan daukar ka cikin mahaifata har tsayin watanni tara cikin halin kaka-nikayi.
Ba ta yi isar da zan hada jini da ita ba. Wannan kawai ita ce magana. Idan ma ka je ka ce masa ka fasa kai masa zancen Radhiyya, idan ka ki kuma kada ka ga laifina a kan duk abin da ya biyo baya.
Kwanaki biyu kacal na baka ka je ka warware kullin naku kai da uban naka, in ba haka ba wallahi za ku sha mamaki, na shirya karbar kowanne bacin rai na Dacta, na shirya masa kana iya tafiya, wannan shine”.
****
Saboda gigicewa Khalipha bai tsaya kara ko mintuna biyar cikin gidan ba, ya juya kan motarshi ya dauki hanyar Abuja.
Karfin zuciya irin ta namiji da karfin imani da tasirin addu’a su suka kawo Khalipha Abuja lafiya, amma ba nutsuwar tuki ba.
Maganar a ce ya hakura da Rayha ma ba mai dadin ji ba ce a kunnensa, gara a soka mai allurai dari ba daya da wannan furucin na Mami, wai ya ce da Baba Dacta ya fasa auren Rayhanah. Ta ya ya? Ta ina? Ta wace hanya? Da wane bakin da wace fuskar zai je ya fadi hakan?”
Sai dai fa wani bangare na zuciyarsa na gaya masa, wannan fa umarni ne na MAHAIFIYA, wanda bai isa ya musunta shi ba. Don haka Khalipha ya shiga wani irin tashin hankali da bai taba shiga irinsa ba. Har kullum Mami da Daddy abin da suke so suke musu, don haka ba duka kalubalen rayuwa suka sani ba. Basu san su so abu ko yaya su rasa ba balle soyayyar zuciyarsa ga Rayhanah! Wadda yakeda yaqinin an halicci zuciyarsa ne tare da sonta, kowanne bugunta kuma ke tafiya tareda kaunarta.
Don haka haqiqatan baima san takamaman inda son Rayhana yake ba specifically azuciyarsa, balle yasa wuka ya yanko mata shi, tunda ya mamaye zuciyar duka, sai dai Mami ta tsigeta gabadaya (zuciyar) daga shi har ita kowa ya huta.
Bayan kaduwa da tsorata, yana cikin mamakin ashe halin mutum yana canzawa haka farat daya daga mai kirki da sanin ciwon kai zuwa mara kirki da tunani?
Iyaka hangensa bai ga hujjar Mami kwakkwara guda ta haramta masa abin da yake so shekaru har takwas da doriya ba, bayan kuma ya riga ya sanar da mahaifinsa ya yi na’am, me Mami take so Daddy ya dauke shi?
Idan ya je ya ce ya fasa auren Rayhanah? Fiye da wannan ma, ya ya rayuwar za ta kasance idan babu Rahane a ciki? Mene ne hujjar Mami na cewa lallai sai ya auri ‘yar kawarta? Ita ba kwadayi ba, su ba kwadayi ba, me Mami take nufi ne? Ka taba auren wadda baka taba jin kana so ba? To ta yaya za ku rayu?
Shi fa ba wai so kawai yake yiwa Rayhanah ba, har da son ya tallafi rayuwarta ya ingantata, idan bai aure ta ba wani ne can da bai san darajarta ba bai san mutuncinta ba zai aure ta.
A yadda mazan yanzu suka mayar da aure kamar sanya riga da tube ta ga ‘ya’yan gata ma ba marayu marasa madafa irin Rayhanah ba, wane ne zai aure ta ya daraja ta? Ya rike musu ita irin yadda sukeso shida Daddy???
Bai yi aune ba sai ji ya yi wani ruwa mai dumi yana fita daga idonsa. Da ya kai hannu ya sharesu, wasu ne suka kara shimfidowa aguje. Wannan karon bai yi wata hobbasa ta hanasu zubowar ba, kyalesu ya yi suka yi ta shatata, fitarsu na rage masa suyar da kirjinsa ke yi.
A gida ko ofis, cikin kwanaki biyun nan Khalipha ya gama fita daga hayyacinsa. Ya rufe waya, ya kasa aiki a ofis, ga shi ya yiwa Mami alkawarin barin shan Marlboro balle ya sha ta wanke mai zuciya. Maimakon hakan ya yanke shawarar fara shan zam-zam ya zamo masa ruwan sha.
A hankali sai ya ji tunanin da yai yawa da katutu cikin kwakwalwarsa da zuciyarsa na raguwa, nutsuwa ta zo mishi, addu’a kawai yake da nafilfili Allah ya sauko da zuciyar Mami, don dai ya kasa aiwatar da umarninta har yau.
An debi kwanaki har hudu, Khalipha bai cika umarnin Mami ba, ya kashe waya tun dawowarsa. Itama Rahanen baya kiranta, don baya son ya zamo heart breaker a gareta. Ko da yake dai-dai da second daya bai taba tunanin wai zai iya hakurin da ita ba.
Mami ta neme shi a waya har ta gaji, domin tana son aiwatar da kudirinta a kan Rayha da Khalipha kamin Daddy ya dawo ne kada ya bata mata lamari. A yau saura kwanaki biyu Dr. Mansur ya dawo Najeriya.
Cikin daren Khalipha ya kasa barci ya kuma kasa kunna waya. Ya lura Mami so take ta zurma shi cikin laifin shi kadai wajen Daddy ba tare da sunanta ya fito ba.
“Ya Allah me ya samu mahaifiyata ne haka? Ya Allah me na yiwa Mami da a yau ta gwammace in sarayar da farin cikin rayuwata a banza? Saboda Rayha ta fito daga tsattson talakawa, ta yi cuta shine kawai hujjar a ki aurenta?
Mami ta manta ita ma tana da ‘ya’ya mata? Abin da ya faru da Rayha zai iya faruwa ga ‘ya’yanta, sai a ce kada a aure su?
Ita ‘yar masu kudin me za ta yi mata? Kudi za ta ba ta ko Makka za ta kaita? A iya sanin Khalipha Mami ta fi uwarta albashi mai tsoka, ubanta ne dan siyasa (arzikinku na dan wani lokaci) balle ya ce wani abu Mami ke hange a kan lamarin. Yadda take daukar al’amarin Dr. Halima da muhimmanci ba ta daukar na mijinta haka yanzu. Ta zama wata irin masifaffiya, ya tabbata muddin ya gayawa Daddy cewa ita ta ce ya yi kaza ya yi kaza Daddy zai sa mata katanga ma ba birki ba.
Ya kuma lura ita ma ta shirya daukar kowanne hukunci daga Daddyn idan ya tuno da kalamanta. Wanda ba zai so haka ba, a kan nasa auren ya raba na iyayensa. Kuma ta ce duk abin da ya biyo baya idan ya ki bin umarninta kada a ga laifinta. Wato za ta iya korar Rayhanah daga gidanta, ta fada wani hannu da basu sani ba tunda su ba mazauna bane daga shi har Daddy.
Wannan tunani da Khalipha ya yi ya razana shi ba dan kadan ba. Bai san sanda ya mika hannu ya dauko wayarsa daga kan center table ya kunnata ba. Bai tsaya karanta sakonnin dake ta tuttudowa cikin wayar ba, ya yiwa Mami text ya tura mata ya sake rufe wayar da sauri a lokacin da kiran Rayhanah ya shigo. Kuwa riris Khalipha yake yi wanda bai taba yin irinsa a rayuwarsa ba.
****
A lokacin da sakon Khalipha ya shiga wayar Dr. Asma’u tana ofis dinta tare da Dr. Halima suna ci gaba da kulle-kullensu na tsiya, a kan mutanen da basu ji ba basu gani ba, son zuciya kawai da raina talaka.
“Ya rufe wayar har yau na kasa samun shi, fargabata gobe Dr. zai dawo, so nake mu gama kafin ya dawo kada ya bata al’amarin don na rantse zai iya yin komai don ya nuna min bacin ransa, mafi kankantar ciki shine SAKI, ni kuma na shirya masa”.
Dr. Halima ta ce, “Wallahi kuwa, ko yau kasuwar ta watse dan koli ya ci riba. Wa zai dube ki ya ce kin haifi Jawahir ma balle Ibrahim da Khalipha? Wallahi za ki yi mamakin yadda consultants za su yo rubdugu a kanki. Dr. Mansur ya raina ki, ki yarda da abin da na ce, ya raina ki”.
Fuskar Dr. Asma’u ta muzanta kwarai, ba abin da ta tsana a rayuwarta irin raini. Babbar hujjarta ta kin Rahane kenan, ta fito daga tsatson raini, abin kunya cikin kawayenta da tsararrakin yin ta.
Shigowar sakon cikin wayarta yasa ta sassauta bacin fuskarta, ta dauki wayar ta bude.
“Uwata da na sani a baya farin cikina shine nata, babban tashin hankalinta shine shigata cikin damuwa, ko wani hali na kaka- nikayi. Mami would never lose her temper to such an extent....... shi yasa har yau na kasa yanke hukuncin yarda da abinda idanuwa da kunnuwa na suka jiye mini daga Mami. Ina cikin tantamar, anya Mamina ce???
A cikin kwanakin da ban yanke hukunci ba, so nake idan mafarki nake Allah ya farkar dani. Mamina ta asali za ta iya kadar da duk abin da ta mallaka saboda farin cikinmu. Sai nake tambayar manazarta halayyar dan Adam cewa, shin dama halin mutum yana canzawa a lokaci daya?
Tunda dai na yarda cewa ba mafarkin nake yi ba, cikin biyayyarki da umarninki na hakura da Rayhanah..... Allah ya ba ta wanda ya fini......ki ce Amin Mami ba don ni ba sai don kasancewarta Musulma ‘yar musulmai ‘yan’uwanmu.
Ni kuma ki aura min duk wadda ta yi miki Mami........ na yi miki alkawarin zama da ita har karshen rayuwata! Amma kada ki yi yunkurin raba gidan nan da Rahane Mami, ko don ki ceto mana aurenki da kwanciyar hankalin Daddy. Idan akwai biyayyar da ta fi wannan Mami ina rokon Allah ya bani ikon yi miki. A yau zan gayawa Daddy na hakura da RAYHANAH......na karbi zabin ki Mami. Ina neman albarkarki. Dan ki.
-Khalipha.
Ta dade tana maimaita karanta sakon dake neman karya mata zuciya, Dr. Halima na ta magana amma ba ta jinta. Sai ta kwace wayar ta soma karantawa. Farin cikinta ya kasa boyuwa a fuskarta.
Ta ce, “Ki ji yaro da lauya magana, wallahi sai ta tafi in ba haka ba ba’a rabu da Bukar ba an haifi Habu muddin tana cikin gidan yana ganinta. Ta ruwan sanyi za ta tafi babu duka babu zagi balle bakar magana”.
A nan ne Mamin ta yi magana, “Ina ganin mu kyale yarinyar nan Halima tunda dai an samu ya yi kokarin da ba’a zata haka cikin sauri ba. Baki san Khalipha ba a kan abin da yake so, kamar kuma yadda ya ce din ne AURENA zai yi tangal-tangal idan ya dawo ba ta gidan, babu kuma wata kwakkwarar magana kan inda ta shiga”.
Dr. Halima a fusace ta ce, “To shi kenan, na rantse kuwa za ta zama kishiyarki idan Khalipha bai aura ba. Kuma ai ba korarta za ayi ba, kiranye za ayi mata ta koma mahaifarta ko za a kasheta ba za ta yarda ta dawo ba. Ai muma Musulmai ne, ba cutarta zamu yi ba”.
Ta yadda da maganar Dr. Halima dari bisa dari har cikin ranta.
** **
“Daddy yaushe za ka dawo?”
Khalipha ya tambayi Baba Dacta a raunane, bayan sun gaisa ta waya. Maimakon ya ba shi amsar tambayarshi sai ya ce, “Ya ya na ji maganarka so cool, wani abu ya faru ne?’
Ya girgiza kai cikin karin hawaye ya ce, “Eh to, magana nake so muyi ta fahimta.....”
Sai kuma ya yi shiru.
“Ba za a iya barin maganar har sai na dawo ayi ta face-to-face ba? Tunda na lura mai nauyi ce?”
“To shi kenan Daddy, yaushe za a dawo?’
“Yanzu haka na taho on transit nake a Germany. Zuwa asubahin gobe ina Kano insha Allahu”.
** **
Dawowar Daddy gida lafiya, da kuma ganin yanayin fuskarsa bai canza ba ko kankani, yasa Dr. Asma’u cikin kokonton anya Khalipha ya yi abin da ya ce zai yi bisa umarninta? Irin kayan da ake shigowa dasu ana jibgewa a (store) ya kara tabbatar mata da lallai Khalipha ya rainata.
Kayan furnitures ne ‘yan ubansu-ubansu da manyan jakunkunan zamani shake da duk wani nau’in suttura ta kwalliyar mata da suka fi kama da kayan lefe.
Dr. cikin walwala yake matuka, a lokacin da yake nuna mata kayan, yana yi mata bayanin lefen Khalipha ne. Ya kaikaice ya zaro warawarai guda shida na farin zinare daga aljihunsa, ya ce ga shi ta adana, shine sadaki.
A wannan lokacin ya kwantar da harshe ya ce,
“Asma’u na san bani da kalaman wanke kaina daga daudar mai laifi a gareki, amma ina baki hakuri, bani kuma da hannu a ciki. Kamar yadda na ce ba zan hada ba ban hada ba, su suka hada kansu, ni kuma na ture komi, na