Showing 15001 words to 18000 words out of 30449 words

Chapter 6 - Rayuwar Rayhana Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

28 Dec 2024

97

zabi in cika umrnin Ubangiji in ya so in yi kaffara a kan alkawarin da na yi miki. Tsakanin ‘ya’yanki da ‘yar amanar da Allah ya bamu.
Zan iya cewa ban karya alkawari ba, tunda kuwa ban hada soyayya tsakanin Khalipha da Rayhanatu ba. Ki sa fahimta a cikin lamarin nan, ki sa albarka, ki dauki duniya da sauki. Khalipha ke son auren Rayhanah, ni kuma na ba shi da na tabbatar da amincewarta. Ga wannan.....”
Ya tura mata bandir din bugaggen (invitation card) na daurin aure da yasa aka buga masa a Dublin..
Ya kare da cewa, “Jibi Lahadi insha Allahu za a daura auren a gida Takai, Hakimi shine waliyyinta. Don haka ga wannan”. (Ya tura mata ATM Card dinsa na bakin (Gruaranteed Trust).
Ya ce, “Ki dauki abin da zai isheki, daga naira dari har zuwa miliyan biyu na lamince miki ki fara shirye-shiryenki. Na taho da komai na kawata gida, kayan kithcen ne sai ku mata. Da sauran abubuwan da babu sai ki karasa. Duk wasu activities da kike ganin za a yi ayi, amma ban da wanda za a hada mata da maza. Kin yi hakurin Mamina kin fahimceni?”
Sakatoto! Ta yi tana mishi kallon takaici, kamar ta amayo zuciyarta ta huta. Ta so yin kissa ta karya, amma ba halinta bane, don ba ta iya ba. Wadanda take yi a baya ma duk Dr. Halima ke koya mata, ga shi kuma ba ta zaci haka ba, ba ta koyo yadda za ta karbi zancen ba.
Sai kawai ta aje warawaran da ya dora mata a cinya da katinan daurin auren a nan gabanshi ta mike ta yi dakinta ba tare da ta ce da shi komi ba.

Ta zauna a gefen gadonta jikinta yana bari ta kira Khalipha. Bugu biyu ya amsa cikin nutsuwa, domin yana bisa sallaya ne yana mikawa Ubangiji bukatunsa, bayan sallame nafila raka’a hudu, wadda a kowacce raka’a ya karanto suratul Ikhlas kafa bakwai.
Sallah ce ta neman zabin Allah ita ma, amma ba Istikhara ba. Tuni Khalipha ya dade da samun nutsuwar zuciyarsa albarkacin ruwan zam-zam mai sanyi da ya mayar ruwan shan sa.
Ko ya ya rayuwar ta zo, ya shirya karbarta, in dai zai wanye lafiya da mahaifiyarsa, kuma mahaifinshi kada ya ga laifinta.
Ya manta shima uba yana da nashi hakkin amma Khalipha ji yake ya gwammace bacin ran Daddy a kan na Mami. Daddy mai saukin hali ne ba ya daukar al’amuran rayuwa da zafi.
Duk da haka ya san idan sunan Mami bai fito ba, duka laifin kanshi zai kare, domin Daddy baya son karanta kuma baya shiri da mai magana biyu, balle a kan ‘yar da ta fi nashi ‘ya’yan a zuciyarsa.
Zai karbi duka laifin in dai hakan shine farin cikin Mami, wadda yake wa wani irin so na UWA wanda ya zarta wanda yake yiwa ubansa Dr. Mansur.
Tana huci kamar mesa ta ce, “Abdallah!”
Ya amsa “Na’am Mami”.
“Ni ka yaudara ka wulakanta ko?”
Ta fada tana nishi kamar wadda ta yi tsaren ceton rai.
Ya ce, “Subhanallah! Kada Allah ya nuna min ranar da zan yi miki dayan biyun hakan, ya dauki raina kafin in yi hakan....”
“Rufe min baki”.
Ta fada cikin tsawar da bai taba ji ta yi ba.
“Ka ce za ka kira Dacta ka fada mishi cewa ka fasa auren matsiyaciyar yarinyar nan Radhiyya kake so, shine baka kirashin ba kuke shirye-shiryen biki ta waya har I.v an bugo jibi daurin aure.
Wane irin tozarci kake so ka yi mini? Na ce ban yarda ba, ba ta isa ba, ba ta isa ba wallahi in yi suruka da ita. Zan la’ance ka Khalipha…….. muddin ka yarda aka daura ma aure da yarinyar nan jibi.....”
Ta kashe wayarta, ba ta saurari uzurinshi ba, ta barshi a wani hali da ya kasa tantance wane iri ne.
Wayyo! Allah sarki Daddy...... ashe shi yana can yana yi min gata ban sani ba...... ashe shi yana can yana so ya yi surprizing dina a kan alherin da ban taba son wani abu kamarsa ba.
Amma sakamakon sa shine in karya masa zuciya in zubar da mutuncina a idanunsa. Kullum cikin hirarsa sai ya ce, “Karamin mutum shine mai saka hairan da wulakanci, yau zan zama mayaudari, a RAYUWAR RAYHANAH! Zan ceci auren uwata, ni in tsira da hakan, Allah ya baki hakuri Rayhana, ya baki wanda ya fini......”
Ya kifa kai jikin gadonsa yana kuka da sauti.
****
[12/24/2019, 21:47] Takori: Daddy na kan hanyar Takai bayan motarsa shake da goro da alawa lokacin da wayar Khalipha ta shigo masa. Don haka bai daga ba domin baya amsa call yana tuki, shi kuma Khaliphan bai fasa kira ba.
Kira a kai a kai wanda ya tabbatarwa Dr. Mansur cewa wannan kira ba na lafiya bane, domin Khalipha baya takurawa mutum da kira, kusan kullum ma shi wayarsa a (voicemail) take. Sai ya ratse kan hanya ya parker motar ya amsa kiran Khalipha.
A nutse suka gaisa shi da Daddyn, sai dai yadda Daddy ya ji muryar Khalipha babu amo (a dushe) kuma sanyinta ya yi yawa ya tabbatar Khalipha ba shi da lafiyar zuciya da kuzari cikin gangar jikinsa. He is always very energetic a murya da zuciya, kuma a muryarsa yake karantar halin da zuciyarsa ke ciki.
Bayan sun gaisa ya ce,
“Ina kan hanyar Takai ne zan kai wa Hakimi goro da alawar daurin auren ka, gobe insha Allahu za a daura karfe goma sha daya na rana.
So ka bar kome kake yi ka taho Takai a yau, abin ne ya zo a kurace, don haka a kuracen za ayi, duk wata gayyata na gamata a jiya sai ko ‘yan office din ku su ma ka yi text kawai ka turawa kowa.
Na jika ba a yadda na saba jinka ba, wani abu?”
Hawaye suka ziraro daga idanun Khalipha, sharrrrr..........suke zuba kamar an sunce famfo. Ya ce cikin rishin kuka, “Daddy na gode da kaunarka da kulawarka gareni, da kyakkyawar zuciyarka mai son faranta min a kullum.
Abin da zan fada yanzu don Allah Daddy kada ka yi masa wata fassara daban, ko ka yi tunanin na yi ne don in mai da kai abokin wasana, ko kuma na yi don in tozarta in wulakanta ka, ko don ban gode maka ba, ko don in karya maka zuciya.
Na yi hakan ne domin neman masalaha tsakanina da Ubangijina. Na fasa auren RAYHANAH a daura da Radhiyyah ‘yar Dr. Halima. Ita kuma Rayhanah Allah ya huci zuciyarta ya ba ta wanda ya fini”. Kawai sai yasa masa kuka.
Dr. Mansur ya dade bai yi magana ba, zuciyarsa ke wani irin tukuki na fushi da Mami mai tsanani, fushi irin wanda bai taba yi ba a rayuwarshi ta duniya.
Tabbas Asma’u ce ta yiwa Khalipha barazana da matsayinta na (uwa) domin dankafar da Rayhanah da martaba nata Dan.
“To ai shi kenan”.
Bai san sanda ya gayawa Khalipha hakan ba.
“Ta nuna power dinta a kanka, nima zan nuna tawa da wanda na haifa nake da iko da shi. Dadin haihuwa kenan. Yau da ban haihu ba da Asma’u ta nuna min iyakata ta nunawa duniya BA NI NA HAIFE KA BA!
Babu komai, daina kuka Khalipha, zan mata yadda take so, nima zan yi yadda nake so. All the best Khalipha, yi biyayya ga mahaifiyarka domin samun tsira a gidan duniya da lahira baki daya.
Kada ka damu da bacin raina, wallahi ko kadan baka bata min ba, ban kalleka da matsayoyin da ka lissafa a baya ba, face na yi maka kallon DA MAI NEMAN ALJANNAH a diga-digan mahaifiyarsa.........”
Ihu Khalipha ya saka masa. “Daddy ba kai ka haifeni ba? To wane ne? Shege ne ni?” Kara yake saki da ihu mai gigitarwa saida shi kansa Dr. Mansur ya razana. Da tsoron kada Khalipha yayiwa kansa wani lahani. Bai san sanda ya soma kuka ba shima ya soma kira cikin lallashi da nadamar bacin ran da ya kai shi ga furta abinda yayiwa kansa alqawarin har abada bazai furta ba,
“Cool down Khalipha!!! Ba shege kake ba, da ubanka, ita ta haifi abinta da mijinta na fari, tun auren saurayi da budurwa, bayan haihuwarka suka rabu, kana da shekara biyu ya rasu.
Ni da ita mun hadu ne a jami’ar Trinity din Ireland (Dublin) ta zo karatu nima na zo, tana zaune da Uncle din ta da matarshi tare da kai, Nanny na kula da kai ita kuma tana karatu. Da muka yi aure ne na karbeka muka karasa karatu muka dawo, da shekaru hudu da auren mu ta haifa min Ibraheem.
To ka ji, kwantar da hankalinka har gobe kai Dana ne Khalipha, ba wanda ya isa, ba abin da ya isa ya kankare wannan sunan Abdullahi Mansur Takai, sai wanda ya halicce ni ya halicceka.
Mahaifinka Balaraben Hurghada ne (Egyptian) ya zo Jos kasuwanci ne ya zauna a cikinta tsayin lokaci har ake kiransa (Ba Hurgade Mukhlis), ya kuma bar maka tarin arziki mai yawa wanda iyayensa suka zo suka kwashe, suka kuma ki karbarka, a cewarsu basu san da zancen auren ba tunda bai gaya musu ba, duk da fata ta nuna amma kamanninka da ita ne sak.
Tun daga lokacin na mai da kai Da na Khalipha, kuma har gobe matsayinka kenan. Share hawayen nan Khalipha bana son su and I’ll stand by you..... ina a bayan ka yiwa mahaifiyarka biyayya domin ta sha wahala da kai yadda baka zato a Dublin. Ga karatun medicine ga rashin lafiyar ka ta ciwon hanta har Allah ya baka lafiya.
Tunda ba ta so to ba ta so din ne, ko anyi abin ba zai yi albarka ba, ba kuma za ta bari a zauna lafiya ba. Kyale Asma’u da kafiya a kan abin da bata so, in fa ba ta son abu ba za ta taba son sa ba.
Tana da hakki mai girma a kanka wanda ni bani da shi. Zan kuma nuna mata nima na haifa, kowa ya yi iko da nasa”.
Ya ci gaba da lallashin Khalipha wanda ke kuka mai keta zuciyar duk mai imani, har suka aje wayar Khalipha bai daina kuka ba. Shima Dr. Mansur hawayen yake ta sharewa da hankicinsa. Ya tada motar ya hau kan titi ya karasa Takai.
A kofar gidan Hakimi ake ta sauke huhun goro da alawa da Dr. Mansur ya zo dasu shake a boot din motarsa. Wajen matan gidan ya fara shiga aka gaggaisa da su Haj. Karima, sannan suka kule a falon Hakimi shi da dan’uwansa suna tattauna mai yiwuwa. A take aka soma gayyatar daurin auren da za ayi a gobe Lahadi.
Bayan Khalipha ya yi kukansa har ya gaji, idanunshi sun soma yi mai zafi da wannan sabon al’amari da ya tunkaro shi. Ya girgiza zuciya da ilahirin gangar jikinsa.
Wai Baba Dacta ba shi ya haife shi ba. To shi din wane irin mutum ne mai karamci da kyautatawa ga al’umma? Mutane irinsa tsiraru ne a cikin al’umma.
Mami ya kira, muryarsa sak kamar babu komi a cikinta.
“Alright Mami. It’s done, sai ki sanar da Dr. Haliman Daddy ya ce in gaya miki gobe in sun dawo daga daurin auren da za suyi a Takai za su zarto nan Kano a daura na Radhiyyah. Mami kisa min albarka! Albarkarki kawai nake nema Mami, bayan wannan babu wani abu. Zan samu Mami???”
Hawaye ne suka sake zubo masa, wanda bai damu da ya sharesu ba, suna ta zuba a kan cinyarsa.
Maimakon Mamin tasa mishi albarka kamar yadda ya roka, sai ma ta hau tambayarshi wai daurin auren wa su Daddyn za su yi a Takai?
Khalipha don bakin ciki sai ya sanya kansa cikin gwiwoyinsa kamar karamin yaro ya ci gaba da kokawa kansa-da-kansa. Ita kuma Mamin a can ta gaza sukuni.
Ga dai Khalipha ya haifu ya yi mata yadda take so, ya hakura da farin cikin rayuwarsa domin ya faranta mata, ya samu albarkarta amma zuciyarta ta gaza nutsuwa da son sanin auren wa za a daura a Takai?
Kada zancen Dr. Halima fa ya tabbata, Rayhanah ta zama kishiyarta Dr Mansur ya yi auren huce haushi da ita. Tasan zuciya irin tasa idan ransa yayi mummunan baci bahagon hukunci yake yankewa. Ai sai ta mike ta zari makullin mota ta nufi gidan Dr. Halima a gigice domin maganar ta fi karfin ayita a waya. Dr. Mansur macijin sari ka noke ne, shirunsa a kan al’amari na nufin daukar mataki wanda ba zai yiwa victim dadi ba.
Tana tafe da gudu tayar motarta ta gaba ta fice, motar ta gangara ta bugawa wata katuwar mota duk fitilunta suka kwankwatse, Allah ya sota ba abin da ya sameta, sai buguwa da kanta ya yi a jikin sitiyari, sai dan gilashin da ya yanki goshinta.
A take jami’an tsaro suka cika wajen suka jawo mata bacin lokaci da biyan cin hanci. Ba ta isa gidan Dr. Halima ba sai da magariba.
Dr. Haliman ta ganta afujajan ga jini na zuba duk ya bata tsadadden swiss lace yellow dake jikinta. Ita ta yi mata dressing din wajen ta rufe da plasta, sannan Mamin ta koro mata bayani.
Maimakon Dr. Halima ta tayata jimamin abin da take wa gigita da tsoro a kai, sai guda ta je ta sakarwa Radhiyya a ka, ta kira Babanta a take ta sanar da shi.
To dama shi Alh. Kabir shanyayye ne, take babu bin ba’asin wannan kagararren aure ya soma gayyatar jama’arsa ta waya. Radhiyya ta kunna (Nancy Agram) tana taka rawa a gaban Mamin har ta ji wani bangare na zuciyarta ya yi mata ba dadi, amma ta kasa nunawa ko a fusaka sai dariyar yake take taya Radhiyyah.
Ta kuma ce, “To Radhiyyah kinga dai kokari da fadi-tashin da muka sha ni da mahaifiyarki don samun farin cikinki, kin kuma san Khalipha ba shi ya ce yana ra’ayinki ba.
Don haka (handle him with care Radhiyyah), ki kular min da shi don Allah shima ki yi hakuri da shi sai a hankali, insha Allahu komi zai daidaita”. Radhiyya ta rungume Mami har da hawayen farin ciki a idanunta.
Haka Mami ta dawo gida a salube gwiwa babu nauyi. Don ko cikakkiyar sallama basu yi da Dr. Halima ba, ba ta tofa wani abu a kan damuwarta ba, she is busy calling her people su zo daurin auren Radhiyya da Khalipha gobe.
Idan Mami ta ce ta yi barci a daren yau ita kanta ta san karya ne. Ga azabar ciwon kai, ga radadin ciwo, ga tunani, fargaba da damuwa.
Har sha biyun dare Dr. Mansur bai shigo gidan ba, tana falo tana dakon shigowarsa amma har karfe biyun dare babu ko inuwarsa, wannan ya tabbatar mata a Takai zai kwana.
Ta soma kiran wayarsa ana cewa a rufe. Sai ta koma kiran Khalipha shima a rufe. Tamkar wadda aka yiwa allura ta zabura ta yo dakin ‘ya’yanta mata, kwayar idanunta sun zurma ciki sosai tashin hankali da zullumi.
Abida da Jawahir kowacce na barci a gadonta, sai Azizah a kan sofa take nata barcin. Daga can kusurwar karshe ta dakin ta hango Rahane tana kan sallaya da hijabin da ya rufe dukkan jikinta sai fuska da tafin hannu, amma ko kafafunta ba a gani, tana rike da Alkur’ani bugun Misra tana karantawa amma ba a fili ba.
Dai-dai lokacin da ladanin wani masallaci dake makwabtaka dasu ya kwalla kiran sallar Asubahi. A yadda Mami ta nufota a fusace kamar kurar dake jin yunwa ya sata rufe Alkur’anin da sauri ta aje gefe, tana karanto duk addu’ar da ta zo bakinta, don ta yi zaton Mami rufeta da duka za ta yi.
Bayan ita dinma bata da lafiya, adalilin duk wasu hanyoyin sadarwa tsakaninta da Khalipha sun yanke. Baya neman ta, ita kuma idan abu ya dameta, bata iya gayawa kowa, kawai tasa a ranta Khalipha ya gama yayinta ne dama ba aurenta zai yi ba, yaudara ce kawai irin tasu ta ‘ya’yan gata. Ya samu wata dai-dai da shi, ita kuma ya rufe duniyarta.
Wannan ciwon da Khalipha ya ji mata a zuciya, shi ya kassara ta, ciwo take a tsaitsaye duk da bata kwanta ba. Wani bangare na zuciyar tata kuma sai ya ce, “To ai Khalipha ba shi da laifi, bai yaudareki ba, ke kika yaudari kanki, da kika dauki dukkan amana da soyayyar duniya kika bashi, da saninki kan cewa kina zaman ‘yar karo ne a gidansu amma kika zarme kika wuce gona da iri, wai shine life-mate dinki......”
Wannan tunanin din dai, bai rage komi daga son da takewa Khalipha ba, sai beken kanta da take gani. Ba ta gama tunane-tunanenta ba da mamakin abin da ya kawo Mami dakinsu yanzu da asubahi haka kamar Damisa, ta ji Mamin ta finciko ta babu ko takalmi a kafarta.
Figarta kawai take har a kan step din bene wanda zai sadata da reception din gidan, tana buguwa tana komai amma Mami ba ta fasa janta ba sai da ta dangana da gate.
Ta bude kofar wucewar mutum ta cillata wajen gidan tana cewa,
“Ki tafi gidan ubanki! In ya mutu ne ki nemi danginki. Ba nufina in wulakanta ki ba, amma ke kin dauko hanyar wargaza min rayuwar iyali, kin rabani da mijina da ‘ya’yana da kwanciyar hankalina.
Taimako ba hauka bane, Allah ya gani na yi iya wanda zan iya. Ina rokonki Rayhanah kada ki sake waiwayen inda muke, ki je kauyenku ki yi aure ya fiye miki da ci gaba da zama cikin iyalina kin ji na gaya miki”.
Garammm! Ta rufe kofar. Karar kofar kenan da ta razana Malam Dahiru dake sallah ya fito da gudu ya ga shigewar Mami da kulle kofofin reception dinta da ta yi.
Sai kuma ya ji shesshekar kukan mace a wajen get dinsa. Da azama ya bude ya fita yana haskatata da tocilan dinsa.
“Wace ce a nan?”
Ya tambaya cikin barazana, a lokacin da kwayar idonsa suka shaida wadda ke tsugunne a gefe tana kuka.....
“Rayhanatu?”
Ya ambaci sunanta cikin kokwanto. Hawaye kadai ke zuba ta ce, “Taimakamin da kudin Motar da zai kai ni Takai Malam Dahiru......... don Allah ba don ni ba......”
Ta ci gaba da kuka mai matukar ban tausayi.
A kidime ya ce, “Rayhanatu ba inda za ki, shigo daga nan, sai Dacta ya dawo koma mene ne ba zan barki ki tafi ba don kin yi ma Mami laifi. Ki yi hakuri ki daina kukan ya dawo”.
Tana kuka sosai ta ce, “Malam Dahiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login