Showing 18001 words to 21000 words out of 30449 words

Chapter 7 - Rayuwar Rayhana Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

28 Dec 2024

92

za ka iya bani ko ba za ka bani ba?”
Yadda ta fiddo masa manyan idanunta dake jike jagab da hawaye sun kuma kada sunyi jawur, sai jikinsa ya hau bari.
Ya ce, “Zan shiga matsala ne Rayhanatu idan na barki kika tafi....... ki ceci hanyar cin abincina ni da iyalina kada ki yi sanadin rabuwata da karimin mutum irin Babanku. Ita ma dai Hajiya wane irin laifi danka zai yi maka ka kore shi? Korar ma cikin duhun Asubahi?”
Da ta ga Malam Dahiru ya tsaya ya tsinke mata da surutu mai ban haushi a gareta, ba kuma shi da niyyar taimakon nata. Bakin ciki ya yi bakin ciki a zuciyar Rayhanah, sai kawai ta tattare doguwar jallabiyyar dake jikinta ta yanka da gudu, gudun da ba ta taba zaton ta iya ba kamar filfilwa a lokacin gari ya soma haske.
Ko kabarin iyayenta ne ta yarda ta koma da ta kara kallon ko da get din gidan su Khalipha, Abida da Mami, da suka yiwa zuciyarta rauni mai zurfi da ba zai taba warkewa ba.
Malam Dahiru dai girma ya soma cimmasa, ba zai iya wannan gudun da Rahane ta fyalla ba balle ya kamata. Sai ya dau wayarsa ya kira Dacta ya gaya mishi iya abin da ya gani.
Ga mamakin Mal. Dahiru, Dacta bai wani razana ba, bai yi mamaki ko fadan da ya yi tsammani ba, cewa ya yi da shi,
“Don me baka ba ta kudin motar ba? Hau babur dinka maza ka bita ka ba ta kudin ka yi tafiyarka”.
Ya jefa waya a aljihunsa ya tashi babur aguje shima ya bi hanyar da ta bi wadda za ta sadata da bakin titi.
Unguwar Lamido Crescent unguwa ce a Kano ta wadanda suka san muhimmancin BIRO (‘yan boko). Babu ruwan kowa da kowa, ba cinkoso ba sa-ido kamar kana Abuja.
Don haka ko gilmawar motoci babu a dai wannan lokacin. Sanda Mal. Dahiru ya hawo kan titi ya hangota can gaba da shi tana bin gefen titi sauri-sauri gudu-gudu kamar mai yin Safah da Marwah.
Ita kanta ba ta san ina take jefa kafarta ba, fatanta kawai ta ganta a Takai, koda akan iska ne, kuma hawaye basu bar tsere a kan kundukukinta ba tana ta sharewa da zurmemen hijabinta.
Da ta ji karar babur a bayanta ai sai ta kara artawa a guje, shima kuma ya nuna mata mutum da inji ba daya bane, ya sha gabanta har ya dan bugeta ta fadi a kan titin.
Ya taimaka mata ta tashi ya rike hannunta gam-gam domin kiciniyar kwacewa take tana rokonsa kada ya maidata gidan Dr. Mansur, ya tafi ya kyaleta tunda ba zai taimaka mata ba.
Mal. Dahiru ya ce, “Na rantse da mahaliccina ba zan mai da ki ba. Hau bayana in kai ki tashar Mariri in sa ki a motar Takai”.
Kukan dai bai tsaya ba, amma ta ji sa’ida a ranta. Ta dane bayan babur ya ja suka tafi. Lokacin gari ya fara haske misalin karfe shida na safiyar Lahadi kenan.
A tasha Mal. Dahiru ya sata a motar Tsangaya, ya sanar dasu a Takai za su sauke ta. Ya kirgo kudin da suka bukata ya basu ta shiga gefen taga daga baya ta zauna.
Tana share idonta tana dagawa Mal. Dahiru hannu da godiya. Ya zagayo tagar da take ya mika mata naira dari biyu da kunshin kosai mai zafi. Hannu biyu tasa ta karba, tana gode masa. Ta share hawaye ta ce,
“Sai wata rana...... Malam Dahiru na gode a gai da Sahura”. (Matarsa).
Bai bar tashar ba sai da ya ga tashinsu, bayan motar ta cika. Shima sai ya ji danshi a kan fuskarsa, yarinya-yarinyar kirki, me ya raba ta da mutanen kirki irin wadannan? A fuskarta da yanayinta dai ya nuna ko yatsa kasa mata a baki ba za ta ciza ba, in baka yi mata izini ba. To me ya hadata da Dr. Asma’u haka? Ita ma ai mutuniyar kirki ce”.
Haka ya yi ta sake-sakensa shi kadai har ya koma gida ya jingine babur dinsa ya ci gaba da harkokin gabansa.

****
[12/24/2019, 21:47] Takori: Haj. Karima wadda ta amsa sunanta (Mai Karamci) kuma uwargida abun alfahari ga miji da iyalanta, ta yi sallama dakin da amaryar take a lokacin Inna Juma na faman yi mata fadan ta ki shan jarkar tsumin da Haj. Karima ta kawo tun jiya.
A sanyaye Rahane ta ce, “Inna zaki ne da shi mai yawa, bama shan sukari. Baba Dacta ya ce yana sanya Diabetes (ciwon suga), kuma yana lahani cikin hakora”.
Inna Juma ta ce, “Ciwon sukarin ya ci uwatar, mu da muka shanye fiye da jarkoki dubu ai kin gammu a asibiti”. Ta tsiyayo a kofi.
“Ungo kwankwade ki bani kofin, don kushewar Ubanki.........”
Ita Hajiya Karima sai dariya take da jin muhawarar tasu. Ta idasa shigowa cikin dakin tana ce da Inna Juma.
“Kyaleta Inna, da kanta za ta ce ki bata idan ta san amfaninsa, sanda za ta kwankwade jarka goma ma ba za ta sani ba”.
Rahane ta kyabe baki ta zumbaro shi ga Inna Juma, ta ce, “Don Allah Maman Anty Nabilah mene ne amfaninsa a lafiyar dan-adam? Zaki yana sa basir da….......”
Ai buge bakinta Inna ta yi da mafici har leben kasan ya kumbura. Da sauri Haj. Karima ta kwace maficin Inna na shirin kara mata, ta ce
“Rufa mata asiri Inna kada angon ya ganta da kumburarren baki ya ce ya fi son ki. Rayhanah sha kawai rabu da Inna, ki sa a ranki kawai Inna ba za ta dage ki ci abu ba, alhalin ta san zai cutar dake ba”.
Inna ta ce, “Sanabe a gun Rahane har da na tsiya, komai ta ce yana sa kaza yana sa kaza, komai ka yi baka yi dai-dai ba sai ta kwakulo ma illah”.
Hajiya Karima na dariya ta ce, “Inna rainon likitoci ce fa, ‘yar likita (uwa da uba) matar likita, kinga kuwa ko ba ta shiga aji don ta koyo likitanci ba za ta iya yi miki allura ta baki maganin kowacce cuta, ai ke gaba ta kai ki, wai gobarar titi a Jos, babu ke babu hawa layin ganin likita a asibiti”.
Haka dai suka yi ta barkwanci, Inna da Haj. Karima, Rahane ba ta tsoma musu baki ba. Cewa take cikin ranta; Haj. Karima daban ce cikin matan gidan nan wajen saukin kai da karamci, dole mijinta ya sota fiye da su Haj. Indo. Don ta kama girmanta, ta iya zama da kowa dake samanta ko karkashinta da zuciya daya.
Kusa da Rahanen ta dawo ta zauna, ta ciro wasu tablet din na Indonesia tana cewa, “Rahane maza kora wadannan da ruwa, kinga yanzu za a kai ki gidanki a Kano kafin sati mai zuwa Daddy ya danka ki hannun angonki. A sannan ne wadannan magunguna da muke takura miki ki sha za suyi miki amfani. Ki daina mai da kanki yarinya mana, kin girma fa, aure GIRMA ne, ko shekaru basu kai ba”.
Rahane murmushi ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, kanta ya kumbura, don tana son GIRMA. Tana so a ce ta girma, she’s no more a kid now!!!
Ta karbi magungunan daga hannun Haj. Karima tana dubawa, ta kasa karanta rubutun chinese dake jiki. Ta ce cikin ranta, “How can I take drugs without Doctor’s order?” Ta karba ta hambuda su a baki, ta boye su a kasan harshenta ta kora da ruwa.
Haj. Karima na ba da baya domin ta je ta dawo ta yi toilet da gudu ta tofo su cikin masai ta yi flushing ta wanke bakinta. Inna Juma da ta fahimceta ta hau salati da sallallami.
Rahane ta rungumeta tana rokonta kada ta gayawa Hajiya har da ‘yar kwallarta. Ta ce, “Inna ni ba zan sha maganin da ban san na mene ne ba, ba zan sha tablet din da ba likita ne ya yi Prescribing din ta gareni ba”.
Inna Juma ta tureta daga jikinta tace, “Ni da Allah daga ni, ai shi kenan ke kika sani. Ana miki gata kina iyayi. Sai ki je wa mijin salam! Ina ruwan wani”.
Da dan mamaki a fuskarta ta ce, “Inna da da gishiri kike so in je masa?”
Inna Juma ta ce, “Eh mana, ai gara ki je da dandano ko ya so ki, tunda ba kiyo kyawun Yalwati ba, kin dauko bakar fuskar ubanki. Ko da yake yanzu kin dan fara washewa ba kamar sanda kina yarinya ba”.
Rahane na dariya ta ce, “Inna har da cin fuska?”
Inna ta ce, “Har da cin kafafuwa kuwa, idan kika yi wasa in kwace mijin idan ya yi mini. In ta tsuma kaina yadda zai ji ni cau!”
Wadannan languages na Inna Rahane ta kasa gane musu, kuma Innar ta ki fitowa fili ta yi mata bayani sai dukunkune maganar take. Ta je da dandano? Ta yi cau? Sai ka ce wata abinci. May be Inna Juma bata iya Hausa ba.
Barorin gidan Hakimi ke ta shigowa da manyan jakunkuna. Haj. Karima ta biyo bayansu ta zauna sosai tana bude jakunkunan tana fadawa Rayhanah cewa lefenta ne a dinke.
Ta dinga daga atamfofin super da swiss lace kamar debo su akai a kasuwa ba kudi aka sa masu yawa aka saya ba. Takalma da jakunkuna ‘yan Italy abin sai wanda ya gani. Kayan shafe-shafe, turaruka, gyaluluwa, sabulai abin ba’a magana. Ta gaya mata cewa duk nata ne. To abin ya fi karfin Rayhanah ta yi magana sai ido, kuma shi ta zuba mata.
****
RAHANE A GIDAN AURENTA!
A al’adar babban gida musamman irin na sarauta, lokacin bikin aure an saba gwangwajewa a cashe ayi almubazzaranci da dukiya. Amma wannan auren na ‘ya’yan Dr. Mansur biyu (Khalipha da Ibraheem) ya zo da sabon sauyi, ko algaita ba a busa ba, ko kwarya ba a buga ba, haka ko guda babu wanda ya rangada.
Wannan kuma ya samo asali ne da yadda auren ya zo ba cikin shiri ba, ga kuma duka angwayen babu ko daya. Gidan bangaren daya amaryar kam sun cashe sun gwangwaje yadda ransu yake so, an wulakanta naira. Amarya ta daura sittiru na kece raini, anyi hotuna da sauransu.
Amma a bangaren daya amaryar ba ta da wannan gatan, ba ta ma sa-aka ba, ba ta ma kuma da wanda za ta gayyato a duniya idan ba Jawahir ba, ga shi kuma watakila har abada ba za ta koma inda Jawahir din take ba, da aminiyarta Azizah.
Sannan ‘ya’yan Hakimi da yawa da sauran matansa basa farin ciki da aurenta da Ibraheem saboda Nabilah. Don haka ko taron wuni ba kowacce ce ta zo ba, wannan bai damu amaryar ba, balle danginta da suka zo rakata gidan mijinta daga Albasu, Takai da Tsangaya dukun-dukun da su, bayan su a wurinsu sun kure adaka.
Hakimi da kansa yana gaban motar Dr. Mansur wanda ya zo daukar amaryar da kansa, a bayan motar Haj. Karima ce, Inna Juma (wadda za ta zauna tare da ita) da Zinaru da babbar ‘yarta Hansai. Bai tsaya ba sai farfajiyar wani matsakaicin mansion mai rufi ruwan kasa da fenti ruwan madara. Guda biyu ne a jere amma cikin get daban-daban a unguwar ‘Farm Center’ dake bayan shagon Kasa (Country Mall).
Babu yawaitar jama’a a unguwar babu cinkoso, yawanci ma duk gidajen ma’aikatan gwamnati ne da sababbin gine-gine da aka fara ba a karasa ba. Sai kamfanoni da shaguna sababbi wadanda ba a fi shekara da bubbude su ba.
Hannun Rahane cikin na Baba Dacta har dakin barcinta, cewa yake
“Da a Takai gidanki yake, a kan doki zan kai ki Rahane. Shiga gidanki kina mai neman aminci daga Ubangijinki, ta hanyar cewa “Assalamu Alaikum”. Shiga gidanki cikin neman dukkan alkhairan dake cikinsa, ki nemi tsari daga sharrinsa. Ta hanyar shiga da kafar dama.
Ina rokon Allah yasa mutuwa ce kadai za ta fitar dake din-din-din daga gidan mijinki, ita ma din ina fatan ta dauke ku tare. Amma fa bayan kun bar min jikoki, tattaba kunne da uhm-hm-hm”.
Hakimi murmushi ya yi ya ce, “Har da uhm-hm-hm Mansur? Anya baka zarmewa duniyar ba? Kana da hamsin da bakwai yanzu, amma kana neman wasu sittin a nan gaba?”
Dr. Mansur ya ce, “Yaya Abdulkadir ina son tsufa mai tsaho, tsufan dake da sanyin idaniya (‘ya’ya da jikoki da tattaba kunne) dadi ne da shi, musamman idan suka baibaye ka suna jan farin gemunka......... Hurry Rahane....... yearly! (wato tayi sauri duk shekara ta kawo jika)”.
Kowa dariya yake banda Rahanen, wadda take jin ina ma kasar ta tsage ta shige cikinta da kunyar wannan magana da Baba Dacta ya yi. Ta sake kudundunewa cikin mayalwacin mayafinta.
Doguwar addu’a Hakimi Abdulkadir Balarabe Sardauna ya ja aka shafa. Rahane ba ta tashi tsinkewa da kuka ba sai da suka sa kafa suna fita daga dakin, bayan sun gama yi mata tofin albarka.
Da gudu ta mike ta bi bayan Baba Dacta ta kama kafafunsa tana kuka sosai ta ce,
“Allah ya fini sanin alherin da ka yi mini. Don haka shi nake roko ya saka maka da fiye da shi. Ina rokon ku idan na taba bata muku a shekarun da muka yi tare Baba Dacta kana gina rayuwata positively… ka dubi Allah ka yafe mini, ka daina fushi da Mami a kaina don Allah Daddy.......” Ta ci gaba da kuka mai keta zuciyar duk wani mai birbishin imani a zuciyarsa.
Hannu biyu yasa ya dagata, “Bari kukan nan haka Rayhanatu bana son shi, in ma kin min laifin ai afuwa ce har kullum tsakanin Uba da dansa. Guda dai-dai har dubu malala gashin tunkiya, na yi miki ita Rayhanah, na yiwa Mamin ki, ban taba riketa da komai ba a kanki, sai ajizanci irin na dan Adam.
Ni na gaya miki WATARANA na zuwa da Asmau da kanta za ta goya ‘ya’yanki, MADALLAH! Da zuciya mai tsafta irin taki Rayhanah!!!” Da sassarfa ya wuce ya bi bayan Hakimi. Don baya so taga kwallar data sauko daga idaniyarsa.
Inna Juma ta bisu ta rufe kofofin gidan suka gaisa da maigadin Buzun Nijar ne. Ta dawo ta kama hannunta suka koma dakin barcinta tana lallashinta.
Ta ce, “Gani ni dake zamu yi zaman mu, zama mai dadi cikin kwanciyar hankali har Allah ya kawo mana angonmu lafiya. In kika yi sakwa-sakwa sai in kwace shi”.
Ta ce, “Daga ido Rahanen Yalwati, mai sunan Yalwati ki sha kallon gidan mijin da Allah ya baki”.
Ta yaye mata lullubin gaba daya ta nuna mata wani dan karamin hoto cikin dan ‘frame’ din dake kan durowar gadonta. Ibraheem ne rungume jikin Baba Dacta ranar ‘graduation’ dinsa daga MBBS. Kin kallon hoton ta yi, ta yi maza ta kunshe idonta cikin kafafunta.
Sai Juma ta yi dariya a ranta ta ce, “Kunya kamar Yalwati, ga rayuwar birni ba ta sa kin yi watsi da ita ba. Ta soma tunano kuruciyar mahaifiyar Rayhanah, haka take da kunya da rashin wayo.
****

ASALINSU
Su ‘yan asalin Takai ne gaba da baya, basu da wata daukaka ko wani mulki ko suna (reputation) kawai bayin Allah ne da suka fi karfin abin da za su ci, da wanda za su daura. Da ita da Gwaggo Jummai kakar su Rahane uwarsu daya ubansu daya.
Lokacin da Malam Rashidu ya fito neman auren Rahane (Yalwati) dukkansu babu wanda ya marawa al’amarin baya, ba don komi ba kuwa sai don cewa ba haifaffen Takai bane bakon haure ne daga Tsangaya, wani kauye cikin karamar hukumar Albasu. Amma ba don karancin samunsa ba.
Ko da Rashidu ya yi alkawarin ba zai raba ‘yarsu da mahaifarta ba basu yarda ba, Babanta ne ya yi musu bazata ya karbi sadakin Rahane daga Mal. Rashidu, ya ce ko bangon duniya ne ya kaita, ba inda aure baya kai mace, balle ina Tsangaya ina Takai? Ban da neman zance irin na mata?
Sai kuma Rashidun ya basu mamaki da soyayyar da yake yiwa Yalwati. Ya je ya tattaro komi nasa daga mahaifarsa, bai bar ko allura ba. Dama gaida mahaifiyarshi Iya Bilki ke kai shi Tsangaya sai ya je ya dauko abarsa ya ajiyeta kusa da shi, uba ya jima da rasuwa, dangi sun kare, ita kadai ta rage mishi. Ya kawo ta ya ba ta daki a gidan mahaifin Ado da yake haya a ciki.
Bayan mahaifin Ado ya rasu, Ado ya gaji gidan. Zamane suka yi mai dadi shi da Rahane da mahaifiyarsa, domin Iya Bilki ba tsohuwar banza ba ce ta san abin da take yi. Ashe zaman nasu na dan takaitaccen lokaci ne (shekara biyu) Allah ya karbi ranta wajen haihuwar Rayhanah.
Don haka iyayen Yalwati (Rahane) basu ji ko dar wajen ba shi Zinaru ba, a lokacin da Iya Bilki ta nemi hakan. Ta je ta zuba musu rashin mutuncinta ta fito ta koma gidan tsohon mijinta a Albasu.
A lokacin da Iya Bilki ta rasu Inna Juma ba ta Takai tana birni tana wanke-wanke tsayin wasu shekaru masu yawa tun bayan rasuwar mijinta Malam Saleh, ba ta kara jin duriyar Rahane ba sai da ta dawo birni take tambayar al’ummar kauyen, su ma suka ce basu sani ba, amma dai kowa ya san sunyi rikici da Ado, wanda shima ya dade baya kauyen sai da cutar zamani ta dawo da shi jinyar dole gida.
A bakin Ado ne ya ce ta bincika gidan Hakimi shi can ya barosu. Inna Juma ba ta yi kasa a gwiwa ba ta ci gaba da binciken Rahane da Zinaru har Allah ya hada su.
Ta kawo gwauron numfashi ta daga ido tana duban Rahane, wadda barci ya yi awon gaba da ita. Ta mike ta kashe mata fitila ta kunna mata na’urar sanyaya daki, da yake ta yi rayuwar Birni ba ta da duhun kai sam. Ta jawo kofar dakin ta nufi wanda aka ce shine nata.
****

Rahane ba ta kara tsinkewa da irin kaunar da Baba Dacta ke mata ba sai a washe garin ranar da safe. Safiya ta farko a gidan miji, wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login