Showing 24001 words to 27000 words out of 30449 words
nausheta, mugun naushi kuwa, rokonta take ta yafe mata, alhakinsu ya sanya ta wulakanta a rayuwarta.
Abinki da ‘yar likitoci, da dai ta samu Zinaru ta saketa ai sa ta yi toilet din Haj. Karima da gudu ta rika kelaya amai cikin sink kamar ta amayar da ‘yan hanjinta. Su sun dauka kuka ta je tana yi, don haka ba wanda ya bi ta.
Da ta wanko fuskarta ta dawo ne Zinaru take mata bayanin sauran matan su hudu, biyu tsofaffi biyu za suyi shekaru arba’in haka, amma wahalar rayuwar karkara tasa sun fi kama da tsofaffin.
Akwai mai fara’a sosai cikin dattijan mai amsa sunan Inna Juma, Zinaru ta ce, “Juma kanwar kakarki ce wadda ta haifi ubanmu, Inna Hanne Yayar mahaifinmu ce, don haka uwa ce a gareni ke kuma kaka a gareki. Ta-sidi da Kubra kannen mahaifiyarmu ne gasu duk a Albasu suke aure, ni kuma a Jahun.
An nemo ni Takai ta hanyar Inna Juma da yake ita tana nan Takai ko bayan mutuwar mijinta Malam Saleh, bata taba haihuwa ba, mu kam akwai tarin iyali. Ina yi miki ta’aziyyar Iya Bilki da Malam Rashidu, ki dubi Allah Rahane ki yafe mini..........”
Kuka sosai Zinaru take yi har Rahane ta ji zuciyarta ta girgiza. Ba ta son kukan babba ko kadan balle Zinaru da take jin ta kamar mahaifiyarta. Duk da bata kasance mai kyautayi a gareta ba.
Ta yi saurin rike hannunta, “Na yafe miki Inna Zinaru, wallahi na yafe muku baki daya Allah ya yafe mana”.
Juma ta ce, “Bar ‘yar banza da kukan munafurci, sai yanzu da kika ganta a matsayin mutum mai daraja da kyawun gani kika san ta yafe miki? Kin taba zuwa kin ganta ko sau daya bayan barinki gidansu? A matsayinta na diyar shakikiyarki?
Al’umma ban san bolar da muka kai zumunci a wannan zamanin ba, na cikin ka kawai shine naka. Sau nawa ina tambayarki inda take kina cewa ba za ki rike ta ba? Duk ma inda take ta je kowa ya yi ta kansa? Sai da na bi diddigi ta wajen marigayi Ado ya gaya min inda ta fada? Kauce daga nan kada in maganre ki........”
“Inna komai ya wuce”.
In ji Haj. Karima.
“Rayuwar duka ‘yar afuwa ce, kema ki yi hakuri. Mun godewa Allah da ya hada ku cikin sauki, a taru duka a yafewa juna komai na duniya dan afuwa ne. Da Ubangijinmu baya yin afuwa a garemu da bamu kawo yanzu ba”. (In ji Hakimi).
Duk cikinsu Rahane ji ta yi Inna Juma ta fi kwanta mata. Ita ce tsohuwar ciki, amma ta fi su kwari da kyan gani, da alamun tsafta a tattare da ita kuma da jin cewa tana sane da ita, har tana neman ta.
Bayyanar dangin Yalwati mahaifiyarta shi ya shafe firgicin da rudanin da zuciyarta ta shiga na auren mutumin da rabonta da shi shekaru goma cif, wadanda tsayinsu da shudewar su basu mantar da ita waye shi ba; Dan Mami! Wanda ta fi so fiye da kowa da komai a rayuwarta (YA HEEMU).
“An gudu ba a tsira ba, an rabu da Bukar an haifi Habu!!!”.
In ji masu iya magana. Har gara-gara ma Khalipha a kan son da Mami ke yiwa HEEMU da burirrikan da ta ci a kanshi. Wadannan tunane-tunane basu bar zuciyar Rahane ta huta ba a wannan dare, basu bar idanuwanta sun runtsa ba. Jin al’amarin take kamar almara.
Wane irin aure ne irin haka? An taba yin aure irin nata a duniya kuwa? Babu shiri? Babu zato babu tsammani? Babu so babu kauna daga kowanne bangare? Babu shakuwa babu alaqa? HIMU? I.M? IBRAHEEM MANSUR? Wai shine mijinta? Ya ALLAH! Idan mafarki nake kayi gaggawar farkar dani kafin na zama zautacciya!!! Rayhanah ta fada a fili tana mai kaiwa da komowa kamar mai yin safah da marwah a dakin data ke ciki.
Wane irin matsayi Baba Dacta ya bata ne a zuciyarsa haka? Me take das hi day a bata wannnan matsayin? Ba ta cancance shi ba, matsayinta bai kai nan ba! Hadin bai yi matching ba sam..... Ibrahim ya fi karfin ta!! Sau dubu gara Khalipha. Shi wannan ko babu komai akwai shakuwa da fahimtar juna akwai kuma shimfidar fuska idan babu ta tabarma ba wannan zundumemen dan bokon ba.
Ta daga hannunta na dama a hankali ta kalli warawaran farin zinare da Haj. Karima ta zura mata, wadanda Hakimi ya ce Sadakinta kenan. Sai walainiya suke a hannunta cikin rangwamen hasken lantarkin dake dakin da take kwance (bedroom din Haj. Karima). Wadanda karbarsu da ta yi sun tabbatar da cewa ta zama matar IBRHEEM, ba Khalipha ba.
Mafarke-mafarken da ta rinka yi a Informatics farkon kulluwar soyayyarsu da Khalipha a kan Ibraheem suka shiga dawo mata filla-filla, wadanda a yau ta fassarasu da cewa, Allah ne yake nuna mata Ibrahim shine uban ‘ya’yanta ba Khalipha ba.
To ya za ta yi da son Yaya Khaliphan? A wannan sabon matsayin nata na matar kaninsa? Daddy na nufin ta haka rami ta binne soyayyar Khalipha wanda har zuwa yanzu zuciyarta ta ki yarda da cewa ya ki aurenta ne don yaudara, sai ko don wani muhimmin al’amari beyond his ability. Haka nan zuciyarta ta yi masa wannan uzurin duba da tsayin lokacin da Khalipha ya diba cikin soyayyarta tun tana kankanuwa, wannan ba yaudara ba ce.
Laifinsa daya ya ki su magantu balle ta san daga ina matsalar take? Sai dai kaso tamanin cikin dari na zuciyarta ce mata yake “Daga Mami ne”.
To in daga Mami ne ya ya akai ta amince ayi da wanda ta fi so ta fi ciwa buri fiye da Khalipha?
Da ta ga wadannan lissafe-lissafe da saka da warwara da tunane-tunane na neman tarwatsa mata kwakwalwa da wargaza kwanyar kanta, ba kuma zasu samar mata da amsoshin data ke son sani ba, haka bazasu zamo solution ga halin da take ciki a yanzu ba, sai ta tattarasu duka ta mikawa Allah! Wahidun Qahharun!! Mai tsarawa bawa rayuwa ta inda bai zata ba.
Minsharin Inna Juma ya dameta, wadda suke kwance tare a dakin anyi mata shimfida a kan kilishi da filo sai kwasar rabar A.C take tana kwararo minshari mai sauti.
Kallonta Rahane ke yi cikin shudiyar fitilar barci dake kunne tana jin wani sanyi a zuciyarta.
Kafin wata sabuwar fargabar ta zo ta lullube mata zuciya........ yaushe za su hadu da Ibrahim? Yaushe zai zo? Da wace fuska zai karbi al’amarin? Wace irin karba zai yiwa auren nasu? Maganar so ma ta san babu ita in aka yi la’akari da irin yanayin rayuwarshi wadda ta sha bambam da ta Khalipha ta kowanne bangare.
Ita dai kam a yanzu zuciyarta neutral. Wato ba ta bayan kowanne bangare (neither tana son sa nor ba ta son sa). Lamarin zai kasance ne da fuskar da ya zo mata, da ita za ta karbe shi. Babu soyayya cikin zuciyarta kuma babu kiyayya, kai ita duk jinin Dr. Mansur ma abin so ne da girmamawa a gareta.
Ba don komi ba sai don cewa, su suka rufa mata asiri a lokacin da ta bude ido ta tsinci kanta tare dasu, babu kowa nata.
Ba ta taba kullatar Mami ba ko ta sawa ranta Mami ba ta sonta. Rikon shekara goma shag Dan da ba kai ka Haifa ba ba karamin sadaukarwa bane. Ta yarda da abin da Mami ke ikirari na cewa ba kinta take ba, asalinta ne da tsohuwar lalurar ta ya sanya bata isa ta hada zuri’a da ita ba.
Ita ma kuma ta yarda da cewa asalin nata (idan aka hada da nasu) kaskantacce ne. Sannan lalurar ta abin gudu ce ko don tsoron genetic wato gado. Sai dai kuma Mami ta mantacewa ba’a yiwa Allah wayo itama bata gada ba iftila’I ne na Ubangiji. Hakan baya nufin suma ba mutane ne da Ubangiji ya halitta don baya son su ba,kowa da kaddarar rayuwarsa in one way or the other! Dukkanmu masu nakasu ne idan bata nan ba ta can. Maganar asali kuwa Ubangiji guda ne ya halicce mu yana kuma son bayinsa bakidaya.
Ba don baya son su bane ya hana su ilimin, mulkin da arzikin, sai don cewa ko ‘yan yatsu bai yi mana su kai daya ba. There is always hierarchy...... a tsakanin bani-Adam. Abin da ta yarda da shi shine, “Inna akramakum indallahi atqakum”. Wato mafi girmanku a wajen Ubangiji shine wanda yafi tsoron sa.
Don haka zamu iya cewa, a wannan daren baki dayansa, idanuwan Rahane basu runtsa ba. A kan kunnenta aka kira Asubahi, sai ta yi amfani da damar don gusarwa da kanta damuwar da ta gallabeta ta addabeta, ba kuma za ta amfanata da komai ba.
Ta yo alwala ta fito ta tashi Inna Juma. Yayin da ta nabba’a a gaban mahaliccinta don nemawa zuciya, kwakwalwa da rayuwarta sauki a wajen Mai duka. Tana rokon sa ya cire mata firgici da faduwar gaban da take samun kanta a ciki, a duk lokacin da ta tuno ranar da zata yi arba da IBRAHEEM MANSUR TAKAI. Har yanzu tana tantama tana kuma shakkun kasancewar wai Ibraheem ne mijinta ba Khalipha ba.
A hankali ta kai duba ga warawaran hannun ta masu kara tabbatar mata da hakan, ta hanyar fidda dan sauti kas-kas da walainiyar da sukeyi a duk kankanin motsin da ta yi. Abubuwan ban mamakin rayuwa yawa garesu, wasu ma basu zo ba tukunna….. wasu ba’a fara su bama RAYHANAAAAH!!!
****
Washe gari ya kasance litinin, su Daddy tun jiya bayan daurin aure suka wuce Kano aka daura na Khalipha da Radhiyyah. Daddy shi ya biya sadaki da wara-waran zinare kamar yadda ya biya na Rayhanah. A take kuma gidan su amarya suka zarce da biki na tsere ma sa’a.
Ita dai Mami har zuwa lokacin ta gaza nutsuwa da samun kwanciyar hankali, don har zuwa lokacin Daddy bai bude baki ya ce mata komai game da Rayhanah ba, bai tambayeta ina Rayhanah ba, bai gaya mata auren wa aka daura a Takai ba.
Ba ta kara ganin Khalipha ba har zuwa lokacin, ya wuce Abuja ya mai da kansa kamar inji saboda aiki, ya ki yarda zuciyarsa ta kadaice ko kadan balle ta samu filin saka mishi damuwa, tashin hankalin jin cewa shi ba dan Baba Dacta bane ya shafe komi, wato ya fi karfin soyayyar Rayhanah wadda ya kira da sunan bygone issue. Sawun Giwa ya take na Rakumi kuma gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta……….
Daddy ya gama masa komai tunda bai bar Rayhanah ta wulakanta ba, wanda shine babbar damuwarsa kuma babban abinda ke kara ingizashi cikin son ya aure ta ya tallafi rayuwarta bayan Kalmar SO, ya zaba mata miji na garari na likawa a goshi in ana likawa, wanda zurfin tunaninsa bai taba bashi kasancewar hakan ba. Damuwarsa daya, wace irin tarba Ibraheem zai yiwa Rahane ‘as a wife??? Yana yi mata fatan alheri.
Shi yanzu haka ma shirin zuwa Jos yake wajen dangin Mami na can don ya fara bincike a kan al’amarin mahaifin nasa, ya dangana da Hurghada. Ya mance da wata aba can wai amarya Radhiyyah.
Lafiya sumul Daddy ya tarbi Dr. Asma’u da fara’a da komai a sanda ya shigo gidan daga ofis ranar da ya dawo daga Takai, ta yi mishi barka da zuwa. Rungumeta ma yayi, ya ce,
“Mami naaa.....”
Ita ma ta ce,
“Dacta naaah....”
Tana loosing tie din wuyan shi.
“Ya aka baro su Hakimi?”
“Kowa lafiya”.
Ya zagayeta da hannayenshi.kanshi cikin wuyanta yana sunsunar ta yake fadin;
“Gashin ba saloon..... Mami na tsami ba wanka, kayan jikinta yau kwana uku ba ta canja su ba. Lebenta a bushe kyamas, kamar tayi sati bata sha ruwa ba! Allah ya isa........ tsakanina da duk mai canza min Asma’u na zuwa Ta-ma’ule!”.
Ya dan ture ta ta yi taga-taga ta fada kan gado ya wuce toilet ya hada ruwa mai zafi ya zuba dettol da sabulun ASDA, ya dauko Mami ya wanketa tas, ya wanke gashinta da kumfar shampoo (pert-plus) ya nado ta cikin shawul ya jona dryer yana busar da gashin kanta. Ya dauko doguwar riga ruwan madara mai kyau dinkin Dammam ya sanya mata, ya juyota ya rungumeta.
Runguma mai karfi da tsanani. Kamar zai tsaga kirjinsa ya sanyata. Mami don tausayin Dacta, sai tasa kuka.
Kyaleta ya yi ta yi kukanta mai isarta bai katse ta ba, tana rungume a kirjinsa.
“Ni kaina na rasa me ke damuna Dacta, na zama rikitacciya, abu kadan sai ya ruda ni, ya tsorata ni. Kaina na gaya min abubuwa wadanda na kasa gane musu........”
Hannu ya kai ya toshe mata baki.
“Ba komai bane, sakaci da ibada ne, da rashin tsai da salloli biyar a kan lokaci. Mami ki nutsu ki koma Asma’unki, you are not my precious Asma’u, Dacta guda da warin hammata???”
Ya fada yana dariya yana fesa mata ‘Carolina Herrera’ sai ta rungume shi kam’kam, da haka al’amarin ya sauya. Ko bayan da suka koma cikin nutsuwarsu suka yi wanka suka yi sallah bai gaya mata ya aurawa Ibrahim Rayhanah ba. Sai batun dauko amaryar Khalipha.
Gidan da Daddy ya ginawa Ibrahim da Khalipha na nan a (Farm Center). European Flat zallah, mai dakin barci uku, falo, katon kitchen da bandaki, can ya ce a kai kayan Radhiyyah, har da Mami a ‘yan jere da Dacta Haliman kanta. Naira kam ta sha kuka, aure na GIRMA da KASAITA irin wanda Mami ke so.
Washe gari aka kai amarya dakinta, sai dai babu ango babu alamarshi. Wayoyinsa duk a kulle, basu sani ba shi a lokacin kwanansa biyu a Hurghada tare da Uncle Yohan Yayan Mami suna binciken dangin Mukhlis Imran a birnin Hurghada.
Haka suka hakura suka baro amaryar ita kadai da ‘yan aiki a gidanta ta ci gaba da jiran ango, a karbe shi da soyayya marar misali, da aka tanadar masa.
****
A TAKAI
A Takai, Rayhanah ta wayi gari a gidan Hakimi matsayin daya daga cikin surukan gidan, yadda Haj. Karima da Hakimi ke kula da tarairayarta basa yiwa ‘ya’yan da suka haifa su Nabilah. Ga wani girma na musamman da barorin gidan ke bata.
Su Zinaru sun koma gidajensu. Juma kawai aka bar mata, Hakimi ya ce ta rufo gidanta kwata-kwata ta zauna da jikarta a duk inda Allah ya kaita zaman aure. Tunda bata da miji, ba Da, ba jika. Don dadi Rayhanah kuka ta saki ta rungume Inna Juma tana yiwa Hakimi godiya.
Ya ce, “Babu komai Rayhanah, yadda zamu kula da ‘ya’yan cikinmu, haka muke kula da surukanmu. A kalla kina bukatar budar ido ki ga jininki ko yaushe a kusa dake. Allah ya ji kan Malam Rashidu, na zauna da shi cikin amana don haka Rayhanah ke amanar Allah ce a hannunmu”.
Tunda aka daura auren nan Nabilah ke ta kuka, ta hana uwarta sakat da jama’ar gidan baki daya. Kowa na da masaniyar cewa ta zauna ta kai shekaru talatin a gida ne cikin jiran dawowar Ya Himu, ta kori duk masoyanta amma ba a duba hakan ba, mahaifinta da mahaifiyarta sune ja-gaba wajen aurawa Ibraheem din da ta kallafawa rai wata bare ‘yar talakawa ba ita ba.
Duk mai tausayi dole ya tausayawa Nabilah a bisa yadda ta mai da kanta kamar matar mamaci, balle kuma iyayen da suka haifeta.
Haj. Karima mutum ce mai tsananin kawaici da zuciyar mai da nata ba nata bane, da kuma biyayya ga mijinta. Tabbas tana tausayin Nabilah amma ita a ganinta gara haka, gara da hakan ta faru da Nabilah ta yi auren da ba za a ga kimar ta ba, tunda ita ce mai son, wanda ake son bai san tana yi ba.
Tabbas kulluwar aure a tsakaninsu zai iya kawo babbar baraka cikin zumuncin iyayensu da suka budi ido suka gansu tare ba a taba jin kansu ba (Dr. Mansur da Hakimin Takai Abdulkadir Balarabe Sardauna).
Ta kuma yi la’akari da cewa, Dr. Mansur ya san da zaman Nabilah, amma ya kawo baren ya ce ita ya zabawa dansa. To nacin na mene ne? Dama ita ta maida kanta tsohuwa, amma manema wane iri ne Nabilah bata gani ba? ‘Yan boko, attajirai, masarauta babu irin wadanda basu nemi auren ta ba amma ta ki.
Yanzu da hakan ta faru a ganin Haj. Karima, sai ta nutsu, ta san tudun dafawa (in fa har tana da hankali). Ibrahim ba shine autan maza ba, ta yiwa kanta suttura kamar yadda Hibbah ta yi, gata can da ‘ya’yanta dugwi-dugwi dasu har uku. Soyayya daban, aure daban. Aure ana yin shi ne don Ibada, ba don son zuciya ba, soyayya ba ita ce aure ba.
Sai ayi soyayya kamar a cinye juna shekaru aru-aru, amma idan Allah ya kawo aure, sai a yi shi cikin kwana uku. Masana a ilmin halayyar dan Adam sunyi ‘analysis’ a kan soyayya sun gano cewa, majority (akasari) long-dating (doguwar soyayya) ba a yin nasarar yin aure da ita, iska take bi, kamar ba a yi ta ba.
Sai ayi aure ba a san juna ba kuma a zauna lafiya, a hankali sai so ya shiga. Shi wannan son ba irin na soyayyar iska bane, so ne na halitta wanda gamayyar jiki (physical relationship) ke haifar da shi. Yana da karfin da soyayya bata da shi, yana da tasirin da soyayya bata da shi, yana da tubalin da dan Adam bai iya hako tushensa wanda shine tsakanin Adamu da Hauwa’u, sune kuma suka haifemu, Allah ne ke sanya shi ba long-dating ba.
Don haka ita Haj. Karima addu’a take yiwa autarta Allah ya yi mata zabin miji mafi alheri, wanda zai so ta fiye da yadda take son shi, amma ba bahaguwar soyayyar da take yiwa Ibraheem ba. Gara ka auri wanda ke sonka a kan ka auri wanda kake so!!!
****
[12/24/2019, 21:48] Takori: Mukhlis Abu-Arab, shi ya musuluntar da ita a Jos, ba da sanin yayanta Yohan ba, wanda yake rike da ita a lokacin bayan mutuwar iyayensu. Mukhlis abokin cinikin Yohan ne, yana kawo kaya daga Egypt su Yohan na saye su zuba a shagunansu a babbar kasuwar Jos. Galibi gayan yara ne (Children