Showing 9001 words to 12000 words out of 30449 words

Chapter 4 - Rayuwar Rayhana Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

28 Dec 2024

95

ya fita daga harabar makarantar yana yi mata addu’a kala-kala cikin zuciyarsa.
****


RAYHANAH A KAZAURE
Rayuwar Rayhanah a Informatics, have brought new insights a kowanne fanni na ci gaban rayuwarta. Malaman duk Asians ne, mostly Indians da Singaporeans.
Ba neman kawaye ya kaita ba, don haka ba ta tsaya neman sabo da kowa ba. Tsakaninta da ‘yan hostel da ‘yan ajinsu gaisuwa ce ta Musulunci ta hanyar sallama da musabaha.
Rahane ba ta wasa da addininta, ba ta wasa da sallolinta guda biyar a kan lokaci, duk sanyi, duk zafi, duk ruwan sama basa hanata yinsu tare da liman a masallaci.
Da farko ta samu kanta cikin rikicewa da rudanin ganin kamar karatun ya fi karfinta. Amma a hankali da taimakon malamanta, ta soma gane kan karatun nasu, har ta hada da wayar da kan wadanda basu gane ba cikin ‘yan ajin nasu a lokacin da babu darasi (Tutorial).
Satinta biyu a Kazaure ba ta taba kunna wayar da Daddy ya bata ba, sai wata ranar Lahadi da yamma bayan ta gama duk abin da za ta yi. Tana ninke kayanta ne wayar ta fado daga inda ta tusa ta, domin a wurin Rahane ai sai da matsala ko lalura waya take da amfani.
Haka nan ta samu kanta da son sanyata a caji. Bayan awa daya ta cika ta kwanta a rigingine a gefen gadonta, kyan wayar ya isa, ba ta taba ganin waya mai kyan wannan ba.
Tana kunnawa sakonni hudu suka shigo, na farko daga Daddy ne, lafiyarta yake tambaya da yanayin karatun nasu, a karshe ya kare da yi mata addu’a da fatan alheri.
Sako na biyu babu suna, sai dai anyi saving lambar da ‘husband’. Wane ne husband? Ba ta sani ba. Ga abin da ke rubuce.

“Idanuwana sun makance a laluben neman uwar ‘ya’yana. Shekara da shekaru zuciya na fada min ba za ka sameta nan kusa ba. Sai dai kuma Allah ya yanke min wahalar a lokacin da ban zata ba. To amma Rayhanah wife din ba ta san ina yi ba”.

Ba ta fahimci komai ba, amma da ta ji an ambaci sunanta ta tabbata sakon nata ne. To wane ne ya turo? Lambar ba iri daya ce da ta Daddy ba.
Sai ta matsa ga sako na gaba.

“Wani lokacin idan na yi yunkurin in bayyana kaina gareta, sai kwarjininta da fargabar yadda zata karbi al’amarin ya hanani, saboda matsayin da ta bani ba matsayi ne na uban ‘ya’yanta ba.
Mai yiwuwa kuma ba zan zama irin zabin mijin da take so ba, sai ta yi amfani da karamci da halarci ta karbe ni, wanda nikuma bana son hakan. Rayhanah soyayyarta nake nema, ba halacci da karamci ba”.

Sako na gaba.

“Bude zuciyarki ki sanya mata wani hoto na wani mutum da kika yiwa farin sani. Kin bashi matsayi kala-kala a rayuwarki, amma cikin kwayar idonki bai taba ganin SO ba! Rayhanah sai girmamawa da sadaukarwa! When he decided to turn the relationship to a more complex one, more important, more valued, ya zamo ya shigo cikin rayuwarki ta kowanne bangare right, left and central........ would it be accepted?”
Ba ta san sanda ta yi murmushi ba, haka nan ta samu kanta da yin replying a gajarce.

“Who is he???”
“Someone that love u unconditionally Rayhanah!!!y”.

A dai-dai lokacin ne kuma kiran waya ya shigo daga wata lambar daban wadda babu ita cikin wadanda Baba Dacta ya yi saving. Hakan bai hanata dagawa ba, Yaya Khalipha ne.
Yadda ya ji muryarta tana rawa sanda take gaisheshi sai ya ji babu dadi, bai so ya yi hakan ba, da ya san zai sata cikin damuwa. To amma bai da mafita sai hakan, don baya son ya yi mata fin karfi. Ya sani ya kuma tabbata ba ta taba yin mu’amala da wani namiji ba a rayuwarta, balle ya yi tunanin tana son wani. A shekarunta na yanzun (goma sha takwas) a ganinsa ta isa ta tantance abin da take so da wanda ba ta so.
“Ya na ji muryarki kamar tana rawa?”
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Wasu sakonni aka turo min Yaya Khalipha, na kasa gane musu”.
“Wa ya turo?”
“I don’t know!”
Ta fada a hankali. Domin a wurin Rahane rashin tarbiya ne a ce maka (I love you) har da unconditionally.
Khalipha sai ya yi murmushi, ya sake kwanciya sosai cikin sofa din bed room dinsa.
“Me ya ce cikin sakon?”
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Something like rashin kunya Yaya Khalipha”.
Dariya ya yi mara sauti. Ya lumshe ido cikin murya kasa-kasa ya ce, “Ya ce miki I love you ne?”
Sai da ta rufe fuska sannan ta ce, “Eh mana”.
Ya ce, “To ke baki son shi?”
Ta girgiza kai ta ce, “Yaya Khalipha a bar maganar nan, ni bana son irin wannan maganar”.
“Why Rayhanah? Kin girma fa, amma ki kasa sanin abin da duk mai shekaru kamar naki ya kamata ya sani?”
Shiru ta yi, wanda ya ba shi damar ya fallasa kansa kawai komai ta fanjama-fanjam. Ya ce, “Idan kuma nine fah?”
Ta zaro ido sannan ta rufe da karfi, ta kasa cewa da shi komai.
Shiru ta ratsa na wani ‘yan dakikai, zuciyoyinsu da gangar jikinsu ke aiki iri daya. Rahane ta dade tana son Yaya Khalipha, sai dai ita kanta ba ta san cewa son nashi take yi ba. Ta dauka kawai shakuwa ce da kauna a dalilin kulawar da ya nuna cikin rayuwarta. Sai dai ba ta taba kawo wani abu da ya wuce wannan cikin zuciyarta ba. A yau da Khalipha ya yi mata wannan misalign, sai ya zamanto kamar yayi fami ne akan tsohon gyambo, sai kaunar da kwantacciyar soyayyar suka taso gaba daya.
Soyayyar da Khalipha ke yiwa Rayhanah yana jinyarta shekara da shekaru unexpressable ce. Don haka a yau daga Khalipha har Rayhanah babu wanda ya yi barcin kirki, tunda ya ji ta yi shiru ba ta da niyyar tankawa ya kashe wayar. Bai kuma kara kiranta ba sai bayan kwana biyar.
Kwanaki biyar din nan tamkar shekaru biyar ne a wurin Khalipha. Duk da haka ya daure bai kira Rayhanah ba, yana so ya ba ta sarari ne ta karbi soyayyarsa a hankali.
Ita kuma Rahane sai ta ji dadi da bai kara kiran nata ba, don in da wanda take jin nauyi yanzu a duniya, to Yaya Khalipha ne. Sai dai ita ma kwanakin sun dafa ta, har ta dafu lugub.
Sai dai wani mafarki da ta yi a kan Khalipha ya tsaya mata a rai matuka, a rana ta hudu da yin wayarsu. A al’adarta idan ta yi mafarki ta tashi ba ta kara tunawa da shi, amma ta rasa dalilin da yasa ta kasa manta wannan mafarkin.

Cikin wata gona ce mai cike da korran gangayyaki, ga kayan itatuwa nunannu irin su goba, kashu, inibi, tuffah, mangoro har da fasa-dabur da roman, yara goma kyawawa lafiyayyu na ta tsinkowa suna kawo mata inda take zaune cikin wani gado na alfarma.
“Momi ga kashu......Momi ga roman...... Mommy ga Inab.....”
Sai ta ce musu, “To ku raba su biyu, ku kai wa Daddy rabi ga shi can”. Ta nuna musu managarcin mutum da ke tsaye yana yiwa fulawoyi ban ruwa. Ya juya bayansa, wanda take da tabbacin Khalipha ne.
Da gudu yaran suka doshe shi ko wanne irke da kayan marmari nunanne na karshe.
“Take it Daddy..... Momy ta ce mu kawo maka, she said she love you much...... and we love u either...... do you love us, Dad?”
Sai ya juyo da murmushi yana karba yana gutsira yana basu, ya janyo su duka ya rungume yana cewa, “Daddy love you too...... and he love mummy as well, a kiss plzzzz???”
Ya tura musu kumatunshi, ko juyowar da ya yi ne ta bata damar ganin fuskarsa. Ba Khalipha bane….. IBRAHEEM NE!.
Wannan mafarki ya tsaya a zuciyar Rayhana, mene ne hadinta da Ibraheem da har take mafarkinsa? Mutum na farko da ta tsana saboda girman kansa. Duk da ba ta da shekaru masu yawa sanda Ibraheem ya bar Nigeria, ta yi mishi farin sani, ba ta kuma manta halayensa ba.
Idan za ta fassara mafarkinta, yana nufin Ibraheem shine uban ‘ya’yanta? “Noooo!!!” Ta fada a fili. Mafarki ne kawai ba gaskiya bane, kuma ba duka mafarki ne yake gaske ba. Don tasa abin a ranta ne kawai.
Ko da kiran Khalipha ya shigo a rana ta biyar, Rahane kasa dagawa ta yi saboda jin nauyi da nauyin zuciya hadi da rashin abin ce masa.
Bai yi fushi ba ya ci gaba da kira a kai a kai amma ta kasa dagawa. Zuciyarta bugawa take yi a duk lokacin da sunan Yaya Khalipha ya bayyana a screen din wayar.
Da ya kira a karo na bakwai sai ta yi shahada ta daga a hankali wayar na neman subucewa saboda rawar da hannunta ke yi.
Khalipha ya yi ajiyar zuciya a galabaice ya ce,
“Rayhanah sabauta ni kike so ki yi? Laifin me na yi miki haka da kika zabi ki azabtar dani ta wannan hanyar?’
Shiru ta yi. Da ya tabbatar bata da amsar ba shi sai ya ce,
“Alright, maybe am not good enough to be your husband. Bari in barki ki huta. Good night”. Ya kashe wayar.

Shi kansa ya san ya fada ne don ya yi causing damuwa a zuciyarta, amma ya san nauyi ne da rashin sabo ya hanata daga wayar.
Ai kuwa ya kunnata, da sauri ta kira lambarsa ta sake kira ta ci gaba da kira amma ya share ya ki dagawa. Rahane sai ta soma kuka, Allah ya sota ita kadai ce dakin lokacin.
Hawayenta na zuba a kan wayar ta yi typing text ta tura masa.
“Ka yi hakuri Yaya Khalipha ba haka bane, ban san me zan ce maka bane”.
Shima shiru makatau ya ki replying. Sai ta rufe wayar gaba daya tana tsane hawayen idonta da gefen hijabin sallarta. Wahaltaccen barci Rahane ta yi, da mafarkai barkatai wadanda babu Khalipha a cikinsu sai IBRAHEEM!!!.
Wannan al’amari ya fara tsorata Rahane, wanda take so yake sonta daban, wanda take gani cikin mafarkinta daban. Ya Allah! Meye gaminta da Ibraheem? Da ta manta shekaru takwas? Ba ta kara tuno shi ba, balle wani abu da ya shafe shi, sai yanzu da Khalipha da soyayyarsa suka shigo cikin rayuwarta?
Washe gari ranar Juma’a kenan, tana masallaci tana Azkar bayan an sakko daga sallar Juma’a, tana yi tana share hawaye saboda damuwa, ta yi alkawarin ba za ta sake kunna waya ba tunda ita tasa Yaya Khalipha ya yi fushi da ita.
Gobe ne Asabar din karshen wata, kuma gobe Baba Dact zai zo ya dauke ta. Yau watanta guda kenan a Informatics Kazaure.
Zaituna classmate dinta ce, ita ce ta shigo cikin masallacin tana dube-dube, ta hangota a can lungu ta dukunkune cikin farin hijabin sallar ta ko jan carbi take ko karatu take ita kadai ta sani.
Ta nufeta da hanzari ta ce, “Tun dazu ake nemanki Yayanki ya zo za ku tafi”. Cikin mamaki ta ce a ranta, “Wane Yayan nawa?” Haka dai ta mike ta bi bayan Zaitunan.
Daga nesa ta hango wata dalleliyar Cadillac srx ruwan makuba, gilasanta masu duhu ne (tintics), don haka ba ta gane ko waye a ciki ba. Don haka ta ja gefe ta tsaya, Zaituna ta wuce hanyar hostel.
Hannuwanta a kirji tana harare-harare da jiran ko ta kwana don ta yi zaton irin lalatattun ‘ya’yan masu kudin nan ne da suka cika Informatics suna diban ‘yammata su fita dasu. Ta yi tsaki ta juya za ta tafi, sai ya sauke gilasan motar gaba daya ya ce,
“Rayhanah!:
Da sauri ta juyo, Yaya Khalipha ne.
Ya fito daga cikin motar ya yi tattaki har inda take.
‘Yar ciki da wando na farin yadin filtex ne a jikinshi, da alama babbar rigar na cikin motar da hula ruwan kasa a kanshi. A yau ne ta taba yiwa Yaya Khalipha kallo na sosi, na cikin ido da ido. Ta gano ba karamin kyakkyawa bane, sannan kamanninshi da Mami a sarari suke bai da digon Baba Dacta ko kadan, fari ne shi sol kamar Mami, bai da digon bakar fatar Baba Dacta.
Sannan fatarshi ta nuna alamun ba cikakken dan Nigerian bane ya fi kama da mutanen Middle East. Idan ta hada da kanta ta yi judging za ta fidda tambayoyi da dama, me Khalipha ya gani a tare da ita da har ya zabe ta ta zame masa uwargida kuma uwar ‘ya’yanshi?
Ita dai ta san ita ba kyau ne da ita ba, ba ‘yar kowa ba ce, bata da abin da za ta ja hankalinsa dashi. Babu wanda zai ba ta amsar wannan tambayar sai shi Khaliphan kansa.
To sai take tambayar kanta ita din ai ta san da hakan amma take sonshi, kuma kyawun sura ba shine dalili ba. Tana son Khalipha ne saboda halayensa kawai da yadda yake mutunta ta yake martabata tun tana nakasasshiya. Kaskantaccen asalinta ba abin juyawa a kalla bane a wajen Khalipha. For him, (Inna akramakum indallahi atqakum).
Da idanun dake cike da wadannan maganganu Rayhanah ta daga ido tana duban Khalipha.
“Idan ni munafuka ce don ina son Yaya Khalipha kamar yadda Abida ta ce, na yarda a rada min sarautar munafukai”.
Rahane ta ce a zuciyarta.

Bata san ina zata saka kanta da fushin da khalifa keyi da ita ba, bata san da wace kalma zata roke shi ya daina fushin da yakeyi da ita ba, da ace zata iya data gaya masa cewa zuciyarta mai rauni ce a kansa ba za ta iya jurewa ba.
Sai hawaye suka balle a idonta, ta yi saurin juya masa baya tana sharewa da gefen hijabinta.
Hannunta Khalipha ya kama ya janyota har seat din mai zaman banza na motarsa, kansa ya daura a kan sitiyari ya lumshe idonsa, ya jima kafin ya bude (but she is still wiping tears).
Khalipha bai tausaya mata ba duk da ya karanci dalilin tashin hankalinta, ya kuma san duk wani motion na zuciyarta a kansa. Sai cewa ya yi, “Sorry for the uninvited visit, na kasa jurewa ne Rayhanah! Ban zo don in saki kuka ba, ki yi hakuri. Insha Allah ba zan kuma zuwa ba da izininki ba. Now go to your hostel tunda na saki kuka......”
Da karfi take kokarin kafar da hawayen, sannan cikin karkarwar murya ta ce, “Ni Yaya Khalipha kana misjudging dina, kana yanke min hukunci da abin da ba shine a raina ba”.
Da sauri ya ce, “To mene ne a ran naki?”
Ta sunkuyar da kai, hawayen na son kara gocewa ta ce, “Daban ne da abin da kake tsammani.....”
Sai a nan ne ya tausaya mata, ya yi murmushi ya ce, “Is it opposite?”
Ta daga mishi kai a hankali ba tare da ta bari fuskarta ta kalle shi ba.
Sai Khalipha yasa gefen babbar rigarsa yana share mata hawaye yana cewa, “Kin karbe ni a matsayin uban ‘ya’yanki Rayhanah ba tare da hakan ya zamo karamci, sakayya ko tursasawa kai ba?”
Wannan karon ma girgiza kai ta yi sama wato eh, wata zuciyar na gaya mata cewa,
“Ki bude baki ki gaya masa kema ba yau kika fara son nasa ba”. Amma kawaici da mutunta kai a matsayin ta na diya mace ya danne komai.
Sai ya rankwafo ya leka fuskarta, tana ta fyace hanci. Duk kokarinsa na son ta kalle shi cikin ido ba ta yi hakan ba, ta runtse idonta da karfi.
Sai ya zakuda kadan ya ce, “Rahane, haba Rahanena, dube ni mana”.
Ba ta san sanda ta yi dariya ba ga hawaye a idonta, ta ce, “Idan na ce maka Audu ai na rama”.
Khalipha ya kama baki, “A ina kika san real name dina Rahane?”
Ta juya masa keya ta ce, “A idon matambayi”.
Khalipha ya rikice gaba daya, ya kasa controling effect din (tasirin) wannan acting na Rayhanah. Hular ma cireta ya yi a hankali ya dora mata a kan cinyarta.
“Dama kina da baki Rayhanah?”
Turo mai siraran lebbanta ta yi gaba tareda juya masa keya ta ce,
“Shafa ka ji”.
Ya ce, “A shafa labari-shuni???”
Dariya ta yi wadda ta fiddo fararen lafiyayyun hakoranta masu sheki, ta ce, “Ko a Jakar-Magori idan ka shafa za ka ji”.
“Shake my hands RAYHAH......”
Ya fada a wahalce tare da mika mata hannun damansa wanda ke daure da ruwan kasar agogon ‘Swatch’.
Ba ta mika mishin ba, sai ta bude kofar motar tana fadin “An kira sallah Yaya K....... can I go?”
Ya shafo sumar kansa ahankali daga goshinsa har zuwa keyarsa idanunshi a lumshe, sun kada sun zama brown dinsu ya ce a wahalce,
“Go to Masjid Rayhah........! tun kafin ki kashe ni da raina!!”.

****
[12/24/2019, 21:47] Takori: Wannan shine dan mabudin da ya bude kofar soyayyar Rayhah da Khalipha. Alkunyarta, rashin son magana, saukin kai da kawaici, rikon addininta sune manyan halayen ta da suka jawo Khalipha gaba daya ya afka a rijiyar soyayya ruwan ya sha shi har wuyansa.
Duk yadda ya yi tsammanin Rayhanah ta wuce nan a qualities din da yake hasashen tana dasu, wadanda yake so a matar aurensa.
Washe garin ranar Daddy ya zo ya dauketa suka wuce Kano, ta kwana biyu ya maidota Talata saboda Monday aiki bai barshi ya samu sukuni ba, ba kuma zai sata a motar haya ba.
Yadda Rayha ta ga Mami cikin kwanaki biyun nan da ta yi abin ya tsoratata. Completely Mami ta canza kamar wahainiya, muraran take nuna ba ta son zaman Rayhanah a gidanta yanzu, duk da Baba Dacta bai fito fili ya gaya mata Khalipha son ta yake ba. Amma ya ce da ita aure zai mata ba za ta shiga B.U.K ba.
Ta tambaye shi waye mijin? Ya ce da ita, “Time will tell you!” sai tasa mishi ido tana cewa a ranta, “Kai ma lokacin zai gaya maka ko wace ce Anita Shiyana, tunda Asma’u ka sani.
Lallai gaskiyar Dr. Halima ta yi sakaci da yawa da Dr. Mansur, tana ganin cewa wai yana sonta, ba za ta taba bin malamai a kansa ba. Yanzu kam ta yarda cewa ta yi sakacin, tunda ya fara munafuntarta ya soma boye mata wasu al’amura da ya lura ba za ta yi na’am dasu ba.
Shi kuma har ga Allah zuciyarsa daya, bai ki gaya mata don munafurci ba sai don baya son bacin ranta ko nasa cikin al’amarin, ya fi son sai komi ya kankama tukunna sannan ya zauna ya yi mata bayani ya ba ta hakurin karya alkawarin da ya yi mata, a dalilin ajizanci irin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login