Showing 27001 words to 30000 words out of 36765 words

Chapter 10 - Fadeelah Book 1 Hausa Novel Complete

Fadeelah   

03 Jan 2025

250

ta sanar da shi k'udirinta amma ya ce ta jira tukun.



Yau sati d'aya kenan da Fadila suka yi magana da MD zai zo amma har yanzu bai zo ba . Fadila na zaune ta yi ma Ahmad wanka ta kwantar da shi saboda ya yi barci, ta ji shigowar MD bakin shi dauke da Sallama .



Fadila kai ta d'aga tana kallan MD sannan cikin jin dad'in zuwan MD d'in dan yau ta k'uduri barin zaman gidan ta ce " Barka da zuwa " MD kai ya jinjina ma Fadila sannan ya ce " Kin kirani akan zaki koma gida ? Kina ganin babu matsala ?, Mama ta hak'ura ne ? " Zan gwada in gani ne " Kai MD ya jinjina nan ma , sannan ya mik'a mata hollondia Yoghurt d'in da ya zo da shi ya ce " Ga shi ki sha wannan sai mu wuce " Fadila amsa ta yi ta sha dama yau ta kasa yin girki tsabar tasa ranta a tafiya gida .


Fadila na gama shan hollondia d'in take ganinta ya fara d'aukewa ta fara ganin duhu-duhu . Fadila cikin rud'ewa da yadda ta ji take ta sauya ga ganinta ya d'auke dishi-dishi take gani ta ce " MD, ba fa na gani duhu-duhu nake gani ? " Fadila ta fad'i maganar a rud'e


MD baitanka ma Fadila ba.


Fadila tashi ta yi ta fara laliban hanya sai ji ta yi an rungomata baki d'aya, daga nan jinta da ganinta ya d'auke bata k'ara sanin abin da ake ba.




ADAMAWA STATE



Yau ya kama Weekend Muhammad na gida, dama shi an fi samun shi a falon Hajiya Baturiya in dai yana gida. Muhammad zaune ya ke suna fira da Hajiya Baturiya Alhaji Sagir ya shigo falon wanda dawowarshi kenan daga maiduguri. Zama ya yi yana cewa " Tom , Alhamdulillahi. Yanzu dai muna sa ran komai ya kusa zuwa k'arshe ko ince ya zo k'arshe , Muhammad, wannan tafiyar tawa da na yi baki d'ayanta taka ce, wato wani abokina ne mu ka yi magana da shi akan mutuwar matanka, shi ne yake sanar da ni wai yawanci idan ana samun irin haka kuma har mun yi bincike babu wani information da muka samu to shairin iska ne , ya ce yawanci Al'jana ce ke aurar mutum haka ke faruwa, daga ya yi aure ta kashe matar , dan kamar yadda ya sanar da ni yarinyar abokinshi haka ta faru da ita , itama duk wanda ya aureta washegari za a farka a ga gawarshi, intakaice muku zance yanzu haka ya kaini har wajan shehin malamin da ya yi ma 'yarinyar addu'a yanzu haka ta yi aure har ta haifafa ma , tom sai dai malamin ya mutu amma akwai yaronshi babba wanda shi ya gadai , dan baka ga mutanan da ke zuwa wajan shi d'aukar karatu ba, Muhammad , yanzu haka a maganar da nake maka an sauke al'qur'ani har so uku , kuma gashi nan an rubuce shi ya ce a baka kasha , sannan duk gidan da zaka zauna a tabbatar an sauke al'qur'ani a gidan . Kai in tak'aice muku gaba d'aya yanzu haka shi wannan abokin nawa da nace muku ya kaini inda aka yi addu'ar nan yanzu haka ya ba Muhammad auran 'yarsa Kadija, dan haka duk lokacin da ka samu lokaci cikin Week din nan ka je ka ganta "


Muhammad da gaba d'aya yanzu babu maganar aure a gabansa sai be ji dad'in hakan ba , amma sai ya boye ma nahaifinsa ya ce " Daddy, duk da zuciyata har yanzu cikin fargabar abun da ya faru nake ba zan k'i na'am da duk abin da kuka yanke akaina ba , a koda yaushe uwarninku kawai nake jira , dan haka ba sai na ganta ba na aminta " Muhammad ya fad'i haka dan faranta ran mahaifinshi kamar yadda yaga shi ma akoda yaushe yana k'okarin ganin nashi farin cikin .



Alhaji Sagir kallan Hajiya Baturiya ya yi ya ce " Mommyn Muhammad , biki ce komai ba?" Hajiya Baturiya murmushi ta yi ta ce " Indai Muhammad ya amince nima a shirye nake da amsa tayin " Alhaji Sagir murmushi ya yi ya ce " Tom , alhamdulillah , yanzu zan samu mahaifin yarinyar mu tsaida magana inda ka yi na'am. Saidai kamar yadda nace maka ka shirya ka je ku ga juna , dan muna son yi abun cikin lokaci "



Bayan kwana biyu da maganar Muhammad ya shirya inda Jibirin d'an'uwansa ya yi masa rakiya suka je suka ga Kadija . Kadija ba wani yi ma Muhammad ta yi ba amma kasancewar ita d'in zab'in mahaifinshi ce sai ya hak'ura .


B'angaran Kadija ko take ta amince saboda Muhammad babu macan da zata gan shi ta k'i shi ,dan ya ji komai kota ina mutum ne .


Haka babu b'ata lokaci aka fara shirye-shiryen biki.


Ana gobe biki Malamin nan da aka had'a Alhaji Sagir da shi suka kwana karatun al'qur'ani a gidan da za a kai Kadija shi da d'alibanshi.


Washegari aka d'aura auran Muhammad da kadija.


Usman da sauran abokan Muhammad su suka kai amarya da k'awayanta har gidanta , wanda ya kasan ce shima sabo ne .



Bayan an akai amarya ba jimawa Muhammad bai tafi ba , Usman jin Muhammad shiru-shiru bai zo ba Alhaji Sagir ya Kira ya sanar da shi suna can suna jiran Muhammad ya zo kafin su wuce.


Alhaji Sagir d'akin Muhammad ya shiga zaune ya iske Muhammad da photon Hafsat yana kallo yana kuka. Alhaji Sagir fusge photon ya yi ya ce " Muhammad har yanzu ka kasa yadda wanda yafi ka son Hafsat ne ya d'auke abarshi , idan har ba kana son samun damuwa bane ko kasa ma kanka ka tashi ga su Usman can suna jiranka sai ka je su tafi " Muhammad goge hawan idonshi ya yi ya ce " Daddy, bana d'akko photon Hafsat ba dan in sa ma kaina damuwa na yi haka ne dan innuna ma Hafsat har yanzu tana raina ban manta da ita ba kuma ba zan tab'a mantawa da ita ba har ranar da numfashina zai bar gangar jikina " Alhaji Sagir goge hawayan Muhammad ya yi ya ce " Addu'a zaka yawaita yi mata ta haka ne kawai yanzu zaka nuna soyayyarka a gareta , jeka su Usman na jiranka "



KADUNA GARIN GWAMNA


Fadila tun safe ba ita ta farka ba sai a azahar



Fadila kwance ta ganta kan katifar d'akinta, jin jikinta take yi ya yi sanyi sosai kamar dai irin wanda ya tashi jinya .
Shiru ta yi tana tunani take duk abin da ya faru da ita ya dawo mata na zuwan MD gidan da kuma hollondia yoghurt d'in da ya bata ta sha daga nan ganinta ya d'aushe, shi ne fa bata sake sanin abun da take ba sai yanzu da ta farka ta ganka kwance.


Fadila da sauri ta tashi tana bin sassan jikinta da kallo, tashi ta yi da sauri tana duba kanta saidai ita bata ga wata alama ba a jikinta wanda zata shaida ko MD ya kusanceta , saidai tana jin gaba d'aya jikinta babu dad'i. Da sauri Fadila ta kai duba ga Ahmad amma bata gan shi ba.

Fadila tashi ta yi da sauri ta nufi falon nan ma babu Ahmad. D'akunan ta fara diddubawa nan ma babu shi . Ji ta yi hankalinta ya tashi sosai dan take jikinta ya fara rawa .


Fadila Kiran MD ta yi a waya sai jin wayarshi ta yi a kashe. Take ta rud'e hankalinta ya tashi , dan tunaninta ya bata MD ya bata abun da zai b'atar mata da hankali ne dan ya gudu mata da Ahmad , hakan ya sa Fadila jikinta na rawa ta d'auki hijab d'inta ta fit.✍🏻



Ku bar gaggawa za ku fahimta, ku dai ku biyoni a hankali , ku bar sani ina gudu kar in ji ciwo mana 😰




πŸ“š FADEELAH πŸ“š
πŸ””πŸ“š
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

πŸ’ͺ🏻J.A.W πŸ’ͺ🏻


Na
Fadila Sani Bakori.



SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban- daban da zan kawo na gyaran jiki acin wannan littafi mai suna FADEELAH .




*🀝 SDEENDTM DATA SERVICES🀝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½
*πŸͺ€08066268951*



Page 11



Fadila Kiran MD ta yi a waya amma wayarshi akashe, take ta rud'e hankalinta ya tashi dan tunaninta ya bata MD ya bata abun da zai b'atar mata da hankali ne dan ya gudu mata da Ahmad, hakan ya sa Fadila jikinta ko ina ya kama rawa , hijab dinta ta d'auka ta fita. Fadila da sauri - Sauri take tafiya ahaka ta samu keke-Napep ta hau. Fadila na cikin Napep din tana kuma Kiran number MD amma akashe.


Fadila ak'ofar gidansu tasa mai napep din ya tsaya. Tsabar a rud'e take kai tsaye ta shiga cikin gidansu ta bar mai napep d'in nan tsaye bata bashi kudi ba, mai napep din ko jinta shiru kuma ganin hankalinta kamar a tashe ya ke ya sa ya juya ya tafi.

Fadila a d'akinsu ta iske mahaifiyarta da Aisha da sauran k'annanta suna zaune jigun - jigun kamar masu zaman makoki.


Mahaifiyar Fadila da sauran k'annanta da dukkansu da kallo suka bi Fadila. Fadila ko koda taga bata ga Ahmad a gidan ba tunaninta ya bata tabbas MD ya gudu da Ahmad, hakan ya sa Fadila ta d'ad'e da kuka .


Aisha da sauri ta nufi inda Fadila take tana tambayarta lafiya , inda mahaifiyarsu ta bi ta da ido .


Aisha cikin sanyi jin Fadila bata tanka mata ba kuma ta ci gaba da kuka ta kuma cewa " Aunty Fadila , lafiya ? Ina yaron fa ? " Sai sannan Fadila ta bud'e baki ta ce cikin kuka " MD ya gudu da shi " Aisha a zuciyarta ta ce " Alhamdulillah " Amma a fili sai cewa ta yi " Lafiya ya gudu da shi ? " Nima ban sani ba " Fadila ta bata amsa.


Suna a haka ne Kira ya shigo wayar Fadila , koda ta duba ta ga number MD da sauri ta d'aga kiran .


MD sanar da Fadila ya yi yana k'ofar gidansu .


Fadila fita ta yi da sauri. MD na ganinta ya fito cikin motar rungume da Ahmad a hannun shi ya mik'a ma Fadila shi . Fadila amsar Ahmad ta yi tana sauke sanyayyar ajiyar zuciya , Sannan ta kalli MD ta ce " Me ka sa min a yoghurt d'in da ka kawo min ? " Fadila ta fad'i maganar tana kure MD da ido .


MD cikin mamaki ya ce " Me na sa miki kuma ? Ni dai na kawo miki yoghurt ina jiran ki sha mu tafi in kawo ki gidanku amma abun mamaki kina sha ko da ma barci kike ji ne ban sani ba ,daga kina zuwa kika je kika kwanta kika kama barci , nima ganin haka sai ban tasheki ba na d'auki Ahmad muka fita " Fadila shiru ta yi sannan kamar za ta yi kuka ta ce " MD , dan Allah ka ji tausayina ka sanar da ni abun da ban sani ba , dan Allah ka cireni a kokonto ka sanar dani ? " Wata magana kike yi ne haka Fadila ? , Me ye biki sani ba ? Me ye ya shige miki duhu wanda biki sani ba kike son sani ? , Yi min bayani yadda zan gane ? " Cewar MD ya k'ure Fadila da ido.


Fadila cikin sanyi ta ce " MD me kasa min a cikin yoghurt d'in da ka ban ? " Oh ! Ya Allah , Fadila me zansa miki ? Wata magana ce kike yi haka ? " Fadila kallan MD ta yi da raunannun idanunta ta ce " Baka samin komai ba kace ? , Tom na ji baka samin komai ba , amma ka sani kafin ganina da jina ya d'auke naji lokacin da ka rungume ni , sannan na farka na ji jikina ba yadda nake ba " Fadila ta idasa maganar cikin kuka ta ce " Ta ya hakan ta faru ? " Shiru MD ya yi , sannan cikin sanyi ya ce " Fadila , atakaice dai idan na fahimceki kina zargina na yi miki wani abun ne . Haba Fadila ki tuna fa ko gidan nan bana zuwa in ba yauba da shima ke kika bukaci in zo in kawo ki gidanku na zo shi ne daga k'arshe abun da zaki sakamin dashi kenan , sannan Fadila ki tuna fa ko kafin Baba Lami ta tafi idan na zo ko dakinki bana shiga hasalima bana dadewa nake tafiya . Amma ki yi hak'uri sai yanzu na gano dalilin da ya sa kike zargina, yoghurt din da na baki kika sha a daidai lokacin kina jin barci kika sha, kika yi barci acikin barcin kika yi mafarkin an rungumeki kina ganin duhu - duhu kamar yadda kika ce , amma kuma yanzu kika dawo da mafarkinki gaba d'aya akaina " Fadila kallan MD ta yi yadda ya ke ta kawo mata hujjojin kare kai ta ce " Shi kenan , na yadda duhun da na gani da rungumata da aka yi duk a mafarki ne , tom amma da na tashi na ji jikina babu dadi bacin lafiya lau nake jin jikina kafin in sha yoghurt din da ka ban shi kuma fa? " Fadila kenan , to so nawa mutum zai kwanta barci ya tashi da zazzab'i ko ciwan kai ? "


Fadila da taga duk inda ta bulloma MD yana k'ok'arin kare kan shi hakan ya sa ta ce " Shi kenan MD Allah ya na tare da mai gaskiya idan har ka zalinceni na barka da Allah " Fadila na fadin haka ta shige gida da sauri ta bar MD nan tsaye.


MD na kiranta amma bata saurare shi ba. Yara ya samu ya basu kayan Fadila da na Ahmad da ya kwaso musu ya ce a shigar mata da su cikin gidan , sai kayan abinci Taliya , makaroni , cous -cous sai buhun shinkafa . Siyayya ce sosai ya yi musu .


Mahaifiyar Fadila ita kanta da mamaki take bin kayan da kallo , sai da aka gama shigo da su tas sannan ta kalli Fadila ta ce " Kin je kin sake saida mutunci naki ne ? Baku da abinci shi ne aka kawo mana ? Tom ki tattara da ke da duk kayan nan ki koma inda kika fito ! "


Mahaifiyar Fadila ta fara cilli da kayan da aka kawo ma Fadilar tana ta fitar mata gida ba zata zauna da karuwa ba , kuma ba zata ci abincin da aka samai ta hanyar sab'on Allah ba .



Mahaifiyar Fadila bayan ta gama cilli da duk kayan da zata iya d'agawa ta koma tura Fadila dake rungume da Ahmad cikin hijab tana cewa " Fita ! ba zan zauna da karuwa ba "


Aisha ganin mahaifiyarsu na niyyar tara musu jama'a rik'eta ta yi tana kuka ta ce " Mama, dan Allah ki bar furta mata kalmar karuwa , Aunty Fadila ta sanar da ni ainihin abun da ke faruwa da ita . Mama , naje wajan Aunty Fadila , kuma ta yi min rantsuwa da al'qur'ani mai girma akan bata tab'a kusantar abun da muke zarginta da aikatawa ba , mama , ke kika haifemu na tabbata ke kanki har yanzu zuciyarki ta kasa amince miki da abun da idanunki ke ganin hak'ik'anin gaskiyarshi , Mama , kinsan Aunty Fadila ba za tab'a rantse min da al'qur'ani ba akan k'arya dan kawai a yadda da ita , sannan ke da kanki kina shaidar fad'in gaskiyarta komai d'acinta . Me ya sa yanzu ba zaki yi mata uziri ba ki zauna ki tattauna da ita kamar yadda kika saba yi abaya , haba Mama, ke Uwace fa me ya sa ba zaki rungumi 'yarki ba zaki watsi da ita taje ta idasa lallacewa kenan ? Haba Mama kar yi abun da zaki zo kina danasani "


Allah Sarki mahaifiyarsu Fadila sakin Fadila ta yi tana kuka .Aisha kuma zuwa ta yi duk ta gyara kayan da mahaifiyarta ta yi watsi da su.


Mahaifiyar Fadila kuma take jikinta ya yi sanyi ta kuma tuna wacece 'yartata abaya , tabbas ta yadda da maganar Aisha cikin Fadila k'addararsu ce inda ida kanta duk da yaron da take gani zuciyarta ta k'i aminta mata da Fadila zata aikata zina .


Fadila da ta kasa jure kukan mahaifiyar tata zuwa ta yi ta tsugunna kusa da ita ta ce " Mama , dan Allah ki bar kukan nan ina tsoran fushin Allah ya sauka akaina , dan ni ce silar kukan naki " Mahaifiyar Fadila kai ta d'aga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login