Showing 6001 words to 9000 words out of 36765 words

Chapter 3 - Fadeelah Book 1 Hausa Novel Complete

Fadeelah   

03 Jan 2025

243

wa'adin ya cika"


Fadila shuru ta yi kanta a k'asa.Mahaifin Fadila kallanta ya yi ya ce"Idan har muka kai watan sha biyu ba tare da kin kawo daidai da ke din da kike jin za ki aura ba,karki kuskura in zo in iskeki a gidana ,ba dai gidana ba Wallahi saidai ki naimi wajan zama"


Mahaifin Fadila sai da ya kuma nanata ma Fadila akan karka kuskura ta k'are shekarar nan ba tare da wata magana ba,sannan ya ce ta tashi ta bashi waje.



ADAMAWA STATE




Alhaji Bala yana komawa gida ya sanar da matarsa hajiya Halima maganar ba da Maryam da ya yi ga Muhammad.
Hajiya Halima sosai ta ji dad'in maganar ,dan Alhaji Sagir mai shadda abin alfahari ne ka had'a iri da shi.



B'angaran Maryam ma ko da mahaifiyarta ta tareta da maganar take ta amince babu ja.



Mahaifin Muhammad ko da ya sanar da hajiya baturiya ta ji dad'in hakan,dan acewarta k'ila hakan ya kwantar ma Muhammad da hankali.




Da daddare alhaji Sagir ya samu Muhammed da maganar.Amma har ya yi maganar shi ya gama Muhammad bai tankamai ba.Hajiya baturiya ta ce"Muhammad,ba ka ji abin da daddynka ya ce bane,sun yanke shawarar had'aka da Maryam yarinyar alhaji Bala aure,saboda tunanin hakan ko zai sa ka kwantar da hankalinka"



Muhammad da ya rasa abin cewa,kuma baya son gwalishe mahaifinsa hakan ya sa ya ce"Tom,mommy"


Hajiya baturiya za ta sake magana alhaji Sagir ya d'aga mata hannu alamun ta yi shiru.




Kwana goma suka tsaida auran,hakan ya sa b'angaran amaryar suka ci gaba da shirye-shiryan biki,inda b'angaran alhaji Sagir babu wani shiri da su ke yi.Maganar lefe ma alhaji Sagir kud'i ya ba su ya ce su yi komai.




B'angaran Muhammad ko yama manta da maganar wani aure da za a yi mai.



Ranar da ta kama d'aurin aure ba wani taro a ka yi ba,garama gidan su Maryam d'in sosai su ke shirin auran.



Ranar Juma'a da safe aka d'aura auran Maryam da Muhammad,in da ba wani taro a ka yi ba na ku zo ku gani.



Lokacin da labarin d'aurin auran ya isa kunnan Muhammad,sosai abin ya d'aga mai hankali ,dan sai da a ka Kira alhaji Sagir aka sanar da shi halin da Muhammad d'in ya ke ciki.




Alhaji Sagir sosai hankalinshi ya tashi ganin yarda Muhammad ya ke kuka.Babu irin lallashin da alhaji Sagir bai yi mai ba,amma kamar ma ba da shi ya ke ba.





Alhaji Sagir ganin yadda Muhammad ya ke kuka ko ranar da Hafsat ta rasu ma bai yi kuka haka ba,hakan ya sa cikin tashin hankali da damuwa ya ce"Muhammad, ko auran ne ba ka so?"
Muhammad cikin kuka ya d'aga ma mahaifinshi kai ya ce"Daddy ,bana son auran nan dan Allah,mu yi alk'awari da Hafsat ba zan tab'a auran wata in ba ita b..." Muhammad ya karashe maganar cikin tsantsar kuka da bayyanar tsantsar ta shin hankali a tare da shi.




Mahaifin Muhammad cikin damuwa ya ce"Muhammad, ka yi hak'uri ,Hafsat ta mutu ta je in da dukkan mu za mu je,dan haka dan ka auri wata ba laifi bane"




Haka alhaji Sagir da hajiya baturiya su ka yi ta yi ma Muhammad nasiha da lallashi a haka suka sa mu ya yi shiru .




D'aya daga cikin gidajan alhaji Sagir ya ba Muhammad in da za su zauna,dan acewar shi ba za'akai Maryam in da akakai Hafsat ba,itama gidanta sabo za a kaita.



Usman abokin Muhammad shi ya jagoranci komai game da d'aukar amarya aka kaita gidanta.




Usman da sauran abokan Muhammad babu yarda ba su yi ba bayan sun kai amarya sun dawo akan Muhammad ya shirya a kaishi gidan amaryar amma ya k'i.Daga k'arshe sai da su ka fad'ama alhaji Sagir.
Alhaji Sagir babu yarda bai yi da Muhammad ba akan ya tashi abokanshi su raka shi,amma ya k'i.Da suka damai ma kuka ya sa musu,hakan ya sa dole suka rabu da shi.



Usman da d'aya daga cikin abokan Muhammad d'in suka koma gidan amaryar.Lokacin ko sun samu kawayan duk sun watse sun barta ita kad'ai.



Ita ko Maryam ta yi sunanin angon ne ma ya shigo,amma sai ji ta yi Usman na cewa"Amarya,ki yi hak'uri za ki kwana ke kad'ai, Muhammad ba shi da lafiya saidai zuwa gobe in sha Allah za ki ganshi.Amma idan kina jin tsoro sai in kai ki gidansu ki kwana "Maryam murmushi ta yi ta ce"Ya jikin na shi?" Alhamdulillah, da sauk'i"Shi kenan,karka damu kanka zan iya kwana ni ka dai babu wata damuwa"





Alhaji Sagir cikin fargaba ya yi barci,duk da ya sa ma'aikatan tsaro sosai a gidan gani ya ke kamar itama Maryam din za a iya yi mata abin da a ka yi ma Hafsat.




Cikin dare alhaji Sagir ya farka a furgice sakamakon mummunan mafarkin da ya yi.
Hajiya baturiya jin tarin alhaji Sagir ne ta farka tana tambayar shi "Alhaji,lafiya kuwa? yanayinka kamar a furgice kake?"Alhaji Sagir jan numfashi ya yi,sannan ya ce kamar zai yi kuka"An kashe Maryam kamar yadda a ka yi ma Hafsa.."Hajiya baturiya katse shi ta yi da cewa"Haba,alhaji mafarki fa ba gaskiya ba ne,na san mafarki ka yi,ka kwanta da tunanin haka ne a ranka shi ne hakan ya zo maka a mafarki, amma in sha Allahhhu babu abin da zai samu Maryam."



Shiru alhaji Sagir ya yi gaba d'aya ya k'osa gari ya waye dan ya je ya dubo 'yar mutane.



Alhaji Sagir na nan zaune har a ka kira sallar asuba.Ana Kira ko ya tashi ya d'auki key d'in motar shi zai fita.
Hajiya Baturiya cikin damuwa ta ce"Alhaji,in sha Allah babu abin da ya samu Maryam,ka daure mu yi sallah sai in raka ka mu je"



Da kyar hajiya baturiya ta shawo kan alhaji Sagir ya yarda su ka yi Sallah.Suna yin Sallah suka fita gidan zuwa D'an maliki road in da aka kai Maryam.





Suna zuwa ma su gadin suka bud'e alhaji Sagir ya shige cike da tarin fargabar abin da idonshi zai gani.



Sun dad'e suna bubbugawa,amma shiru.Hakan sosai ya d'aga hankalin alhaji Sagir da hajiya baturiya. Hajiya baturiya cikin fashewa da kuka ta ce"Mun shiga uku,alhaji kar mafarkinka ya zama gaskiya!"




Alhaji Sagir ya na son ya Kira mahaifin Maryam ya ce ya ba shi numberta ya Kira ya ji,amma kuma yana ganin kamar zai d'aga mai hankali.



Alhaji Sagir ci gaba da bugun k'ofar ya yi,inda kamar daga sama sai ji ya yi an ce"Waye?"Alhaji Sagir cikin jin sanyi aranshin jin muryar Maryam d'in ya ce"My daughter daddynki ne bud'e ko"



Maryam bud'ewa ta yi tana mamakin dalilin zuwan alhaji Sagir da asuba haka.



Alhaji Sagir da hajiya baturiya haka su ka bi Maryam da kalo.



Maryam wadda cikin barci ta ji yo bugun kofar falon,cikin sanyi ta ce"Daddy Allah ya sa dai lafiya na ganku da asuba ko jin Muhammad d'in ne?" Dan ita ta d'auka ko Muhammad ne ma ba lafiya.



Alhaji Sagir cikin sauke bayyanannar ajiyar zuciya ya ce"Maryam, Wallahi wani mugun mafarki na yi hankalina ya k'i kwanciya shi ne dalilin zuwanmu muga lafiyarki"



Murmushin jin dadi Maryam ta yi ganin yarda surukan nata suka nuna kulawa sosai akanta, ta ce"Ayyah,babu komai Daddy,in sha Allah babu abin da zai faru da ni,wancan ma wani rubutaccan al'amari ne"



Alhaji Sagir kai ya jinjina ya ce"Haka ne Maryam.Shi kenan bari mu tafi"



Hajiya baturi cikin marairaicewa ta ce"Ni dai alhaji duk da Maryam ba ita kad'ai bace a gidan hankalina ya fi karka ta akan mu tafi da ita,Allah bashi sai su dawo da Muhammad tare"



Alhaji Sagir cikin gamsuwa ya ce"Haka ne,Maryam d'akko mayafinki mu tafi ,kun dawo anjima da Muhammad tare"




Haka alhaji Sagir suka tasa Maryam su ka tafi da ita.






KADUNA GARIN GWAMNA



A yau jama'ar gasuwar magani ta Kaduna suka tashi cikin tashin hankali saboda rusan kasuwa da a ka yi musu,wanda abin ya had'a harda shagon mahaifin Fadila da ke saida kayan gwari.



Sosai rayuwa ta fara sauya wa su Fadila,inda dama kullum sai an fita kasuwa an nemo suke samun abin da su yi cefane.



Yanzu rayuwa ta fara tsananta wa su Fadila,Yanzu haka yau sun tashi babu abin da za su ci,ga shi kasuwar da aka dogara da ita wadda kullum sai an fita ake samo kudin cefanan abin da za su ci, gashi an rushe kasuwar.



Mahaifin Fadila kwance yana tunanin abin da za su ci,kallan mahaifiyar Fadila ya yi ya ce"Maman Fadila,na ce ko shinkafan nan za a auna a saida a samu kud'in cefanan abin da za mu ci?"
Shiru mahaifiyar Fadila ta yi,sannan ta ce "To,shinkafar ita kasan ta kare saura mudu uku ta rage mana,idan an saida mudu d'aya kaga saura mudu biyu kenan?" Tom,Ya za a yi haka nan za a saida in da za a zauna da yunwa ne?"




Mahaifiyar Fadila ba dan ta so ba haka nan taba yaro ya je ya saida mata mudu daya daga cikin shinkafar da ta yi ragowa,bayan yaron ya dawo ne su ka yi cefanan kayan mahad'in girkin shinkafar.



Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya,inda ya kasance komai nasu Fadila ya kare,duk wata dabara ta kare.


Yanzu haka tun safe har dare ba su ci komai ba.Mahaifiyar Fadila cikin taushin murya ta fara yi ma mahaifin Fadila magana kamar haka"Baban Fadila,dama cewa na yi inda dai ka ga in rushe maka hanyar da muka dogara da ita,wadda muke ci da sha a cikinta,me zai hana ka yi hak'uri Fadila ta koma aikinta kodan mu samu abin da za mu rik'a ci"



Shiru mahaifin Fadila ya yi kamar ba zai tanka ba sannan ya ce"Shi kenan zan yi tunani akan hakan ✍🏻




πŸ“š FADEELAH πŸ“š
πŸ””πŸ“š
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

πŸ’ͺ🏻J.A.W πŸ’ͺ🏻



Na
Fadila Sani Bakori



SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki a cikin wannan littafi mai suna FADEELAH .






Page 4


Yau sati d'aya kenan da maganar komawar aiki da mahaifiyar Fadila ta yi ma mahaifin Fadila , ya ce zai yi shawara amma har yanzu shiru kuma har yanzu da kyar suke samin abin da suke ci.



Mahaifiyar Fadila bayan ta idar da sallah, fadila ta zo ta same ta ta ce"Mama, dama nace ko za ki ma Baba magana in koma aiki Kafin Allah ya kawo mai wata hanyar "


Mahaifiyar Fadila d'ago kai ta yi tana kallan Fadila ta ce"Nima tunanina kenan har magana na yi mai amma ya ce min in saurare shi zai yi tunani, yau sati d'aya kenan amma kin ji shiru sai ka ce baya ganin halin da muke ciki, amma ki bari anjima zan kuma yi mai magana "



Da daddare mahaifin Fadila na zaune yana lazimi ,har lokacin tun kokan da suka sha na safe ne ke cikinsu , Mahaifiyar Fadila ta zo ta zauna gefan abun sallar tashi , sannan zuwa can ganin lazimin nashi ba na kare bane ta ce "Baban Fadila, dan Allah ka bar Fadila ta koma aikinta mana ko dan mu samu abin da za mu rik'a ci, idan kace zaka biye ma maganar mutane Allah mutum ba zai yi abun kirki ba , shi ya sa ka yi abun da ke gabanka kawai , yanzu su mutanan da ke kawo ma maganganin k'arya akanta halinnan da muke ciki cikinsu waya taimaka maka? kuma babu wanda bai san an rushe kasuwarku ba.Wallahi ka toshe kunanka daga maganganun mutane ka barta ta koma ta ci gaba da aikinta mu kuma mu dage mu rakata da addu'a "




Mahaifin Fadila d'ago kai ya yi yana kallan mahaifiyar Fadila kamar ba zai tanka ba sai zuwa can ya ce"Shi kenan ta koma aikin"
Daga jin yarda ya yi maganar kasan dole ce ta sashi furta hakan.


Mahaifiyar Fadia zuwa ta yi ta sanar da Fadila mahaifinta ya amince ta koma bakin aikinta.


Allah sarki Fadila take ta Kira Jamilu abokin aikinta ta sanar da shi gobe zata dawo aiki ,ta k'ara da cewa"Amma Jamilu kana ganin wannan Karan MD zai yarda kuwa? Dan ya kikkira wayata ban d'auka ba, kuma kaga ban tab'a dad'ewa irin na wannan Karan ba ? "



Jamilu dariya ya yi ya ce"Fadila , kema dai kina tonona ne , amma kinsan ko shekara za ki yi biki zo aiki ba kema dai kinsan MD hannu bibbiyu zai amshek ba tare da wani k'orafi ba "



Haka dai su ka yi sallama bacin Fadila ta sanar da shi dawowarta aiki gobe .



Washegari da wuri Fadila ta yi shirin tafiya aiki , bayan ta gama shiryawa ne ta shiga d'akin mahaifinta, bayan sun gaisa ne ta ce"Baba, na shirya zan tafi" Za ki tafi ina ? " Cewar mahaifin Fadila .
Fadila cikin sanyi ta ce "Zan koma wajan aiki , jiya mama ta ke sanar da ni ka amince in koma"
Mahaifin Fadila shiru ya yi yana kallanta kamar ba zai bata amsa ba dan har ta cire rai ma sannan ya Kira sunanta ya ce"Fadila "
Fadila cikin sanyi ta amsa da "Na'am ,Baba"
Ya ci gaba da cewa"Fadila , dan Allah ki ci gaba da tafiya kamar yadda na sanki , kwanakin baya surutun mutane da kuma tsoron bakin mutane akanki ya sa na dakatar da ke aiki ba wai dan na yarda da abin da su ke cewa ba" Shiru mahaifin Fadila ya yi sannan ya ci gaba da cewa"Fadila , ki sani duk abin da za ki yi Allah na kallanki , tashi ki tafi Allah ya tsare "



Fadila cikin sanyi ta tashi tana mai amsawa da "Ameen ,Baba"



Misalin k'arfe takwas (8:00AM) Fadila ta shiga Rahama TV tana zuwa office din MD ta shiga.


Kamar a mafarki haka ya ga Fadila.Seat d'in da ke facing d'in shi ya nuna mata alamun ta zauna.


Bayan Fadila ta zauna ne ya ce"Fadila , me na yi miki kike son fasa zuciyata? Tun da kika bar zuwa aiki ban tab'a kiranki kika d'aga ba? "


Fadila ji ta yi kunya ta gamata, saboda kodan alfarmar da ya ke yi mata be cancanci ta yi mai haka ba , saidai ba daga ita bane daga zuciyarta ne ,zuciyarta ta ka sa aminta da shi bare kuma har ta yi waya da shi.
Fadila cikin alamun ban hak'uri ta had'a hannuwanta ta ce"Afuwa rankashi dad'e , kana kirana duk bana kusa da Wayar ne , kuma babu kati a wayar bare in biyoka "



Shiru ya yi sannan ya ce" Shi kenan Fadila za ki iya zuwa ki ci gaba da aikinki , saboda ganinki na sa zuciyata cikin damuwa "


Fadila ta shi ta yi ta ce"Shi kenan bari in tafi ba zan so in zama silar damuwarka ba,in da ganina damuwa ya ke saka"
Da sauri ya tashi ya sha gabanta ya ce"Tsaya mana, ba haka nake nufi ba, ke d'in ce kin kasance wani abu mai girma gaske a zuciyata ,da zaki yarda da sai in ce miki ban tab'a so wani abu kamar ki ba, dan Allah ki ban dama mana Fadila?"


Fadila tafe kai ta yi, dan dama tunaninta kenan na dawowa aiki daga ta dawo MD zai fara ta kura mata da maganganun shi da baya gajiya.
Fadila cikin k'osawa tabar Office d'in shi ta ce"Shi kenan, zan yi tunani"
Kai MD ya girgiza ya ce " A'a , Kullum haka kike ce min , ki ban amsa ta kawai ko zuciyata zata samu sukuni dan Allah "



Fadila tana tsoran ta furta mai kalmar k'i ta zo ta samu matsala a wajan aiki ga shi a halin yanzu tana buk'ar aikin sosai, hakan ya sa cikin sanyi ta ce"Shi kenan, zan ba Jamilu sak'o ya baka "



Tana fad'in haka ta fita office d'in da sauri kafin ya k'ara wata magana.




ADAMAWA STATE



Alhaji Sagir bayan sun dawo da Maryam Kiran mahaifinta ya yi ya sanar da shi masu zuwa ganin gidan amarya sai dai su bari in ta koma zuwa an jima yanzu tana gidan shi .



Mahaifin Muhammad yana gama wayar mai da kallan shi ga Muhammad ya yi ya ce " Muhammad, saboda masu zuwa ganin gidan amarya ka shirya yanzu ku tafi, kudin kar a zo bata nan "


Muhammad shiru ya yi baice komai ba .
Alhaji Sagir ya kuma cewa " Muhammad ba ka ji abin da na ce ba ne, ka tashi ka shirya kafin a fara zuwa ba kowa gidan "


Muhammad ba dan ya so ba sai danne zuciyarshi da ya yi gudin kar ya watsa ma mahaifinsa k'asa a ido ganin duk yana yin hakan ne dan farincikinsa , hakan ya sa cikin sanyi ya ce"Tom, Daddy "



Alhaji Sagir wayar shi ya ciro ya kira Usman abokin Muhammad ya sanar da shi ya zo yanzu.



Alhaji Sagir kallan Muhammad ya yi ya ce"Idan akwai abin da za ka yi na kira Usman ya zo ya kaiku ka yi kafin ya k'araso "


Muhammad kamar zai yi kuka ya ce"Babu abin da zan yi Daddy"

Sunanan zaune Usman ya yi sallama ya shigo.Bayan sun gaggaisa ne alhaji Sagir ya ce" Muhammad ka tashi ku tafi"


Muhammad d'ago kai ya yi yana mai zubar da hawaye ya ce"Daddy , da bakinka kake cewa in tashi in tafi in zauna da wata ba Hafsat ba , Daddy me ya sa ka yi saurin mantawa Hafsat ? Da ace Hafsat zata dawo duniya za ta yi mamakin hakan Daddy"
Kuka ne ya kwace ma Muhammad ,cikin kukan ya ci gaba da cewa "Daddy, ka yi hak'uri ba zan iya zama da kowa ba in ba Hafsat ba, ita kadai idaniyata ke gani,ita kad'ai zuciyata ta yarda ta so,haka ruhina da gangar jikina da ita kad'ai ta aminta za ta yi rayuwa.Haba Daddy me ya sa kuka dage sai kun tursasa ruhina zama da wata ba Hafsat ba? Bacin na yi mata alk'awarin ruhina ba zai taba rayuwa da ruhin wata ba in ba ita ba.Daddy dan Allah ka bar ni in yi rayuwa da Hafsat ita kad'ai"


Daga Hajiya Baturiya har Usman kallan Muhammad kawai suke, Alhaji Sagir ko ya ma rasa abin da zai ce masa.Inda Maryam ta fita d'akin da sauri tana kuka jin zantikan da Muhammad d'in ya ke yi.


Alhaji Sagir dafa Muhammad ya yi cikin damuwa ya ce " Muhammad , ka yi hak'uri Hafsat ta tafi, ta tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login