Showing 15001 words to 18000 words out of 36765 words

Chapter 6 - Fadeelah Book 1 Hausa Novel Complete

Fadeelah   

03 Jan 2025

248

drip d'in da aka samata saura kiris ya kare .


Jamilu cikin sanyi ya ce" Sannu Fadila , ya jikin naki ? " Fadila fashewa da kuka ta yi ta na cewa " Jamilu , ka ji shairin da su ka yi min ko ?" Fadila ta idasa maganar cikin tsantsar tashin hankali da damuwa.


Jamilu shiru ya yi yana kallan Fadila ya ma rasa abin cewa.



Fadila tashi ta yi tana kallan Jamilu ta ce" Jamilu , dare ya yi za a naimeni a gida , gida zan tafi " A'a , Fadila ki yi hak'uri jikin ki ya yi sauk'i , Sai in je gidanku yanzu in sanar halin da kike ciki " Fadila kallan Jamilu ta yi ta ce " Me za ka ce musu yana damuna ? " Zan sanar da su ne cewa baki jin dadin jikinki" Kai Fadila ta girgiza ta ce " Karka fad'a musu komai , bari na ji sauk'i zan iya kowa"


Babu yarda Jamilu bai yi da Fadila akan ta kwana Asibitin zuwa gobe a bata sallama in da ance jikin nata da saura, amma tak'i .


An sallami Fadila suna bakin titi za su tari Keke-Napep motar MD ta tsaya .Bud'e ma Fadila ya yi ya ce " Shigo in k'arasa da ke gida " Fadila ji ta yi bata da wani zab'i wanda ya wuce ta shiga , in da dakyar take tsayuwar dan gaba d'aya bata jin k'arfin jikinta ,hakan ya sa ta shiga motar.



MD sai da ya kai Fadila har k'ofar gidansu sannan ya mik'a mata ledar maganungunanta ya juya ya tafi ba tare da ya ce mata komai ba.



Mahaifin Fadila ya fito kenan za shi masallaci sallar Issha'i aka sauke Fadila a mota akan idon shi, Mahaifin Fadila bin bayan Fadila ya yi da kallo ganin yadda take tafiya kamar wata 'yar maye.


Fadila ahankali cikin raunanniyar murya ta yi sallama ta shiga gidansu.
Mahaifiyar Fadila da kallo tabi Fadila ganin yadda ta shigo kamar wadda tasha ta bugu .Fadila na zuwa ta kwanta kan d'an madaidaicin gadonsu.

Mahaifiyar Fadila tashi ta yi tana cewa" Fadila , lafiyarki kuwa ? " Ban da lafiya " Fadila ta bata amsa a takaice.
Mahaifiyar Fadila shiru ta yi sannan ta ce " Shi ne dalilin dad'ewar taki kenan ? " A'a mun je Asibiti ne " Me ke damunki ? " Mahaifiyar Fadila ta tambayi Fadila.
Fadila cikin rashin sanin amsar da zata bata ta ce" Ban sani ba nima" Ta fad'i maganar tana goge hawayan da ke zubar mata.


Mahaifiyar Fadila ko da bata kawo komai aranta ba dan ita ta yi tunani ma kodan lokacin da mahaifinta ya bata yana gaf ya cika ne ya sa kila take son sa kanta cikin damuwa, hakan ya sa ta zauna bakin gadon da Fadilar ta ke, ta ce " Fadila , me ke damunki ne ? Lokaci guda haka kika rikice, In dan ma maganar mahaifinki ce ki kwantar da hankalinki shi aure ai lokaci ne , dan haka karma ma ki sama kanki damuw..."
Sallamar mahaifin Fadila ce ta sa Mahaifiyar Fadila ta yi shiru. Mahaifin Fadila ya ce " Fadila , wa ya kawo ki k'ofar gidan nan a mota ? " Fadila tana goge hawayan da ke zubar mata ta ce " Ba ni da lafiya ne ba na jin k'arfin jikina shi ne MD ya kawoni a motarsa " Shiru mahaifin Fadila ya yi dan sosai ya ke yabawa da hankalin ogan nata .
Ya san tabbas in ba rashin lafiya ba kodan munafukan layin nasu ya san Fadila ba zata yarda ta hau motar kowa ba ya kawoka har k'ofar gida , kuma a cikin wannan lokaci haka ba rana ba .



"Shi kenan, Fadila dan Allah a k'ara kulawa da kai , duk in da kike kisan in ba ma ganinki mahaliccinki na ganinki " Fadila dakyar ta iya bud'e baki tana mai k'ok'arin danne kukan da ke taso mata ta ce " In sha Allah, Baba "



Mahaifiyar Fadila da kanta ta sawo ma Fadila tuwon da ta yi ta kawo mata .


Fadila ko ba dan tana son cin tuwan ba sai dan kar a fahimci halin da take ciki ta daure taci kad'an , Sannan ta lallab'a ta yi sallah ta koma ta kwanta.



Kasancewar har washegari Fadila bata jin k'arfin jikinta hakan ya sa bata yi wani yunk'urin zuwa aiki ba.



Mahaifiyar Fadila na kitchen tana dama musu koka k'anwar Fadila wadda ke bi mata Aisha kenan wadda satin d'aya kenan da dawowa hutu da yake bording School take yi .Bayan ta gaida mahaifiyar tasu ne ta ce " Mama , anya kuwa ba akwai abin da ke damun Aunty Fadila ba ? Jiya fa kwana kuka ta yi ? Ko yanzu haka idan kika shiga d'akin za ki ganta tana kuka kad'an-kad'an " Mahaifiyar Fadila barin abun da take yi ta yi tana kallan Aisha ,sannan ta ce" Biki tambayeta me ke damunta ba ? " Jiya da daddare dai bayan kin fita na tambayeta ta ce min babu komai , daga nan ni kuma ban kuma tambayarta ba " Shiru mahaifiyar Fadila ta yi , sannan ta tashi ta nufi d'akinsu Fadilar.



Kwance mahaifiyar Fadila ta samu Fadila tana kuka k'asa-k'asa sosai , sai uban ajiyar zuciya da take ja .Mahaifiyar Fadila zama bakin gadon ta yi tana bubbuga k'afar Fadila , ta ce " Fadila , tashi ki zauna"
Fadila da sai yanzu ta ji alamun da mutun ad'akin goge hawayanta ta yi da sauri ta tashi ta zauna.


Mahaifiyar Fadila ganin yadda idon Fadila ya kumbura ya yi jajir tsabar kuka , cikin damuwa ta ce " Fadila , lafiya me ke damunki Wanda ya sa kika kwana kina kuka tun jiya har yau ?" Fadila k'asa ta yi da kanta tana mai goge hawayan da ke zubar mata.



Mahaifiyar Fadila ta kuma cewa " Fadila, me ya faru dake ne haka wanda ba zaki iya fad'imin ba? Idan ni biki fad'a min ba sai ki sanar da Aisha , kalli fa yadda idonki ya kumbura "



Fadila ci gaba da kukan ta yi kuma tak'i yin magana .Mahaifiyar Fadila kamar ta yi zuciya ta rabu da ita ,amma kuma ta kasa , hakan ya sa cikin damuwa ta kuma cewa " Ko wajan aikin naku ne akai miki wani abun ? " Kai Fadila ta girgiza. " Me a kai miki to? " Nan ma dai Fadila shiru babu amsa.


Atak'aice Mahaifiyar Fadila babu irin tambayar da ba ta yi ma Fadila ba akan abun da ke damunta amma shiru tak'i magana sai kuka. Suna cikin haka ne Aisha k'anwar Fadila ta shigo .Aisha cikin damuwa da halin da taga Fadilar ta kalli mahaifiyarsu ta ce " Mama, me ke damunta ne ? " Aisha ban sani ba , tak'i fad'a min , kira min Jamilu awaya mu yi magana da shi in ji ko wani abun ne ya faru jiya acan wajan aikin nasu "



Mahaifiyar Fadila Jamilu ta sa aka kira mata, bacin sun gaisa ne ta ce " Jamilu , lafiya ? Tun jiya Fadila da ta shigo gidan nan take kuka na yi na yi ta k'i fada min abun da take ma kuka , shi ne na ce bari in tambayeka ko ka sani ? "


Jamilu shiru ya yi dan baisan amsar da zaiba mahaifiyar Fadila ba , hakan ya sa ya ce "Mama, idan na tashi aiki zan biyo ta nan "


Mahaifiyar Fadila da Aisha tashi su ka yi suka bar Fadila anan tana mai ci gaba da kukanta.



Har Jamilu ya tashi aiki ya zo gidan idanun Fadila ba su bar zubar hawaye ba.
Mahaifiyar Fadila bayan sun gaisa da Jamilu ta ce " Jamilu, tun jiya Fadila ke kukan nan har yau , mun yi mun yi ni da 'Yar'uwarta ta k'i fad'amana abun da ke damunta , shi ne dalilin kiranka na ga taku ta zo d'aya ko kai ta fadi maka ? " Jamilu shiru ya yi ,ya ma rasa ta ina zai fara . Tabbas zuciyarshi ta kasa aminta mai da wai Fadila na da ciki .
Jamilu kallan Fadila ya yi ya ce " Fadila, ko dai ki fad'a mana damuwarki ko kuma ki yi hak'uri da kukan nan da kike yi , kina sa 'Yan'uwanki da mahaifiyarki cikin damuwa, dan Allah ki daure ki sanar damu gaskiyar lamarin abun da ke damunki ? ".


Fadila kai ta d'aga tana kallan Jamilu da idanunta wa inda har sun fara kankancewa tsabar kuka .Sannan cikin kuka ta fara magana kamar haka " Jamilu, nima bansan abin da ke damuna ba. Saidai ina jin rayuwata ta zo k'arsh..." Aisha k'anwar Fadila rufe mata baki ta yi ta ce kamar za ta yi kuka ,dan tabbas kome yake damun Aunynta mai girma ne, wanda har ta kasa fad'a musu.
Aisha da hawaye har ya fara zubo mata ganin yarda Fadila ke kuka ta ce " Haba, Aunty Fadila, dan Allah kar ki sa zuciyarmu cikin waswasi mana, kisa mu yi ta canke-canke abun da ba shi kenan ba , dan Allah ki fad'amana damuwarki ? Idan kuma kink'i zan je in kira Baba in sanar da shi abun da ke faruwa na san shi zaki fad'i mai " Aisha na fad'in haka jin Fadila bata ce komai ba ta tashi zata fita alamun zata kira mahaifin nasu.



Fadila da sauri ta kamo hanun Aisha tana mai k'ara tsananta kukanta ta ce " Mama , ku yi hak'uri zan sanar da ku ? Amma dan Allah ina rok'onku ku ban nan da sati d'aya sannan ✍🏻



*🀝 SDEEND MTN DATA SERVICES🀝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For



πŸ“š FADEELAH πŸ“š

πŸ””πŸ“š
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

πŸ’ͺ🏻J.A.W πŸ’ͺ🏻



Na
Fadila Sani Bakori.



SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH.




*🀝 SDEENDTM DATA SERVICES🀝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½
*πŸͺ€08066268951*



Page 7



Fadila da sauri ta komo hannun Aisha tana mai k'ara tsananta kukanta ta ce " Mama, dan Allah ku yi hak'uri zan sanar da ku abin da ke damuna amma ba yanzu ba , ku ban nan da sati d'aya sannan " Shiru Mahaifiyar Fadila ta yi sannan ta ce " Fadila ,na yarda zan baki nan da sati amma saidai da sharad'in ba za ki zauna kina mana koke-koke ba " Fadila kai ta d'aga ta ce " Eh, na yarda "


Haka mahaifiyar Fadila ta tashi jiki babu kwari ta fita , dan tana ji ajikinta abu mai girma ke damun Fadila .



Bayan mahaifiyar Fadila ta fita ne Aisha ma ta ta tashi ta fita, ya rage daga Jamiu sai Fadila .


Jamilu kallan Fadila ya yi cikin tausayawa ya ce " Fadila, wai da gaske ne maganar da Ummi ta fad'amin kina da ciki? " Fadila d'ago idanunta ta yi dake zubar da hawaye ta ce " Ban sani ba nima Jamilu, amma haka likitoci har biyu suka ce " Jamilu shiru ya yi , sannan ya ce " Fadila , amma babu wani wanda kika tab'a ba dama ? " Fadila kallan Jamilu ta yi ta ce " Kamar ya kenan ? " Nufina ko kin ba wani dama ya kusanceki kamar MD da naga kuna tare ?" Fadila fashewa da kuka ta yi , cikin kukan ne take cewa " Jamilu, na zaci kana cikin mutanan da za su bada shaida akaina, saidai kash jibi tambayar da kake jifa da ita , hakan ya tabbatar min in wasu sunmin irin tambayarka ba zan ji haushi ba, MD kuma saninkane bana son shi,ko wanda nake so ba zan bashi damar haka ba bare MD, dama Jamilu ba zaka iya bada shaida akaina ba? "


Shiru Jamilu ya yi sannan ya ce " Fadila, kina da ciki fa aka ce , kuma kina fadin ni kike tunanin zan shaideki ? to taya ? In ce ma mutane me ? " Fadila kamar za ta yi kuka ta ce " Ka fada musu abin da ka sani akaina " Jamilu tashi ta yi tsaye alamun zai tafi sannann ya ce " Fadila, shawarar da zan baki ki sanar da mahaifiyarki abun da ke damunki " Ba zan iya ba Jamilu " Tom shi kenan ni na tafi"



Jamilu sallama ya yi ma Fadila ya tafi.



Bayan Jamilu ya fita Aisha d'akin ta shiga. Zama ta yi kusa da Fadila ta ce cikin sanyi "Aunty Fadila , nasan Jamilu ya san abun da ke damunki ya b'oye mana ne kawai , Aunty Fadila , ko ni ce in dai kin yarda zan iya rufa miki asiri dan Allah ki sanar da ni abun da ke damunki? "


Fadila hanun Aisha ta rik'e ta ce "Aisha zan sanar da ke zuwa gobe "



Aisha ta shi ta yi ta je ta kawo ma Fadila tuwan dare sa su ka yi, amma da kyar ta samu ta ci.



Duk abun nan dake faruwa na koke-kok'en nan da Fadila ke yi Mahaifinta be sani ba.



Yauma dai kamar jiya Aisha tana jin kukan Fadila kad'an-kad'an a haka barci yakwasheta ta bar ji.


Washegari bayan sun karya ne Aisha ta kalli Fadila da ta yi tagumi ta yi shiru, daga gani ta yi nisa a duniyar tunani " Aisha cikin damuwa da damuwar Auntynta ta ce "Aunty Fadila , yau ne kika yi min alk'awarin za ki sanar dani damuwarki ? " Fadila shiru ta yi , sannan ta ce " ki kai min ruwa a bayi in yi wanka ki shirya ki rakani wani waje " Aisha tashi ta je ta kaima Fadila ruwan , sannan ta dawo ta sanar da ita.


Bayan Fadila ta fito wankan ne ta ce ma Aisha ta sanar da mahaifiyarta zata raka wani waje yanzu za su dawo.



Mahaifiyar Fadila da kallo tafi su lokacin da za su fita.


Bakin titi suka je Fadila ta tarar musu Keke-Napep suka hau . Fadila ta ce ma me keken ya kai su 44 Hospital.


Aisha da mamaki ta kalli Fadila ta ce " Aunty Fadila , Asibiti kuma ? Me za mu je mu yi acan ?" Fadila cikin sanyi ta ce " Aisha, ina son mu je canne dan sanin ainihin abun da ke damuna , ance suna da kwararrun likitoci "Aisha dai kai ta jinjina bata ce komai ba.



Koda suka je Asibitin Fadila bayanin duk yadda take ji ta yi ma likitar. Wata roba likitar ta ba Fadila ta ce ta kawo mata fitsarinta.


Kasan cewar 44 babban Asibiti ne hakan ya sa a ka yi ma Fadila duk wani aune-aune da ya kamata.


Bayan an gama ne likitar ta kalli Fadila ta ce " Kina dauke da cikin wata d'aya da kwanakai "


Aisha k'anwar Fadila zunbur ta mik'e tana kallan likitar cikin rud'ewa ta ce " Likita ciki kuma ? Auntyna fa ba matar aure ba ce budurwa ce! ? " Abin da ke damun Auntyki nasanar da ita k'anwata "



Fadila tana kuka ta rik'e k'afar likitar tana cewa " Dama mutum zai iya samun ciki ba tare ya d'aya namiji ya kusance shi ba likita? " Kai likitar ta girgiza ta ce " Haka ba zai tab'a faruwa ba k'anwata mace d'aya ce a duniya haka ya faru da ita ita ce Maryama Mahaifiyar Annabi Isa "



Fadila cikin kuka ta ce " Nima Wallahi irin nata ya faru dani ,dan Allahi ki taimaka min ki rufa min asiri ki cire min shi " Dokar Asibitin nan ko maganin da zaizubar miki da shi bamabadawa bare kuma acire miki , za ku iya tafiya " Likitar ta fad'i maganar tana nuna ma Fadila hanyar fita .


Fadila fita ta yi tana goge hawayan da ke zubar mata ita da k'anwarta Aisha.


Aisha tsayawa ta yi ta goge hawayan dake zubar mata tana yi ma Aunty nata wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login