Showing 36001 words to 36765 words out of 36765 words
badan ina so ba dan kin fira raina , amma ba zan zauna dake da Ahmad ba da kuma cikin jikinki ki je duk inda zaki idan kika haihu sai ki dawo amma da su ba ki naimi ubansu ki ba shi su , ba zan zauna da yaran shegu har biyu ba, ki fita kije ki naimi ubansu dan wallahi ba zaki kwana gidan nan ba yau "
Aisha cikin marairaicewa ta ce " Mama , dan Allah ki yi hak'uri idan kika koresu ina za su ? " Mahaifiyarsu Aisha cikin d'aga murya ta ce "Aisha , Wallahi in duniya zata taru akaina ba zan zauna ina kallan Fadila da shegeba tana raino ga kuma wani aciki yana shirin zuwa duniya , amma ta je duk inda zata ta haihu , k'ila in ta haihu ta dawo min ba da su ba in yafe mata "
Aisha zata k'ara magana mahaifiyar Fadila ta ce " Wallahi , indai Fadila bata bar gidan nan ba na bar ganinta zan mata baki "
Fadila sanin halin mahaifiyarta da ta yi na indai ta yi zuciya babu mai iya lankwasata ya sa ta shiga d'akinsu ta d'akko wasu daga cikin kayanta da na Ahmad , tana rungume da Ahmad ta je wajan mahaifiyarta tana kuka ta ce " Mama , zan tafi in sha Allah kuma ba zan dawo da Ahmad da abin da ke cikina ba , amma dan Allah mamana ki bar fushi dani ki samin albarka ko zan samu sukunun zuciya dan Allah kar ki yi fushi dani "
Allah sarki mahaifiyar Fadila ma kuka take cikin kunan ne ta ce " Fadila , ki tabi zuciyata ta kasa jure ganin Ahmad da abin da ke cikinki dan Allah ki tafi bana son ganinku baki d'aya ! "
Fadila tana kuka ta juya ta fita gidan har tana sake juyowa .
Fadila na fita Aisha ta durkushe awajan tana kuka sosai .
Fadila ko koda da ta fita rasa inda za tabi ma ta yi , hakan ya sa ta mik'e hanya tana tafiya tana kuka ga Ahmad rik'e ahannunta . Fadila sai da ta yi tafiya sosai tabar unguwarsu baki d'aya sannan ta samu wani waje ta zauna tana tunanin inda zata . Tunanin Kiran Jamilu ta yi sai kuma taga shi ma yanzu d'auke mata kai yake hakan ya sa ta fasa .
Fadila na nan zaune , Muhammad Sagir mai shadda ya fad'o mata arai , charting d'insu ta tino da yake ce mata zata bar mai Ahmad ,ta ce shi da bai da mata wa zai rik'e mai , ya ce ga mommynshi nan .
Fadila shiru ta yi tana tunani ta ce " Tom kodai da gaske yake , kai koma bada gaske yake ba yana da kirkin da zai iya taimakamin "
Fadila da keneman ceto da kuma tunanin kamar zaitaimaka mata ya sa ta Kira number shi .
Sai dai ta Kira bai d'aga ba, sai da ta yi mai kira uku amma bai d'auka ba .
Fadila ganin bai tauka ba ta fara tunanin ko gidan marayu zata ta kai Ahmad ita ma ta zauna in ta haifu ta bar abin da ta haifa acan ta dawo gida , in da mahaifiyarta ta ce zata amsheta in dai babu su Ahmad .
Fadila tashi ta yi ta samu Napep ta ce ya kaita gidan maru dan Allah da ke nan kusa .
Fadila koda suka isa gidan marun ce mata akai sai ta zo da wani nata sannan a amshi Ahmad .
Fadila bacin ta biya mai Keke - Napep d'in , tafiya ta fara yi ak'asa batare da ta san inda zata ba. Fadila jin ta gaji ta fara ganin jiri ga Ahmad har ya fara kuka , hakan ya sa ta samu waje ta zauna , ta na zama ta sake tunanin k'ara kiran Muhammad , nan ma sai da ta yi kira uku amma bai d'aga ba .
Wani tunani ne ya zo ma Fadila a zuciyarta ta ce " Tabbas , Muhammad Sagir ya na da kirki kuma ina ji ajikina zaitaimakamin dan haka Adamawa zani kafin in isa zanta kiran numbersa har Allah ya taimakeni ya d'aga "
Fadila na gama wannan tunanin ta tashi ta hau Napep ta nufi tasha , tana zuwa ko ta samu motar Adamawa ta cika saura mutum d'aya ta hau suka tafi ✍🏻
FADEELAH free page ya k'are ga mai muk'ata # 300 kacal 👌🏻
Kud'in littafin FADEELAH d'ari uku ne dan Allah idan ba siya zaki ba karmu b'ata ma juna lokaci 🙏🏻
My Number 08063830828