Showing 30001 words to 33000 words out of 36765 words

Chapter 11 - Fadeelah Book 1 Hausa Novel Complete

Fadeelah   

03 Jan 2025

251

da jajayan idanunta tana kallan Fadila ta ce " Fadila, abu d'aya nake so ki sanar da ni yanzu waye mahaifin yaron nan ? " Mama , Wallahi tallahi ! Ban sani ba nima , dan Allah ki yafe min ki bar fushi dani ko zan samu sununin zuciya " Cewar Fadila tana kuka.


Mahaifiyar Fadila tashi ta yi tana tada Fadila ta ce " Na yafe miki Fadila , ni kuma Allah ya sa mun dangana "




ADAMAWA STATE



Muhammad da kan shi ya tuk'a kan shi har zuwa sabon gidan shi . Bai shiga ba sai da ya yi addu'o'i sannan .


Ango d'an kwalisa kad'an ya rage da ka zo kaga wayam , dan da amarya za mu tafi . Muhammad murmushin yak'e ya yi ya ce " Haba , kun isa ma "


Nan dai suka yi ta tsokanar Muhammad sannan su ka yi musu fatan alkairi suka tafi .



Muhammad bacin abokanshi sun tafi kallan Kadija ya yi wanda har ga zuciyarshi yake jin bata yi mai ba , amma dai ya yi alk'awarin zama da ita saboda mahaifinsa .


Muhammad ledar da ya shigo da ita ya mik'a ma Kadija ya ce " Bismillah " Na yi fushi gaskiya , tun dazu baka zo baka barni da abokanka suka ci kani da surutu " Muhammad bai k'ara jin baya son Kadija ba sai da ta yi magana ya ji baki d'aya ma ba ta yi mai ba , dan shi yana d'aya daga cikin abuwan da yake son mace dasu , yana son mace mai murya , amma wannan baki d'ayanta ba ta yi mai ba , ga shi da alama ma tana da surutu .


Kadija ko jin Muhammad ya yi shiru ta ce " Baka ji abin da nace ba ne ? Ba zan ci ba na yi fushi idan kana so in ci to ka kallasheni "


Muhammad kallan Kadija ya yi ya ce " Saina lallasheki zaki ci ? " Wayyo Kadija muryar Muhammad ta tafi da ita , kasa bud'e baki ta yi ta yi magana sai d'aga ma Muhammad kai ta yi .


Muhammad kallanta ya yi ya ce " Ki yi hak'uri ki ci kin ji amarya kwana da yunwa babu dadi " Muhammad na fad'in haka ya yi shigewarsa ciki ya barta anan zaune .


Kadija bin bayan Muhammad ta yi da kallo ta ce " Wayyo dace kan dace gaskiya na shigo duniya a sa'a , kyakkyawa ne mai daddadar murya , dole ma in bisa yadda yake so kodan in samu damar mallake zuciyarsa "

Kadija ta dad'e tana sambatunta akan Muhammad sannan ta d'akko ledar da Muhammad ya aje mata . Tana gama lashe -lashenta barci ya kwasheta a wajan.



Muhammad cikin barci ya jiyo gurnanin mutum , tashi ya yi yana fitowa falon da sauri .


Kadija ya gani kwance sai haure - haure take .

Muhammad da sauri ya idasa inda take saidai take ya zazzaro idanunsa ganin Kadija kwance cikin jini an mata yankar rago amma har yanzu ran bai gama fita ba .


Muhammad cikin furgita ya ke nanata " Innalillahi wa inna ilaihirraj'un ! "

Muhammad na nan tsaye kan Kadija har ranta ya fita ya bar gangar jikinta . Muhammad da gaba d'aya tsoro ya fita ranshi da sauri ya bud'e k'ofar falon ya fita , wajan masu gadin gidan ya je hankali tashi , ya na tambayar su waye suka shigomai gida . Sai dai Muhammad a lurar da ya yi gaba d'aya masu gadin basa cikin hayyacinsu , hakan ya sa bai bi takansu ba ya bud'e get d'in ya fita.



Saidai unguwar shiru bai ga komai ba bai ga kowa ba. Ahaka tsabar rud'ewa Muhammad ya kama hanya cikin daran ya isa gidansu a k'afa , Muhammad na zuwa ya yi ta bubbuga get d'in gidan amma shiru sai da ya dade yana yi sannan aka ce " Waye ? " Muhammad ne ku bud'e " Jin muryar Muhammad da sauri suka bud'e get d'in ya shiga.

Da mamaki suka bi Muhammad da kallo dan daga gani ma kamar ba a hayyacinsa ya ke ba . Hakan ya sa kafin Muhammad ya idasa shiga gidan d'aya daga cikin masu gadin da yake na hannun damar Alhaji Sagir ne ya kirashi awaya ya sanar shi ga Muhammad ya zo kuma da alama a furgice ya ke .


Alhaji Sagir cikin tsoro da jin Muhammad ya zo cikin tsakiyar daran nan ya tashi ya fita ya biyoshi . Gaf k'ofar da zata sada Muhammad da falon Alhaji Sagir suka had'e .


Muhammad na ganin mahaifinshi ya ce " Daddy , ka ga ni ko abun da nake tsoro kenan itama sun kasheta , Daddy , an mata yankar rago kamar wa incan "


Iya furgita alhaji Sagir ya furgita da kalaman Muhammad , kama Muhammad d'in ya yi ya zaunar da shi dan ganin kamar ba ya cikin hayyacinsa .


Atakaice dai cikin daran Alhaji Sagir suka je da motar 'yan sanda suka taho da gawar Kadija . Haka dai aka yi duk wasu binciken da za ai akan gawar .


Sosai mahaifin Kadija ya furgita lokacin da sakon mutuwar Kadija ya isarmai . Haka dai ita ma Kadija aka sallaci gawarta aka kaita gidanta na gaskiya .



KADUNA GARIN GWAMNA




Mahaifiyar Fadila haka ta sama kanta hak'uri da dangana dan yanzu har daukar Ahmad take . Yanzu dai atakaice kusan duk sun saki ransu sun dawo rayuwarsu kamar da . Abu d'aya ke damun mahaifiyar Fadila shi ne surutun 'yan unguwa , dan haka nan tana zaune sai taga an shigo gidan wai an zo gaidata da wayan aga dan da Fadila ta haifa .



BAYAN WATA D'AYA


Yanzu watan Fadila d'aya kenan da dawowa gida . Yau Fadila ta samu mahaifiyarta da maganar zata koma aiki.


Maifiyar Fadila shiru ta yi sannan ta ce " Tom , Fadila Allah ya tsareki dan Allah ki kula sosai " Fadila cikin kwantar ma mahaifiyarta da hankali ta ce " Karki damu Mama , babu abin da zai faru dani in sha Allah "



Yau Fadila ta koma aiki , in da MD ya amsheta babu yabo ba fallasa , dan abun da ya ba Fadila mamaki gaisuwarta ma ciki - ciki ya amsa , ta zaci ma zai dakatar da ita aikin ne amma sai ta ji ya ce " Ta je ta samu Jamilu su yi magana " Fadila ta juya zata tafi ne , MD ya ce " Ahmad fa ? " Fadila kamar karta bashi amsa amma sai cewa ta yi " Ahmad yana gida " Kina nufin acan zaki barshi ? In yana kukan abinci fa ?, Gaskiya ba zai yuwu ba sai dai ko ki rik'a zuwa da shi ko kuma ki bar aikin "


Fadila kallan MD kawai ta yi bata tanka mai ba ta fita.


Koda taje ta samu Jamilu take ya sanar da ita akwai aikin da za su yi yanzu haka . Haka Jamilu ya yi ta nuna ma Fadila tsare - tsaran da suka canza . Bayan ya gama nuna mata ne suka gabatar da Shirin da suke gabatarwa tare in da rashin Fadila ya sa suke yi da Ummi .


Bayan sun gama kabatar da shirin ne suka bada damar aiko da sak'onni ta waya ko ta Gmail address nasu . Bayan sun dawo hutun takaitaccan lokaci da suka je ne Fadila ta fara karanto sak'onin kamar haka , ta ce " Mai sakon farko Hassana Sani ta ce " Shin macan da ta haihu agida za'a iya kiranta da sunan mace mai daraja itama ? " Fadila ta gama fad'in sak'on tana kallan Jamilu wanda tasan duk wanda ya yi tambayar nan da ita yake kuma dan ita aka yi .


Jamilu ma ya gane hakan , hakan ya sa ya bada amsa kamar haka " Eh , sosai ma kuwa za'a iya kiranta mace mai daraja itama idan har ya kasance ta hanyar tsautsayine ta same shi "


Abun mamaki tambaya ta biyu ma suna kamancece niya da ta faro , haka dai ita ma Jamilu ya bada amsa a ilimance .


Haka dai suka gama shirin Fadila ranta yana mata duk ba dad'i .



Fadila ta tashi aiki zata tafi gida MD ya tareta ya ce " Fadila, kamar yadda nace miki kodai ki rik'a zuwa da Ahmad aiki dan bai isa barshi a gida ba ko kuma ki dakata da zuwa aikin har ya yi kwari ✍🏻




πŸ“š FADEELAH πŸ“š

πŸ””πŸ“š
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

πŸ’ͺ🏻J.A.W πŸ’ͺ🏻


Na
Fadila Sani Bakori


SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban - daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .



*🀝 SDEENDTM DATA SERVICES🀝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½
*πŸͺ€08066268951*



Page 12



Fadila ta tashi aiki zata tafi gida , MD ya tare ta ya ce " Fadila , Kamar yadda kika ji na ce miki kodai ki rik'a zuwa da Ahmad aiki ko kuma ki dakata da zuwa aiki har ya yi k'wari "

Fadila juyawa ta yi ta fita ba tare da ta tanka ma MD ba .


Fadila koda ta koma gida bata b'oye ma mahaifiyarta yadda su ka yi da MD ba . Mahaifiyar Fadila shiru ta yi Sannan ta ce " Fadila , kodai MD shi ne mahaifin Ahmad ?" Tom , mama ni ma ban sani ba , amma ni ma ina zargin hakan " Cewar Fadila .


Aisha da ke zaune kusa da su ta ce " Nifa mama da za ku bi ta tawa Wallahi d'aukar yaran nan za'ai akai mai abinsa , dan babu ma makawa d'ansa ne Wallahi " A'a Aisha har yanzu ba mu da wata k'wak'k'warar hujjar da za mu yi haka , amma idan mu ka yi hak'uri Allah zai kawo mana hujjar da za mu kamashi da ita "


Da daddare Fadila tana hau Facebook, anan ta ci karo da posting d'in Usman abokin Muhammad yana cewa " Assalamu alaikum. Jama'a dan Allah ku taya mu addu'a Allah ya kawo ma abokin Muhammad Sagir mai shadda mafita akan halin rayuwar da ya tsinci kansa . Muhammad Sagir auranshi uku kenan , amma daga ankai matan gidansa washegari zai farka aga anyi musu yankar rago , gashi duk wani bincike da kuka sani babu wanda ba mu yi ba , amma har yanzu dai Allah bai bayyana mana wanda suke haka ba . Dan Allah kusa Muhammad Sagir a addu'a Allah ya toni asirin duk mai akatamai haka, idan kuma iskace Allah ya yi mai maganinta "


Fadila haka taita bin comments din jama'a , inda mutane da dama sukan ce " K'ilama al'jana ce ta aurai take ta mai ta'asan nan " Haka dai jama'a kowa da abin da yake cewa .


Fadila shiru ta yi , dan tabbas idan bata manta sunan wanda aka ce ya yi mata aiki ya ciro mata Ahmad ba shi ne , dan tabbas haka ya gabatar da sunan shi ga jama'a ranar taron bikin cikar shekara goma da RAHAMA TV ya yi . " Muhammad Sagir mai Shadda tabbas haka sunan ya ke"

Fadila dan ta cire ma kanta kokwanto Jamilu ta kira , bayan sun gaisa ta ce " Jamilu , dan Allah ko zaka iya tuna min sunan wanda ya yi min theater ya ciro min Ahmad ? " Eh , sunansa Muhammad Sagir mai shadda " Fadila shiru ta yi sanan ta ce " Shi kenan, na gode sai anjima "


Fadila bayan ta kashe wayarta number Muhammad ta kira acewarta ya cancanci ta yi mai gaisuwa . Abun mamaki kira d'aya Muhammad ya d'aga .


Fadila da bata yi tunanin ma zai d'aga ba take ta rikice , haka dai ta daidaita natsuwarta ta fara magana kamar haka " Assalamu alaikum . Ina wuni " Muhammad adak'ike ya amsa da " Lafiya , bangane wake magana ba ? " Sunana Fadila daga nan Kaduna , ni ce wadda ranar da ka zo taron anniversary namu na haihu ka yi min theater , tom yanzu nan na cikaro da wani posting da abokinka ya yi akan mutuwar matanka , Allah sarki Allah ya yi musu rahama Allah ya sa maka juriya na rashinsu , Allah ya kuma tona ma wanda yake aikata maka haka asiri "


Muhammad sosai ya ji dad'in addu'ar Fadila , cikin jin dadi addu'ar tata ya ce " Ameen ya Allah . Ina yaronki fa ? " Ahmad yana nan ya fara wayo watan shi hudu kenan " Ok ki tura min photonsa ingansa " Fadila cikin jin dad'i ta ce " Tom "

Daga haka Muhammad ya kashe wayarshi.


Fadila kuma take tahau WhatsApp ta tura ma Muhammad pics din Ahmad kala uku .


Muhammad koda ya hau online ya ga pics din Ahmad da Fadila ta tura mai sosai ya yaba mata kyan yaran , dan har yana tonanta da cewe " Za ki ban shi ko ? " Fadila da hawanta Online kenan ta ci karo da sak'on Muhammad, dariya ta yi ta ce " Eh , zan baka , amma kuma ai baka da matar da zata rik'e maka shi " Amma kuma ai ina da mama kinga mamana zata rik'emin saidai in kina min wasa ne ba bani zaki ba " Cewar Muhammad da ya biye ma Fadila .


Fadila ta maida mai amsa da cewa " Kai ma wasa kake ba amsa za kai ba "


"Hmmm, ki bani ki gani " Daga nan Muhammad ya sauka .



BAYAN WATA D'AYA


Fadila watanta d'aya kenan da daina zuwa aiki , inda MD ya dakatar da ita ya ce sai Ahmad ya yi kwari . Saidai kullum sai ya aiko ma Fadila dubu d'ayar da yake bata , yanzu kuma acewarshi ta saima Ahmad Pampers .


Ahmad yanzu watan shi biyar kenan .


Fadila 'yan kwana kan nan jiri take fama da shi da yawan ciwan kai . Dan ma sauk'inta mahaifiyarta da Aisha suke rainon Ahmad .


Fadila yau gaba d'aya kwance ta wuni kuma kusan bata ci komai ba .Mahaifiyar Fadila da shigowarta d'akin kenan ta ce " Fadila , kinga yaron nan kuka yake d nono bai isheshi ba , gashi kin k'i tashi ko wani abun ma ki ci " Fadila cikin murya irin ta mara lafiya ta ce " Mama, jiri nake gani ga ciwan kai dake damuna Allah ji nake ko zama bana iya yi " Tom ki tashi ko chamise d'in kusa damu din nan ku je Aisha ta rakaki a baki magani mana " Tom bari Aishar ta dawo "



Bayan Aisha ta dawo ne ta raka Fadila chamise .


Lokacin da suka je za su shiga chamise din kenan Aisha ta had'u da wata k'awarta hakan ya sa Fadila kad'ai ta shiga . Fadila ba yani ta yi ma mai chamise d'in na yadda take ji . Kallanta ya yi ya ce " Madan anya ko ba ciki gareki ba ? " Fadila a furgice ta d'ago dara-daran idanunta tana kallan shi a furgice ta ce " Ciki kuma ! ? " Tabbas , amma zaki iya zuwa Asibiti dan tabbatarw..." Tom shi kenan na gode sai anjima " Fadila ta ce haka sakamakon Aisha da ta shigo.


Aisha kallan Fadila ta yi yadda ta fita da sauri kuma yanayinta gaba d'aya a furgice take . Aisha da mamaki ta k'ara sauri ta iddo Fadila tana cewa " Aunty Fadila , Wai lafiya ? " Eh ce min ya yi ciwan kaine da jiri ke damuna " Aisha da mamaki ta ce " Dama ai akan abun da muka je kenan yana damunki ina ? " Eh ,haka suka ce " Aisha da mamaki ta bi Fadila da kallo dan gaba d'aya ta rud'e maganar ma kamar bata san me take cewa ba .


Aisha da bata kawo komai a ranta ba , haka suka tafi ba tare da ta k'ara magana ba .


Koda suka shiga gida mahaifiyar Fadila tambayar Fadila ta yi ta ce " Me ke damunki ne ? " Jiri ne da ciwan kai kawai " Fadila ta fad'i maganar a furgice dan ta rud'e sosai da jin cewa tana da ciki.


Mahaifiyar Fadila ta ce " Sun baki magani ko ? " Eh, cewa sukai jiri ne da ciwan kai " Mahaifiyar Fadila da mamaki ta bi Fadila da kallo jin tambayar da ta yi mata daban da amsar da ta bata , haka dai ta kuma cewa " Fadila ! Cewa na yi sun baki magana ni ? " Mama , Allah ciwan kai ne " Fadila ta fad'i maganar tana goge hawayan da ya fara zubar mata .


Mahaifiyar Fadila da mamaki ta kalli Aisha ta ce " Ikon Allah , Aisha wai me ke damun Fadila ne ?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login