Showing 3001 words to 6000 words out of 36765 words
rago.Hajiya baturiya ko suna shiga ta yanke jiki ta fad'i.
Alhaji Sagir cikin gigita yake cewa"Hafsat! Hafsat !! Hafsat!!! Ki tashi mana dan Allah! Ki tashi ki fad'imin wanda ya yi miki haka"Alhaji Sagir ya dad'e cikin wannan gigitar kafin ya lalibo wayarshi ya yi kira ba tare da yama san wanda ya kira ba.Ya na kira tun kafin ya ji an d'aga yake cewa"Dan Allah ku tafo da folisawa an kashe min Hafsat"
Usman da mamaki ya kuma bin wayar da kallo ,cewa ya ke "Daddy,lafiya? Me ya faru ? Daddy ka na inane?" Alhaji Sagir ko ya rud'e cewa kawai yake ataho mai da folisawa an kashe mai Hafsat.
KADUNA GARIN GWAMNA
Fadeela yanzu har ta dangana da maganar wani aiki ,haka take zama gida tana taya mahaifiyarta aikin gida,saidai acikin zuciyarta sosai rashin aikin nata ke damunta.
Mahaifin Fadila da mahaifiyarta zaune suna fira,mahaifin Fadeela ya kalli mahaifiyarta ya ce"Ina yaran nan?, dan gidan Sale mai kifi?"Mahaifiyar Fadeela ta jinjina kai alamun ta tuna shi,ya ci gaba da cewa"Tom yau ina kasuwa mahaifin yaron ya zo ya saman akan yaron yana son abashi izinin zuwa wajan Fadila"Tom,ai shi kenan ,yaran yana da hankali ba laifi"Cewar mahaifiyar Fadila.Nan dai suka ci gaba da zantawa akan maganar.
Fadeela na zaune da wani littafi anhunta tana dubawa mahaifiyarta ta shigo d'akin.
Mahaifiyar Fadila zama ta yi gefan Fadilar.
Fadila ko ganin haka tasan magana ce mahaifiyar tata ke tafe da ita,hakan ya sa ta aje littafin hannunta.
Mahaifiyar Fadila shiru ta yi kamar mai tunani ,sannan ta ce"Fadila ,akwai wanda kuke tare ne? Ma'ana wanda kuka yi wata magana da ta shafi aure?" Kai Fadila ta girgiza.
Manaifiyarta kuma ta ci gaba da cewa"Dama Babanku ne ya ce in sanar da ke koda yau she zaki ga bak'o,dan haka ni abin da zan ce miki nasan yaran da mahaifinki ya yi magana akanshi dan haka in ya zo ki amsheshi hannu biyu,dan abisa alama da na gani mahaifinki sun yi magana mai k'arfi da mahaifin yaron,kuma nasan yaran yana da hankaki sosai da natsuwa sannan yana da abun yi"
Fadila shiru ta yi ta rasa abin cewa,sannan dai gudin kar ta yi laifi ta ce"Tom, Mama"
Fadila na zaune mahaifinta ya aiko kiranta ta je waje ta yi bak'o.
Fadila tashi ta yi ta sa Hijab dinta ta fita.
Zaune ta sameshi kan mashin din shi ,ba yabo ba fallasa Fadila ta gaida shi.
Bayan sun gaisa ne,ya fara jero bayanai kamar haka" Malama Fadila,na dade ina ganinki kina wuce ni kullum da safe in za ki wajan aiki,tuntuni na so bayyana miki hak'ik'anin gaskiyar abin da ke raina,amma Allah bai yarda ba sai yanzu, ina fatan za ki amshi tayin soyayyata hannu bibbiyu?"
Ya idasa maganar ya na mai kallan Fadila.
Jin shuru bata tankamai ba,kamar ma ba zata tanka ba ya ce cikin fargaba "Malama Fadila,kin yi shiru?"
Nan ma dai shirun ta yi kamar ba zata tanka ba, sai zuwa can ta ce"Ka yi hak'uri dan Allah ina da wanda nake so zan aura,ina mai baka hak'uri"
Fadila na fad'in haka bata saurari amsarshi ba ta tafi ta bar shi nan tsaye.
Tun daga ranar kullum sai ya zo wajan Fadila fira,inda har ya yi maganarshi ya gama bata tanka mai,dan fitowar ma sai in mahaifiyarta ta yi mata dole take fita.
Ana cikin haka kuma mahaifin Fadila ya sanar da Kabiru in dai ya shirya to ya aiko kawai a tsaida ranar auransu.
Kabiru bai yi k'asa agwiwaba ana sanar da shi ya sanar da mahaifinshi,inda washegari iyayan Kabiru suka zo .Atakaice dai a ranar aka tsaida auran Fadila da Kabiru.
Fadila ta ga dai mahaifinta ya yi bak'i amma bata san wainar da ake toyawa ba.
Zaune take suna waya da abokin aikinta yana mata magana akan MD fa ya matsa mai akan maganarta dan Allah ta ba shi dama,shigowar mahaifiyarta ne ya sa ta ce mai "Ina zuwa "ta kashe wayar.
Mahaifiyar Fadila bayan ta zauna ne ta wurgoma Fadila tambaya kamar haka,ta ce"da wa kike waya?" Jamilu ne abokin aikina"Shiru mahaifiyar Fadila ta yi,sannan zuwa can ta ce"Fadila, mahaifinki ya amshi kud'in auranki,dan har sun tsada ranar aure wata uku"
Fadila cikin alamun mamaki da tsaro ta ce"Mama ,kud'in aurena kuma? Da wa to?" Da Kabiru mana"Mahaifiyar Fadila ta bata amsa kai tsaye.
Fadila da sauri ta tashi ta zuk'unna kusa da mahaifiyarta ta kamo hannunta ta ce"Mama,dan Allah ku yi hak'uri ku k'ara min lokaci ,Wallahi ba na son wanda kuke k'ok'arin had'ani da shi,ki yi ma Baba magana ya ya janye dan ..."Aure babu fashi,kuma babu mai sawa in janye koda ko kin kawo min wanda kiki so,inda na riga na fita hak'inki sai da na baki zab'i"Cewar Manaifin Fadila kenan da ya na bakin k'ofa ya na jin maganar da Fadila ke yi.
Fadila da ta rasa abin cewa fashewa da kuka ta yi.
Haka Mahaifin Fadeela ya ci gaba da shiye-shiryan auran Fadila,inda ta b'angaran Fadila kuma har yanzu tana nan akan bakarta na ba zata aure Kabiru ba.
Dan yanzu ko wajanta ya zo ko gaisuwa bata had'asu,abin da ya fara ba Kabiru tsoro kenan,amma da ya sa mu mahaifin Fadila akan zai hak'ura ya ce "Kabiru,ka yi hak'uri ina sane da abin da Fadila kema,kuma daga zarar kun yi aure in sha Allah zata bari,hakan duk ta na yi ne dan ka ce ka fasa"Wannan maganganun da Mahaifin Fadila ya yi sai suka k'ara ma Kabiru kwarin gwiwa sosai.
ADAMAWA STATE
Usman jin alhaji Sagir kamar ba ya cikin hayyacinshi hakan ya sa ya kastse kiran ya kira Muhammad amma bai d'aga ba,ganin haka ya sa ya tashi ya d'auki mota ya yi gidan Muhammad d'in in da ya san alhaji Sagir na can in da ance shi da iyalinshi za su raka Muhammad d'akin amarya.
Yana tafiya a mota ya yi tunanin kiran 'yan sanda ya sanar da su dan gaskiya yanayin yadda ya ji muryar alhaji Sagir ba lafiya ba .
Usman bai yadda ya shiga gidan ba har saida 'yan sanda da ya Kira suka k'araso sannan suka shiga tare. Suna shiga gidan shiru ,dan lokacin alhaji Sagir har ya sume shi ma. Tun kafin su k'arasa cikin d'akin su ka ci karo da d'ige-d'igen jini ,cikin tsallake jinin suka k'arasa cikin d'akin.Inda suka iske su duk asume ,sai alhaji Sagir da ya suma kan gawar Hafsat da ke kwance cikin jini an mata yankar rago.
Haka suka kama alhaji Sagir da Muhammad da hajiya baturiya su ka yi asibiti da su. Gawar amarya kuma suka d'auki hotunan da za su d'auka sannan itama su ka yi asibiti da gawar.
Alhaji Sagir da iyalanshi ana kaisu asibiti aka basu taimakon da ya dace,inda cikin lokaci aka samu kansu duk kansu.
Alhaji Sagir na farkawa ya fara kiran Muhammad, ahakan ya sa dole aka kai shi wajan Muhammad d'in wanda shi ma farkawarshi kenan.
Alhaji Sagir cikin danne yadda ya ke ji ya karasa wajan Muhammad wanda ke kwance yana fusge-fusgen shi sai an barshi ya je ya ga Hafsat ,wato amaryar shi kenan.
Ana cikin haka ne aka shigo da alhaji Sagir d'akin. Alhaji Sagir da sauri ya k'arasa inda Muhammad d'in ya ke. Cikin danne yarda ya ke ji game da abin da ya samesu ya fara magana kamar haka"Muhammad, ka yi hak'uri mu je gida Hafsat na gida ka ji"
Muhammad kallan mahaifinshi ya yi ya na girgiza kai ya ce"A'a Daddy ,Sun kashe min Hafsat? Su waye daddy?"Alhaji Sagir so ya ke ya yi ma Muhammad magana amma ya kasa ,saboda kukan da ke son kwace mai,hakan ya sa ya fita d'akin da sauri ya koma motar Usman ya na kuka.
Ya dad'e ya na kuka sannan ya samu ya lallashi kan shi ya yi shiru.Hafsat ta kasance ita kad'aice ta rage mai wadda zai kalla ya tuna da kanwarsa, ga shi itama ta tafi ta bar su ko kuma an rabasu da ita lokaci guda.
Alhaji Sagir sai da ya yi kuka mai isarsa sannan ya fita shima sakamakon Kiran da Usaman abokin Muhammad ya yi mai ne.
Usman cikin sanyi ya kalli alhaji Sagir ya ce"Daddy,dole abin akwai tashin hankali da tsantsar damuwa amma za mu iya barin haka a matsayin lokacin Hafsat ne ya yi,saboda wani bai isa ya kashe wani ba sai in kwananshi ne ya k'are. Yanzu kaga 11:49 PM, bari in kira Muhammad mu je gida"
Alhaji Sagir kallan Usman ya yi da jajayan idonshi sannan ya ce"Ina hajiya baturiya fa?" Ita da Muhammad ga shi nan za a fito da su mu tafi"
Alhaji Sagir da Usman suna nan tsaye aka fito da Muhammad da hajiya baturiya,hajiya baturiya hannunta rik'e da na likitar da ta dubata,inda Muhammad hannun shi ya ke rik'e da na d'aya daga cikin police d'in da Usman ya kira da ya ke abokinsu ne.Shiga su ka yi su ka tafi.
Hajiya baturiya na kuka kad'an-kad'an,in da kukan nata ke kuma d'aga hankakin Muhammad da alhaji Sagir.
Lura da hakan da Usman ya yi ne ya sa ya ce"Mommy,dan Allah ki yi hak'uri duk mai rai dama mamaci ne Hafsat lokacinta ne ya yi ,yanzu addu'a ya kamata mu bita da ita"Haka Usman ya yi ta lallashin hajiya baturi da kyar ya samu ta yi shiru.Shi ko uban gayyar Muhammad ajiyar zuciya kawai ya ke ja ,kallo daya za ke mai za ka hango tsantsar tashin hankalin da damuwar da ya ke ciki.Ahaka dai suka isa gidan alhaji Sagir mai shadda.Suna fitowa daga cikin motar dukansu suka nufi part din alhaji Sagir.Suna shiga idonsu ya yi tozali da photon Muhammad da Hafsat da ya ke manne jikin kusurwar d'akin,wannan photon da Muhammad ya gani sosai ya k'ara d'aga mai hankali hakan ya sa lokaci guda jikin shi ko ina ya fara rawa ,ko kafin Usman ya taro shi har ya yanke jiki ya fad'i awajan a sume.
Muhammad har gari ya waye bai farfad'o ba,hakan ya sa daddyn shi ya sa aka yi da shi wata private hospital dake kusa da su.
Gawar Hafsat ko anyi duk wani aune-aune da gwaje-gwaje da za ai an bada gawar dan a yi mata sutura .
Ko kafin a iso da gawar Hafsat gida gidan ya kuma cika da mutane dama kuma da akwai sauran mutane da ba su watse ba na biki.Isowa da gawar Hafsat sosai ya d'aga hankalin mutane,hakan ya sa gaba d'aya gidan ya rud'e da koke-koke.
Hajiya baturiya ko ta na ganin an shigo da gawar Hafsat ta yanke jiki ta fad'i.
Haka dai jama'a akaita koke-koke dan Hafsat kowa na tane bata da damuwa.
Cikin lokaci aka yi zana'idar Hafsar aka kaita gidanta na gaskiya ,in da aka bar folisawa da bincike.
Muhammad ko sai da ya yi sati biyu a asibiti kafin ya fara dawowa daidai.Yaune aka dawo da shi gida dan alhamdulillah jikin nashi,saidai rashin k'arfin jiki wanda hakan ya farune a dalilin rashin cin abinci da kuma rashin kuzari da ke faruwa da duk Wanda akai mai rashi irin haka.
Muhammad na zaune hajiya baturiya ta tasa shi kamar za ta yi kuka tana lallab'arshi akan ya daure ya ci abinci,ana cikin haka ne mahaifinshi alhaji Sagir da abokin shi suka shigo falon.
Alhaji Bala abokin Alhaji Sagir ,zama ya yi gefan Muhammad ya na dafa shi cikin alamun tausayawa ya ce"Muhammad, ka yi hak'uri ka ji ka saki ranka ka dawo rayuwa kamar da,Hafsat lokacin ta ne ya yi In ba haka ba babu wanda ya isa ya d'auki rayuwarta.
Haka alhaji Bala da mahaifin Muhammad suka ta sa Muhammad sai na siha da lallashi suke mai,amma har suka yi su ka gama Muhammad bai d'auki abinciccikin da aka aje mai a gaban shi ba ko d'aya.Haka suka gaji suka tashi suka barshi.
Falon Alhaji Sagir suka koma suka zauna,bacin sun zauna ne alhaji Bala ya kalli alhaji Sagir ya ce"Alhaji, ni fa ina ganin aima Muhammad wani auran cikin satin nan,kila a samu kwanciyar hankalinsa,dan gaskiya yanda na ga Muhammad abin ya ta da min hankali"
Shiru alhaji Sagir ya yi sannan zuwa can ya ce "Ni ma na yi tunanin haka? Amma wa zan aura wa Muhammad shi ne abun tunanin? " Maryam yarinyar wajena ita za a aura mai βπ»
π FADEELAH π
ππ
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπ*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen Hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
πͺπ»J.A.W πͺπ»
Na
Fadila Sani Bakori
SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki a cikin wannan littafi mai suna FADEELAH.
Page 3
Falon alhaji Sagir Suka koma suka zauna ,bacin sun zauna ne alhaji Bala ya kalli alhaji Sagir ya ce"Alhaji,ni fa ina ganin a yi ma Muhammad wani auran cikin satin nan ,kila a samu kwanciyar hankalinsa,dan gaskiya yanda na ga Muhammad abin ya tadamin hankali sosai"
Shiru alhaji Sagir ya yi sannan zuwa can ya ce"Ni ma na yi tunanin haka ,amma wa zan aura wa Muhammad ?Shi ne abun tunanin"
Maryam,yarinyar wajena ita za a aura mai cikin satin nan kuwa in sha Allah"
Mahaifin Muhammad hanun alhaji Bala ya kamo ya na cewa"Na gode sos...."Dakatar da shi alhaji Bala ya yi ta hanyar cewa"Haba ai yi ma kaine,babu godiya tsakaninmu dan na yi ma Muhammad wani abu"
KADUNA GARIN GWAMNA
Bikin Fadila yanzu saura sati shida inda har yanzu ta na kan bakarta na ba za ta auri Jamilu ba.Mahaifin Fadila ko ya ce babu gudu babu ja da baya aure kamar ma an yi sa ne.Haka aka ci gaba da shirye-shiryan biki.
Yau kwananan Jamilu goma kenan rabanshi da zuwa wajan Fadila,inda ko ya je shi ke kid'ansa shi ke rawar shi,Fadila ba ta tankamai.
Fadila na zaune ta yi shiru kamar kullum,k'anwarta ta zo ta sanar da ita Jamilu na d'akin Babansu wai ta zo. Tun da aka tsaida ranar auransu Mahaifin Fadila ya ce su rika shiga d'akinshi suna fira.
Fadila tashi ta yi ta sa hijab dinta ta nufi d'akin mahaifinta.
Fadila zama ta yi ba tare da ta tankamai ba.
Jamilu kallanta ya yi ya ce"Barka da zuwa malama Fadila,da fatan kina lafiya? Ina Kiran wayarki amma baki d'agawa,hankakina ya tashi na ce bari in zo in ji lafiya,daga nan inga kyakkyawar fuskarki"Ba na kusa ne"Fadila ta ba shi amsa a tak'aice,sannan ta d'ora da cewa"Jamilu,ina son in fallasamaka abin da ke cikin zuciyata,saidai babu lallai ba dole ka aminta da abin da zan ce,amma kuma duk abin da ya biyo baya ban yaudareka ba,kuma ban d'auki alhakinka ba.Magana guda d'aya ta gaskiya ita ce,Zuciyata ta kasa aminta da taka zuciyar,na yi iya k'ok'arin ganin na tursasata amma abin ya ci tura,atakaice har rauni na yi mata wajan jajircewa da bujire mata akan aminta da kai amma ta k'i,ina had'aka da girman Allah ka yi hak'uri ka hak'ura da zuciyar da ta kasa aminta da kai ka janye maganar da ke tsakaninmu,saboda ko ka aure ni zai zamana gangar jikina kadai zaka aura"
Jamilu shiru ya yi zufa na keto mai kota ina,daga k'arshe ma ba tare da ya tanka ba ya tashi ya tafi.
Yau sati d'aya kenan da Fadila ta sanar da Jamilu akan ya janye maganar auranta,saidai har yanzu ba ta ji wata magana ba mai kama da an janye
,saidai tun daga ranar Jamilu bai kuma kiranta a waya ba,saidai akwai abu d'aya da ta lura da shi mahaifinta kwana uku kenan baya amsa gaisuwarta,yau ne kuma ta k'udirci tuntub'ar mahaifiyarta dan jin ko ta yi ma mahaifinta wani laifi ne.
Mahaifiyar Fadila da daddare bayan ta idar da sallar magriba ta na zaune kan sallaya Fadila ta zo ta zauna gefan mahaifiyar tata,shiru-shiru kamar mai tunanin ta in da za ta fara,sannan ta ce"Mama,kwana biyu idan na gaida baba baya amsawa dan Allah ko na yi mai wani laifi ne Wanda ni ban sani ba?"
Mahaifiyar Fadila d'ago kai ta yi tana kallan Fadila,sannan ta girgiza kai ta ce"Tom,Fadila ni in kin yi mai wani abu ma ban sani ba,dan bai fad'amin ba,saidai in ya dawo ki je ki tambaye shi ki ji"
Fadila cikin marairaicewa ta kalli mahaifiyarta ta ce"Mama,dan Allah ki mai magana da kanki kin ga ni ba zan iya yi mai ba"Tom,shi kenan sai ki hak'ura ,dan nima ba zan iya yi mai ba."
Fadila haka ta hak'ura ta tashi.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya,in da ya rage har saura sati d'aya d'aurin auran Fadila kamar yadda mahaifinta ya sa.
Fadila ko yanzu abin da ke damunta bai wuce na gaisuwarta da mahaifinta ya bar amsamata ba.
Jamilu ko har yanzu tun da ta yi mai maganar nan bai kuma kiranta a waya ba.
Fadila har ya kama saura kwana uku biki bata ga ana wani shirye-shirye shirye na biki ba,haka ya tabbatar mata da babu bakin kenan,kuma dama ta dad'e tana zargin hakan.
Yau ne ya kama ranar da za'a daura auran Fadila kamar yadda mahaifinta ya tsaida,amma kuma shiru ka ke ji.
Fadila sosai ta yi murna da hakan,amma b'angare d'aya na zuciyarta cikin fargabar mahaifinta ta ke.
Da daddare Fadila na kwance mahaifinta ya aiko kiranta.
Fadila koda ta je ta dad'e a tsuk'unne ba tare da ya tanka mata ba,kamar ba zai tanka mata ba sai zuwa can ya ce"Fadila, kin maida ni karamin mutum, mutumin banza mai k'aramar magana,dama mutane na namin kallan wanda baisan abin da ya ke ba na je kamar ki a gida ba aure,idan an ce rashin mijine yanzu gashi mijin ya zo kin korai.Yanzu fad'amin me ye nufinki in ji?"
Fadila shiru ba amsa.Mahaifinta ko ya ci gaba da cewa"Fadila,Allah ya sa ni na fita hak'inki,na baki ilimin na addini da na zamani,na had'aki da mijin aure har uku duk kin k'i kin nuna min ke wayayyiyace ba aure ba ne a gabanki,dan haka ga mahaifiyarki nan ta zama shaida"Mahaifin Fadila dakatawa ya yi ya na kallan mahaifiyar Fadila,sannan ya ci gaba da cewa"Watan uku muke ko?"Kai mahaifiyar Fadila ta d'aga alamun haka ne. Ya ce "Kafin nan da k'arshan shekarar nan in dai Fadila ba ta kawo wanda take jin zata iya aura ba,Wallahi Allah d'aya na gama zama da ita acikin gidan nan,saidai ta san in da zata zauna amma ta gama zamam min a gida in dai wannan