Showing 33001 words to 36000 words out of 36765 words
"
Fadila da sauri ta amshe zance ta kuma cewa " mama , Allah ciwan kai ne da jiri " Daga Mahaifiyar Fadila har Aisha da kallo suka bi Fadila . Sai zuwa can mahaifiyar Fadila ta ce cikin sanyi " Aisha , lafiya wai ? " Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce " Mama tunda muka fito chamise din gaba d'aya Aunty Fadika ta rud'e " Tom , ko wani abun ya ce mata ne ? " Mahaifiyar Fadila ta tambaya .
" Da yake ba tare muka shiga ba , na gamu da Aunty zee muna gaisawa ita kad'ai ta shiga "
Mahaifiyar Fadila batare da ta kuma cewa komai ba ta d'akko hijab dinta a daki ta fita . Daga Fadila har Aisha da kallo suka bi ta .
Mahaifiyar Fadila chamise din da su Fadila suka je ta je . Bayan sun gaisa da mai chamise din ne ta tambayeshi abun da ke damun Fadila . Ya bata amsa kamar haka " Mama , gaskiya abisa alamomin yadda ta sanar da ni ciki ne , amma na sanar da ita ta je Asibiti a dubata ta gani "
Mahaifiyar Fadila a rud'e ta dawo gida dan tabbas idan bata manta ba cikin Ahmad ma haka Fadila ta yi , sannan yana yin laulayin nata yana kama da na mai cikin .
Mahaifiyar Fadila lokacin da ta isa gida jikinta ko ina rawa yake . Su Aisha na zaune ita da Fadila da itama har yanzu a rud'e take , ba kamar da mahaifiyarta ta fita ba dake ta k'ara rud'ewa dan tasan chamise din da suka je mahaifiyarta zata .
Mahaifiyar Fadila nuna Fadila ta yi tana cewa " Fadila , gwanne za ki a haihuwar shegen ? Ciki fa aka ce kina da shi , dan babu wata tantama alamun ki gaba d'aya ya nuna na masu ciki , nima so kike ki kasheni kamar yadda kika kashe mahaifinki ? Fadila , mu zaki tozarta a idan duniya ? Tom Ina rok'on Allah ya tsaida wannan tozarcin da kike kok'arin yi mana akan ki ke kad... " Aisha da sauri ta rufe bakin mahaifiyarsu tana kuka ta ce " Mama , dan Allah duk abin da zaki mata ki yi mata amma karki mata baki dan Allah "
Mahaifiyar Fadila kallan Aisha ta yi tana kuka ta ce " Aisha , shi kenan ba zan yi mata baki ba , amma Wallahi idan duniya zata taru akaina bazan zauna da Fadila ba , kodai tabar gidan nan ko kuma ni in bar muku gidan . Aisha , tun yanzu shiga mutane yana naiman gagarata duk in da na yi nunani ake , naga alamar so take ta maida mu abun kwatance a idon duniya gwanne fa Aisha ! Watan Ahmad nawa Aduniya ? "
Usaini wanda ke bima Aisha ma kuka ya sa cikin kukan yana cewa " Wallahi Mama rannan da mu kai fad'a da abokina gori ya yi min wai su gidansu ba a aje abun kunya ba , gaskiya Aunty Fadila , gara ki tafi kawai da ki maida mu abin kwatance a unguwa "
Fadila ko badan kuka ta kasa cewa komai .
Mahaifiyar Fadila ko da yake irin iyayannan ce masu zafi ta ce cikin hargagi " Fadila , ki fita nace ke ba mai son shiryuwa ba ce gwanne acikin shege ? Wallahi ba zan zauna da ke ba ki zo ki fita in bar ganinki ! "
Fadila tashi ta yi jikinta na rawa kota ina ta ce " Mama , ki yi hak'uri ba da sanina ba ne amma zan sanar da ke iya abun da na sani " Bana buk'ar jin komai daga gareki ki ! ki fita kafin in miki illah "
Mahaifiyar Fadila da yake bata iya bacin rai ba ganin Fadila har yanzu bata fita ba , da sauri ta fita sai gata da wata sanda ta shigo , tana shigowa kuma ta yi kan Fadila da ita .
Aisha cikin tsoro da gigita ta rik'e sandar katakam tana kuka ta ce " Mama , dan Allah ki daure ki saurareta ki ji abun da zata ce " Aisha ki sakar min sandata kafin ranki ya b'ace " Fadila ko ta d'are can k'arshen gadonsu tana kuka jikinta ko'ina kakkarwa yake kamar mai jin sanyi .
Aisha cikin kuka ta kuma cewa " Mama , dan Allah ki yi hak'uri kar ki buga mata za ki mata illah fa "
"Shi kenan , na hak'ura amma ta d'auki Ahmad su fita bana son ganinsu duka " Cewar mahaifiyarsu Fadila .
Aisha cikin sanyi ta ce " Mama , dare ne fa idan kika koreta ina zata ? "
Mahaifiyar Fadila cikin b'acin rai ta wanka ma Aisha mari ta ce " Dan ubanki ba zaki sakeni ba , Duk in da zata ta je, ana tattalin abun da bai riga ya lallace bane , wanda kuma ya riga lallace me ye amfanin ? me ye abun tsoro dan ta fita cikin daran ? "
Aisha tsabar jin zafin Marin da mahaifiyarsu ta yi mata ya sa ta saki sandar bata sani ba . Tana ko sakin sandar mahaifiyarsu ta yi kan Fadila da ita ta ta buga mata wanda ya sa Fadila ta fasa ihu jin zafin saukar sandar a goshinta .
Mahaifiyarsu Fadila ta d'aga zata k'ara buga mata ne , Usaini da Aisha suka rik'e sandar suna kuka .
Duk yadda mahaifiyar Fadila ta yi akan su saketa sun k'i dan sosai suka rud'e yadda suka ga ta fasa ma Fadila goshi.
Wata mak'ociyarsu Fadila jin hayaniya ta yi yawa a gidansu Fadila shigowa ta yi tana tambayar lafiya .
Bud'ar bakin mahaifiyarsu Fadila sai cewa ta yi " Gwanne za ta yi min ! " Ciki ! ? to fa " Matar na fadin haka ta lallab'a ta bar gidan .
Aisha kuma cikin takaici ta ce " Haba , mama wannan wana kalar b'acin raine wanda zaisa ki tona mana asiri " Tonan asiri kuma na nawa ? Asiri ya gama tonuwa ai "
Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce " Mama , dan soyayyarki da annibi Muhammadu ( S . A . W ) ki yi hak'uri mu saurari abun da Aunty Fadila zata ce ? "
Mahaifiyar Fadila shiru ta yi bata kuma magana ba sai ajiyar zuciya da take saukewa .
Aisha kuma ta ce " Aunty Fadila , muna jinki "
Fadila da kyar ta iya bud'e baki ta ce " Aranar da zan dawo gidan nan da zama tabbas na yi zargin MD ya aika wani abu dani dan ya bani Yoghurt na sha kuma tunda na sha Yoghurt din bankara sanin kaina ba sai bayan dogon lokaci "
Fadila ta idasa maganar da kyar .
" In dai ko haka ne ya zama dole mu yi karar MD " Cewar Aisha .
Mahaifiyar Fadila dai bata tanka ba ta tashi ta fita ta koma d'akin ta .
Bayan mahaifiyar Fadila ta fita ne Aisha ta d'auki Ahmad da ke kuka ta goya shi .
Atakaice dai ranar gidan babu wanda ya yi barcin dadi .
Washegari Aisha da wuri ta shirya bayan ta shirya ne ta kalli Fadila ta ce " Aunty Fadila , nifa na shirya ki zo mu je sharia court mu kai karar MD can, za su kwatar miki hak'inki "
Fadila tashi ta yi ta zumbula hijab dinta suka tafi .
Su Aisha na zuwa wani lawyer ya buk'aci su bada kud'in shigar da k'ara , dama Aisha ta taho da kudi a hannunta ta mik'a musu . Nan Fadila ta bada address d'in MD .
Aranar aka kaima MD takaddar sammaci βπ»
SANARWA : Saura page d'aya in gama free page , idan biki biya ba ki hanzarta .
# 300 ne kacal ππ»
My Number 08063830828
π FADEELAH π
ππ
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπ*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
πͺπ»J.A.W πͺπ»
Na
Fadila Sani Bakori
SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban - daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafin mai suna FADEELAH .
*π€ SDEENDTM DATA SERVICESπ€*
*MTN* . *Airtel*
1GB = β¦300. 1GB = β¦300
2GB = β¦600. 2GB = β¦600
3GB = β¦900. 3GB = β¦900
4GB = β¦1200. 4GB = β¦1200
5GB = β¦1500. 5GB = β¦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = β¦350. 500Mb β¦250
2GB = β¦700. 1GB β¦500
3GB = β¦1050. 2GB β¦1000
4GB = β¦1400. 3GB β¦1500
5GB = β¦1750. 4GB β¦2000
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½
*πͺ08066268951*
Last free page 13
Aranar aka kai ma MD takaddar sammaci.
MD koda ya gama duba takaddar sammaci ya ji dalilin k'arartasa , waya ya ciro ya Kira Fadila .
Fadila lokacin sun koma gida babu dad'ewa Kiran MD ya shigo wayarta , nuna ma Aisha ta yi , Aisha ta ce " Ki d'auka ki ji abun da zai ce miki " Fadila d'agawa ta yi .
MD cikin lallashi ya fara magana kamar haka " Haba , Fadila tsakanina da ke kuma me ya yi zafi wanda har sai an had'a da kotu ? Indai maganar Ahmad ce ni na ji ki janye k'arar zan mai komai na rayuwa , kuma ai ba gazawa na yi da hidimominsa ba bare kice . Ni dai yanzu rak'on da nake miki ki janye karar nan zan zo mu sasanta aji yadda za a yi " Ba ni na kai ba iyayena ne " Cewar Fadila.
MD shiru ya yi sannan ya ce " Amma hakan ba kya ganin karar tonuwar asirinki ne ? , ki yanje karar nan ni kuma na yi miki alk'awarin zamema Ahmad Uba harda wanda zaki haifa ma , kuma duk abin da uba ke yi ni zan musu , na yi miki alk'awain ba za su tab'a kukan rashin uba ba " Ba ni na kai kara ba ba ni da ikon janyewa " Ok , shi kenan , inda na biki ta lallama kin k'i mu je kotun sai me " MD na fad'in haka ya kashe wayarsa .
Fadila bin wayar ta yi da kallo .
Aisha kallan Fadila ta yi ta ce " Aunty Fadila , ina tsoran kar mu je kotin ma ya kadamu dan naga alamar yana da baki " Hmm, Aisha Allah ya fishi " Cewar Fadila .
Washegari ya kama za a gabatar da k'ararsu Fadila .
Fadila sammakon tashi su ka yi suka je Asibiti kamar yadda lawyer da suka samu ya ce su zo da takardar shaidan ciikin jikinta . Bayan sun dawo asibitin ne Aisha ta kalli mahaifiyarsu ta ce " Mama , kin ga ko ba aje kotu ba gaskiya fa ta bayyana , Ahmad da cikin jikin Aunty Fadila duk na MD ne , saboda kin ga cikin wata biyu suka ce , kuma wata biyu kenan da dawowar Aunty Fadila gidan nan " Mahaifiyarsu Fadila kamar ba zata tanka ba sai zuwa can ta ce " Aisha , ni dai abun da nake so indai gaskiya ta bayyana to dan Allah karku dawo da Ahmad ku bashi d'an shi , cikin jikinta ma daga ta haihu zata bashi abun shi " Tom, mama ki mana addu'a mun tafi " Cewar Aisha .
Kutu ta cika duk wani wanda ake buk'a ya halarta har MD ma ya zo .
Kasan cewar kotun kotun musulinci ce ya sa aka fara gabatar da k'ararsu babu wani bata lokaci . Inda aka sanar da MD dalilin da ya sa Fadila take k'ararsa. Inda MD ya fara kare kanshi kamar haka " Eh , tabbas ni na san Fadila na zargina da cewa Ahmad da kuma cikin jikinta na yanzu duk naune , amma kuma a hak'ik'agin gaskiya ba haka bane , ina tausayin Fadila ne shi ne silar yimata komai da nake yi wanda ya janyo min zargi a wajanta , ni kuma da harda yaran da zata haifa ashirye nake da in taimaka mata akan shi , saboda kasan cewarta marainiya , hakan da nake mata dan tausayi shi ne ya jawomin zargi a wajanta , amma a hak'ik'agin gaskiya bani jib'i da Ahmad da kuma cikin dake jikinta yanzu haka "
Alk'akin kai ya jinjina sannan ya ce " Aranar da Fadila zata bar gidan da ka bata ta zauna ka kawo mata wani yoghurt wanda tana shansha jinta da ganinta ya d'auke , inda take zargin ka yi anfani da haka ne dan ka cika burinka akanta, me za ka ce akan hakan ? " Eh , haka nima tace min , kuma tabbas na kawo mata yoghurt , amma maganar gaskiya ni ban mata komai ba kamar yadda take zargi "Cewar MD.
" Amma kuma tana shan yoghurt d'in barci ya kwasheta kuma kafin haka ta ji lokacin da ka riketa kamar yadda ta ce , shi fa me za ka ce akan haka ? " Cewar alk'alin .
Nan ma dai MD ya fara kawo hujjojinshi kamar haka " Eh , nima tace min haka wai ta ji lokacin da na rungumeta amma a hak'ik'anin gaskiya ni ban rungumeta ba , nafi tunanin hakan ya zo mata a mafarki ne "
Alk'akin kotun kai ya jinjina sannan ya ce kamar yadda kuka sani dai ana yi a kotun musulinci ga duk shari'a da ta gagara sanin ainihin gaskiya . Alk'akin ya kalli MD ya ce " Yanzu zaka iya rantse mana kenan da al'qur'ani akan Ahmad da kuma abin da ke cikin Fadila ba kai bane mahaifinsu ? " Shiru MD ya yi ya fara waige - waige kamar mai neman wani . Alk'alin jin ya yi shiru ya kuma cewa " Shin zaka iya rantsuwa da al'qur'ani ba kai bane mahaifin Ahmad da cikin dake jikin Fadila kamar yadda take zargi ? " Nan ma dai MD shiru ya yi kamar mai nazarin wani abu , sannan ya ce " Eh , zan iya rantsuwa " Zaka iya rantsewa da alqur'ani mai girma ? " Eh , z..a..n.. iya " MD ya fad'i maganar yana rawar baki .
Alwalla aka raka MD ya je ya yi , bayan ya dawo ne aka bashi Al'qur'ani mai girma . In da MD ya amshi Al'qur'anin jikinshi ko ina ya na rawa .
Inda aka Umarci MD da duk abin da aka ce ya maimaita . Nan mai gabatar da rantsuwar ya fara jero mai kamar haka " Ka ce Ka rantse da wannan Al'qur'anin da ke hannunka baka tab'a kusantar Fadila ba , sannan ba kai bane mahaifin Ahmad da cikin jikinta , idan kuma kai ne ka b'oye Allah ya sa wannan Al'qur'anin ya cika , Allah ya hanaka abun da kake nema duniya da lahira , Allah ya nisanta ka da duk rahamominsa " Haka MD ya nanata kamar yadda mai karanto mai ya karanto , inda MD ya idasa maganar jikinshi ko ina yana rawa ga zufa da ke keto mai kota ina, wadda hakan ya ba kowa mamaki .
MD na kai rantsuwar Alk'alin ya kalli Fadila wadda ke kuka ya ce " Fadila , babu zargi yanzu kan MD saboda ya yi rantsuwa da Al'qur'ani mai girma , dan haka ya wanke kanshi daga zargi "
Alk'alin na fad'in haka ya tashi .
Fadila kuka take sosai , inda Aisha ma kukan take , sannan ita ta lafa da nata ta kamo hanun Fadila ta ce " Ki tashi mu tafi " Fadila tashi ta yi , sun zo k'ofar da za su fita ne su ka ci karo da MD , MD kallan Fadila ya yi ranshi b'ace ya ce " Fadila , da ace kin ji maganata biki kawoni nan ba da na rufamiki asiri , amma yanzu ki sani natsame hannuna akan duk abin da ya shafeki dake da Ahmad har da ma wanda zaki haifa " Fadila kai ta d'aga tana kallan MD sannan ta ce " Ka ji tsoran Allah MD , ka amshi cikin jikina ko ba zaka amshi Ahmad ba , ni nasan cikin jikina naka ne koda ko zaka had'iyi Al'qur'ani ne , saidai da ya ke ka kasance cikin marasa tsoran Allah masu rantsuwa akan k'arya ka ji tsoran Allah" MD kallan Fadila ya yi cikin tausasa zancesa dan sai kuma ya ji tausayinta ya ce " Fadila , bani da jib'i akan cikin jikinki shi ne gaskiyar lamari , na so in ci gaba da taimakonki saidai gudin zargin zama'a akaina ba zan iya ba , ina miki fatan alkairi sai watarana duk da nasan akwai ranar da zaki sake naimana " MD na fad'in haka ya yi tafiyarshi da sauri "
Aisha hannun Fadila ta ja suka tafi .
Mahaifiyar Fadila a gida ko ta k'osa su Fadila su dawo ta ji yadda suka k'arke . Tana nan zaune su Fadila suka shigo . Mahaifiyarsu Fadila tashi ta yi da sauri tana kallan Aisha ta ce " Aisha , ku tsaya daga nan kusanar dani yadda ake ciki ? " Aisha cikin kuka ta zayyana ma mahaifiyarsu duk yadda aka yi.
Mahaifiyar Fadila kallan Fadila ta yi ta ce " Fadila , zan miki wata alfarma guda d'aya, zan ci gaba da zama dake