Showing 9001 words to 12000 words out of 36765 words
har'abada ba za mu sake ganinta ba sai a mafarki, ka yi hak'uri ka amshi Maryam wadda mahaifinta ya baka ita dan samun kwanciyar hankalinka kaga baikamata mu zuba masa k'asa a ido ba, da Maryam da Hafsat duk kusan d'aya ne awajanja, yadda Hafsat take k'anwarka Maryam ma k'anwarka ce ahankali watarana za ka sota itama "
Haka dai suka taru suka yi ta ba Muhammad ba ki a haka suka samu ya tashi.Saidai ana dubawa kuma ba Maryam.
Alhaji Sagir kallan Hajiya Baturiya ya yi ya ce " Ina Maryam d'in fa? "
Hajiya Baturiya cikin mamaki ta ce"Muna nan tare da ita fa bari in dubata muga "
Hajiya Baturiya a falonta ta iske Maryam ta kifa kai a kan caution sai kuka take.
Hajiya Baturiya da sauri ta k'arasa wajan Maryam tana d'agota tana cewa "Haba Maryam ki yi hak'uri kin ji ki yi ma Muhammad uziri , har yanzu yana cikin damuwar rad'ad'in mutuwar Hafsat, kuma yadda abin ya yi kusa babu nisa tsakani dole sai kin yi hak'uri har ya fara mantawa, kin ji 'yata ? "
Maryam d'aga kai ta yi.
Hajiya Baturiya ta ce"Yauwa, ko ke fa , share hawayanki "
Hajiya Baturiya tana rik'e da hannun Maryam suka k'arasa har in da Usaman ya yi parking suna jiran Maryam.
Suna zuwa Maryam ta shiga suka yi musu sallama su ka tafi.
Suna zuwa k'ofar gidan masu gadin suka bud'e musu suka shiga tank'ameman falon amaryar wanda ya ji kayan alatu da abubuwan more rayuwa.
Maryam ko har yanzu ta kasa na tsuwa ta saki jikinta, dan ta gama furgita da jin kalaman angon nata akan marigayiyar amaryarshi .
Usman lura da hakan da ya yi ne, ya kalli Muhammad da ke kwance kan three seater kanshi a sama kamar wani sabon maraya ya ce"Muhammad, da farko dai ina son in ce maka ka ji tsoran Allah ka rik'e Maryam amana, Hafsat kuma a halin yanzu tana buk'atar addu'arka ne ta haka ne zaka nuna mata soyayyar da kake mata, amma kukan da kake yi mata azaba ne a gareta,Manza Alllah (S.A.W) Ya ce ana ma mamaci a zaba da kukan wanda yake da rai"
Shiru Usman ya yi sannan ya maida kallanshi gun Maryam ya ce" Maryam, na dawo gareki, da farko dai abun da nake son in ce miki , sai kin daure kinsa hak'uri da juriya kafin ki samu komai ya wuce, ki daure kar ki sa gajiyawa dan Allah. Ina mai yi miki albishir d'in za ki ji dad'in zama da abokina , Muhammad ba shi da wata matsala ga shi da tausayi da son fita hak'in duk wanda wata hurd'a ta had'a shi da shi, hakan ne ya sa nake mai kyakkyawan zaton adalci agareki , sboda shi d'in adaline mai tausan na k'asa da shi "
Usman sosai ya yi musu nasiha da jan hankali akan zaman aure sannan ya tafi.
KADUNA GARIN GWAMNA
Fadila cikin sanyi ta k'arasa office d'insu, kasan cewar Jamilu ya sanar da dawowar Fadila aiki babu wani mamaki da abokan aikinta su ka yi.
Bayan sun gaggaisa ne, Jamilu ya fara nuna ma Fadila shirin da za su tattauna yau akan shi.
Fadila na zama babu dad'ewa ,Jamilu ya kalleta ya ce"Lokaci fa ya yi mu je "
Kamar yadda kuka sani kuke kallo haka Fadila ta fara gabatar da Shirin da take aiki akai.
Zaune take ad'akin gabatar da Shirin nasu ga masu aikin d'aukar shirin, komai dai an shirya kamar dai yadda kuke kallo a TV.
Fadila ta fara magana kamar haka"Assalamu alaikum barkamu da sake saduwa da ku acikin shirinmu mai suna DARAJAR 'YA MACE, wanda ni Fadila Sani nake gabatar muku tare da Jamilu Hassan.DARAJAR 'Ya mace,in ji Hausawa suka ce aure "
Yau za mu yi bayanine akan ta yarda ake gane fiffofin mace mai daraja.
Fadila mai da kallanta ga Jamilu ta yi ta ci gaba da magana kamar haka, "Malam Jamilu, shin taya ake gane siffofin mace mai daraja? "
Jamilu mai da kallan shi ya yi ga camera ya fara bayani kamar haka "Da akwai alamu da dama da ake gane wannan ita ce mace mai daraja, ana gane mace me daraja ne ta hanyoyi da daban-daban, amma zan kawo kad'an daga ci:
Ana gane mace mai jaraja ta yanayin maganarta, ko ta d'abi'unta, yanayin maganarta da mutane da kuma mu'amalarta da mutane, da kuma yanayin suturar da take sawa , da kuma yanayin abokan hurd'arta "
Jamilu kallan Fadila ya yi ya ce " Wannan suna daga cikin siffofin mace mai daraja "
Fadila cikin gamsuwa ta ce" Wasu hanyoyi zan bi dan in kasance d'aya daga cikin mata masu daraja ? "
"Duka-duka dai anan muka kawo k'arshen shirinmu mai suna DARAJAR 'YA MACE.
Ku kasance da mu acikin mako na gaba dan jin yadda za ki kasan ce mace mai daraja"
Bayan su Fadila sun gama gabatar da Shirin DARAJAR 'YA MACE ne, ta kalli Jamilu ta ce"Jamilu, MD fa ya matsamin, d'azu hanani fitowa office din shi ya yi wai sai na fad'a mai matsayin shi a guna, da narasa yadda zan ce mai shi me nace zan baka sak'o ka ba shi, yanzu mi kake ganin zan ce mai? Allah ya sani bana son shi "
Jamilu shiru ya yi sannan ya ce"Ni kuma da zan baki shawara sai in ce ki hak'ura da shi , kin ga kin fada min yarda kuka yi da iyayanki, ki amshi tayin soyayyar MD kodan ki rik'a aikin ki cikin dad'in rai, K'in amsa tayin nashi ina tsoran kar ya jawo mik wata matsala anan, dan haka zance masa kin amince "
Shiru Fadila ta yi tana kallan Jamilu sannan ta ce "Amma kasan Ina sonsa ba wai yana nufin zan aureshi ba ne ?" Eh, na sani , kuma shi ma ya san hakan" Cewar Jamilu.
Haka dai Jamilu ya yi taba Fadila shawara akan Ogan nasu.
ADAMAWA STATE
Bayan Usman ya tafi Falon ya yi shiru sai kukan Maryam da ke tashi kad'an-kad'an. Muhammad tashi ya yi ya barta a wajan ba tare da ko in da take ya kalla ba.Hakan sai ya kuma in giza Maryam ta ci gaba da kuka, haka dai ta ci kukanta ta gaji babu mai lallashi, karshe da ta gaji ta yi shiru.
Yau satin Maryam d'aya kenan a gidan ,amma kusan har yanzu ban da gaisuwa babu wata kwakkwarar maganar da ke shiga tsakaninta da Muhammad.Saidai yanzu ya fara sakin ranshi ba kamar daba,in da yana fita sosai kuma takan ji suna fira da Usman in ya Kira shi a waya, haka Alhaji Sagir ma da Hajiya Baturiya duk ya fara sakin rashin su yi fira in sun zo.
Maryam a yarda ta lura kusan da ita kad'aice baya sakin jikinshi da ita .
Tun da Maryam ta zo gidan daga gidan Alhaji Sagir mahaifin Muhammad ake kawo musu abinci kullum, amma yau ta k'udiri a niyar da kanta zata shiga kitchen ta yi musu girki.
Koda ta shiga kitchen d'in kusan a kwai komai na buk'ata ,so take ta yi abin da zata burge Muhammad wanda zai ci kuma ya ji dad'in shi, saidai bata san wana kalar abinci ya fi so ba.
Wayarta ta d'akko ta kira Hajiya Baturiya, bayan sun gaisa ne ta ce"Mommy, ina son in shiga kitchen ne yau in mana girki, tom ina son in yi wanda Muhammad zai ji dad'in shi ne sosai shi ne na kira in fambayeki best food d'in shi"Hajiya Baturiya dariya ta yi sannan ta ce"Taliya da miyan kwai shi ne girkin da Muhammad ya fi so"
Atak'aice Maryam ta shiga kitchen ta dafa mai taliyan ta soya mai miyan k'wan.
K'arfe shida Muhammad ya dawo, saidai yana dawowa ya yi alwallah ya fita.
Bashi ya dawo ba sai da ya yi sallar issha'i acan,dan Muhammad akwai ibada.
Maryam zaune take a falon tana jiran shigowar Muhammad.Sanye take da abaya jikin abayar baki d'aya ya sha ado da stones.
Maryam na nan Zaune Muhammad ya shigo, hanyar steps d'in bedroom d'in shi ya yi Maryam ta yi saurin cewa"Ga abinci na girka maka" Bana buk'ata na koshi" Muhammad ya ce atak'aice ya yi tafiyar shi ya bar Maryam nan tsaye.
Maryam d'akko kulan abincin ta yi ta bi Muhammad da shi.
Yana zaune ta yi sallama shiru ya yi mata baice ta shiga ba, da ta gaji da tsayuwa shiga ta yi.
Muhammad da ido ya bita da kallo,alamin lafiya.
Maryam aje kulan abincin ta yi, ta fita ta d'akko plate d'in da zata samai aciki.
Bayan ta dawo ta bud'e kulan ta zuba mai taliyan da miyan kwan,sannan ta kallai ta ce"Na zab'i in yi abin da ka fi so ne dan ka ci , dan Allah karka ce ka k'oshi ko d'iba daya ka yi ka ci zan ji dadin hakan, sannan in samu ladar ciyar da mai gida" Maryam ta idasa maganar a hankali tana murmushi.
Muhammad kallanta ya yi ya ce"Waya ce miki ina son taliya?" Mommy na tambaya"
Kasan cewar Muhammad nasan taliya sosai kuma dama kusan bai ci kimai ba, hakan ya sa ya fara cin taliyar.
Yana tsak'ar cin ne Kira ya shigo wayar shi, yana ganin mahaifin shi ne ya tuna da kiran da yake mai, kafin ya d'aga Kiran ya katse.Muhammad kallan Maryam ya yi ya ce "Zani gida zan dawo yanzu "
Muhammad na fad'in haka ya aje abincin ya tafi.
Allah sarki Maryam sai ta ji dad'in sanar da ita din da Muhammad ya yi,dama in bata manta ba abokinshi ya ce mata yana da sauk'in kai ba shi da damuwa tabi a hankali zata samu kanshi.
Muhammad koda yaje mahaifinshi ya yi mai magana ne akan tafiyar da zaiyi Lagos gobe zai yi kwana biyu ya dawo.Haka dai suka d'an zanzanta sannan ya tafi, tare da mai alk'awarin zai zo ya kai shi airport.
Misalin k'arfe Tara Muhammad ya shigo, yana shiga direct bedroom d'in shi ya yi.
Muhammad cikin tsananin furgici da tashin hankali ya ke kallan Maryam da ke kwance male-male cikin jiniβπ»
π FADEELAH π
ππ
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπ*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
πͺπ»J.A.W πͺπ»
Daga
Fadila Sani BaBakori
*π€ SDEEND MTN DATA SERVICESπ€*
*MTN* . *Airtel*
1GB = β¦300. 1GB = β¦300
2GB = β¦600. 2GB = β¦600
3GB = β¦900. 3GB = β¦900
4GB = β¦1200. 4GB = β¦1200
5GB = β¦1500. 5GB = β¦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = β¦350. 500Mb β¦250
2GB = β¦700. 1GB β¦500
3GB = β¦1050. 2GB β¦1000
4GB = β¦1400. 3GB β¦1500
5GB = β¦1750. 4GB β¦2000
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½
*πͺ08066268951*
SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .
Page 5
Muhammad cikin tsananin furgici da tashin hankali ya ke kallan Maryam wadda ke kwance cikin jini an mata yankar rago.
Tsananin tashin hankali da furgici ya sa Muhammad ko kukan ma ya kasa yi.Zuwa ya yi yana ta girgiza gawar Maryam da ke kwance cikin jini.
Zuwa can kuma ya fad'i gefanta a sume.
Washegari alhaji Sagir ya yi ta sauraran zuwan Muhammad ya kai shi airport kamar yadda su ka yi zai zo ya kai shi amma shiru .Hakan ya sa ya kira Muhammad d'in a waya.
Alhaji Sagir sai da ya yi ma Muhammad kira hud'u amma bai d'auka ba, take hankalin Alhaji Sagir ya tashi.Kallan Hajiya Baturiya ya yi ya ce" Anya ko Muhammad lafiya na kira shi bai d'auka ba?" Tom, ka kira matarshi Mana" Cewar Hajiya Baturiya .
Alhaji Sagir Maryam ya Kira, itama dai ta b'angaranta haka ya yi ta Kira ba ta d'auka ba.Take jikin alhaji Sagir ya fara rawa ya ce "Ina ji ajikina babu lafiya na kira Muhammad bai d'aga ba haka Maryam ma "
Alhaji Sagir ya na maganar ya na tafiya da sunan za shi gidan Muhammad d'in.Hajiya Baturiya da sauri ta taro shi tana cewa "Alhaji, ka kwantar da hankakinka babu abin da zai samu Muhammad in sha Allah, bari in zo in yi driving d'inmu yadda ka rud'e haka ai ba zaka iya tuk'i ba"
Hajiya Baturiya ita ta tuk'asu duk da itama hankakin nata a tashe yake dan ta kusa yaddasu .
Suna tafiya a mota Alhaji Sagir ya na kuma Kiran numbobinsu amma shiru.
Suna zuwa Alhaji Sagir ya tambayi masu gadin cewar jiya ko sun ga dawowar Muhammad.Suka amsa mai da "Eh"
Ya ci gaba da cewa "Lafiya dai ko babu wani abu da ya faru?" Nan ma suka amsa mai da"Eh,ranka shi dade babu abin da ya faru wani ne ya ce maka wani abu ya faru ne ?"
Alhaji Sagir bai amsa musu ba ya nufi in da zai sadashi da k'ofar falon Muhammad d'in.
Saidai babu kalar bugun da ba su yi ba amma shiru.
Hajiya Baturiya na ganin haka tasa kuka cikin kuka take cewa "Na shiga uku sun kashe mana Muhammad" kukan Hajiya Baturiya ne ya sa d'aya daga cikin masu gadin ya k'araso yana tambayar " lafiya? "
Alhaji Sagir goge zufar da ke feso mai ya yi ya na nuna mai k'ofar falon alamun ya bud'e mai ita.
Babu kalar jijjigawar da bai yi ma kofar ba amma tak'i bud'uwa, saida ya Kira wani daga cikin su suka taru suka bud'e k'ofar da kyar.
Alhaji Sagir da Hajiya Baturiya atare suka shiga cikin hanzari.
Koda suka shiga bedroom d'in Muhammad lokaci d'aya tsoro,ranaza,tashin hankali ya mamaye zukatansu...
Hajiya Baturiya da gudu ta yi kan Muhammad da ke kwance babu alamun rai a jikin shi tana jijjigashi .
Alhaji Sagir gun Muhammad ya yi da niyyar amsarshi daga hannun Hajiya Baturiya jiri ya dibai ya yanke jiki ya fad'i, dan a tunanin shi Muhammad d'in ya mutu ne.
Mutum biyu daga cikin masu gadin gidan jin alamun kuka suka biyo bayan su Hajiya Baturiya suka shigo .Sosai suka rud'e ganin gawar Maryam kwance ak'asa an mata yankar rago.
D'aya daga cikin su ne ya yi ta maza ya kira office d'in su ya sanar da su.
Cikin lokaci motar folisawa ta iso gidan.
Atak'aice dai nan 'yan sanda su ka yi bincike- binciken su sannan suka d'auki gawar su ka yi asibiti da ita.
Duk wani bincike an gudanar akan gawar Maryam sannan aka yo gida da ita.
Haka aka yi zana'idar Maryama aka kaita gidanta na gaskiya. Har aka yi aka gama daga Alhaji Sagir har Muhammad basu san abin da ake ba saboda allurar barcin da likita ya yi musu.
Iyayan Maryam lokacin da idonsu ya yi tozali da gawar Maryam sun yi kuka sosai da danasanin had'a auran Maryam da Muhammad da su ka yi.
Muhammad ba shi ya farkaba sai gaf magriba, inda Alhaji Sagir har lokacin baisan wanda ke kanshi ba sai can cikin dare ya farka.
A wannan lokacin abin ya fi tab'a Alhaji Sagir dan har ya farka baya magana, saidai ya kalli mutane.
Muhammad na kwance kan shi a sama, yana tunanin me ke faruwa da rayuwar shi haka ne. Yana a wannan yanayin ne Hajiya Baturiya ta shigo. Kallan Muhammad ta yi tana shafa kan shi ta ce "Muhammad, kar ka sa kanka cikin tunani wani mugun ciwan ya zo ya kamaka, sannan ni kaina idan ina ganinka haka hankalina ba zai kwanta ba"
Muhammad tashi ya yi ya zauna yana kallan
Hajiya Baturiya ya ce "Mommyna, soda dama ba zafin ciwo ake ma kuka ba, tunanin halin da ake ciki ne .Sannan, mommy duk jarumtar Jarumu ba kowana rad'adi yake iya juremawa ba" Hajiya Baturiya kai ta d'aga ma Muhammad alamun haka ne, ya ci gaba da cewa "Mommyna, na rasa yadda zan lallashi kaina in yi hak'uri da rashin Hafsat a rayuwata. Amma da na yi wani nazari sai naga ko ba wannan lokacin ba Hafsat zata mutu watarana,sai na yi tunanin fara ba kaina hak'uri in amshi Maryam a matsayin mata, saidai ina cikin tunanin hakan ne zuciyata na gaf da amince min da ita suka kasheta suka rabani da ita itama" Muhammad shiru ya yi kamar mai tunani ko mai son tuna wani abu, sannan ya ce"Mommy! Su waye ne? Waye ya kashe su? Me su kai musu ? Shi nake son san..." Hajiya Baturiya rufe bakin Muhammad ta yi tana kuka, ta ce "Ka yi shiru Muhammad, karka sa kanka cikin wata damuwar, koda ace abin da mahaifinka ya mallaka zai kare ne sai an binciko wa inda suka aika haka, ni na san haka. Ka tashi mu je ka ga mahaifinka abun nashi ya fara bani tsoro, baya magana tun da ya farka na yi na yi ya k'i yin magana"
Muhammad cikin daure yadda yake ji da tsoran karya rasa mahaifin shi ya nufi bayan Hajiya Baturiya suka yi falon Daddynshi.
Kwance ya samu mahaifin nasa kansa a sama kamar mai k'okarin tuno wani abun da ya shege mai .
Muhammad cikin k'arfin hali ya kalli mahaifinshi ya ce"Daddy, ka tashi ka ci abinci plz"Alhaji Sagir da sauri ya mai da kallan shi kan Muhammad .
Ya dad'e yana kallan Muhammad d'in sannan ya ce "Muhammad, ka ci abinci kai ?" Kai Muhammad ya d'aga mai.
Muhammed Hajiya Baturiya ya sa ta kawo mai tea ya ba Alhaji Sagir. Kad'an dai su ka samu ya sha.
BAYAN SATI D'AYA DA RASUWAR MARYAM .
Ma sha Allah. Yanzu Alhaji Sagir da Muhammad sun fara kwantar da hankalinsu.
Bincike ko har masu gadin gidan an kama amma babu wata hujja ko d'aya da aka samu daga kan rasuwar Hafsat har ta Maryam.
KADUNA GARIN GWAMNA.
Yau Sati d'aya