Showing 18001 words to 21000 words out of 36765 words
irin kallo na kyama ta ce " Aunty Fadila , dama fuska biyu gareki? kullum maganarki akan mutunci hasalima aikin da kike yi duk dai magana d'aya ce nan ma maganarki kullum DARAJAR 'YA MACE ashe ke ba ki da DARAJAR da kike yawan b'ab'atu akanta, da haka kika yi amfani kika yaudari Iyayanmu " Shiru Aisha ta yi tana goge hawayanta, sannan ta ci gaba da cewa " Amma basu kika yaudara ba kanki kika yaudara "Kuka Fadila take yi sosai , da kyar ta bud'e baki za ta yi magana , Aisha ta d'aga mata hannu ta ce " Aunty Fadila, babu wata magana da zaki yi min , dan ko me za ki ce babu wanda zai kuma yarda da mayaudaran kala manki " Aisha na kaiwa haka ta tafi da sauri ta bar Fadila nan tsaye tana kuka.
Aisha da sallama ciki-ciki ta shiga gida. Mahaifiyarsu da kallo ta bita ganin Aisha ta zama wata iri ga fuskarta ta nuna alamun ta ci kuka.
Cikin Sanyi Mahaifiyar su Fadila ta kalli Aisha ta ce " Aisha, Ina Auntyn taki fa ?" Aisha ta bud'e baki zata yi magana ne ta fashe da kuka.
Mahaifiyar Fadila cikin alamun rud'ewa ganin yadda Aishar ke kuka ta ce " Wani abu ya samu Fadilar ne ? "
Mahaifin Fadila dake d'aki fitowa ya yi yana tambayar mahaifiyar Fadila lafiya . Mahaifiyar Fadila cikin sanyi na alamun damuwa ta ce " Nima ban sani ba, haka ta shigomin tana kuka "
Mahaifin Fadila kallan Aisha ya yi " Ya ce ina Fadil..." Shigowar Fadila ya sa ya yi shiru . Saidai abun mamaki Fadila ma da kuka ta shigo tana zazzare manyan-manayan idanunta , dan ita a tunaninta Aisha ta sanar da su tana da ciki.
Mahaifiyarsu Fadila cikin fad'a-fad'a ta ce " Wai lafiyarku za ku zo ku tasa mutane kuna musu kuka ba za ku fad'i abun da akai muku ba? " Dukkansu shiru ba magana sai kuka.
Mahaifin Fadila da shi sai yanzu ma ya san abun da ke faruwa cikin fad'a da yake irin mutanan nan ne masu fad'an, hakan ya sa cikin d'aya murya da hargagi ya ce " Aisha!, bada ku mahaifiyarku ke magana ba ? "
Aisha da ko Karan haka ya cijeta ba zata tab'a iya furtama ma Iyayan nata abun da ke faruwa ba bare kuma ita kanta Fadila. Aisha cikin rashin sanin abun cewa, ga iyayan nasu sun tsaresu da ido ta ce " Baba , wa'adin da kaba Aunty Fadila saura sati d'aya ya cika , shi ne abun da ke damunmu "
Mahaifinsu Fadila ajiyar zuciya ya sauke , in da mahaifiyar Fadila bata yarda da abun da Aisha tace ba .
Mahaifin Fadila ba tare da ya tanka ba ya girgiza kai ya fita.
Aisha da Fadila ko haka suka dawo kamar wasu marayu, ranar dai gaba d'aya gidan sai ya zamana kamar anyi mutuwa .
Da daddare Mahaifiyar Fadila ta shiga d'akin yaran nata . Zama ta yi tana fuskantar su Fadila da ko wacce idonta ya kunbura tsabar kuka.
Mahaifiyar Fadila cikin sanyi ta fara magana kamar haka " Fadila , yanzu idan kuna da damuwa akwai wanda zaku fad'amawa wanda ya wuce ni ? Haba Fadila , haka d'in da kuke yi bakwa tunanin sani cikin wani halin ? Tom in dai kun d'aukeni Uwa mahaifiya agareku ina son yanzun nan ba sai gobe ba ku fad'a min damuwarku ? "
Aisha tashi ta yi ta kifa kanta a cinyar mahaifiyarsu tana kuka, cikin kukan ne take cewa "Mama , Aunty Fadila ta b'ata mana suna , ta jawo mana abun gori a gari , ta aje mana tabon da ba zai taba gogewa ba "
Mahaifiyar Fadila gabanta dukan uku-uku ya fara , cikin sanyi a hankali dan jikinta har yau d'auki rawa ta ce " Aisha, me ya faru ? Ki min bayani da sauri ? "
Aisha cikin kuka ta ce " Mama, Aunty Fadila na da ciki " Ciki ! Wana irin ciki kuma ? " Mahaifiyar Fadila ta fad'a arud'e cikin rawar baki.
Aisha kai ta d'agama Mahaifiyarsu ta ce "Haka likita ta fad'a a gabana "
Mahaifiyar Fadila tashi ta yi ta yi kan Fadila ta niyyar bugu , saidai tana zuwa ta b'ungire ta sume awajan tsabar razana da jin abun da Aisha ta ce.
Aisha da gudu cikin fasa kuka ta d'ebo ruwa tana yayyafa ma mahaifiyarsu, sannan ta farfad'o .
Mahaifiyar su Aisha kuka take sosai ta ma kasa magana. Fadila ko ganin yadda mahaifiyarta ke kuka tana jan numfashi kamar wadda numfashinta zai d'auke ,sosai abun ya furgitata.
Mahaifiyar Fadila tana a wannan halin ne mahaifin su Fadila ya shigo gidan da sauri cikin tashin hankali dan Husna k'anwar su Fadila ta samai a kofar gida ta sanar da shi da Mama da su Aunty Fadila sun had'u sai kuka suke . Hakan ya sa ya shigo gidan a rud'e , tun kan ko ya k'araso ya jiyo sautin kukan mahaifiyarsu Fadila , hakan ya sa ya'idasa cikin d'akin su Fadilar a rud'e yana cewa " Maman Fadila , Lafiya za ki zo ki tasa yara ku taru kuna kuka sai kace bani gidan da ba za ku fad'imin abun da ke damunku ba, In kuma maganar da na fad'a ce kan Fadila ni na janye tuni ina mata addu'a Allah ya kawo mata miji na gari "
Mahaifiyar Fadila , ido ta d'aga tana kallan mahaifin Fadila ta kasa magana sai kuka.
Mahaifin Fadila tsugunnawa ya yi kusa da Fadila da idonta gaba d'aya sun k'ank'ance tsabar kuka ya ce " Fadila, yi shiru kin ji ki natsu ki yi min bayanin abun da ke faruwa ? " Fadila da ido ta bi mahaifin nata da kallo dan ba zata tab'a iya fad'amai abun da ke faruwa da ita.
Mahaifin Fadila da sosai suka d'aga mai hankali, zama ya yi yana fad'a yana cewa " Wai me kuka maidani ne zan zo in tambayarku abun da ke faruwa babu wanda ya saurareni? " Mahaifin Fadila k'asa ya yi da murya cikin sanyi kamar zai yi kuka ya ce " Ko dan kun d'aukeni talaka ne ba zan iya yi muku maganin damuwarku ba ya sa ba za ku fad'a min ba? , Tom indai kun d'aukeni uba wanda kuke kallan zai iya sharemuku kukanku ku fad'a min damuwarku dan Alllah ? " Mahaifin Fadila ya idasa maganar kamar zai yi kuka . Dan sosai hankalinshi ya tashi ganin yadda yaranshi da mahaifiyarsu suka had'u sai kuka suke , daga gani dai wani babban al'amarin ne ya faru.
Mahaifiyar Fadila d'ago jajayan idanunta ta yi ta duresu a fuskar mahaifin Fadila.Da katawa da kukan da take yi ta yi tana tunanin ta inda zata fara sanar da mahaifin Fadila Fadila na d'auke da ciki.
Mahaifiyar Fadila da ta rasa ta inda zata fara sai cewa ta yi " Ka tambayi Fadila , ita ta fi cancanta ta sanar da kai abun da ke faruwa da bakinta "
Mahaifin Fadila mai da kallan shi ga Fadila ya yi ya ce " Fadila, sanar da ni abun da ke damunku kin ji?" Fadila k'ara tsananta kukanta ta yi.
Mahaifin Fadila ganin haka sai ya koma kan Aisha ya ce " Aisha, inda su sun k'i sanar dani , ke fad'a min abun da ke faruwa koma me ye zan muku uziri zan fahimta " Aisha cikin kuka ta fara magana kamar haka " Baba, zan sanar da kai duk da zuciyata ta kasa yarda a abun da kunnuwana suka ji min, saidai kukan da Aunty Fadila kad'ai take yi ya isa ya sa in yarda da abun da kunnuwana suka ji min , sannan dan in tabbatar da kanta ta d'aukeni ta kaini Asibitin 44, da farko na zaci bata da kafiya ne amma sai na ji akasin haka , ashe bata son ta sanar da nine da bakinta cewar tana da ciki " Aisha ta idasa maganar tana kuma rushewa da kuka .
Mahaifin Fadila cikin tsananin furgici da razana da jin abun da Aisha ta ce, ya ce " Ciki ! ? Wa ke da cikin ?" Aisha cikin kuka ta ce " Aunty Fadila ke da ciki Baba " Mahaifin Fadila baki ya bud'e zai yi magana take k'in-k'ina ta shigai ,da hannu ya ke nuna Fadila jikinshi ko ina yana rawa.Magana ya ke son yi amma ya ka sa, jikinshi ko ina rawa yake. Ya d'urk'ushe a wajan ya yi yana dafe da k'arji yana nuna Fadila .Tari ya ke sosai wanda hakan har ya ba su Aisha tsoro, lokaci guda kuma numfashinshi ya tsaya cak ya fad'i a wajan.
Mahaifiyar Fadila da sauri su ka yo kan mahaifinsu suna girgizashi suna kuka.Ana cikin haka ne Ahmad mai bi ma Aisha ya shigo gidan, mahaifiyarsu Fadila cikin rud'ewa ta ce " Ahmad jeka taho da keke-Napep a kai mahaifinku Asibiti " Ahamad matashin yaro ne d'an kimanin shekara goma sha biyar.Ahamad juyawa ya yi da gudu ya fita ya je ya zo da mai keke-Napep d'in.
Da taimakon mai Napep d'in su ka sa mahaifinsu Fadila a cikin Napep d'in su ka yi da shi Asibiti.
Suna zuwa ko da aka duba gawa suka kawo.
Daya daga cikin likitocin ne ya zo ya samu mahaifiyarsu Fadila da su Fadila da ke zaune jugum-jugum ya ce " Saidai ku yi hak'uri fa gawa kuka kawo mana , Zuciyarshi ta riga ta buga" Mahaifiyar Fadila a razane ta kalli likitan ta ce " Likita, kana so ka ce min ya rasu kenan !?" ta fad'i maganar cikin kuka.
Kai likitan ya d'aga mata ya ce " Saidai ku yi hak'uri ya rasu, ku yi hanzarin zuwa d'aukar gawar kafin su kaita mutuwari "
Da taimakon wani mak'ocin su Fadila da Ahmad ya sanar da shi aka d'akko gawar mahaifin Fadila daga asibiti.
Haka aka yi zana'idarshi cikin lokaci aka kai shi gidanshi na gaskiya βπ»
π FADEELAH π
ππ
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONπ*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
πͺπ»J.A.W πͺπ»
Daga
Fadila Sani Bakori
SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala dabn-daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .
*π€ SDEENDTM DATA SERVICESπ€*
*MTN* . *Airtel*
1GB = β¦300. 1GB = β¦300
2GB = β¦600. 2GB = β¦600
3GB = β¦900. 3GB = β¦900
4GB = β¦1200. 4GB = β¦1200
5GB = β¦1500. 5GB = β¦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = β¦350. 500Mb β¦250
2GB = β¦700. 1GB β¦500
3GB = β¦1050. 2GB β¦1000
4GB = β¦1400. 3GB β¦1500
5GB = β¦1750. 4GB β¦2000
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½
*πͺ08066268951*
Page 8
Haka aka yi zaman zana'idar mahaifin Fadila, Inda mahaifiyar Fadila da su Aisha sosai mutuwar mahaifin nasu ta tab'asu, dan gaba d'ayansu sun fita yayyacinsu ba kamar Fadila ba da take ganin kamar ita ta ce silar mutuwar mahaifin nasu , inda silarta ne zuciyarshi ta buga.
Haka suka kasance cikin jimamin mutuwar har aka yi addu'ar bakwai. Bayan an yi addu'a ne 'Yan'uwansu Fadila da suka zo gaisuwa da sauran mutane duk su ka watse, ya rage daga mahaifiyarsu Fadila sai su Fadila.
Daga Aisha har mahaifiyar Fadila babu wanda ke mata magana abinci ma babu mai ce mata ta ci ko karta ci. Abunka da mara lafiya hakan sai ya k'ara ma Fadila ciwo sosai.
Yau Aisha jin Fadila shiru ko sallar Asuba bata tashi ba hakan ya sa bayan ta je ta dama musu koko ta zo ta zauna bakin gadon da Fadila take tana Kiran sunanta, amma shiru . koda Aisha ta duba sai taga ashe Fadila asume take. Hakan ya sa Aisha cikin tashin hankali ta yi d'akin mahaifiyarsu da gudu ta sanar da ita halin da Fadila take ci.
Allah sarki mahaifiyar Fadila dake zaune tana kurbar kokan da Aisha ta dama musu cikin rud'ewa ta tashi har tana zubar da kokan bata sani ba.
Mahaifiyar Fadila koda ta je taga halin da Fadilar ke ciki, cikin tsananin damuwa ta ce " Aisha, Kira Napep mu kaita Asibiti "
Kacan cewar babu nisa tsakanin su Aisha da bakin titi hakan ya sa Aisha na fita ta zo da mai Napep. Da taimakon Aisha da mahaifiyarta suka sa Fadila acikin Napep d'in.
Wata k'aramar Asibiti da ke kusa da su suka kaita.
Suna zuwa ko aka fara ba Fadila duk wani taimako da ya dace.
Saida aka sama Fadila ruwa leda uku sannan ta fara dawowa hayyacinta. Likitar kallan mahaifiyar Fadila ta yi ta ce "Mama, gaskiya indai kina son yarinyarki da abun da ke cikinta to ku yi ma mijinta magana , tana buk'atar kulawa sosai idan ba haka ba zaku iya rasa abun da ke cikinta, sannan ta rik'a rage ma kanta damuwa , dan yanayinta duk ya bayyana ha...." Maganar da Fadila ke yi ce ta sa likitar ta yi shiru ,dukansu suka kai dubansu gareta.
Fadila cikin sanyi dan muryar tata ta yi k'asa sosai, ta ce " Mama, dan Allah ku yafe min kubar fushi da ni akan abin da nima bansan yadda ake ba. Mama dan Allah ku yadda dani Wallahi mama bansan ya akai nake da ciki ba, dan Allah ku yadda da n.." Marin da mahaifiyar Fadila ta yi mata ne ya sa ta yi shiru .
Mahaifiyar Fadila ta d'aga hannu zata k'ara ma Fadila wani Marin ne likitar take rik'e hannunta tana cewa " Ki yi hak'uri Hajiya k'addara ce , haka Allah ya k'addara miki " Likitar ta fad'i maganar tana rik'e da hannun mahaifiyar Fadila dan ta fahimci Fadila bata da aure.
Mahaifiyar Fadila ko cikin tsantsar takaici ta ce " Wallahi, indai kika kuskura kika k'ara yi min irin wannan maganar zaki ga abun da zan miki , wato har yanzu kina nufin ke ta kirkice kina da bakin kare kanki ko ? " Fadila dai ba magana sai kuka
Likitar nasiha ta yi ma mahaifiyar Fadila sosai ta ce " Hajiya mai faruwa ta riga ta faru saidai ki yi mata addu'ar Allah ya raba su Lafiya "
Mahaifiyar Fadila kasa jure zaman Asibitin ta yi ta koma gida, dan idan tana kallan Fadila ji take kamar ta shak'eta ta mutu ta huta, hakan ya sa ta dawo gida tabar Aisha. Kwanansu biyu Fadila ta warware baki d'aya.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya , yanzu haka an yi arba'in d'in mahaifin Fadila.Saidai ta b'angaran Fadila ta fara dangana da k'addarar ta ta farka ta tsinci kanta acikinta. Yanzu abu d'aya ke damunta fushin da mahaifiyarta take yi da ita dan ko gaisuwarta bata amsawa .Aisha ma sai taita yi mata magana ta yi banza da ita.
BAYAN WATA UKU
Yanzu kimanin wata uku kenan da rasuwar mahaifin Fadila , kuma har yanzu Fadila na gida bata koma aiki ba, haka 'yan wajan aikin nasu ma babu wanda ya k'ara tuntub'arta ya ji ya jikinta, garama Jamilu yakan kirata su gaisa .
Yanzu rayuwa ta fara sauya ma su Fadila, dan komai nasu kusan ya k'are, yanzu haka yau sun tashi basu da abin da za su ci.
Fadila yanzu cikinta watanshi hud'u kenan, saidai da yake ba mai girman ciki ba ce in ka ganta ba lallene gane tana da ciki ba, sannan kuma dama yanzu kullum da hijab take zama a jikinta.
Yanzu abu d'aya ke damun Fadila shi ne saurin jin yunwa gashi abun da za su ci yana naiman gagararsu . Hakan ya sa Fadila ta yanke ma kanta shawarar komawa ta ci gaba da aikinta .Fadila tashi ta yi ta je ta samu mahaifiyarta a d'aki zaune kan sallaya tana lazimi , dan tun da mahaifin Fadila ya rasu ta maye gurbinshi,dan shi mutum ne da kusan koda yaushe zaka ganshi da carbi a hannu yana lazimi.
Fadila cikin fargaba ta fara yi ma mahaifiyarta magana, dan ita kanta yanzu kusan bata son abin da zai had'asu magana da mahaifiyar tata. Fadila cikin sanyi ta ce " Mama, idan kin amince zuwa gobe ina so zan koma wajan aiki ? " Mahaifiyar Fadila kallan Fadila ta yi tana tab'e baki ta ce " Abun da ake gudu har ake hanaki ada ya riga ya faru , tom me ya rage ? , duk inda kika ga dama ki je ba aiki ba tashi ki bani waje " Fadila tashi ta yi a sanyaye dama tasan haka zata faru.
Fadila d'aki ta koma tasha kukanta ta gaji ta ba kanta hak'uri.
Bayan Fadila ta gama kukan ne Aisha ta shigo d'akin ,Fadila da sauri ta ce " Aisha, dan Allah ki tsaya mu yi magana " Aisha tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba ta ce "Ina jinki " Aisha, dama aiki na ke son in kama gobe dan Allah ki yi ma mama magana ko zata fahimce ni "
Aisha batare da ta tanka ma Fadila ba ta juya ta yi tafiyarta.
Fadila ganin yunwa zata kashesu dan yau kwana biyu kenan ba su yi girki ba sai 'yan dabe-bare da suke yi, hakan ya sa yau ta shirya ta nufi d'akin mahaifiyarta.
Duk da bata amsa gaisuwarta haka Fadila ta gaidata ,amma bata amsa ba, Fadila ta ci gaba da cewa " Mama, zani aiki? " Fadila ta fad'i maganar a tak'aice a hankali saboda yunwar da