Showing 1 words to 3000 words out of 31694 words

Chapter 1 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

175

 ______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈💎
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
_______________★★★________________

______________°°°°°_____________

*__GABATARWA__*
Bismillahir Rahmanir Raheem. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mamallakin Ranar sakamako, tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu kuma masoyin mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, da iyalen shi da Sahabban shi, da duk wanda suka bi shi zuwa ranar sakamako.
Ina ƙara gode wa Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi Mai suna “BABBAN GIDA” ina roƙon shi da ya bani ikon gamawa lafiya ya kuma yafe min kuskuren da na tafka cikin labarin yasa ƴan uwa su amfana da shi.
Ameeeen.
Labari ne ƙirƙirarre, haka nan sunayen cikin shi ma ba a yi su dan cin mutuncin wasu ba, sai dai duk wanda wani ɓangare na littafin yayi daidai da rayuwar su sai su gyara kuskuren su da suka fahimta daga ciki.
DIAMOND LADY 💎

*___SHIMFIƊA___*
Littafi ne mai ɗauke da soyayya, cin amana, rashin tausayi, gwagwarmaya ƴan uwan taka, cakwakiya da kuma zanen ƙaddara.

*___GARGAƊI___*

Babban gida littafin mallaki na ne, ina da haƙƙi a kan shi saboda haka ban amince a karanta min shi zuwa audio ba sai da izini na, ban Amince wasu su haɗa min document ɗin shi ba.
Takun farko garaɓasa ne, haka na biyu (ƙarshe) ya kasance na kyauta shima. .
Comments ɗin ku kawai nake buƙata...domin shine ƙarfin guiwa tah.

*____SADAUKARWA____*

Dukka littafin Babban gida sadaukarwa ne gare ki Aishatu Usman (Baby).
Tabbas kin kasance ta musamman gare ni. Bazan taɓa mantawa da alkhairin ki gare Ni ba. Allah ya cika miki burukan ki baki ɗaya ya bar ƙauna💋

_____________°°°°°______________

______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝔒𝔲𝔪 ℨ𝔞𝔦𝔫𝔞𝔟🖊️






PROLOGUE


𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣1️⃣

Wannan shafi naku ne masoya littafin _babban gida_.
Ina ƙaunar ku loadi loadi. Ku ci gaba da kasancewa da alƙalamin DIAMOND LADY 💎🤟 tare da comments.
Barkan ku da Sallah.

SHARE AND COMMENT PLEASE
_______________★★★________________

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya ne na safe (11:00am) yayin da hasken rana ya fito yayi ƙwal kasancewar yanayi ne irin na zafi da wuri rana take haskaka.

Ihun da naji yasa na nufi gidan domin ɗauko report.

Gida madaidaici ginin block, sai ƙofar ƙarfe me jan paint Wanda tsabagen dukan da ruwa ke mishi ya koma brown saboda tsatsa.

Mutane ne zaune a ƴar rumfar dake jikin gidan wacce aka kafa ta daidai bishiyar yandi dake wajen. Gabaɗaya kallo ɗaya zaka yi wa mutanen ka tabbatar ba na kirki bane don kuwa siffar su na ainihin bayyana ɗabi'ar su ta shaye_shaye ga kuma ihu da hayaniya da suke alamun wani musu ake bugawa.

Kai tsaye cikin gidan na nufa domin ganin su waye ke ihu, abun mamaki wata kyakkyawar mata ce wacce bazata wuce 32_34years ba tare da yarinyar ƴar kimanin shekaru 10years.

Jibgar su mutumin yake yi wanda kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar ba kan shi ɗaya ba kuma da gani mahaifin yarinyar ne wato mijin matar.

Ba ko ƙaƙƙautawa kamar wanda aka bawa contract ɗin hakan yayin da Mamah babu abun da take sai hawaye.

Ita kuwa Zahrah bakin ta bai mutu ba yayin da shima yaƙi dakatar da dukan da yake mata.

“Wallahi ba zamu taɓa yafe maka ba, mugu kawai azzalumi”

Cike da mamakin ta mutumin wanda ba zai wuce shekaru 45years ba yake duban yarinyar baki buɗe.
Ina da sabo ai ya saba da rashin kunyar Zahrah sai dai bai yi tsammanin ta kai har haka ba. Yanzu tsofai tsofai da shi ko kunyar shi ba zata ji ba take zazzaga mishi rashin kunya. (Ni Ko na ce ina tsufa a nan, bayan ko mutuncin kanka baka kama ba)

Ganin shirun nasa yayi yawa yasa ta goge hawayen da ke kan fuskar ta tana watsa wa mutumin kallon banza

“Wallahi Kawu ba zaka taɓa shiga aljanna ba in dai baka tuba ba, haka kawai bamu maka laifin komai ba ka kama jibgar mu, wallahi Allah sai ya saka mana...”

Bata kai ga ƙarasa abun da tayi niyyar faɗa ba taji an hanɓare mata baki, ba tayi mamaki ba saboda haka halin mamah yake sai kace damo, Gashi dai babu laifin da suka yi wa kawu yake dukan su, amma ta kasa yin komai, ita da take ƙoƙarin yi kuma an hanata.. wannan ai shi ne a dake ka a hana ka kuka.

“Ke Zahrah me yasa kam baki da hankali? Eyeh!! Ɗan uwan ubanki ne fa kike zagi”
Ta faɗa tare da jan hannun Zahrah zuwa ɗakin ta.

Shi kuwa Kawu tsabagen mamakin Zahrah da ya cika shi bai iya taɓuka komai ba har sai da suka shige ciki sannan ya samu damar ficewa daga gidan yana mai nufar dabar su dake ƙofar gida ranshi a ɓace.

Hawaye na kawai ke zuba idon Zahrah yayin da Mamah ta ɗan murmusa tana jin takaicin irin halin da ta sanya kanta. A hankali ta fara magana cikin sassanyar murya wacce ke ɗauke da zallar sarewa..

“Haba Zahrah! Wai sai yaushe ne zaki sauya ɗabi'un ki?”
Ta ƙarasa tare da bin ta da kallon tuhuma.

Tura ɗan ƙaramin bakin ta Zahrah tayi sannan ta kalli Mamah
“Haba Mamah manah, wai sai yaushe ne zaki samu ƴanci a cikin gidan nan! Kin san dai Kawu ba ƙaunar mu yake yi ba kuma don meh zai ke dukan mu kamar wasu bayin sa, Ni wallahi Mamah ba zan ƙyale shi yayi ta zaluntar ki ba! Shine kawai.
Ta ƙarasa tana gurmuɗa bakin ta tamkar tana gaban Kawu.

Jikin Mamah kuwa sanyi yayi da maganar Zahrah, Zahrah dai yarinya ce amma in ta zari magana ko wani babban iyakaci sai dai ba zata zuba mata ido ta lalata mata aure ba. Sam Zahrah bata da haƙuri ko na misƙala zarratin ammah ta ɗauki aniyar sauya ta da yardar Allah.

Bayan sun gama kukan su ne Mamah ta ƙara jan hankalin Zahrah kan rashin kirki da take tafkawa.

“zahrah'u ke har yanzu yarinya ce, ammah zan ci gaba da nuna Miki hanya saboda gaba, idan babu Ni zaki sha matuƙar wahala”

Zahrah da gabaɗaya ta ƙosa da zantukan Mamah yasa ta gyaɗa kai sannan ta miƙe ta nufi ƙofa.

“mamah nikam na tafi can gidan su Amira wasa na”

Mama dai da addu'a ta bi ɗiyar tata sannan ta tashi don ta kammala wankau ɗin da aka Kawo Mata zuwa yamma kuma zata wuce kasuwa.

★★★★★★

Ɓangaren kawu kuwa cikin fushi ya nufi dabar dake ƙofae gidan shi kamar an aika mishi da saƙon mutuwa. Mutanen da ke zaune a dabar kuwa da wata mahaukaciyar dariya suka kece suna tafa hannaye.....kallon banza da Kawu ya watsa musu yana muzurai kamar wani dodo yasa suka tsagaita.

“Haba Ale Idrisu, kar ka bamu kunya Manah! Kai da kace yanzu zaka fatattako su har waje ya naga kai ka dawo”

Faɗin Baba Mola kenan wanda shima mazaunin dabar ne kuma ɗaya daga cikin tawagar Ale Idrisu.

Kallon shi Ale Idrisu yayi sannan ya sauƙe murya ƙasa saboda kada sauran tawagar su ji yace
“wallahi wannan tsinanniyar yarinyar ce da ke hana ni rawar gaban hantsi, ammah zan ci ubanta ne shegiya”

Dariya Baba Mola yayi sannan ya dubi abokin shi Ale Kabir kafin yace
“kada ka damu aboki na, shawara ɗaya kawai zaka bi domin samun muradin ka!”

Cike da ƙaruwar Ale Idrisu ke kallon Baba Mola Wanda ke wani lumshe idanuwa tamkar mai jin bacci yana washe bakin shi da ya koma baki tsabar zuƙar sigari da yayi mishi kanta.

“Na faɗa maka yarinyar nan kawai ka samu ka haɗa ta ka kai ta gidan mata, tun yanzu inda ta saba da can kaga shikenan, ko ka manta da alƙawarin da kayi wa shugaba ne?”

Zaro idon shi yayi nan da nan alamun rashin gaskiya suka bayyana akan fuskar shi. Hakan yayi daidai da fitowar Zahrah zuwa gidan su ƙawar ta. Kallon banza ta bi su da shi tana tofar da yawu irin taga kashi ɗin nan ta wuce.
Shi kuwa Kawu ganin ta sai ya ɗaure fuska yana ƙara maida hankalin sa ga Baba Mola.

Ɗan baƙi ne ya juyo ya kalli uban gidan sa bayan wucewar Zahrah yana wani lashe baki tamkar maye.

“Yah oga nifah nayi kamun yarinyar nan, kyakkyawa ce son kowah, ah nidai zan jira nan da shekara biyu zuwa uku kawai ka wullo min ita”

Ya ƙarasa yana tanɗe baki. Kallon baka da hankali Kawu ya wulla wa ɗan baƙi.
“Lallai ɗan baƙi baka da hankali, in kai ina yarinyar da ko shekaru goma bata wuce ba! Wai ma an ce maka duk rashin son ta da nake zan baka ita ne, Toh ita ɗin mallakin ɗan masu kuɗi ne kuma jari ce a gare ni! Saboda haka ka kauda idon ka a kanta tuntuni ka riga kasan da hakan koh?”

Ya faɗa yana cije leɓen shi sannan ya maida hankalin shi ga Baba Mola suka ci gaba da maganar su.

Ɓangaren Zahrah tunda ta wuce dabar su Kawu ta fara ɗan gudun ta tana tsalle tsalle irin na yara da ta saba yi har ta zo wajen wasu yara da suke wasa waɗanda su ma ba zasu wuce sa'annin ta ba. Wani daga cikin yaran ne ya watso mata ƙasa ai kuwa bata yi wata wata ba ta cakumo shi ta fara narka kamar ɗan ta. Wani tsoho ne yazo wucewa ya fara raba faɗan ammah Zahrah ta ƙi sakin Yaron nan. Duka kawai take kai mishi yayin da yayi la'asar har abun tausayi. Tsoho kuwa da yaga yarinyar ta fi ƙarfin shi yasa ya koma gefe yana jiran ko Allah zai kawo wani matashi..

Cikin motar shi yake ƙirar Mercedes Benz Mai tinted glass ya shawo corner ɗin. Ganin yarinya ƙarama ta kama yaro sai jibgar sa take gashi ya kasa tsinana komai alamun ya jima a hannunta ya sa shi yin parking.

Cikin takun sa na ƙasaita ya fito. Ba tare da ya ce komai ba ya nufi wajen da yarinyar take su kuma sauran yara sai kallon su suke saboda suma tsoron yarinyar suke kada su je garin rabiya ta dawokansu.

Hannun ta ya riƙe tare da jan ta gefe ammah ina Zahrah ta yi wani kukan kura zata ƙwace, jin ƙoƙarin ta na kwacewa yasa yayi murmushi sannan ya juyo da ita tana fuskantar shi.

“ke bari Manah!” abun da kawai ya faɗa sannan ya ɗago yaron da ke kwance a ƙasa jikin sa kaca kaca da ƙasa. Bata yi yunƙurin sake kamo yaron ba saboda irin kwarjini da yayi mata sai ta ja gefe tana saita numfashin ta.

Yaro kuwa ganin an ƙwallon e shi ai gidan su kawai ya nufa ba tare da yace komai ba.
Ishaq kenan, ɗa ɗaya ga Cancellor wanda ya kammala karatun shi na mass communication yanzu haka next month zai wuce America for his masters.

Kallon ta yayi lokaci ɗaya yaji yarinyar ta burge shi, yana so yaga mace jaruma, wacce bata bari a gano raunin ta. Murmushi yayi mata sannan yace

“ƴan mata ya sunan ki”
Zahrah kuwa tayi tunanin zai dake ta ne amma jim tambayar da yasa ta ce
“Zahrah”

Yace “wow! Nice name" duk da cewa bata San meh yace ba da turanci kawai sai tayi murmushi har dimple ɗin ya ya lotsa.

Ishaq kuwa samun kan shi yayi da zuba mata ido sannan yace
“which class are you now, yau Monday Mai ya hana ki zuwa makaranta?”

Lokaci ɗaya yanayin Zahrah ya sauya gashi yayi mata turanci kuma bata so ya gane cewa bata iya ba. Can tace

“ai ba a yin komai a makarantar ma, shi yasa bamu zuwa yanzu ma gidan su Amira zanje”
“waye ce amirah?”
“ƙawa ta ce”
“toh muke na kai ki sai kike nuna min hanya”

Kafaɗa ta maƙe alamun ba zata je ba, ko kaɗan Mamah ta hana ta kwaɗayi balle har shiga motar ƴan gayu, inaaaa ba zata shiga ba.

“tsoro na kike ji Zahrah?
Sunkuyar da kanta tayi sannan tace “a'ah”
Cike da kulawa ya tsuguno daidai yadda tsayin su zai daidaita ya kamo hannun ta
“kin ga cutie ki ɗauke Ni matsayin yayan ki, kada ki ji tsoro na bazan cutar da ke ba”

Cike da gamsuwa ta kaɗa kanta sannan yayi murmushi yace
“good! Taho mu tafi"

Bin bayan shi tayi sannan ya buɗe mata seat ɗin mai zaman banza, bayan ta shiga ya rufe sannan suka fara tafiya tana nuna mishi hanya.

“cutie kika ce baa komai a makarantar, wa ce kike zuwa?”
“bamu da nisa da makarantar, primaryn gwamnati ne"

Zaro ido Ishaq yayi sannan yace
“kina so na sauya miki makaranta?"

Tuni ta ɗaga kai abun ka da yarinya babu hankali. Shi kuwa murmushi yayi sannan yace
“alright zan saka ki wata makarantar ammah sai kin daina faɗa irin wannan da na tarar kina yi..."

Bata jira ya ƙarasa faɗin abun da ke ranshi ba tace “na yadda, na ma daina daga yau”
“shikenan zaki raka Ni gurin baban ki ai?”
“aah Baba na ya rasu, sai dai Kawu na da Mamah na, kuma Kawu ba so na yake yi ba kullum sai ya duka mu Ni da Mamah na”

Cike da mamaki Ishaq ke kallon Zahrah sannan yace
“shikenan sai ki raka Ni wurin naman naki" a daidai nan suka iso gidan su amirah sannan yayi parking.

Kallon ta yayi sannan yace “cutie yaushe zaki koma gida?”

“sai da Yamamah zan wuce kasuwa taya Mamah aiki"
“shikenan zan zo da yamma kin ji, sai muje wurin Mamah ɗin"

Daga haka ta fice da gudu ta nufi gidan su Amira ko godia bata mishi ba.
Ya dade kafin ya ja motar shi ya tafi yana mamakin zantukan Zahrah, kuma yayi niyyar tallafawa rayuwar ta.

KO DAI ISHAQ SON ZAHRAH YAKE?
TOH IN SON TA YAKE YA ZAA YI DA KAWU?
KO MAMAH ZATA AMINCE?
MENENE ALAƘAR KAWU DA MAMAH?

Duka amsoshin ku na cikin littafin *_Babban gida_*
Yanzu ma aka fara!

Ku ci gaba da bibiyar alƙalami na don nishaɗantuwa, ilimantuwa da kuma samun faɗakarwa.

COMMENTS ƊIN KU NA DA MATUƘAR AMFANI DOMIN SHINE ƙWARIN GUIWA TA

DIAMOND LADY ce💎🤟



______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈💎
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️





PROLOGUE



𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣2️⃣

Wannan shafi naki ne masoyiya
AISHA MB (MHIZ ISHA) marubuyar littafin _aljanar ruwa ce_
Thanks a lot for ur selfless actions friend, loads of love🤩😘
Barka da Sallah

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________

Anyi sallar azahar kenan sai ga Yaya Ishaq ya zo kamar dai yadda ya faɗa, ya rasa ma ta yaya zai kira cutie ɗin tazo. Wani yaro ne yazo wulgawa ai kuwa da sauri ya dakatar da shi.

“kai yaro zo” ba tare da musu ba yaron ya je wurin yaya Ishaq
Ɗan kallon yaron yayi sannan yace
“ka ɗan shiga gidan nan kace Zahrah ta zo inji yaya ta”

Ba musu yaron ya buɗe ƙofar gidan sannan ya shiga ɗauke da sallama a bakin shi.

“Salamu Alekum”
Maamahn Amira da ke shara ita ta amsa masa tana mai dakatawa da sharar don jin neh yaron yazo yi

“wai Zahrah tazo in ji yayan ta a waje”
Bai jira amsar da maamah zata bashi ba ya fice abun da.
Yayah Ishaq kuwa har kuɗi ya bawa yaro.

Maamah ce ta ƙwala kiran amirah da suka wuce can filin bayan gidan suna wasan su. Jin shiru basu amsa ba yasa ta wuce a fusace

“ke ƴar karuwai ki fito yana jiran ki a waje”
Cike damamaki take kallon mamah. Shin meh yasa ake danganta ta da karuwanci?, Menene laifin ta da za'a ke mata hakan? tunawa da sabon yayan ta Ishaq da tayi, ai kuwa da gudu ta fita tana yi wa amirah sai da safe.

Tana ganin yaya Ishaq ta ɓare baki kamar gonar auduga yayin da shima yake jin ta ajikin shi. Babu abun da yake yi sai aika mata da saƙon murmushi.

“cutie, kin ce zaki kai Ni wurin Mamah koh?”
Zaro ido Zahrah tayi kamar wata munafika. Shi kuwa yaya Ishaq jin. Shiru yasa ya ƙara kallon ta tare da faɗin
“cutieeee...”

Ɗan tunani tayi da ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwar ta sannan tace
“toh yaya muje”
“yauwah cutien yaya.”

A hankali yake driving ɗin yayin da hankalinsa kwacakwam ya dawo gare ta.
“cutie mai Mamah take ji a kasuwa da yamma”
Ɗagowa tayi da har zata yi shiru wata zuciyar tace ki faɗa masa wataƙila sanadiyyar haƙa sai ya samar muku sauƙi daga muguntar Kawu.

“mamah fah masa take soyawa a kasuwar kasan saboda meh?”
Kai ya girgiza kamar wani yaro yayin da ta marakraice fuska

“idan taje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login