Showing 24001 words to 27000 words out of 31694 words

Chapter 9 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

184

hanya tare da taimakon uncle Hashim, bayan an kwatanta wa kowa nashi A. Officer ya ce “ toh bari a gwada kowa Muga yadda zai yi”

Maryam zata yi representing school ɗin ne a junior spelling challenge and pronounciation yayin da Badi'a zata yi essay writing sai kuma Zahrah impromptu speech.

Marya aka fara gwada wa and Alhamdulillah she's done it well. Tayi da kyau har sun saka rai kan spelling challenge nasu..
Badi'a ma ya bata piece of paper sannan ya bata topics.
Within short period of time ta kammala, he's impressed by the way she answer the question, ita ma aka dasa alamun nasara a tattare da ita.

When it turns to Zahrah, a topic is given to her also, and tayi yadda ya kamata, her confidence, gentleness, the way she speaks like she's from Elizabeth's palace.

Bayan sun kammala ya ƙara gyara musu kowa aka faɗa nata corrections nata, and they all master it. Da yake lokacin sallah ya gabato kai tsaye komawa suka yi suka yi alwala suka yi sallah.
After they prayed suka ce su gwada playing Qur'anic trick, Zaki janyo ayah sai ki zaɓi ɗaya cikin su ta faɗi wani surah take, idan ta canka daidai sai ta karanto cigaban.
Haka suka yi tayi har lokacin ishà.

Alwala suka yi suka watso ruwa sannan suka jona sallah, suna idarwa bayan azkar suka Fara hirarrakin su.

Few minutes da fara hirarrakin su aka yi nocking, abincin su aka kawo musu sai lokacin duka tuna a na rana da aka kawo akwai extra bag da basu taɓa ba. Ɗauko ta suka yi kads ayi asara suka fara cin ta.
Bayan sun ci suka buɗe Bags ɗin daren, chips ne sai egg sauce da kuma milk drink. Bayan sun cinye tas suka ci gaba da hirar su. Ba su suka kwanta ba sai around 10:00pm. Safiya mai albarka marvelous squad.

Cikin baccin ta tayi mafarkin Mamah.
Sai ga ta nan kusa da ita suna wata magana, bayan sun gama maganar sai Mamah ta damƙa mata wata haka wacce bata san ta miye ba tare da gargaɗin ta kada ta buɗe ta kwana kusa.
Bayan ta karɓa sai Mamah ta ɓace ɓat, tana ɓacewa sai Zahrah ta fara kuka tana neman taimako, wai sai ga baba amarya ta fito tana sheƙa mata dariya can kuma ta ɓata rai.

A zabure ta miƙe gani gari har ya waye. Ɗaya bayan ɗaya ta tayar da su suka yi sallah, sannan kowacce ta shiga tayi wanka.
Suna fitowa suka shafa cream ɗin da suka ga ajiye gaban dressing mirror dake room ɗin.
Around 7:00am aka kawo breakfast, suna ci suka yi brush suka fara Sanya uniform saboda za'a fara program ɗin ne by 9:00am and suna so su je da wuri.

“Zahrah wannan kam daidai ɗin ki ne ke zaku saka” Badi'a ta faɗa tana miƙo mata wata bujen riga. Zumɓura baki tayi ta harare ta.
“u're out of your mind actually Ni zan saka wannan burgujejiyar rigar?”
Gira Maryam ta ɗaga mata wanda yasa ta cilla mata ita.
“ke maryam ke ce uwar mata cikin mu ke zaki saka ta”
“wannan rigar nimah bazan saka ta ba sai dai na mayar da tsohuwa ta”
Dariya suka kwashe da ita sannan Badi'a ta tsagaita ta ce
“wa yaga new plus old which is equivalent to mark reduction” ta ci gaba da dariyar ta.
Maryam ta ƙulu iya ƙuluwa kafin tace
“shikenan na haƙura zan sa ammah dai kun min wayo ne.
Gwalo Zahrah tayi mata sannan tace
“don't wear it if u like Mamah baby😂”
Jin sunan da Zahrah ta ƙura ta yasa ta wulla rigar.
Suna cikin haka aka yi knocking su a guje Maryam ta janyo rigar ta saka tana hararar Zahrah yayin da Zahrah ke tayi mata dariya.

“if u're ready we can go”
A nutse suka fito suka bi bayan shi zuwa motar su. Daga nan motar su ta lula sai RUCHAS FOUNDATION COLLEGE.

TOH, MU KASANCE GOBE DA KU DON JIN WACECE MAMAH DA KUMA DALILIN ZAMAN TA TARE DA KAWU?
ME KUKE TUNANI ZAHRAH ZATA YI BAYAN SANIN ASALIN MAMAH
SHIN ZASU CI COMPETITION ƊIN NE KO KUWA?
DUK CIKIN LITTAFIN BABBAN GIDA
KU CI GABA DA SAMBAƊO MIN COMMENTS REMEMBER FILIN BADA SHAWARA DA KARƁAR ƘORAFI A BUƊE YAKE

ITZ DIAMOND LADY 💎
Oum Zainab

______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️



PROLOGUE


𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣3️⃣

kada ku mance gabaɗaya littafin sadaukarwa ne gare ku AISHATU USMAN (Baby Unah) sai dai gashi sai ranar da pages ɗin nake ba tare da sanin ki ba ammah na san ke ɗin mai fahimta ce ai... Haka wannan shafin ma dai sadaukarwa ne gare ku
A'ISHAH MB (Baby Isha) marubuciyar littafin Rayuwa da macijiya
Pinky darling marubuciyar littafin SO
FAIZA ALMUSTAPHA (Fa'eeh BG) marubuciyar littafin a mafarki na santa.
I guys mean a lot to me, so much love u....Allah ya ƙara muku hazaƙa da zaƙin hannu.

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________



Suna isa suka yi parking motar su. A lokacin ba'a wani zo da yawa ba saboda sai 9:00am za'a fara. A nutse suka shiga cikin ƙatoton ball ɗin da aka jere shi da kujeru fiye da dubu biyu.
High table already well set kawai mutanen ake jira.

Front seat suka samu suka zauna duk da cewa wurin is meant specifically for audience, suka ci gaba da gwada yadda zasu yi har aka fara zuwa.

The first person to come wani Black timid balded man ya zo wurin su bayan sun gaida shi ya amsa sannan ya tambaye su su waye su.
Cikin nutsuwa Maryam tayi mishi bayanin cewa sun zo representing school nasu ne, ya tambayi wani school suka faɗa mishi nan ya rubuta a paper dake hannun shi daga nan yace su tashi nan wurin isa not meant for them, bayan shi suka bi ya nuna musu wurin da aka wani don participants a nan suka zauna.

Tun daga lokacin aka fara zuwa, people from various schools da wasu ma ba a Jos ɗin suke ba, baƙi duk suna ta zuwa kowa sai wuri yake samu
Abun ku da Nigeria iyayen african time sai wajen 9:15am aka daina shigowa alamun kowa ya kammala zuwa.

Ba tare da ɓata lokaci ba MC ya fara gabatar da programs ɗin da za'a yi tare da welcoming address na manyan baƙi da kuma shuwagabannin taron.
Everything is well set so ba a ɓsta lokaci ba aka fara.

Schools fiye da hamsin ne suka halarci taron, aka fara da Spelling challenge and pronounciation.
Ɗaya bayan ɗaya aka ƙira partipants na kowanne school suka samu wurin da aka tanada don shi wannan program ɗin.

Bayan sanar da su cewa duk wanda ya zaɓa number, bayan yayi spelling ba daidai ba za'a yi withdrawing nashi daga masu participating.
First round aka cire 39 schools second round baa cire kowa ba, third round aka cire 20 schools sai kuma fourth round aka cire 15 schools ya rage saura 5 partipants representing 5 schools.

Da ƙyar aka cire biyu aka bar biyu, Maryam kaɗai sai wata Christian suka rage, sun fafsta sosai kafin daga ƙarshe aka cire wannan ɗayar.....Nan da nan aka saka tafi raf raf su Academic officer da uncle Hashim Baki har kunne student ɗin su won the Trump.

Sara ɗin ta na da ta koma ta zauna kusa da sauran ƴan uwanta, ba'a wani ɓata lokaci ba aka shiga essay writing, Abu da rubutu time kawai aka basu daga nan aka basu question papers. Within an hour suka kammala kowa yayi submitting, Babu wanda ya San Mai nasara a wannan ammah kowa na fatan kasancewa mai nasara.
Daga nan kuma Badi'a ma ta dawo wurin ta.

Hayaniyar da aka fara ne yasa mu ya roƙi mutane da suyi shiru, bayan an yi shiru tamkar babu kowa aka yi introducing last program Wanda duka ya fi tsayi a ciki, sai dai za'a iya ɗaukar four good hours tukunna a kammala.

Shima aka kira partipants ɗin suka fito. Bayan sun fito aka faɗa musu dokokin su da kuma Marks awarded to each step.

Successfully aka fara kuma duk Waɗanda suka yi they performed well.
Mutum 20 ne suka yi daga nan aka tsayar da taron aka je break na 2hours.
Sallah suka yi a wani nearest mosque sannan suka samu wuri suka zauna, suna zaune uncle Hashim ya kawo musu abinci, a wurin suka ci sannan suka koma hall ɗin lokacin kuwa babu kowa a ciki.

Bayan cikar lokacin mutumin ɗazu wasu the first to enter, ya ƙara ɗaukar sunan school nasu. Bayan kowa ya dawo aka ci gaba da impromptu speech.
Zahrah was second to the last to be in the stage.

Cike da nutsuwar ta wacce mutane ke ganin kinibibi ne da kuma yanga sai dai haka abin yake a jikin ta ta wuce ta ɗauki paper ɗin ta miƙa kamar yadda sauran suke yi, abun magana aka miƙa mata a lokacin da ake karanta mata topic nata. Yana kammalawa ta juyo ta fuskanci shuwagabannin, a nutse cikin Muryar ta mai ɗaukar hankali tare da turancin ta wanda mutane da dama ke cewa kinibibi ne da ƙaryata ta fara gaida su mataki zuwa mataki har ta isa ga audience.

Tafi ne kawai ke tashi a ball ɗin duk da cewa mutane da dama sunyi saidai wannan ya kasance daban, everything with her is unique, her approach, Grammer and pronounciation was different uwa uba kuma voice nata da take magana da shi cike da gayu da kuma ƙwarewa.

Ci gaba da zubo turancin ta tayi wanda Ni reporter dai ban samu ikon haddacewa ba balle na karanto manah, Allah i know is tayi fiye da duk wanda suka yi, babu wanda zai ji bai yaba ba sai ɗan hassada.

Abun mamaki sauran na baya basa concluding time ke cika ammah Zahrah sai da ta kammala komai gashi tayi bayani yadda ya kamata, tana gamawa kuma lokacin ta na cika.
Hakan ba ƙaramin burge mutane yayi ba, babu wanda Zahrah bata tafi da imanin shi ba sai ɗan baƙin ciki. Gashi dai mostly ba Hausawa bane partipants ɗin kuma kamata yayi ace sun yi fiye da ita musamman da ya kasance ita ɗin ba ta samu Foundation mai kyau ba ammah duk ta wanke su.

Mutum na ƙarshe na gamawa aka fita hutun rabin hour din cire sakamako da kuma haɗa gifts.
Basu bar halal ɗin ba saboda babu wani abu da zasu yi in sun fita ɗin. Cold and chill drink aka miƙa musu daga malaman su suka sha abun su sannan suka fara ɗan hiran abun.

“kai Zahrah, kin matuƙar ƙayatar fah, wallahi babu wanda ya kai ki yi, Ni har na baki winner na category naku”
Hararar wasa tayi wa Maryam
“kinji fah su chairlady of the occasion, sai ki ga kuma Ni da kike tsammani bana cikin masu nasarar.”
Caraf Badi'a tace
“Allah ma ya tsare ai kin basu a jikin su, ke kam Maryam naki ma a bayyane yake, nice dai cikin duhu"
“nothing but succes from Allah in Sha Allah”
Zahrah ta rufe musu baki da hakan.

Bayan lokacin hutu ya ƙare still dai su kaɗan ne a hall ɗin sai lokacin aka fara shigowa, mutumin na ya ƙara ɗaukar sunan school nasu ya wuce.
Within few minutes kowa ya dawo don jin sakamako.

Ashe duk abun da ake an watsa shi duniya, ta channels da dama sun ɗaura live ne saboda yadda COMPETITION ɗin ya sanu, gashi ana samun kuɗi sosai in mutum yayi winning.
Chairman na taron sai da yayi dogon bayani gamsasshe tukun ya bada space wa shugaban alƙalan COMPETITION ɗin.

A natse ya fara magana,ya fara da gaisuwa da kuma ƙarfafawa partipants baki ɗaya guiwa kan cewa duk sun yi ƙoƙari. Daga nan ya fara faɗin result.

Dummmmm gaban kowa ya faɗi saboda kowa zai so ace school nasu tayi nasara.
“let's start with the first category, that is spelling challenge and pronounciation.
The first and the winner of this category goes to ALMUNAUWARA ACADEMY Bauchi, in person of Maryam Aminullah. You can come forward and receive you gift.
Bayan ta amso ta juya ya ƙara cewa miss Maryam in addition to the gift, Senator Umar Bukola awarded 100thousand Naira to you. You can have it now”
A natse ta amso envelope ɗin ta juyo bayan pictures da aka ɗauka.

“To the second category, the best essay writer of the year award goes to ALMUNAUWARA ACADEMY Bauchi, in person of Badi'a Kabir Umar. Here goes the best essay writer of the year from same school, congratulations ALMUNAUWARA ACADEMY. Your gift and award is here.”

Itama har ta juya zata dawo yace
“i'm not done with you Miss Badi'a, a another gift of 100thousand naira from sir Umar Bukola was added, come forward and get it"

Bayan ta amsa ta dawo yayi shiru, sai bayan tafi da ihu ya kafa ya ci gaba.
“A lady from Elizabeth's palace here won the yeae's impromptu speech with the required Marks without skipping any.
You're indeed an angel Miss Zahrah Abdulkarim Kuru from the glorious ALMUNAUWARA ACADEMY Bauchi.
This shows to us that ALMUNAUWARA ACADEMY promote and produce capacitive intelligent and amazing students, Zahrah Abdulkarim come forward”

A nutse ta ƙarasa ta amshi aware ɗin da gift ɗin ta ta juyo.
Muryar shi ce ta dakatar da ita
“Miss Zahrah again received 100k cash from sir Umar Bukola, in addition to this members of the high table have the sum total of 200k for you miss Zahrah ”

A nutse ta amso su ta dawo, ihu hali ɗin ya saka da ƙyar aka yi shiru Zahrah na dawowa seat ɗin ta tayi hugging colleagues nata kowa ya taya kowa murna daga nan shiru ya biyo baya.

Ci gaba da magana yayi
“Again we've the year's award to the glorious ALMUNAUWARA ACADEMY, participants from the school should come forward”

Ƙyas ƙyas ƙaran camera kawai kake ji na tashi bayan sun amsa sun koma zaman su kenan aka ƙara ƙira..

“people of time, people that have respect for time, being the first to arrive to the hall, the first one resume after the first break and the last to resume after the last break. Your award and gift is ready, ALMUNAUWARA ACADEMY again won this award.
Congratulations ALMUNAUWARA ACADEMY"

Su uku suka amsa sannan suka dawo.
Bayan sun dawo aka fara fita, da taimakon Academic officer da uncle Hashim suka kwashe gifts da award nasu zuwa mota daga nan kuma suka koma wurin da suke.

Bayan sunyi sallah suka yi wanka suka ci abinci sannan suka ɗan huta.
Sallar maghrib suka yi daga nan suka ƙara yasuwa saboda gajiya.

Basu koma ba a ranar saboda haka bayan dinner suka kwanta.
Early morning suka naushi motar su sai Bauchi.
School suka fara isa, daga nan suka ajiye gifts da sauran abubuwa kowacce aka mayar da ita gida.

Tana shiga ta tarar da Mamah tana zabga amai a ƙofar ɗakin da gani ma ta jigata da ƙyar take ƙaƙarin kana ganin ta ka ga gajiya da rauni .
Da gudu ta rugo tana isowa gurin Mamah, duk wahalar da take ji lokaci ɗaya ta ɓace ɓat, rungume ta tayi ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.
“mamah tun yaushe ne baki da lafiya”
Cike da ƙarfin hali Mamah tace
“taimaka na wanke baki na zamani koma ɗaki...”
A hankali ta sake ta ta miƙe don ɗebo ruwan, tana kuskure bakin ta ta taimaka mata suka isa ɗaki... bisa gado ta kwantar da ita daga nan ta fito ta tsaftace wajen.
Ganin basket ɗin gidan Ammi ya tabbatar mata da abinci aka aiko, tsakura tayi ta isa gefen Mamah, da ƙyar ta ɗan ci 3spoons sannan ta koma, ita ma ci tayi ta dawo gefen Mamah ta kwanta.

Bata aune ba baccin gajiya yayi wuff da ita, cikin baccin ta ji mama ta ƙanƙame ta firgit ta farka ta juyo gare ta.
“mamah kina son wani abu ne”
“a'ah ta amsa tana kaɗa kanta. Daga nan suka ƙara kwanciya basu daɗe da kwantawar ba ta ƙara ƙanƙame ta. Wannan karon tana farka wa taji Muryar Mamah a kunnen ta.
“tashi Zahrah zamu yi magana" da sauri Zahrah ta miƙe tana fuskantar Mamah
“mamah menene kike don faɗi haka?”
“zahrah bani da lokaci isasshe ya zama dole na sanar da ke Ni ɗin wacece saboda ina jin kamar ana ka na zaafita da Ni wajene.
Bata kawo komai ranta ba tace
“mamah babu abun da zai faru”
“buɗe wardrobe ki hau kan kujera zaku ga jakar da na ɗauki daren ranar ki fito min da ita kinji?”
Ba tare da ta amsa ba ta ɗauko jakar tana miƙowa Mamah.
“aah Zahrah ki riƙe a hannun ki ban kuma amince ki buɗe ta ba har sai ranar da kika ji zama gidan kawun ki ya ishe ki ko kuma lokacin da wanin su yayi ƙoƙarin Cutar da rayuwar ki” ta ɗan yi shiru yayin da zuciyar Zahrah ta riga ta karye da bayanin Mamah.

MU HAƊU GOBE, KADA KU MANCE COMMENTS ƊIN KU SHINE ƙWARIN GUIWA TA!
INA ƘAUNAT KU SOSAI.



______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️



PROLOGUE


𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣4️⃣



SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________


FLASH BACK
ABATCHA ESTATE
ABUJA

Tun daga titin da zai sada ka da ABATCHA ESTATE zaka tabbatar wa kanka wuri na musamman zaka dosa. Ga kuma wani ƙaton signboard da ke ɗauke da ABATCHA ESTATE make a roundabout.
Wani makeken Black gare ne wanda tunda nake ban taɓa ganin irin shi ba ko da kuwa cikin manya manyan estates dake birnin Abuja. ABATCHA ESTATE kenan. Hamshaƙin ESTATE

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login