Showing 27001 words to 30000 words out of 31694 words

Chapter 10 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

183

da in dai kana rayuwa cikin birnin Abuja ne toh ka sanshi sai dai ba kasafai zaka samu labarin wadda ya taɓa shigan shi.

ESTATE ne da ya tsaru iya tsaruwa, an kashe kuɗi sosai wurin gina shi. Uwa uba ba kowa ake bari ya shiga ESTATE ɗin ba don kuwa hardly kaga wani bare ya je, sun keɓe kansu kuma ba sa mu'amala da Barr in ba larura ba, a cewar su iya su sun ishi kansu rayuwa.

Wasu manya manyan guards ne wanda girman su kaɗai ka gani hankalin ka sai ya tashi, tsaye suke bakin gate ɗin fuskokinsu su tamkar ta shanu, babu fara'a ko kuma alamun ta. Ga wasu irin khaki da suka sanya mai colourn Blue. Da ƙyar na samu hanya don na shiga in ɗauko report.

“masha Allah” Naira tayi kuka cikin wannan ESTATE, wani titi na ƙara miƙewa yayin da nayi arba da wani haɗaɗɗen mansion Wanda Kai tsaye zan iya cewa fada ce ta wani mai sarauta.

ABATCHA ESTATE,
Ainihin sunan mamallakin wannan ESTATE shine Mohammad Abatcha, haifaffen garin Birnin Gwari ne dake jihar Kaduna. Ammah asalin iyayen su Fulani ne na ƙasar Niger.

Alhaji Kabir Abatcha da kuma matar shi Sa'adatu Fulani ne usul daga garin Birnin Gwari dake jahar Kaduna. Kiwo ita ce ainihin sana'ar su kuma sunyi auren zumunci ne da Sa'adatu.Bayan haihuwar ɗan su na fari wanda yaci sunan kakan da ABATCHA shine dalilin sayar da shanun su suka dawo cikin Kaduna da zama. Bayan tattaunawa ta musamman tsakanin su suka yanke shawarar fara sayar da babur da kuma keke.
Alhamdulillah cikin ikon Allah Allah ya buɗa musu sosai sai dai tunda suka haifi ABATCHA Allah bai ƙara basu wani ɗan ba.

ABATCHA ya taso ne ciki gata, kulawa ga uba soyayyar iyaye. Tun yana ƙarami Allah yayi masa farin jini da saboda tsantsar kyau da yake da shi irin na dukkanin asalin nan.
Yayi karatun primary ɗin da ba kamar iyayen shi ba da suka yi iya karatun Allo. Bayan ya kammala secondary school ɗin shi kuma ya fara karatu a ATBU, mechanical engineering yayi saboda yana son ci gaba da kula da kasuwancin mahaifinsa wanda a yanzu ya bunƙasa sosai.

A lokacin da yake karatun ne suka haɗu da Karima ɗiyar Abokin Baban sa ne wanda kasuwanci ya kai shi Kaduna. Duk da cewa iyayen sun so ya koma tushe ne yayi aure basu ƙi ba kasancewar mahaifin Karima aboki ne na kusa ga baban sa.
Ba'a daɗe ba kuwa aka yi musu aure.

Bayan auren su da watanni kaɗan Baffa ya damƙar da kasuwancin da hannun ɗan shi, a lokacin kuma suka koma Birnin Gwari da zama a cewar su zasu fi samun nutsuwa.
Abun ka da zamani yayi wa kasuwancin sa register da “ABATCHA AUTOMOBILES”.
Lokaci ƙalilan Allah ya sa albarka ciki kafin kace meh wuri ya sanu ga kuma uban ci gaba da aka samu.

A lokacin ne kuma Hajjaty matar Alhaji Baba ta samu cikin farko zo kuga ɗauki wajen su da kuma iyayen su. Bayan wata tara ta haife ɗan ta mai suna Abubakar. Kyakkyawa da shi kamar mahaifinsa ga kuma farin jini da yaron ke da shi.

Bayan shekara biyu da haihuwar shi ta ƙaro ɗanta mai suna Umar, daga nan Uthman sai kuma Aliyu wanda shine ƙarami cikin maza.Daga nan Hajjaty bata ƙara haihuwa ba.

Dukkan yaran sun tashi cikin kulawa da kuma gata, ahali ya ginu gashi suna matuƙar jin daɗin rayuwar su. A lokacin da Aliyu yake Aji biyar na primary Alhaji Baba ya ƙara aure. Basu wani damu da auren shi ba kasancewar basu sanya damuwar wasu a ran su.
Amarya Khadijatu bata yi dogon zango ba Allah yayi mata rasuwa.
Babban ɗan ta Muhammad mai sunan Baffa sai ƙaramin Yusuf. Bayan haihuwar Yusuf ne Allah yayi mata rasuwa, to da yake lokacin ita ma Hajjaty cikin ta ya kusa haihuwa kawai aka yi inducing labour ta haife shi kafin lokacin. Wannan karon mace ta samu saboda irin farin cikin zuwan yarinyar suka saka mata suna Madina.

Madina da Yusuf duka Hajjaty da kanta ta shayar da su cike da so da ƙauna.
Madina ta ga gata fiye da kowa cikin gidan, gatar kuwa ta ko'ina tun daga wurin babban yayan su Abubakar har zuwa kan yayanta Yusuf ga kuma soyayyar iya duka kasancewar ta ƴaƴan ɗaya tilo da suke da.

Madina tayi karatun Addini MASHA Allah haka boko ba'a barta a baya ba. Tun tana ƙaramar ta bata da ƙirininya da rashin ji irin na yara. Bayan ta gama secondary Yaya Abubakar ya samar mata admission a nan KASU.
Wasa wasa tana karatu sosai har ta cinye semester ta farko. Kowa yayi farin ciki da ita sosai. Daga nan ne kuma ƙaddara ta sauya mata salo haɗuwar ta da Abdulkarim Kuru wanda shi ma ɗalibi ne cikin makarantar sai dai shi yana dab da gamawa. Soyayya suke yi mai cike da kulawa yayin da shi Abdulkarim iyayen sa Allah yayi musu rasuwa tun yana yaro.

Ya taso ne a gidan ɗan uwan mahaifiyar sa wanda rayuwarsa tare da su babu abunda yake tsinta sai wahala musamman wurin matar gidan da kuma yaron ta Idrisu. Haka ya daure ya ci gaba da zama tare da su har suka kammala primary. Tun lokacin kuma ya fara neman sana'ar hannu don tallafawa kan sa. Sai dai kash, ko da yayi ya damu ƴan kuɗaɗen sa sai umman idrisu ta ƙwace ta bawa ɗan ta gashi kuma shi babu aikin da yake yi sai zama a dabar ƴan shalli tun yana yaron sa.

Bayan ya kammala secondary bai sa ran ci gaba da karatu ba saboda mahaifin idrisu ma Allah yayi masa rasuwa,hakan yasa tun lokacin ya fara sana'o'in hannu, dako, garuwa da sauran su babu wanda bai yi ba sai dai kuɗin duka a gindin ummah ya ke ƙarewa, ko kaɗan bata tausayin sa gashi da shi yake cefane a gidan ammah abincin gidan babu rabon shi.

Haka ya ci gaba da rayuwa bayan wani lokaci wata rana suka haɗu ad abokin sa na primary wanda yanzu baban sa shine chairman na yankin su, da taimakon abokin ya samu damar tafiya jami'a ammah baban abokin ya zaɓa masa KASU saboda kada yake mantawa da shi.

Tare da abokin sa Bello gadauji suka ci gaba da karatun su kuma Alhamdulillah Abdulkarim na samun ci gaba sosa yana kuma samun nasara.
A shekarar shi ta ƙarshe ne suka haɗu da Madina Abatcha ɗiyar hamshaƙin attajjirin da babu kamar sa cikin Kaduna state da kewaye. Da farko ya ji tsoron alaƙar su ammahdaga baya suka ware suna zabga soyayya.

Ranar da Madina ta tunkari Hajjaty da maganar aure take so bata kula ta ba sai ma cewa da tayi ta samu yayan ta Abubakar wanda yanzu yaron sa na da Shekara biyu a duniya.
Tunkarar yayan ta da tayi ya jawo babbar matsala don kuwa cewa yayi ba ta isa tayi aure yanzu ba kuma ko zata yi sai dai shi da kan shi ya samar mata miji ko daga dangin Hajjaty ne.

Kuka sosai Madina tayi bayan jin bayanin yayan nata gashi kuma Hajjaty da Alhaji Baba sun ƙi saka baki. Ana cikin haka Abdulkarim ya kammala karatun sa sai dai bai samu aikin yi ba. Basu rabu ba har bayan komawar sa gida. A nan yake sanar da baban Bello maganar Madina.
Kwantar masa da hankali yayi daga nan ya wuce don gaida umman su. A lokacin ya tarar da mummunan abu don kuwa idrisu shaye shaye yake ba kuma ƙafar yaro, ga kuma bin ƴaƴan unguwa yana lalata su tun iyaye na kai ƙara har suka gaji suka fauwalala Allah komai. Ɓoyayyen batu ma ashe har boka gare shi wanda yake rufe masa bakin iyayen yara.

Idrisu yayi baƙin ciki sosai gani ɗan uwan sa cikin rahama gashi kuma wai har karatu yayi.
Wurin Bokan shi kai tsaye ya nufa bayan yayi masa aiki kan cewa Abdulkarim ba zai taɓa samun aiki ba ya dawo.
Shiru shiru babu aikin yi gashi kuma tsakani da Allah shi yana ƙaunar Madina kuma auren ta yake so yayi.

Aikin hannu ya fara yana zama a matsayin yaron shago ma wani ɗan kasuwa cikin haka da idrisu ya gano ya haɗa masa ramin mugunta har aka kore shi. Yanke shawarar neman auren Madina yayi dai dai iyayen ta sun ce aah saboda sun riga sun mata zaɓi.

Madina tayi kuka sosai kamar ba gobe har rashin lafiya tayi ammah yayun ta suka ƙi amincewa da batun ta. Ana cikin haka sheɗan yayi mata huɗuba ai kuwa ta hau tayi daram.
A hankali ta fara haɗa kayayyakin ta masu muhimmanci wuri ɗaya, sarƙoƙin ta da kuma abubuwan ta masu tsada duk ta haɗa su wuri ɗaya sai dai bata san ta yaya zata fita da su ba.

Shawara ce ta faɗo mata ai kuwa tayi na'am da ita.
Dare nayi tazo ta fito da su a hankali ta zuba cikin motar ta da take fita school da ita, bayan ta gama ta kwanta tayi bacci kamar bata da wata damuwa.
Da safe ta shirya kamar dai zata wuce school tayi wa Hajjaty sallama sannan ta ja motar ta. Maimakon ta wuce school sai ta nufi hanyar garin Bauchi.

Sai bayan azahar ta isa tana isa ta samu wani restaurant ta ci abinci daga nan ta shiga cikin gari neman habibyn ta wanda tasha wahala kafin samun sa.
Bayan ta sanar da shi ƙudurin ta da kuma dalilin guduwar ta ne ya fara lallamin ta akan ta koma gida ammah fit ta ƙi daga ƙarshe ta e wallahi in Basu je anyi musu aure ba to zata sheƙe kanta. Babu yadda ya iya ya sanar da baban Bello da ya so yin jayayya shima daga ƙarshe ya yadda.

Sati na zagayowa aka ɗaura auren su tare da masoyin ta Abdulkarim, sai dai shi ko gida bashi da shi, cikin sarƙoƙin ta masu daraja ta bada ɗaya aka siyar, da kuɗin ya sayi gida ɗan madaidaici, two bedroom apartment with one parlour sai kuma kitchen da toilet.
Sauran kuɗin kuma ta sashi ya nemo jarin kayan shago tunda akwai jikin gidan su ya zuba. Sannu a hankali suka shimfiɗa rayuwar su mai cike da soyayya da kulawa. Wasu lokutan Madina kan shiga ɗaki ta sha kuka ta fito ammah ta ɗauki alwashin ba zata raba auren ta da masoyin ta ba, su kuma familyn ta suje ita ma ta yafe su.

Duk wannan waina da ake toyawa idrisu bai sani ba sai ranar yazo wucewa ya e bari ya tsaya ya siya sigari. Yana shiga yaga Abdulkarim a shagon, tun daga lokacin ya wuce wurin Bokan sa.
A lokacin Bokan ya sanar da shi ai shagon Abdulkarim ɗin ne kuma yana da mata ma, har da juna a jikin ta.

Cike da hassada yace boka ya durƙushe kasuwancin kowa ya rasa kuma shima ya kashe masa shi. Boka yace gaskiya shi duk hatsabibancin sa baya kisa sai dai ina shi da kan sa ya kashe shi tunda ɗan uwan sa ne.
Ana cikin haka fah kasuwanci ya fara ja baya, kafin shekara shago ya zama fankayau. Shawara ta bashi kan su sayar da gidan su nemi wanda bai kai wannan ba. Bayan sun sayar suka koma wata unguwar a haka ahaka bar ta haihu.....yarinya kyakkyawa ta haifa wacce kowa ya gani sai ya yaba don kuwa bata bar komai na Madina ba.

Ranar suna yarinya ta ci sunan Fatima Zahrah sunan mahaifiyar Abdulkarim taci. Sannu sannu yarinya ta fara wayo gashi sai ƙara kyau take yi.
A haka suka ci gaba da rayuwa har zuwa lokacin bata san wani idrisu ba ballantana shirin sa.

Kwatsam wata rana mai baƙin tarihi wacce ta kasance katanga tsakani ta da masoyin ta Abdulkarim. A ranar ne aka samu gawar sa a kusa da wani gidan mai an yi mishi kisan wulaƙanci, Madina tayi kuka sosai har sai da aka kwantar da ita a asibiti. Bayan taji sauƙi aka sallamo ta. Kai tsaye gidan ta aka wuce da ita da taimako mamar Bello.

Bayan ta gama takabar ta ne ta yanke shawarar komawa gida saboda wanda ta gudo domin shi ya tafi ya barta. A ranar da ta gama shirye shiryen ta ne aka ce ana sallama da ita a waje.
Bayan ta fita ta tarar da shi cikin wani koɗaɗɗen yadin sa da yaji jiki.
Suka gaida ta tambaye shi ko shi waye yace ai shi ɗan uwa ne ga marigayi idan ba zata damu ba shi yana so ya aure ta ne. Cikin zuciyar ta kuwa wani tsoron mutumin ne ya ɗarsu lokaci ɗaya ta amince da batun sa aka ɗaura musu aure. Cikin gidan ta na da ta tare sai dai tun da ta shiga gidan farin cikin ta ya ƙare.

Farkon auren ya kan kyautata mata, abinci haka baya mata shamaki da shi.
Bayan watanni kaɗan da auren salon shi ya sauya, a kowacce rana sai ya jibgi Madina tamkar dai mahaifin ta haka ya mayar da ita, yarinyar ta Zahrah baya ƙyale ta, akan idon ta yake jibgar ɗiyar ta ta sai dai babu yadda ta iya saboda mugun tsoron shi da take ji.

Shan giya da sauran kayan maye babu abun da ya bari sai ƙaruwa ma da yayi gashi bata da ikon hana shi, a na haka ya fara kafa majalisar matasa irin shi masu zaman kashe wando haka zasu yi ta busa hayaƙi a ƙofar gidan.
Ranar da ta yijarumta ta tunkare shi da maganar majalisa sai da yayi mata dukan Kawo wuƙa, a lokacin Zahrah bata haura shekara biyu a duniya ba haka ita ma tayi ta kuka ganin irin dukan da ake wa mahaifiyar ta. Tun daga wannan rana yarinyar ta sanya tsanar kawun ta a cikin ranta har zuwa girman ta.

Abinci da yake hana su daga gidan mamar Bello ake kawo musu, su ma bayan wani lokaci suka tarkata komatsen su suka koma Birnin Abuja da zama, hakan ba ƙaramin tayar da hankalin Madina yayi ba, takan ji ina ma ta gudu ta koma ga iyayen ta sai dai duk lokacin da tayi yunƙurin hakan sai ta gwammace bata yi ba, rashin lafiya ce zata kamata ga wani abu da zai tsaya mata a ƙirji kamar dutse. Hakan yasa ta fauwala lamurran ta ga Allah ta bar batun guduwa.....

Yanke shawarar sayar da wata sarƙar ta tayi bayan ta siyar ta siyo kayan suya kama daga tanda, bahuna plates na roba da sauran su ta fara soya Masar siyarwa sai dai ba'a kai ko ina ba mutanen unguwar suka daina siya dalilin mijin ta idrisu. Ganin yunwa zata iya yi musu illa ita da ɗiyar ta yasa ta fara soya Masar a kasuwa wanda hakan ya zama maslaha gare ta.

Bayan Zahrah ta kai shekarun shiga makaranta ta sanya ta a makarantar gwamnati, Zahrah ta tashi da rashin haƙuri da kuma masifa ga rashin kallon mutuncin manya, tun tana ƙarama tsanar kawun ta ta ɗarsu a ranta shiyasa ta ƙudurta a ranta duk ranar da tayi ƙarfi sai ta ramawa Mamah dukan ta da yake yi.

Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah har Zahrah ta shiga primary school wanda Mamah ke ɗawainiya da komai nata kama daga sutura zuwa karatun ta da kuma cikin ta.
Sam yarinyar ta tsani maza, a tunanin ta duk maza haka suke mugage marasa tausayi shiyasa ta ɗauki aniyar kare kanta daga kowanne irin farmaki namiji zai kawo gare ta, faɗa da maza baya damunta kuma koyaushe takan yi ƙoƙarin ganin tayi nasara kan su.
A kullum burin Zahrah bai wuce ta zama alƙali ba saboda take kulle duk wani mai laifi.

★★★★★



______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️



PROLOGUE


𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣5️⃣



SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________





Zahrah yarinya ce ƙarama sai dai Allah ya bata kaifin basira tamkar wata babba. Kukan da take yi ta tsayar jin kiran Sallah yayin da Mamah ta rungume ta kamar za'a ɗauke mata ita.
“Zahrah ta! Ke ɗin ta musamman ce kuma inada yaƙini akan ki, zaki iya ɗaukar fansar mahaifin ki ta hanyar da ta dace koda kuwa bayan Ni bana nan domin ina ji a jiki na zama na da ke ƙaiyadadde ne.”

Zame jikn ta tayi a hankali sannan ta share hawayen ta yayin da ta mayar da hannayen ta bisa kafaɗar Mamah.
“Na ɗauki wannan alƙawarin Mamah tah! Nayi miki rantsuwa da wanda rai na ke hannun shi duk wanda na kama da laifin raba mahaifi na da rayuwar shi bazan ƙyake shi ba, dole doka ta hau kanshi kamar kowa.”
Murmushin yaƙe Mamah tayi ta ƙara rungumo Zahrah jikin ta.
“na yadda dake ɗiya ta, Ni na kasa ɗaukar fansar masoyi na ammah nasan ke zaki ɗau fansar mahaifin ki. Fatan nasara takasance dake a kowanne yanayi.”

Da ƙyar suka tashi suka yi sallah musamman Zahrah da ke fama da gajiya shiyasa ta ce yau ba zata je islamiyya ba, abinci Mamah ta girka bayan sun ci suka kwanta don su huta.
Yinin ranar Zahrah a sukwane tayi shi ga wata fargaba da take ji. Zuciyar ta wani irin bugu take yi innalillahi wa inna ilayhi rajiuun kawai take maimaitawa.

Bayan Badi'a ta kawo abinci kamar kallum Zahrah ta amsa suka ɗan yi taɗin su kafin ta wuce. Serving nasu tayi a plate ɗaya ita da Mamah daga nan suka zauna suna ƴan zantukan su.

Ita dai yau Zahrah cike take da mamakin Mamah, yadda yau take ta ɓarin magana kamar mota maras birki, tun daga taɗin family nata har zuwa kan rayuwar ta gidan Abban Zahrah. Daga ƙarshe da ta ɗauki hakan a matsayin kewa tayi wa Mamah yawa shiyasa take maganar.

Bayan sallar isha'suka yi addu'a kamar kullum suka kwanta bacci.
Bacci mai uban nauyi ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login