Showing 12001 words to 15000 words out of 31694 words

Chapter 5 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

179

ta ce “Mamah bari naje banɗaki na dawo” Mamah bata ce komai ba saboda bata ji MEH suka ce ba. Zahrah na fita ta Banka musu wani bazan kallo mai ɗauke da ƙasƙanci da tsana kafin ta ja wani tsaki
“Mtsssss....daɗin ta ma gidan aka zo ana same ta”

Matar da ɗazu aka ƙira da lantana ce ta zaro idon ganin yarinya ƙarama na mata rasar kunya. A fusace ta yo man Zahrah babu shiri ta goje, wani ice ta gani a gefen ta tayi saurin rarumar shi”
Lantana Bata haƙura ba ta ƙara biyo Zahrah ai kuwa bata aune ba taji ice a bayan ta.
Ƙarar da tayi ne yasa Mamah da sauran ƴan kawo amarya fitowa.


Tunda ta jinka mata icen ta ja gefe tana sauƙe numfashi, lantana kuwa zube wa ƙasa tayi tsabar azabar da bayan ta yake yi. A hankali Mamah ta tako saboda ta taimakawa Lantana. Hannu ta miƙa mata cike da ƙuluwa ta doke hannun Mamah ta miƙe. Still ta ƙara yin kan Zahrah a fusace

“yau mai hana Ni cin bura uban yarinyar nan shima sai naci uban sa”

Babu alamar tsoro a tattare da ita sai karkaɗa jiki take. A hanzarce Mamah ta taho zata ja hannun Zahrah. Ɗaya daga cikin ƴan kawo amarya kuwa ta bangaje Mamah.

Abu ƙarami dai ya dawo babba. Don kuwa Zahrah janye Mamah tayi zuwa ɗakin ta. Jawo ƙofar tayi ta fito ta fara by bubbuga musu icen nan, ance Sarkin yawa yafi Sarkin ƙarfi ammah wannan karon naga ikon Allah.

Hayaniyar da ta kaurece ga kuma ihun matan ya jawo hankalin ƴan unguwar. Tuni gida ya cika ana ta tambayar ba'asi da ƙyar Ammi ta lallashi Zahrah suka wuce ɗakin Ammi. Labarin ya matuƙar ɓata ran Ammin. Saboda haka ta ja hannayen su duka biyun suka bar gidan.

Dare na yi aka kawo amarya tare da ƙawayen ta wanda shigar su kaɗai kaga kaga ƴan jagaliya, guɗa ce kawai ke tashi sai uban habaici da ake gabzawa wanda wacce suke yi wa bata ma san suna yi ba. Damah tuntuni labari ya isa kunnen Saudatu Kwalba, shi yasa ta tattaro duk ƙawayen ta da niyyar sai sun ci uban uwa da ƴar, sai dai babu yadda zasu yi takaici ya cika su ganin babu kowa a ɗakin, kenan har sun gudu?. Ai kuwa dabara ta zo wa Aunty Amarya kan in ango ya shigo ta haɗa shi da matar.
Ai kuwa ta samu na nasarar hakan. Ran kawu ba ƙaramin ɓaci yayi ba
“zasu dawo gidan su same Ni ai"

Su Kawu an ci amarci an gaji da amarci. Kwana biyu su Mamah basu dawo ba nan fah Kawu yasa sha jinin jikin sa.

“Fatan na Allah yasa dai ba aikin da nayi bane ya ɓaci, idan kuwa haka ne toh akwai matsala!”
“kai bazai yiwu ba!!! Inaaaah! Madina wallahi bayan barki ba!, Dole mu rayu tare kuma dole kiyi rayuwar ƙasƙaci!.

Yanzu dai ina da zaɓi ɗaya ne, dole na fita ko ina na zaga saboda na nemo su!, Ina sun tafi fa komai ya lalace, duk burin da naci zasu ruguje!!!
Zan nemo ku duk yadda kuka je ne”.

Ɓangaren yaya Ishaq kuwa ya keta hazo tare da kewar ƙanwar shi.

Wasa wasa sai da su Mamah suka shafe sati guda a gidan Ammi tukun na suka haɗo domin dawowa, Ammi ta bawa Mamah kayayyakin sakawa nata, na Badi'a kuma ta bawa Zahrah. Zuciyar su wasai suka dawo abun su. Lokacin da suka dawo Saudatu Kwalba na zaune akan shimfiɗar tabarma da tayi, gefen ta kuma ƙawar ta ce Asabe Bala'i sai hira suke yi.

Ɗauke da sallama su Zahrah suka shiga, Asabe ce ta ɗago tare da mamakin da ke bayyane akan fuskar ta sai kuma ta sauƙar da kan ta ƙasa. Ƙasa ƙasa gudun kada baƙin su ji ta tace
“ke Kwalba waɗannan su waye”
“ina kuwa zan san su waye” ta juyo wurin su Mamah. Ganin sun tunkari ɗakin kishiyar yasa ta miƙe zuwa wajen su. Cike da hatsabibancin ta irin na ƴan Iskan matan bariki ta wani riƙe kunkumi.
“baiwar Allah uban meh zaki yi kin shigo gidan miji na ba izini kin dashi ɗaki kumah?”

Murmushi mamah ta cilla mata wanda yasa zuciyar ta ƙara tafasa.
“kut!!!! Ina miki magana, toh don Ubanki jawo hannun ƴar ku mai zubin aljanun nan ki fita min gida”
“a'ah!, Shi mai gidan bai faɗa miki cewa mata biyu gare shi ba?”

Amsar da mamah ta bata ne ya tabbatar mata da cewa ita ce Madina matar Idrisu. Lokaci ɗaya ta shiga ruɗu. Mamah kuwa ta ciro key ta buɗe ɗaki suka shige ita da Zahrah.

Mamaki ya matuƙar kama Saudatu har sai da Asabe ta zo ta ja ta suka wuce ɗaki..
“ke Bala'i ammah idrisu ya raina Ni, irin wannan yaudara haka”
“wai MEH ya faru ne?"
“ke da kike gani wannan tsuleliyar matar da kika gani da yarinya mai shegen kyau kamar ɗiyar Mayu matar sa ce fah!!”
Shaye da mamaki Asabe ke kallon ƙawar ta.
“lallai in dai haka ne toh bamu ga ta zama ba”
“ai kuwa, yanzu meyeh abun yi?”
“rabu da ita kawai, zan bata shekara biyu zuwa uku ta sarara sannan na aika ta lahira shikenan, ɗiyar ta kuma ta zama jaka ta”
“Ammah Kwalba bakya tunanin a samu matsala kafin lokacin da kika bata?”
“A'ah Bala'i, ba a so a fahimci komai game da mutuwar ta, yanzu haka zan aika a kawo min Bibalo ta dawo waje na da zama ko dan saboda cikar buri na.
Idan Bibalo ta dawo nan kinga ai Sa'ar yarinyar ce, xan sa take cin zalin ta kuma na hana ayi magana har baƙin ciki ya kama uwar, daga ƙarshe cikin shekaru ukun da na ɗebar mata ciwon damuwa yayi mata mummunan kamu, sai na sa boka Bulebule ya ƙarasa min ita, daga nan kuma ɗiyar ta ta zama tawa, sai yadda nayi”

Dariya suka kwashe da ita suna tafa hannu
“kai ƙawa ta baki da dama!, Ƙwaƙwalwar ki tana mugun ja”
“ke dai ki bari, ko kin manta suna na ne ‘kwalba’?”
“hhhhhh haka ne fah, shiyasa nake daɗa ƙaunar ki”

(TOH KUN JI FA KUDIRIN AMARYAR KAWU, KO YA ZA'A KAYA?

Ɓangaren Mamah kuwa suna shiga ta ƙara kaɗe ɗakin ta, ta gyara zaman kayan abincin su da kyau, sai lokacin ta tuna yau da Ishaq ya tafi. Addu'a da fatan alkhairi tayi ta jera masa. Daga nan suka yi zaman su a ɗakin..

“zahrah” jin mamah ta ambaci sunan ta yasa gaban ta faɗuwa don ta San in tayi mata irin kiran nan toh abun is serious.
“na'am Mamah ta”
“kina ji na koh”
“eh Mamah ina jin ki”
“ko da wasa ban amince kiyi wa matar kawun ki tsiwa ba, kinga idan kika yi mata zaki jawo mana kawun ki ne shiga rayuwar mu, don Allah Zahrah ki mata biyayya kin ji"
Cikin sanyin jiki ta ce
“toh mamah naji ammah wallahi idan ta shiga harƙa ta ba zan ƙyale ta ba”
“zahrah kenan! Ba zaki taɓa sauya wa ba, baki tunanin gaba ne kam? Yanzu in aka ce bana nan rai yayi halin sa gashi kuma baki da kowa a duniyar nan fah? Su ɗin dai sune dolen ki a lokacin, kuma baki da wanda suka fisu, ya kamata zuwa yanzu ac kinyi koyi da hali na”
“haba Mamah Allah ma ya sauwaƙe, Ni zan riga ki mutuwa ma kuma mamah ai ko kin mutu akwai ahalin ki, shiyasa nake cewa Ni ki haɗa Ni da su ko da ace ke ba zaki je gare su ba”

Lokaci ɗaya yanayin Mamah y sauya, abun da take ji a ƙirjin ta Allah kaɗai ya sani, hawaye ne kawai ke zuba daga idon ta. Nan hankalin Zahrah ya tashi don. Ko kaɗan bata son ɓacin ran Mamah.
“mamah ta don Allah kiyi haƙuri Ni nayi miki laifi ko"
Jijjiga kai tayi don a halin yanzu ko kaɗan ba zata iya magana ba.
“shikenan kiyi haƙuri ba zan ƙara tambayar ki ahalin ki ba tunda na fahimci ba kyaso, kiyi shiru haka don Allah” ta ƙarasa itama hawaye na zuba daga idanuwan ta yayin da take goge wa Mamah nata hawayen.

Da ƙyar Mamah tayi shiru sannan ta kamo hannun Zahrah ta ƙanƙame cikin nata tamkar za'a ƙwace mata ita.
“ɗiya ta Zahrah, ba wai bana so ki san ahali na baneh sai dai kawai in anyi maganar ina shiga wani yanayi, kada ki damu wata rana da yardar Allah zaki gan su har ki rayu da su”
“shikenan Mamah na ta kaina na daina ba zan ƙara tambayar ki ba, to yi murmushi muga"
Ta faɗa tana lakuce kumatun Mamah. Nan da nan kuwa suka ware suka ci gaba da hidimar su.

Wajen azahar Ammi ta aiko Badi'ah da basket ɗin abinci ta kawowa Mamah. Sun daɗe suna hira da ƙawar tata kafin ta tafi. Suka ci abincin su kafin su fitar da kayan Masar Mamah su ka ƙara tsaftace su.

Da yamma Mamah ta wuce kasuwa wurin kasuwancin ta, alhamdulillah yau kam da wuri ta gama har aka zo ana neman masa. Da taimakon Lauwali suka dawo. Bayan ta sallame shi ya tafi. Duk abun da yake faruwa akan idon amaryar Kawu, jira kawai take mai gidan ya dawo ta zuba mishi yasha.

Ana yin Sallah sai ga Badi'ah da basket ɗin abinci, Mamah ta amsa tayi godiya sannan ta bata wancan na ranan because it's already washed. Badi'a na shirin fita taji an riƙe kafaɗarta, a tsorace ta ɗago ɗin ganin waye. Murmushi mai ɗauke da ma'anoni ta ke zuba mata.

“ƴan mata nace waye yake aiko ki kawo abinci?” tun da ga nan ta harbo matar,
“kenan wannan ce auntyn Zahrah, tab, tallai akwai matsala dole na sanar da Ammi" jin bata bata amsa ba yasa ta ƙara maimaita mata
“ƴan mata wai waye ke aiko ki kawo abinci ne”
“nimah ban sani ba, sake Ni na tafi gidan kada a neme ni”
“kenan ba aiko ki ake yi ba”
“eh Ni nake kawowa da kaina, sake Ni"
Banu yadda Saudatu ta iya ta sake Badi'a, a tsorace ta isa gida.

“Ammi Ammi Ammi!”
“kai Badi'a irin wannan ƙira haka ba ƙaƙƙautawa?” ta faɗa yayin da take fitowa daga bedroom ɗin ta.
“Ammi wallahi amaryar gidan su Zahrah abun tsoro ce, kamar ƙaruwa take. Ammi har tsayar da Ni tayi tana tambaya ta wai wa yake aiko Ni na kawo abinci”
“subhanallah sai kika ce mata MEH?”
“cewa nayi Ni nake Aiko kaina manah"
“yauwah good girl, u're very clever daughter, Allah yayi miki albarka”
“Amin ameen Ammi na”

Kawu bai shigo gida ba sai wajen 11:00pm na dare, yana shigowa kuwa ya fara washe baki yana nufar ɗakin amaryar shi. Lokacin tayi shirin ta ta zaba kwalliya tamkar zata fita yawon bariki.
Da sauri Kawu ya nufi yadda take. Peck tayi mishi haɗi da hugging nashi
“sannu da dawowa mai gida na“
Cike da ɗauki yace
“yace sannu amarya ta abar ƙauna ta”
Ɗan sake shi tayi,
“oyah muje kayi wanka kaji” ba musu Kawu ya biyo ta suka fito da yake toilet ɗin su a waje yake. Cike da ƙwarewa a harƙar barki ta kama hannun shi ta raka shi bayan yayi wanka suka dawo tare ta taya sanya kaya. Abincin da Rubber ta aiko musu da yammah ta zuba mishi, bayan yaci yayi hani'an tukun ya ɗago yana kallon amaryar.

“ko wannan matar ko ta dawo”
Cikin halin ko ina kula tace
“wace mata kenan?”
“ina nufin wannan banzar mai ɗakin can”
Ita kuwa jin ya ambaci matar shi da banza farin ciki ya mamaye zuciyar ta, cike da murnar samun nasara a Oman ɗin ta tace
“eh toh wata jemammiyar mata da yarinya dai sun shigo lokacin ƙawa ta Asabe tana nan, ai ka santa?”
Cike da ƙaguwa yace
“eh na san Asabe ƙawar ki”
“toh matar tana shigowa ita da yarinyar ta suka yo kan mu suna tambayar wacce ce daga cikin mu amarya.
Da Asabe ta nuna musu Ni sai suka kwashe da dariya, duk fushi da rashin mutunci irin namu kasa mata magana nayi ina jin ta riga da ta asirce Ni ne”
Ta faɗa tana sakin kukan munafurci.
Shi kuma sai lallaɓa ta yake kamar wata uwar sa.
“yi haƙuri amarya ta ki faɗa min me ke faruwa manah, tabbas duk wanda ya taɓa min ke zai ga fushi ne”
Ɗan guntun hawayen ta ta goge ta ci gaba da fuskantar shi
“kawai matar sai ta rufe mu da zagi, a nan ta kora Asabe sannan ta juyo kaina, yarinyar da suka shigo tare ita ma ta ɗaurabkan yadda matar ta tsaya sai zagi na suke wai Ni karuwa ce, abun babu daɗi” ta ci gaba da kukan munafurci nata.
“shine na basu haƙuri da ƙyar suka haƙura kuma sun ce idan na faɗa maka sai ta min shegen duka.
Daga haka ta juya ta nufi ɗakin gefen can naga ta buɗe, sai a lokacin na gane ita ce matar ka da kuma ƴar ka”

GA FA WANI SALO DA AMARYAR KAWU TA FARA
MUJE ZUWA, BA'A FARA WASAN BA.
KUYI COMMENTS DA YAWA DON SHINE ƙWARIN GUIWA TA.

ITZ DIAMOND LADY 💎
Oum Zainab


______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️



PROLOGUE


𝕻𝕬𝕲 0️⃣8️⃣

Bazan manta da ke ba ƙawa ta Murjanatu Abdulwahab Yusuf, ina matuƙar ƙaunar ki saboda Allah.
Na gode da ƙaunar ki gare Ni. Ubangiji ya ƙaunace ki.

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________


Ran Kawu idan yayi dubu toh duk ya ɓaci a fusace ya fita daga ɗakin amarya yayin da ta daka tsalle saboda murnar cin nasara.
Yana isa ko sallama bai yi ba ya fara buga ƙofar ɗakin yayi shaye da mamaki maka ta buɗe
Bata aune ba kawai taji sauƙar mari s fuskar ta. Bata tsaya ba kawai ita ma ta rama.
Mamaki ne ya kama Kawu wai yau shi Madina ta mara don ya mare ta, gaskiya akwai matsala. A kasalance ya koma ɗakin amarya yana huci..

“mai gida ba dukan ta kayi ba koh, bana so ko kaɗan taji haushi na”
Murmushin yaƙe yayi
“shikenan mata ta damah warning na kashe mata”
“yauwah mai gida ammah gobe ya kamata ace an raba mana girki da kuma kwana ko”
Shaye da mamaki yake kallon ta kafin yace
“ai nikam kullum ina nan, MEH zanyi da waccar matar kuma”
“aahmai gida ba za'a yi haka ba, zata ga kamar ina zaluntar ta ne” nan kuwa cikin ranta daɗi take ji.
“aah mu bar zancen nan, Ni anan zan je kwana”
“shikenan tunda ka ce haka” ta ɗanyi shiru sannan ta ci gaba.
“sai batun girki, ai yanzu tunda ta dawo sai a raba“
“ke dai zan ke baki ki girka, ita dama can ita take ciyar da kan ta da ɗiyar ta”
Daga haka ya miƙe zuwa gado, su basabun ba Kawu an samu gadin banza. Ita kuwa amarya farin ciki ne fal ranta.

Mamah kuwa tunda ta rama marin da Kawu yayi mata ta fara jin wani sanyi a ranta, kullin da take yawan ji a ƙirjin ta sai taji kamar ya ragu....ɗaki ta koma tayi alwala sannan ta fara jera nafilfilu daga nan bacci ya ɗauke ta. Washegari da wuri suka tashi, Zahrah ta shirya cikin uniform ɗin ta sannan ta zauna jiran Badi'a, ba'a jima ba ta shigo hannun ta ɗauke da basket,
“mamah Ina kwana"
“lafiya ƙalau Badi'a ya su Ammi?”
“suna lafiya, ga breakfast in ji Ammi Zahrah ki samu ki shirya kafin Abba ya gama breakfast”
“toh Allah ya amfana, ki gaishe da Ammi”
“toh" sannan ta juya zuwa gida.
Chips ta zuba a plate ta fara ci, tana gamawa tayi brush ta fito.
Sai da ta shiga ta gaida Ammi suka fito ita da Badi'a don jiran Abba.
Abba na fitowa suka gaida shi sannan suka tafi sai school.

Rayuwar school tana yi wa Zahrah daɗi a halin yanzu don kuwa cikin sati da ƴan kwanaki ta fara gane darasi sosai, uncle Hashim na yin iyakar iyawar shi wajen ganin Zahrah ta na koyon abubuwa. Alhamdulillah, da yake ƙwaƙwalwar ta na ja tuni tayi nisa.
Ga kuma Badi'a ita ma ba'a barta a baya ba wurin taimaka mata.

Yau suna da English, uncle Hashim ya shigo yayi delivering class ɗin shi kuma kowa ya gane daidai gwargwado. Bayan ya fita aka yi sauran three classes ɗin daga nan aka tashe su.
Kamar kullum.ya Abba ne ya zo ɗaukar su, suka gaida shi. Bayan su isa gida kowa ta wuce gidan su.
Zahrah na shiga taci karo da amaryar Kawu na girki, ɗauke kanta tayi don ita ba mai shiga abun da ba'a sanya ta baneh. Kamar daga sama taji Muryar matar
“ƴata babu gaisawa ne?”
Harara Zahrah ta cilla mata tare da nufar hanyar ɗakin Mamah. Murmushin mugunta amaryar Kawu tayi sannan ta ci gaba da girkin ta.

Wanka tayi sannan ta ɗauko uniform ɗin ta na islamiyya ta zura..Mamah na fitowa daga bayi daidai isowar Badi'a da abinci ita ma cikin shirin ta na islamiyya. Sannu Mamah tayi mata ta amshi abincin.

Zahrah na gama ci ta ɗauki jakar ta ta fice, da yake islamiyya ba wani nisa sosai daga gidan su yasa suka taka da ƙafa.
An samu sauyi sosai don yanzu Zahrah tana maida hankalin ta ga karatun ta na islamiyya, kuma hadda sosai take bayar wa.

Bayan sun dawo daga islamiyya wanka kwai tayi ta sauya kaya sannan tayi wanki. Tana gamawa ta fice zuwa kasuwa wurin Mamah. Sai bayan maghrib suka dawo. A daren suka wanke kayayyakin amfanin su kafin suyi dinner da aka aiko daga gidan Ammi.

Haka rayuwa ta ci gaba a gidan Kawu, babu abun da ya taɓa haɗa Baba Amarya da Mamah har suka shafe watanni uku a gidan sai dai a ɓangaren baba amarya kullum akwai abun da take ƙunsawa kuma har yanzu Kawu baya ciyar da Mamah da Zahrah.
A irin wannan lokacin ne su Zahrah suka fara exams, Alhamdulillah an gama kuma sakamako yayi kyau, Badi'ah Kabir Umar ita ce first sai Umar Yusuf sai kuma Zahrah Abdulkarim Kuru. Farin ciki kamar suyi yaya Abba yayi musu kyauta ta Musamman kuma lokacin Hutu Badi'a da Zahrah suka tafi Jos gidan yayar Ammi.

Hajiya Barira yayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login