Showing 9001 words to 12000 words out of 31694 words

Chapter 4 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

180

mutumi na, wannan ce yarinyar da muka yi magana da kai kenan"
“eh ita ce”
Wasu takardu ya fitar ya miƙa wa yaya Ishaq. Bayan ya kammala cike su ya ɗauko books cikin wani bag ya miƙa mata.

Haka dai aka gama komai a ranar aka bata uniform ɗin ta set II, farin ciki wurin Zahrah ba'a magana.

“ki jira Ni waje zan yi magana da malamin ku”
Ko amsawa bata yi ba ta fice zuwa jikin motar yaya Ishaq ɗin.

“Yauwah Man Please Please ka sanya wa yarinyar nan ido, ina so tayi karatu sosai”
“Alright I'll in Sha Allah”
Daga haka suka yi sallama.
Direct gida ya yi dropping ɗin ta.
“ki shiga zan shigo gobe na miƙa ki, ki gaida Mamah"
“toh yaya Allah ya kiyaye hanya”.

Kar kuso ku ga murna wurin iya Zahrah! Duk sai wani rawar kai take, Mamah kuwa kallon ta kawai take tana ganin ikon Allah. Yayin da wani ɓangare na zuciyar ta ke tausayawa yarinyar Tata.

Da yamma yaya Ishaq yazo.
Sabbin sandals da socks da wata school bag ya kawo mata.
yayi mata ƙarin bayani a kan makarantar sannan ya ja hankalin ta kan ta maida hankali.

“cutie na!" Ɗagowa tayi ta kalle shi
“ki dage da karatu kinji, ina so ki zama wata abu a rayuwa, ki zama abar alfahari gare mu baki ɗaya. Banda wasa, karatu kika je ba wasa ba, ki saboda haka ki maida hankalin ki ga karatun. Banda kula maza babu ruwan ki da su.... sannan banda faɗa. Kin gane ko?”

“eh na gane, in Sha Allah zanyi karatu da yawa"
Murmushi yayi yace
“Alright in naji labarin kinyi faɗa, hmmm”

Sallama yayi wa mama ya wuce shima don ya fara preparations na tafiyar shi London don yin masters ɗin shi. Haka kawai yake jin faɗywar gaba ko dan kawai sabon da suka yi da cutien shi ne ko kuwa,
“only God knows” ya faɗa can ƙasan maƙoshi.

Washegari tun 6:30 ta gama shirin ta. Kayan sun matuƙar ƙarɓan ta tamkar ɗin ita aka yi, Coffee brown trouser be sai Brown coloured hijab da riga. Sun matuƙar haska kyakkyawar fuskar ta tamkar wata sarauniya.

Horn ɗin da taji ne yasa ta ruga a guje zuwa waje.
Ko sallama bata yi wa Mamah ba ta fice abun ta.

Tun daga nesa yake hango ta tana tahowa. Ɗan lumshe idanuwan shi yayi ƙasan maƙoshi ya furta.
“She look so breathtaking, tabarakallah”.
Tana zuwa ta buɗe motar ta shiga

“ina kwana yaya Ishaq"
Cike da zolaya yace
“lafiya ƙalau zumuɗa, live kin daɗe da shirya wa.? Ehnn”
Fuskar ta ta rufe da hijabi tana turo baki
“kai fahimta kace na shirya da wuri”
“shine kika biye min?, Damah dai zumuɗin kike yi faɗa min gaskiya cutie" ya faɗa yana ɗaga mata gira..

A haka suka isa sannan ya ja hankalin ta kan tayi karatu in yazo ɗaukar ta zata biya mishi.
“bye”

Hannu ta ɗaya mishi sannan ta juya ta shiga. A lokacin ne students da dama ke zuwa. Kai tsaye ita ma shiga tayiba tare da nuna bata san school ɗin ba.

Unfortunately wani staff ya ganta. Da gani bai jin Hausa ma
“hey!” ya faɗa yana nuna ta da yatsa.

Wurin da yake ta nufa sannan tace good morning"
“morning, are u new here?”
It's da bata san ma me yace ba kawai sai ta ɗan tura baki da ta tuna da new na yace sai tace
“yes”
“ohk which class?”
Wannan kam da yake ta sani caraf tace “jss one”

Da hannu ya mata alamar ta shiga wannan class ɗin
“go and keep your bag there”
Kai ta gyaɗa kamar ta ji meh yace.

(Nace zaki sani in ya gano baki jin turanci duk buge kike yi😂)

Yaji daɗin yadda suka yi da malamin kawai sai taji tana son ita ma ta ƙware a turancin nan wallahi. a hankali ta shiga class ɗin babu kowa, kawai sai ta ajiye Baga ɗin ta a front seat ta fita.

Hanyar ta ta fitowa taga Badi'a na tunkaro ajin kawai sai taji tana don jiranta..

“Zahrah a makarantar nan aka saka ki" kai kawai Zahrah ta gyaɗa. Badi'a ta ja hannun Zahrah suka shiga cikin class ɗin, dropping bag ɗin ta tayi ta ɗauko ta Zahrah da ta ajiye a left sided front seat zuwa middle raw daga nan suka fita tare.

Bayan anyi assembly suka dawo class. First period Basu English ne, gashi malamin bashi da kirki duk tsoron shi suke. Yana shigowa suka miƙa gabaɗaya

“good morning sir”
“morning how's the weekend?”
“fine sir"
“ohk have ur seats"

Lesson plan ɗin shi ya ɗauko daga nan ya buƙaci marker daga wurin class rep. Bayan ya bashi ya rubuta TENSES sannan ya juyo
“good morning once again, our topic of discussion today is TENSES.
Is there anyone who'll tell us something about tenses?"

Shiru class ɗin yayi babu alamar motsi tamkar ruwa ya cinye su. Jin shirun su yasa ya yi pointing Badi'a,
“Badi'ah Kabir Umar, please say something” shiru tayi tare da sunkuyar kanta.

“Alright, the girl next to Badi'a say something"

Bata san ma da ita yake ba saboda ba jin turancin take yi ba. Zaro ido ƴan class ɗin suka fara jin taƙi tashi. Zata jawo musu bala'i wurin Uncle Hashim. Badi'a ce ta ɗan buge ta hakan yasa ta yi tunani ko so take ta faɗa mata MEH abun yake nufi.

(Ku ji Zahrah, ke da baki san komai ba ke zata tambaya?😂)

Uncle Hashim da ya fusata cikin tsawa yace
“you should get out of the class now” still shiru ita ina ta san ma da ita yake. Zaman ta tayi ta ci gaba da jin abun da ake.
Ganin duka class sun zubo mata ido yasa ta galla musu harara.

Fita uncle ɗin yayi hakan ya baiwa ƴan clsss ɗin damar mata magana, wasu na zagin ta wasu kuma na cewa tayi sauri ta fita.

“Zshrah kina ji yana miki magana kika yi banza da shi ko?, Baya wasa ki fita in ba haka ba zaki ji a jikin ki" Badi'a ta faɗa tana ɗago hannun Zahrah alamun ta fita waje.

Ƙememe Zahrah tayi tace “toh Ni na san da Ni yake ne"
Ku ji ikon Allah fah😂

Wannan shine ZAHRAH'S FIRST DAY AT SCHOOL
MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN ZAHRAH DA KUMA UNCLE HASHIM
SHIN MAKARANTAR NAN KUWA TA DACE DA ƳAR KAWU?

JUST FOLLOW MY INK AND COMMENT & SHARE
ITZ DIAMOND LADY💎🤟
Oum Zainab

______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊

️ ﷽

PROLOGUE

𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣6️⃣

Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________


Uncle Hisham har ya dawo class ɗin Zahrah na zaune kamar ba da ita ake yi ba. Fita ya ƙara yi sai Gashi tare da uncle Suraj (Mr Mugu as hey said). Uncle Suraj na zuwa students suka miƙe suna gaishe shi.
Ba tare da ya amsa ba yace su zauna.
Kallon su yayi fuskar nan ɗaure kamar fuskar shanu
“Among U who's the stupid girl that refused to obey Hashim's order?
Ya faɗa in a husky voice nashi.

Zare idon kowa ya fara. Ƙasa ƙasa Badi'a tace
“Zahrah don Allah ki tashi ki tsaya in ba haka ba in ƴan aji ne suka nuna ki sai ya miki shegen duka, don Allah ki tashi”

Banza Zahrah tayi mata kamar ba da ita ake magana ba. abu fah yayi abu, Zahrah ba dai taurin kai ba.

Duka su biyun sun tunzura,, hakan yasa suka wuce principal's office. Sanar da shi komai suka yi sannan ya ce su ƙyale ta, shi kuma uncle Hashim ya ci gaba da darasin shi after break za'a nemo yarinyar.

Ba don uncle Suraj ya so ba haka ya haƙura ammah tabbas yarinyar nan zata ci ƙwal ubanta.

Bayan uncle Hashim ya gama clsss ɗin yace lallai Zahrah taje principal's office yanzu.
Bata ma San meh yake nufi ba ta dai ji principal kenan ƙarar ta ya kai. Hmm.

Bin bayan shi tayi har suka isa, sai bayan ya shiga ta shiga,

Gaida principal ɗin tayi da turanci, ya amsa mata. Kneel down ya saka ta a gefe yayin da uncle Hashim ke zaune kan kujera..

“What's that your name miss?” principal ya tambaye ta. “Ohoh wannan ai na sanshi” ta faɗa cikin ranta.
“Zahrah Abdulkarim Kuru.” daga haka tayi shiru. Kamar wanda ya gano bata jin turanci sai ya dawo mata magana da Hausa.

“malamah Zahrah MEH yasa malam ya baki umarni kika ƙi bi?"
Kanta ta sunkuyar ƙasa
“mallam Ni ban san da Ni yake ba, kuma ban ji MEH yace ba”

Kallon baki da wayo ya mata
“kina nufin duk maganar da nayi baki ji ba, ƙarya kike” sai a lokacin ta fahimci ashe ya iya Hausa ma kuma shine da tayi shirin bai yi mata ba.

“Wallahi ban ji ba, Ni bana gane turanci da Hausa kayi min ai zan gane, kayi haƙuri”

Haƙurin da ta faɗa yasa ya sauƙo
“meh yasa to baki jin turancin?”
“makarantar gwamnati nayi makaman namu ma ba iyawa suka yi ba kuma yau na fara zuwa nan ɗin”

Nan da nan suka sake suna ta hira shi dai PC kallon su kawai yake.

“kina don ki koyi Turancin ko kuwa”
“ina so sosai, sai dai ban san yadda zanyi ba”
“shike nan kada ki damu zan na koya miki kullum ko abu biyu ne, lokacin break kike zama a aji zan ke zuwa.
Cikin murna tace
“na gode Mallam”
“tashi ki koma class".

Haka suka yi second period ammah lokacin uncle ɗin su bai tayar da ita ba. Lokacin da aka tashi kuwa tana fita taga motar yaya Ishaq, da sauri ta ƙarasa ta shiga.

“ƴan makaranta, hope kin ji daɗin makarantar” ɗan yamutsa fuska tayi kafin tace
“ga ta nan dai, Ni kam yau abun kunya dai nayi"
Zaro ido yayi jin tace abun kunya
“faɗa kika yi ko cutie"
“aah Yaya, wani malami ne yake ta min turanci Ni kuwa ban san meh yake cewa ba ashe wai cewa yayi na tashi na amsa tambaya.”

MEH yaya Ishaq zai yi in ba dariya ba. Ɓata ran da tayi yasa ya tsagaita.
“toh ya kika yi kuma?”
Ɗan bakin ta ta turo
“ Ni zama na nayi ban kula shi ba shine yace na fita, Ni wallahi ban san da Ni yake ba”
“ya zane ki kenan?”
“aah ai ban fita ba saboda ban san da Ni yake ba, shine ya ƙira wani mai fuskar shanu ko dariya da baya yi”

“sai kuma shi mai fuskar shanun ya zane ki?”
“aah shima cewa yayi na fita to ban san duk a kaina ake ba Ni kuwa nayi zama na, duk sai suka fita tare, shine malamin ya dawo ya ci gaba da darasin, Ni ban ma gane ba”

“shikenan kada ki damu zaki koyi Turanci fiye da malamin in kika sa kanki, mu bi na siya miki wani littafi ki gani”
Girgiza kai tayi sannan tace

“baka tambaye Ni ya aka ƙare ba ai"
“ina jin ki ai”
Shine da ya gama yace muje office ɗin wani ina ga dai headmaster be"

Dariya yaya Ishaq ya saka yace
“kai cutie babu headmaster a secondary School sai dai principal"
Ranta ta haɗe tamau
“toh ai Ni ba sani nayi ba”
“shikenan ina jinki, principal ɗin ya duka ki kenan”

“aah shi da Hausa ya min magana shine na ce masa Ni ban fahimci da Ni yake ba kuma bana jin turanci, malamin kuwa yaji tausayi na yace zai je koya min”

Murmushi yayi daidai isowar su wani bookshop.
“ki jira Ni ina zuwa”

Ɗauke da littafai a hannun sa ya fito
“yauwah karɓi waɗannan cutie, ki riƙe su da iya su zaki ita turanci, sannan ki ƙara maida hankali, duk abun da baki gane ba ki tambaya kinji kar kiji kunyar kowa”
“toh"

Ita kaɗai ta shiga gidan shi kuma ya juya.
Duk wainar da ake soyawa Kawu bai sani ba.

Bayan ta ci abinci kawai sai taji sha'awar zuwa islamiyya.
Wanka tayi ta fito. Ganin yadda uniform ɗin suka cakushe saboda rashin ya sa ta ɓata fuska.
“ke kuma lafiya?” Mamah ta tambaye ta
Kayan ta nuna mata sai wani tura baki take yi
“kiga kaya na kamar daga bakin kura aka amso su”
“toh ki shiga gidan su Badi'a ki goge mana kafin lokacin" da kamar bazata je ba sai wata zuciyar ta ce kije.

Sai da tayi nadamar zuwa islamiyya dan kuwa Ustaz Jamil sai da yaci ubanta kan fashi, kuma ya sata duk haddar da yake Binta sai ta biya.

Tun daga ranar kuwa tayi alƙawarin ba zata ƙara zuwa islamiyya ba ko za'a kashe ta, ammah da ta koma gida Mamah tace ai dole sai taje. Tsabagen bakin ciki kamar tayi kuka.

Haka rayuwar Zahrah ta kasance, cikin satin nan kuwa tayi mummunan sabo da ƙawar ta Badi'a yau in suna gidan Mamah to gobe suna gidan su Badi'a.

Ranar Asabat da yammah yaya Ishaq ya zo don yi wa su Mamah sallama.
Mamah kam har da kukan ta saboda yace ba lallai ya dawo ba sai bayan shekara biyu ko uku. Uwar gayya Zahrah kuka kamar zata mutu,

“haba cutie, meneneh kuma abun kukan? Ba dai zamu na waya da sabuwar wayar Mamah ba?, Toh kiyi shiru kinji, idan ma kin dage a school in na dawo sai mu tafi tare kema ki shiga jirgi"

Jin yace jirgi nan da nan ta goge hawayen fuskar ta
“shikenan yaya zan dage kuma zaka yi alfahari da ni”
Murmushi yayi mata sannan yace zo muje ki raka Ni siyayya..

Shopping mall suka je ya siyo mata kayayyaki da mayuka da sauran su. Sandals talkalma duk ya siya mata a cewar shi ko baya nan ba sai ta siya ba.
Daga haka suka dawo gida cikin farin ciki.
Ranar tare suka yi dinner, sai wajen 9:45pm ya tafi cike da kewar cutie ita ma cutie ya bar ta da kewa. Ko ba komai soyayyar mahaifi da ta rasa tana samun ta wurin yaya Ishaq ga kuma sabuwar ƙawar ta da kuma Ammi har da Abba. Hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba tunda Kawu yanzu ko ya zage ta ba kula shi take ba.

Ƙarfe goma da rabi suka fara shirye-shiryen kwanciya kawai suka ji an banko ƙofar ɗakin.. shaye da mamaki Mamah ke duban Kawu da ya shigo fuskar shi ɗaure kamr kumburarriyar fulawa. Zahrah ko ko kallon yadda yake bata yi ba.
Duban Mamah yayi yana wani cika yana batsewa..

“ke Madina, ina so ki share gidan nan gobe tatas kina ji ko?”
Caraf Zahrah tace
“toh kaga gidan cikin datti ne da zaka yi magana?”
Banu yadda ya iya da Zahrah kawai ya ci gaba da muzuran shi
“ni dai na faɗa miki, ɗaki na mah a ciro komai na cikin shi don kuwa gobe dalleliyar amarya ta zata zo gidan nan”

Zaro ido Zahrah tayi lokaci ɗaya yanayin fuskar Mamah ya sauya. Bata ce mishi ƙala ba har ya gama surfa bayanan shi ya fice fuu Kamar Mahaukaci.

Daren Mamah bata samu ta rintsa ba, ba wai saboda kishi ba aah sai don bata san waye Kawu zai auro ba.

Washegari tun safiya Mamah ta cika umarnin Baba, da kanta ta gyara gidan tsab gudun kada taƙi yi ma ya ci mata mutunci gaban baƙin amaryar.

Dawowar Zahrah daga school ta kafa rikici ita ala dole ba zata je islamiyya ba tunda za'a yi baƙi a gidan.

“haba Zahrah, yanzu inda kin zauna uban meyeh zaki yi a gidan”
Fuskar ta a kwaɓe take kallon Mamah
“mamah naga yau za'a kawo amaryar Kawu, Mamah ina tsoro su zo bana nan nasan ko sun miki abu ba zaki rama ba ammah idan ina nan zan tare miki” ta ƙarashe da Muryar tausayi.
“ke yarinya ce Zahrah, idan sun yi min ma a banza suka yi tunda ba kula su zan yi ba, maza tashi ki tafi makaranta.”

Ganin da gaske Mamah so take ta hana ta zama kawai ta ɓare baki ɓaaaaaa sai ihu
“wallahi Mamah in na fita ba zan dawo ba, tsayawa zanyi mota ta buge ni shikenan ai koh” ta fice a guje.
Mamah da ta rasa abun yi sai tabi bayan ta tana ƙwalla ƙira
“zahrah, Zahrah ki dawo shikenan na yadda" duk da ta ji me Mamah tace tayi burus ta ƙara wa bujen ta iska, Mamah na biye da ita har suka kawo ƙofar gida tukun ta juyo. Marakraice fuska Mamah tayi hakan yasa ta dawo ta rungume ta duka su biyun suka fashe da kuka mai ban tausayi.

Sai zuwa yamma tawagar amarya suka zo, ihu da shewa ba'a magana. Sai da suka gama jere suka fito tsakar gida su ka fara zage zage.

“Munafika uwar kishi tayi luƙus a ɗaki”
Wata daga cikin matan tayi caraf
“kin san damah ba zata fito ba ai. Irin matan nan fah sai Saudatu ta dage, don kuwa ko meh kika musu ba zasu ji haushi ba”
Ɗayar matar da ta fara magana tace
“toh ai babu zuciya kin sani, shi yasa tayi shiru”
Hannu suka tafa suna sake guɗa da shewa irin nan matan barikin nan.
“ƙawa ta baki da dama, wallahi gaskiya ne maganar ki, kin san ance bata da dangi, kamar ma Idrisun tsinto ta yayi”
“Toh Allah dai ya kiyaye, ammah dole Saudatu ta dage”
“ke dai lantana kawai ki bari"


______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️



PROLOGUE

𝕻𝕬𝕲𝕰0️⃣7️⃣

Wannan shafi sadaukarwa ne gare ku masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________



A kunnen Zahrah suka faɗi komai yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login