Showing 15001 words to 18000 words out of 31694 words
Chapter 6 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete
Ammi ce, uwar su ɗaya uban su ɗaya. Tana da yara huɗu, yaya Affan, Aunty Fadila, Aunty Aisha sai ƙaramar su Khady.. sun samu tarba ta musamman daga wurin Hajiya da kuma yaranta..
Yaya Affan baya nan yana Cyprus, a can yake karatu, Aunty Fadila da Aunty Aisha su kuma sun gama secondary sun fara karatu a ATBU ammah an saka auren su tare. Khady kuwa sa'ar su ce, yarinya mai ɗan karen kinibibi da rashin ji, rayuwar su a Jos tayi musu daɗi, sai da suka shafe sati biyu suka dawo Bauchi. Abun mamaki duk budurin nan Kawu bai san Zahrah baya nan ba, abinci kuwa kullum sai Ammi ta shigo da kanta ta kawo.
Baba Amarya abun na ci mata tuwo a ƙwarya saboda haka tun da Kawu ya dawo take mishi kuka wai ita ta gaji.
“nikam na ganiii zan bar gidan nan don har ga Allah bazan iya rayuwa cikin sa ba”
“yi haƙuri amarya ta meh aka yi miki har kika gaji da gidan”
Share ƙwallar idon ta tayi tace
“Wannan matar taka bata son zaman lafiya, haka kawai sai ta turo yarinyar ta mai zubin Mayun nan tayi ta zagi na, yarinyar nan har da zubar min girkin da nayi maka wai kowa ya rasa tunda su baka basu, nikam tsiro nake kada wata rana baka nan su yanka Ni"
Rungume ta yayi jikin shi
“aah ki bar Ni da su, zan hukunta su kuma ba zasu ƙara shiga rayuwar ki ba, ke da gidan ki ai ina kin ce na kora su sai na kaɗa su.
“uhm uhm ka bar su zasu ce nayi musu munafurci an kore su, Ni ina son zaman lafiya tare da su, suna bani tausayi”
“shikenan zan bar su ammah zan gargaɗe su akan ki don baza su takura miki ba a Cikin gidan ki,
Yanzu dai zubo min abinci naci”
Bayan yaci abinci yayi wanka ya nufi ɗakin mamah. Ta idar da Sallah a lokacin tana tasbihi ya shigo bata ko kalle shi ba ta ci gaba da tasbihin ta.
“keeee Madina, kwana biyu ina ɗaga miki ƙafa daga ke har shegiyar ƴar ki zaku takura wa amarya ta. Kar ki ga nayi sanyi kiyi tunanin tsoron ki nake ji, wallahi daga ke har ita Zahrah zan azabtar da kuma fiye da tunanin ku akan mata ta”
Daga haka ya fice a fusace, a tsanake Mamah ta bishi da ido har ya fice. Ta girgiza kanta sannan ta maida hankalin ta kan karatun Alkur'ani da ta fara.
Ranar da su Zahrah suka dawo sun dawo da goma sha tara ta arziƙi daga Jos.... kayayyakin sawa da makamantansu duk sun samu ga kuɗin da aka basu.
Mamah tayi farin cikin dawowar Zahrah gida don kuwa kullum sai tayi kuka ina ta tuna ta.
Sun koma makaranta lafiya tare da ƙara maida hankalin su a karatun su both ALMUNAUWARA da kuma IMAM MAKIK. Zahrah ta zamo zakara don yanzu ana matuƙar ji da ita cikin school ɗin su. Sam bata shiga sabgar kowa in ba ƙawar ta Badi'a ba, ammah duk wanda ya shiga sabgar ta toh ya shiga sabgar ta bata ƙyale wa.
Ɓangaren Mamah ta ci gaba da suyar Masar ta a kasuwa, kuɗin kuwa tana adana shi saboda gaba, don a halin yanzu babu abunda ta nema ta rasa, abinci za'a kawo tun daga breakfast, lunch har dinner daga gidan Ammi. Sun ɗauke su tamkar jinin su hakan yasa damuwar Mamah ta ragu uwa uba yanzu babu wata alaƙa tsakanin ta da Kawu, sai ya share watanni biyu basu haɗu ba hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba lokaci ɗaya daga ita har Zahrah suka murmure jiki ya ƙara kyau. Bana amarya ma dai bata shiga sabgar su saboda bata samu damar hakan ba ammah ƙudurin ta yana nan dangane da su.
Tufafi ma dai basu rasa ba saboda Abban Badi'a yana siya musu, school fees kuwa already Yaya Ishaq ya biya mata har kammala junior studies nata.
Wasu lokutan in ta zauna ita kaɗai babu abun da ke faɗo mata sai yaya Ishaq wanda a halin yanzu bata san ya yake ba, ko yana lafiya ko akasin haka. Takan yi mishi fatan alkhairi domin kasancewar shi haske cikin rayuwar ta, sanadiyar shi yanzu ta samu wayewa fiye da da, addu'a kuwa kullum cikin sallolin ta bata mantawa da yaya Ishaq tare da fatan Allah ya dawo da shi lafiya.
Bahaushe yace sannu sannu asarar mai rai yanzu haka Zahrah sun kammala jss 1 ɗin su, sakamako mai kyau mai haskaka wa kowa mamaki yake yadda Zahrah Kuru ta zama popular cikin school ɗin duk da cewa lokacin da tazo makarantar she's nothing but a stupid girl. An now she shines everywhere gata dai yarinya ce ammah akwai ƙwaƙwalwar manya. Hakan yasa ta samu farin jini da ɗaukaka kama daga ƴaƴan uwanta students, seniors ɗin ta, teachers na baa barsu baya ba hakan duk da taimakon uncle Hashim da kuma Aminiyar ta Badi'a.
WANNAN KENAN
TEAM ZAHRAH KUYI FARIN CIKI MUTUNIYAR KU TA DAGE FAH
KO INA YAYA ISHAQ HAR YAU BAI NEMI CUTIEN SHI BA?
HAJIYA BABS AMARYA FA TANA NAN TANA SHIRI, KO ZATA CI NASARA.
KU BIYO NI TARE DA ALƘALAMI NA DON JIN YADDA ZATA KAYA.
BA'A FARA WASAN BA HAR YANZU.
DIAMOND LADY 💎🤟 CE
(Oum Zainab)
______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
﷽
PROLOGUE
𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣9️⃣
Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘
SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________
Yau rana ce ta musamman da aka ware a cikin makarantar ALMUNAUWARA ACADEMY kamar yadda ya kasance cikin tarihin makarantar duk shekara akan gudanar da bikin yaye ɗalibai -speech and prize giving day-.
Ko ina na makarantar ya ƙawatu kasancewar makarantar ta ƴaƴan masu hannu da shuni ne. A nan aka fara gabatar da programs da ke a agenda na taron.
Cikin programs ɗin akwai drama show da wasu students zasu gabatar. Drama ɗin an shirya ta ne only to motivate the students. Cikin lokaci MC ya sanar da agenda na gaba, wanda shine drama show.
Wani curtain da ya kasance tamkar decoration naga an yaye. Babu abun da ya bayyana sai herarrun seats da aƙalla zasu kai 30 daga can baya. Ta gaba ɓangaren hagu akwai evidence box sai kuma ta can tsakiya kujeru biyu da kuma tables biyu. Ɗaya ɓangaren by the right hand side wasu kujeru ne dake facing waɗannan seats sai kuma can jikin bango babban table da wata lallausar kujera.
Haka wajen ya tsaru, babu ɓata lokaci jama'a suka fara shigowa suna zama a waɗannan seats ɗin. Badi'a ce da kuma khalid suka shigo cikin kayan lawyers ɗauke da files a hannun su. Suna zama sai ga Umar ya shigo ya tsaya near the evidence box.
Maryam kuma ta zauna a seat ɗin dake facing mutanen by the right hand side. Onportunately sai ga Zahrah well dressed in judge's dress, ga kuma wasu sanye da kayan police na biye da ita.
A hankali ta ke takowa har ta iso seat ɗin da aka tanada domin ta. Kowa a lokacin ya miƙe har sai da ta zauna sannan ɗaya daga cikin police ɗin ya miƙa mata files da sauran abubuwa gaban ta.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta ciro glasses 👓 ɗin ta ta sanya, nace MASHA ARRAHMAN, Files ɗin ta fara buɗe wa sannan ta umarci Muhammad da ya karanto cases da suke da shi. Cikin harshen turanci ya fara magana a nutse..
"Case na farko:
Ana zargin Mallam Uba Idi da safarar ƴan mata da kuma miyagun ƙwayoyi tare da lalata wata ƴarinya da tazo Companyn shi neman aiki wacce a halin yanzu ta mutu.
Case na biyu:
Ɓarayi guda uku, Dauda, Muhammadu, Idris da shiga gidan wani attajiri don satar daga ƙarshe har ta kai ga kashe mutumin da ahalin sa"
Daga haka ya ɗan rusuna sannan ya zauna.
Zahrah da ta make ta ce
“su waye lauyoyi”
Badi'a ce ta fara tashi haɗe da rusunawa
“Suna na Barr.. Badi'a Kabir, nice lauyan Wanda yayi ƙara” sannan ta rusuna ta zauna.
Khalid ma ya miƙe
“I'm Barr. Khalid Umar, I'm for defense counsel" daga haka ya rusuna.
Cike da ƙwarewa suka yi zaman nan tamkar dai a court ɗin gaske suke gudanar da shari'ar sannan aka yanke wa masu laifi hukunci daidai da laifin su. Daga nan aka sauƙe curtain.
Manyan baƙin mu appreciated the drama sannan sun bada kyaututtuka da dama wa waɗanda suka yi wasan, yayin da wasu suka ware kyauta ta Musamman ga Justice Zahrah Kuru wacce ta matuƙar burge mutane da damah.
Haka aka ci gaba da gabatar da programs har aka kammala. Daga nan aka fara raba prizes.
Zahrah ta karɓi prizes sosai ita da Badi'a. Irin prizes ɗin da ta karɓa yasa a wajen wakili Governor ya Bata kyautar garin kuɗi har 100k haka sauran jama'ah suka yi ta mata kyaututtuka na ban mamaki.
Anyi taro lafiya an gama lafiya. Lokacin tashi Abba yazo ya ɗauke su sai gida. Mamah da Ammi sun yi matukar alfahari da ƴaƴan nasu ammah duk wannan sha'ani da ake yi Kawu da amarya babu wanda ya sani. Shaye shayen Kawu kuwa sai abunda ya ƙaru...dabar su ma ta dawo tamkar dai da yanzu kuwa har shiga cikin gidan suke yi saboda samun dama daga Bana amarya.
Ranar Monday suka je makaranta. Principal ne ya aiko a ƙira mishi Zahrah Kuru. A tsorace ta fito daga class ɗin su ta nufi office ɗin principal da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga bayan ya bata umarnin hakan
“good morning sir"
“morning Zahrah, how's studies?”
“Alhamdulillah sir. I was informed that u want to see me”
Ba tare da ya bata amsa ba ya ɗaya phone ɗin shi ya kara a kunne, bayan few seconds aka yi picking.
“Assalamu Alykum" baa jin meh ake cewa daga ɗaya ɓangaren daga bisani ya miƙa mata wayar. Ba tare da ta san wanene ba cikin Muryar ta mai daɗin sauraro tayi sallama. A lokacin kuma principal ya fita daga office ɗin.
Jin Muryar cutien shi ya sake wani murmushi mai ɗan sauti
“wa alykumussalam cutien yaya”
Bata san lokacin da ta cilla wani ihu ba saboda farin ciki sai kuma hawaye sharrrr
“aah cutien yaya kuka kike yi? Toh shikenan lemme hang off the call and I won't call again”
Da sauri ta share hawayen ta kamar tana gaban shi
“i'm sorry yaya Ishaq, kukan farin ciki ne, ina kwana ya karatun"
“Alhamdulillah cutie, ya Mamah?”
“lafiyae ta ƙalau, kusan kullum sai tayi jajen ka”
“Ayyah ki gaishe ta zan aiko muku saƙo in Sha Allah”
“toh Yaya mun gode, i thought har ka manta da mu"
“ni ina na isa na manta da ƙanwa ta!, Rufa min asiri kullum cikin kewar ku nake"
Murmushi mai ɗan sauti tayi daga ɗaya ɓangaren yace
“ba wannan ba dai cutie, jiya naji abun alkhairi da kika yi, kuma na gani. Ina alfahari da ke ƙanwa ta, ki ƙara dagewa Please”
“in sha Allah yaya”
“shikenan sai anjima, damah I called only to complement on your performance and I'm proud of you zahrah"
“thank you yayah, bye”
Daga haka ƙiran ya katse. Principal ne ya shigo tare da uncle Hashim da uncle Suraj.
A nan kowa ya yabe ta tare da faɗin irin alkhairin da makarantar ta samu sanadiyyar drama show ɗin su, Governor daga baya da kanshi ya aiko wa makarantar saƙo kuɗaɗe masu yawa haka manyan mutane suka bada kuɗaɗe su mah. She's totally speechless on how victorious she's, and she promised to do better than this. Daga ƙarshe yace ta turo baban ta domin karɓa mata kyaututtukan da ta samu, in ta fita ta kira mishi Badi'a.
“ohk sir" daga haka ta fice zuwa class. Badi'a ma same message aka yi passing mata. Finally they decided to send Abba, don ita ko karen huka ne ya cije ta ba zata taɓa turo Kawu matsayin wani nata ba. Toh me mah ya kai ta? Mutumin da bai san ci ko shan ta ita da mahaifiyar ta ba a matsayin shi na wadda hakƙin su ke a wuyan shi, bai don ko da lafiyar su da rashin ta ba. Inaaaah ba zata taɓa ba ko da kuwa alkhairi zai wuce ta ne.
Haka har lokacin tashi suka koma gida daga nan suka tafi islamiyya. Bayan sun dawo kowa ya wuce gidan su.
★★★★★★★
Tafiya suke ita da Asabe Bala'i cikin wani ƙungurmin daji wanda ke da matuƙar duhun tsiya suna tafiya suna sare ice saboda irin bishiyoyi masu canopy ɗin an ne a ciki.
Sunyi tafiyar da ta kai kimanin 2hours kafin su iso wajen wani old building Wanda ke zagaye da wasu bishiyoyi masu baƙaƙen leaves. Daidai ƙofar wajen suka nufa.
Tsawa aka buga musu
“kai!!! ba'a shigowa nan da ƙafar damah! Ku fice”
A tsorace dukan su suka juyo don irin yadda Muryar ta kasance maras daɗin sauraro da kuma mugun tsoratarwa...
“zaku iya shigowa yanzu ammah kada ku kuskura ku shigo min da ƙafafun dama”
A ruɗe suka shiga kamar dole.
Wani irin gini ne maras kyawun fasali, jikin ginin baƙi ƙirin ga wasu ƙwari baƙaƙe dake yawo jikin ginin, duhu ne ya mamaye wajen lokacin ɗaya suka rasa inda da zasu sanya kansu yayin da suka ji wata guguwa ta tashi, rumtse idanuwan su suka yi sannan suka ji iskar ta janye su zuwa wani sashe. Lokaci ɗaya haske ya bayyana a wajen, suna buɗe idanuwan su suka gansu zube gaban wani mutum mummuna..
Idan nace muni to fah munin ya wuce misali, fuskar shi ne baƙa ƙirin ta yamutse ga uban gashin kai kamar na wata baindiya sai dai nashi babu alamun gyara, gemun shi ya kai saitin guiwar shi
Tsayin sa kuwa ba'a magana haka girman jikin sa ya wuce misali. Sam ba shi da daɗin gani.
Dariyar shi ce ta ƙara tsoratar da su suka fara zazzare idanuwan su kamar waɗanda suka yi wa sarki ƙarya.
“Hhhhhhh.....Saudatu Kwalba tare da ƙawar ta Asabe Bala'i.
Hhhhh...hhhhhhh.....barkan ku da zuwa fadar Bulebule Bokan kowa hhhhhhh....hhhhhhh....”
“mun go....de...ran....ka..shi...daɗe....”
Lokaci ɗaya ya haɗe fuskar shi ya fara duban su.
“Kwalba kin zo akan kishiyar ki ko?" Cike da mamaki ta ɗan kalli boka Bulebule.
“kin zo ne akan ta mutu ammah ba yanzu ba sai nan da shekara biyu sannan ki mallake mijin ki da kuma ƴar ɗan uwan sa zahrah”
“eh haka ne ranka shi daɗe ka taimaka min”
“shikenan kada ki damu"
Wata ƙwarya ce ta bayyana a gaban shi, cikin ta ya fara surkulle yana furta wasu maganganu. Can ya buga kwaryar nan da nan ta ɓace
“Akwai matsala! Matar nan ba zata mutu ba sai dai zanyi miki wani aiki da zata haukace, idan ta haukace ita da kanta zata fara jinya sai ta gudu ta bar gidan. Ita kuma ɗiyar ta zaki mallake ta ammah akwai babbar matsala don kuwa akwai manya manyan sheɗanu a tattare da ita wanda Ni kaina tsoron taɓo su nake.
Mijin ki ki sa a ranki kin mallake shi. Hhhhh....hhhhhhh...hhhhhhh..”
“yauwah ranka shi daɗe na gode sai kuma kuɗin aikin"
Dariya yayi sannan yace
“bulebule baya karɓar kuɗi kasafai sai dai ladan aiki da zaki bashi wanda ya kasance mai sauƙi. Zaki zauna a tare da ni na kwana biyu, zan yi amfani da ke sau biyar”
Ba tare da ta damu ba tace
“shikenan ranka shi daɗe na gode”
“ke Asabe zaki iya tafiya ita sai nan da kwana biyu ammah in kina so zaki iya zama zan baki ɗaki kema anan”
“shikenan ranka shi daɗe zan kwana a nan ɗin”
(Authubillah!!! Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yace :duk wanda yake wurin ɗan duba, ko kuma boka, kuma ya aminta da abun da ɗan duban ya faɗa masa toh haƙiƙa ya kauracewa abun da aka sauƙin min”
Mata muji tsoron Allah mu sani mutuwa tana nan tana jiran mu, MEH yasa in muna da bukata bazamu riƙa wurin Allah ba?
Shi fah in ka roƙe shi zai amsa maka kuma baya gori dan ya baki. Saboda haka ki kiyaye in son mallake mijin ki toh ki kyautata masa da haka zaki sace zuciyar sa kai har ma da ta dangin sa matsawar kina kyautata musu.
Allah ya tsare).
★★★★★★★
Abba da kan shi ya amso musu kyaututtukan su. Cike da farin ciki ya dawo yana nunawa Ammi. Sunyi farin ciki da nasarar yaran musamman Zahrah da ta kasance babu mai tsaya mata damah. Sai da yammah dab da dawowar su daga islamiyya suka wuce zuwa gidan Mamah.
Tabarma ta shimfiɗa musu
“sannun ku da zuwa maraba lale”
“sannun mu Maman zahrah”
Bayan sun zauna ta ɗebo musu ruwa. Ba tare da nuna ƙyama ba Ammi ta kurɓi ruwan.
“ina wunin ku ina gajiya”
“lafiya ƙalau Maman Zahrah"
“ya hidima kumah, Allah dai ya saka muku da alkhairi Abban Badi'a"
“amin babu komai Maman Zahrah ai yiwa kai ne,"
Murmushi mamah tayi. Abba ya gyara murya sannan ya fara magana
“toh kamar dai yadda kika ganmu a nan mun zo ne don taya ki murna bisa nasarar da Zahrah ke samu a makarantar su ta boko. Shekaranjiya anyi tarin yaye ɗalibai a makarantar tasu, toh a nan ta samu kyaututtuka da dama, akwai kuɗaɗen ta kimanin Naira Dubu ɗari biyu (200k) Wanda ta samu daga wurin manyan mutane a faɗin jahar da kuma wajen ta.
Saboda haka ne ma na amso musu saƙon ita da ƴar waje na Badi'a.”
Cike da farin ciki Mamah tace
“madallah Allah ya saka da alkhairi Allah yasa mai amfani ne”
Ammi ta amsa da “Ameen”
“toh saboda haka ne nake ganin MEH zai hana kije ki buɗe account sai a zuba miki kuɗin a ciki” girgiza kai mama tayi
“Aah Abban Badi'a ba za'a yi haka ba, kawai ka riƙe kuɗin a wajen ka ina ga zaifi. Idan a waje na ne zai iya salwanta a banza ammah idan a