Showing 6001 words to 9000 words out of 31694 words

Chapter 3 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete

23 Jan 2025

178

mai zafi sannan ta haɗa mata tea Mai kauri da sauran kayayyakin da Ishaq ya siyo musu.

Bayan sallar maghrib yaya Ishaq ya fita sallah sannan Mamah ma tayi. Kallon Zahrah tayi tace “zaki iya sallar?" Kai ta gyada a hankali Mamah ta taimaka mata tayi alwala a zaune sannan tayi sallar ma a zaune.
Bayan yaya Ishaq ya dawo Mamah ta shiga kitchen don girka abinci, ya rage iya yaya Ishaq ne da Zahrah. Kallon ta yayi yace

“cutie, meh ke damun ki haka kike sa damuwa a ranki”
“babu komai yaya Ishaq, meh ka gani?”
Wani kallo ya watsa mata
“baki yadda Ni ɗan uwan ki baneh da ba zaki iya sharing damuwar ki da Ni ba ko?”
Jijjiga kai tayi tace
“aah yaya babu komai fah, Ni mah ban San meh ya same Ni ba kawai dai Kawu ya zo dukan Mamah shine na tare, daga nan ban san ina nake ba”.

Shiru yayi yana nazarin wannan kawun da take faɗa, yana don ganin shi gaskiya.
“shikenan cutie, ki huta kafin Mamah ta gama girki”

Bayan sun ci dinner tukun na Yaya Ishaq ya tafi.

TOH FAH, YA RAI ZA'A KAYA, YAU KAWU ANJI JIKI WURIN ALJANU
KO kAWU ZAI SAUYA HALI?

Duk cikin babban gida.
BA'A FARA WASAN BA, JUST FOLLOW MY INK
THE DIAMOND BHATOOL💎🤟
LIKE AND SHARE


______________★★★_______________
Typing 📲
🏡BABBAN GIDA🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️



PROLOGUE


𝕻𝕬𝕲𝕽0️⃣ 4️⃣

Ina matuƙar godiya masoya na! Wannan PAGE ɗin naku ne. Allah ya bar ƙauna. Much love 😘😘😘

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________



Har zuwa lokacin nan Kawu bai fito ba, ganin haka yasa Mamah zuwa ƙofar ɗakin ta leƙa.
Suna haɗa ido ya galla mata harara hakan yasa ta fito waje babu shiri.

Sai bayan sun shiga ɗaki Kawu ya fito. Jikin sa yayi ruɗu ruɗu kamar wadda aka yi ma bulala.
A hankali ya lallaɓa ya fice.
Kai tsaye gidan Aminiyar shi jummai Rubber ya nufa.

Masu gadi sanin shi da suka yi da irin yadda yake alaƙa da uwarɗakin su yasa suka buɗe mishi. Ba tare da ya kula su ba ya wuce zuwa cikin gidan.

Zaune take daga ita sai wani matsiyacin shiru wanda da shi Gara babu, sai kuma bra.

Fara ce sol, jibgegiya. Can ƙarshen parlourn wasu ƴan mata ne da ba zasu wuce 23years ba tsirara haihuwar uwar su sai masha'ar su suke yi (authubillah). Ko kunya babu haka suke ta abun su basu daina ba har sai da Jummai Rubber ta Basu umarnin fita zasu yi magana da baƙo..

A haka suka fice yayin da Rubber ta zubawa Kawu ido tana nazartar shi.

“Takawar ka lafiya gwarzo jarumi, ka daki kowa ko zagi kowa, ko mutuwa tsoron ka take ji”
Murmushi yayi da jin kirarin Rubber sannan ya maida hankalin sa gare ta.

“Rubber magana mai muyi”
Dariyar shaƙiyyanci ta saka sannan tayi shiru
“ai in na ganka idrisu na san magana ta kawo ka, ina jin ka”

“yau wani mummunan abu ya faru da ni”
Nan ya kwashe drama ɗin su da Zahrah ta bata. Ita kanta abun ya girgiza ta in dai har kuwa da gaske ne akwai matsala.

“ni babbar samuwa ta ma bata wuce sanin Ni na kashe baban ta ba, ga kuma sanin ƙwayoyin da nake miki safara”

Cikin kwantar da hankali Rubber tace “Kaga kada ka wani damu, shawara ɗaya ce zan baka idan ka bita to zaka wuce wannan step ɗin”

Cike da ƙaguwa ya kalli Rubber sannan ya rungume ta (nace oh ita ɗin ma matar shi ne kam?)
Cikin kunnen shi ta faɗa mishi wata magana wanda duk gulma ta ban jiyo meh suke faɗa ba sai ji nayi yace
“gaskiya Rubber me ta daban ce”
Murmushi tayi sannan ta manna mishi peck a kumatu daga nan wasan ya sauya salo
(Authubillah)

Sai da suka gama suka yi wanka tare. A nan ya suka ci abinci kafin ya nemi wani ɗaki ya shiga. Wata ƴar Siriyar budurwa ce ta shiga ɗakin Bayan shi, jikin ta babu wasu kayan arziƙi haka ta shiga tana wani karairaya kamar macijiya. Tare da Kawu suka kwana suna sheƙe ayar su Ni kuwa nace (Allah ya shirye su).

★★★★★★★★

Alhamdulillah! Cikin ikon Allah jikin Zahrah yayi sauƙi, da safe Mamah da kanta tayi musu girki, bayan sun karya Mamah ta kai mata ruwan zafi toilet tayi wanka! Ba'a daɗe ba yaya Ishaq yazo.
Tayi murnar ganin yayan ta sosai shima yaji daɗin ganin jikin da sauƙi..

Gaisawa suka yi da Mamah cike da girmamawa. Ya Ishaq yace
“cutien yaya jiki yayi sauƙi koh"
Cike da jin daɗi tace
“eh yaya na warke”

Cike da zolaya ya ce
“ai na yi zaton da safe zan zo cin jallof ne”
Ya faɗa yana kanne mata ido.
Cike da shagwaɓa tace
“kai yayah! Ai sai ka riga Ni mutuwa ma”
“ni rufa min asiri! Damah so kike na mutu ko”
“aah yaya" ta faɗa tana zare ido
“alright in kin ji sauƙi zuwa gobe sai na kai ki makarantar koh?” cike da farin ciki tayi hugging nashi tightly
“na Gode Yaya Ishaq Allah ya ƙara maka buɗi ya faranta maka”
“ameen cutie, to same Ni kafin ki karya ni ko”
Ɗan tura baki tayi ta matsa gefe.

Haka suka yini suna shan hirar su har azahar, sallah yaya Ishaq yayi kafin ya dawo Mamah ta haɗa mishi nashi abincin.
Ita kuma Zahrah ana rikici ita wallahi ba zata ci abinci ba ta ƙoshi

Da ƙyar da siɗin goshi ya lallaɓa ta suka ci tare, bayan sun gama yake sanar da Mamah batun makarantar da zai saka Zahrah yayin da ta ke ta sharɓar bacci abun ta.

“wacce makaranta da ɗin take zuwa Mamah"
“nan makarantar gwamnati ne bayan inji mai wando”
“ammah ta gama primary ai”
“eh yanzu haka sun shiga jss 1 ne”
“ohk shikenan goben zamu je sai a gama mata shirye shiryen saboda nimah sati mai zuwa zan bar ƙasar”

Da mamaki Mamah ke kallon Ishaq
“ina kuma zaka je”
“mamah zan je nayi masters ɗinah be, zan kammala biyan kuɗin jss ɗin ta, nasan zan shigo bayan shekara uku ko biyu”

Duk da cewa basu wani saba ba ammah Mamah tana jin Ishaq a jikin ta tamkar yaron da ta haifa.

“toh Allah dai ya bada abun da za'a ke nema ɗin”
“Ameen Mamah bari zan wuce nikam, sai goben”
“toh Ishaq sai ka dawo, ka gaida gida, Allah ya saka maka da alkhairi”
“Amin” yace yana ficewa daga gidan.

Majalisar Kawu kuwa yau babu wanda ya zauna tun bayan jijjigar da suka ji anyi duk suka tsorata. Shima Kawu yana can yana sheƙe ayar sa gidan Rubber.

Da yammah jikin Zahrah ya warke, tace wa Mamah bari ta ɗan zagaya unguwar don Allah
Bata hana ta ba ko ba komai jikin ta zai ƙara ƙarfi ai ina ta zagaya.

Wanka tayi ta fita tana ƴar waƙar ta har ta zo ƙarshen layin su, wata ƴar ajin su Lawisa Musa ta gani. Kamar wasu manya suka ɗan fara taɗi abun su
“ah Zahrah Abdulkarim dama a unguwar nan kike?”
Da mamaki Zahrah ta kalli Lawisa
“kar ki raina min wayo mana Lawisa, ina banda uban ƙarya zaki ce baki san nan layin nake ba”

Sanin halin ta da Lawisa tayi yasa ta yi shiru kafin tace
“sorry ƙawa ta, na shafa'a ne, toh ya gida”
Farr da ido tayi tace
“lafiya ƙalau"
“jiya an zo duba masu fashi, Man Labour ya ɗauki sunan ku ammah ke Amira ta ce wai baki da lafiya da gaske ne”
“eh wallahi Lawisa, jiya har asibiti aka kwantar da Ni"
Cike da tausayawa Lawisa tace
“Allah ya sauwaƙe Zahrah Abdulkarim, bari na wuce gida nikam, aika na Umma ta tayi”

Daga haka suka yi sallama. Zahrah ta juyo saboda duk ta gaji ƴar tafiyar da tayi.

A ƙofar gida suka ji karo da Kawu, ko kallon arziƙi bai samu ba daga wajen ta. Duk da cewa yana tsananin shakkar ta ammah hakan ba hana shi dakewa ba don da wuya ka gano tsoron Kawu.

“ke don ubanki baki iya gaisuwa ba neh?”
Cikin halin ko ina kula tace
“mutanen kirki masu daraja mutane su ake gaishe wa” ta faɗa tana gurmuɗa baki.

Shaye da mamaki ta tafi ta bar shi, ya rasa meh yake masa daɗin haka nan lokaci ɗaya yayi wata shu'umar dariya

“shawarar Rubber zata yi aiki kwanan nan inda ba haka ba zasu ruguza min buri na, kai!!! Basu isa ba, dole na dakatar da su. Dole.

Sallahr maghrib suka yi, sannan isha', ana kiran ishà Kawu ya fice ta uwar shayibu.
Bayan sun yi dinner suka ɗan yi hirar su.

“mamah" Zahrah ta ambaci sunan ta
“na'am Zahrah, menene?”
“mamah yanzu haka zamu ci gaba da zama a gidan nan?, Wallahi Mamah Ni na gaji da rayuwar gidan nan, dubu fa duk mutane gudun mu suke yi saboda wannan banzan mijin naki”

“ke Zahrah! Ki kiyaye kalaman ki, kar ki manta ɗan uwan mahaifin ki ne shiɗin kuma miji na! Bana kuma son jin wannan zancen kinji ko”

Takaici duk ya cika ta tace
“shikenan Mamah, toh Ni ki kai Ni wajen wata ƴar uwar ki manah! Ni tunda muke baki taɓa kai Ni wajen su ba”
Ba tayi mamakin jin hakan daga Zahrah ba, tun bata kai haka ba take cewa su gudu gidan su Mamah ammah sai tace iyayen ta sun mutu.

Daga nan Zahrah bata kuma cewa komai ba tun da Mamah tayi shiru.

Ɓangaren Mamah lokaci ɗaya tsohon ciwon ta ya dawo sabo.
Abun da take ƙoƙarin binne wa kullum kenan, sam bata so a dawo mata da zancen ko kaɗan.

Bata manta ranar da ta rabu da iyayen ta, shekaru 14years kenan!
Lokacin da ta yi kunnen uwar shegu da ahalin ta! Gashi yanzu tana don zuwa gare su ammah ta kasa!!

“Ya Allah" kawai ta samu damar furta wa.
Har wajen 2:00am bata yi bacci ba, yanke shawarar yin Sallah tayi ko zata ji sauƙi.
Tana cikin sallar bugun gidan ya dira kunnuwan ta, bata katse sallar ba sai da tayi raka'āt biyu tukun nah ta fito.

Ƙoƙarin ta buɗe mishi sai dai abun haushi yau ma a buge ya shigo da ƙunshi ledar sa a hannu.
Bangare ta yayi ya shigo ciki. Bayan ta rufe ƙofar itama tayi ciki tana takaicin banzan hali irin na idrisu. Ganin ya tsaya be shiga ɗaki ba ta ɗan taɓe baki ta wuce zata shiga ɗakin ta.

Jawo ta yayi ta faɗo jikin shi, cikin zafin Nama ta fizge jikin ta.
Cikin Muryar ƴan maye yace
“haƙƙi na zaki bani Madina" cike da takaici ta wuce zata shiga ɗakin ta ya ƙara jawo ta da ƙarfi. ɗakin ya cilla ta ya rufi kirif.

“Wallahi baka isa ba idrisu! Da ni zaka yi mu'amala kana cikin maye?”
“toh meyeh....na..ga...naga....ke mata...ta...ce”
“haƙƙin mata nawa ka sauƙe da zaka ce ina baka haƙƙin ka? Wallahi ba abun da zai haɗani shimfiɗa da ƙazami irin ka”

Cikin maye ya janyo dorinar da ya saba dukan ta da ita ya fara jibgar ta, ihu take ammah Kawu bai daina dukan ta ba kamar an aiko wahayi gare shi ne.

Duka sosai yake mata da shi kan sa sai da yaji jiki, tun tana ihu har ta daina.
Duk budurin da ake yi Zahrah bacci ta take sha.
Maƙwafta na jin ihu ya wuce misali suka fara fitowa.

Ammin Badi'a ce da mijin ta suka zo, ƙwanƙwasa ƙofar da suke yi shi ya tada Zahrah daga bacci. Jin babu Mamah a gefen ta yasa ta fito. A tsakar gidan ta tarar da ita yashe sai wani irin sauti take fitar wa ga Kawu kuma tsaye kanta da dorinar sa.

Bai lura da Zahrah ba sai da tazo wurin, ba tare da ta kula shi ba ta kwanta jikin Mamah tana sake wani kuka mai tsuma zuciya.

Jin ba a daina buga ƙofa ba yasa ta je zata buɗe, tsawa ya buga mata

“keeee....” bata kula shi ba ta wuce ta buɗe. Ganin Ammin Badi'a da mijin ta abun ya bata mamaki. Shigowa suka yi, Ammi ta riƙe hannun Zahrah suka shige.

Kawu bai jira wata wata ba ya fizgo Zahrah daga hannun Ammi. Dukan ta ya fara nan da nan tayi wani tsalle ta gudo bayan Ammi.

“Wallahi Kawu baka isa ba! Uban me Mamah tayi maka zaka mata irin wannan dukan, wallahi bazan taɓa yafe maka ba wani abu ya same ta.
Meh yasa? MEH yasa nace MEH yasa Kawu? Ka cutar da rayuwar mu iya cutarwa, tabbas sakayyar Ubangiji tana jiran ka. Allah ya isa”

Daga haka ta kece da wani irin kuka mai ban tausayi.
Jikin Mamah ta dawo ta na jijjiga ta

“ki tashi Mamah! Kada ki mutu, in kin mutu bashi da asara nice zan shiga maraici, Mamah ki tashiiiii"

Ta ƙarasa cikin ƙaraji.
Abban Badi'a ne ya umarci Ammi da ta taya Mamah ta kai ta ɗaki sannan ta bata taimakon da ya dace.

Zahrah gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta in ban da suruce suruce babu abun da take

“ke ma Mamah nace miki mu tafi wurin dangin ki kin ƙi toh ai dole muyi ta Fuskantar Matsala. Allah ya isa tsakanin mu da kai Kawu. Sai Allah ya saka manah.

MU HAƊU GOBE
DUK YADDA AKA YI AKWAI WANI ƁOYAYYEN AL'AMARI
MUJE ZUWA DON BA'A FARA WASAN BA SAI MUN JE BABBAN GIDA.
CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY....TARE DA ZABGA COMMENTS.

DIAMOND BHATOOL 💎🤟

______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️



PROLOGUE


𝕻𝕬𝕲𝕰0️⃣5️⃣

Ina ƙaunar ki Qawa ta AISHA USMAN (Baby) namecy.
Allah ya kula min da ke a ko ina ya cika miki burin ki. Much ƙauna ƙawa ta ta kaina.. wannan shafi dai naki ne tawan....🤩😘

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________



Ammi ce ta taimakawa Mamah ta kwantar da ita, sannan ta hango thermoflask Allah ya so akwai ruwa a ciki, a ɗan baho ta haɗa tayi mata tapid sponging. Mamah kuwa kuka kawai take yi. Ta rasa meh yake mata daɗi, Ammi kuwa sai aikin lallashi take tana danasanin abinda mutanen unguwar ke yi wa Mamah duk da cewa ita bata ciki.

”Tabbas matar nan na buƙatar taimako kuma zan taimaka mata iya iyawa ta.”
Ɓangaren Zahrah kuwa Abban Badi'a ne ya riƙe hannun ta suka fita zuwa gidan shi yana Allah wadai da irin halin Idrisu. Tare da fatan Allah ya saka wa iyalen shi da abun da yake musu.

Asubar fari hankalin ta ya dawo jikin ta, ganin ta a ɗakin ƴan gayu yasa ta zaro ido waje. Tunani ta fara MEH ya kawo ta nan sai ta tuna abun da ya faru daren jiya.
“Toh asibiti aka kawo Ni kenan”

Ƙafar mutum da taji a kan tata yasa ta duba,
“Badi'ah, MEH nake yi a gidan su kumah?
Oh ashe jiya Ammin su ne suka taimaki Mamah”

Banɗaki ta nufa wanda yake cikin ɗakin tana mamakin gayu irin nasu Badi'a hala shi yasa ko a islamiyya bata kula Ni saboda gidan masu kuɗi take.
Duk cikin ranta take zance.

A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ta nufi waje. Cikin sanɗa ta ke tafiyar kamar wata ɓarauniya.

“Zahrah ina zaki je asubahi haka”
Abba ne ya dakatar da ita lokacin dawowarsa kenan daga masjid.
Sunkuyar da kan ta tayi kafin tace
“ina kwana"

Murmushi yayi
“lafiya ƙalau Zahrah, ki koma kiyi sallah in gari ya waye sai ki koma"
Bata yi mishi musu ba saboda kwarjininsa. Wucewa tayi simi simi kamar ƙadangare ta koma.
Alwala tayi sannan ta ɗan taɓa Badi'a.

Itama tashi tayi ta shiga toilet Tana mamakin meh wannan maras kunyar take yi a gidan su.
Sai da ta jira fitowar Badi'a cikin sanyin murya tace

“ki ɗan bani hijab nayi sallah”
Bata ce mata komai ba ta buɗe wardrobe ta janyo hijab ta miƙa mata. Buzu buzu tayi sallar Badi'a na mamakin yadda take yi.
Sai da ta idar ta ce mata ai ba haka ake sallah ba.
Duk rashin mutunci irin na Zahrah sai ta ce toh koyamin.

Sai wajen ƙarfe 6:10am ta koma gida. Abun mamaki gidan tas.. ɗakin Mamah ta shiga. Abun mamaki kwance taga Mamah. Kusa da ita ta zauna can tace

“mamah”
Cike da don manta abun da ya faru tace
“zahrah! Kiyi wanka da wuri kafin Ishaq yazo."
Sarai ta gano Mamah shi yasa tayi shiru abun ta.

Wanka tayi ta fito, a ɗakin ta tarar da Ammi zaune gefen Mamah tana bata abinci, haka kawai ta tsinci kanta da farin ciki maras misaltuwa.

“ina kwana Ammi"
“lpia ƙalau Zahrah, ki saka kayan sai ki je ki ɗebo abincin.”

Tana shirya wa ta ɗebo abinci taci sai lokacin Ammi ta wuce gida. Mamah kuwa godia tayi ta shaƙa mata.

Da misalin ƙarfe 9:49am yaya Ishaq ya zo gida.
Sun gaisa da Mamah kamar ko yaushe cikin sakin fuska.
Basu ɓata lokaci ba suka nufi wata private school Mai kyan gaske. Makarantar ta matuƙar burge Zahrah kawai sai ta tsinci kanta da murmusawa..

ALMUNAUWARA ACADEMY

Yara ne ke wasa gwanin ban sha'awa, wasu bisa lilo Wanda da gani nursery students be. Wasu kuma ta wani ɓangaren waɗanda uniform ɗin su ya bambanta da na sauran wasu na guje guje wasu kuma suna wasanni mabanbanta.

Biye take da yaya Ishaq yayin da zuciyar ta ke mata wani irin sanyi. Yau ita ce a cikin ALMUNAUWARA ACADEMY, “makarantar su Badi'ah fah kenan.”
Ta faɗa tana sake wani irin ƙayataccen murmushi.

Daidai wani building suka nufa wanda da alamu shine staff room. Wani room Wanda aka manna signboard jiki ɗauke da “ADMIN" yaya Ishaq yayi knocking, izinin shiga ya samu suka shiga tare.

Sai da ta gaida mutumin kafin ta zauna kamar yadda taga yaya Ishaq ya zauna.

“Mallam Muhammad, Barka da safiya” yaya Ishaq ya faɗa tare da miƙa wa mutumin hannu.
“barka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login