Showing 21001 words to 24000 words out of 31694 words
Chapter 8 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete
lau zahran Mamah, ya jikin mamah”
“da sauƙi”
“toh Allah ya ƙara sauƙi, Badi'a Badi'a ki fito manah tun ɗazu Zahrah ke famar jiranki”
Daga room ɗin ta ta ce
“sorry zahrahty gani nan zuwa”
Bayan Badi'a ta zo suka wuce islamiyya. Yau gabaɗaya Ustaz ya kasa fahimtar Zahrah, fuskar ta ɗauke take da zunzurutun damuwa. Zuwan ma kawai tayi ne ba wai ɗin taso ba. Gani take kamar ina ta bar Mamah mutuwa zata zo ta ɗauke ta.
“Zahrah! Zahrah!! Zahrah” bakin shi uku ammah bata amsa ba. Babu alamun ma ta san MEH ake ko a Ina take. Badi'a na taɓa ta ta zabura sai wani zare ido take yi.
“zahrah baki da lafiya ne yau gabaɗaya hankalin ki baya kan aji. Baki na yafi uku ammah baki san ina yi ba"
Cike da basarwa ta ce
“lafiya ƙalau Ustaz kawai tunani ne yayi min yawa.”
“Zahrah tunani meh kike yi haka ƴar ƙarama da ke da zai sa ki shiga irin wannan yanayin?”
Bata yi tsammanin jin irin wannan tambayar ba daga Ustaz shiyasa kawai tace tunani take yi.
Murmushin da iyakar shi fuska ne tayi sannan tace
“laaaaa Ustaz ba fah wani tunani nake yi ba kawai duniyar ne ban jin daɗin ta”
“toh Allah ya sauqaqa Zahrah ammah ki rage tunani” daga haka ya wuce.
Badi'a dake nazartar ƙawar ta tunda suka fito daga gida gashi yanzu fararen idanuwan ta sun yi jazur da su.
“Zahrah, gaba ɗaya yau tunda muka fito nake nazartar ki, anything wrong?”
“just nothing” ƙura mata ido Badi'a tayi kafin tace
“ƙarya kike Zahrah akwai, kawai dai ban kai matakin ki faɗa min baneh na gode”
Ta faɗa cike da fushi. Kamo ta Zahrah tayi kafin tayi murmushi
“yi haƙuri ƙawa tah, kin kai har kin wuce ki ji damuwa ta. Ba komai ke damu na ba in banda rashin lafiyar Mamah, yau da na dawo abun yayi worst, kin ga yadda Mamah ke shan wahala, Badi'a bazan iya jurewa ba bazan iya jurar ganin Mamah a haka ba”
Ta faɗa ƙwalla na zubowa daga cikin idanun ta.
Cikin sigar rarrashi Badi'a tace
“Zahrah ke musulma ce kuma kinyi imani da Allah da sauran rukunai na imani?”
Gyaɗa kai Zahrah tayi don kuwa maganar ma kawai tana yin ta ne ba don tana so ba.
“kin sani kowanne bawa da kalar tashi ƙaddarar, khairan ta zo ko akasin haka dole ka rungume ta a matsayin ka na mai imani.
Jinyar Mamah na daga cikin jarrabawar ku ke da ita, Zahrah addu'a kawai ita ce mafita, ki ƙara akan yadda kike yi nimah nan ina yi miki haka Ammi na da Abba na”
Maganar Badi'a sun rage mata damuwar da take ji sosai. Murmushi Zahrah tayi ta riƙo hannun Badi'a
“ƙawaye iri iri ne ammah tawa ƙawar ta musamman ce, ban san wani aiki mai kyau nayi Wa Ubangiji ba da ya azurta Ni da ke da kuma ahalin ki, duk wuya duk rintsi ina ƙaunar ki. Allah ya saka muku da alkhairi ke da Ammi da kuma Abba”.
Ci gaba da tafiya suka yi hannun su riƙe da na juna kamar wanda aka yi attempting raba su. Sai da suka iso suka yi sallama kowa ta wuce gida.
Tana komawa ta wanke uniform ɗin ta ta dawo gefen Mamah ta zauna. Mamah da ke bacci bata ma san Zahrah ta dawo ba. Ganin bacci take yasa zahah ɗauko Quran ɗin ta tana rerawa. Kamar daga sama taji tarin Mamah. Ajiye Quran ɗin tayi ta matso wajen ta tana shafa bayan ta.
“Sannu Mamah na sannu, na kawo miki ruwa"
Kai ta gyaɗa. Zahrah ta bata ruwa sannan ta ci gaba da karatun ta.
Lokaci ɗaya kuma tayi shiru yayinda ta faɗa duniyar tunani.
“Kawu ko sau ɗaya bai taɓa leƙowa don duba jikin mamah ba talkless of yace zai kai ta asibiti. Anya kuwa Kawu mijin Mamah ne?, Toh idan mijin ta ne ma ba na tunanin auren soyayya suka yi.
Dubi rayuwa ta fah! Shin ko don Ni ƴar yarinya Mamah ta cancanci kyautatawa daga Kawu idan ma ace tayi masa wani laifi ne a da.
Allah Sarki Mamah nah, in Sha Allah Ni zan zama gatan ki, zan kula dake har lokacin da zaki samu lafiya zan kuma ƙwata mana ƴancin mu da zarar na samu damar hakan. Bani da burin da ya wuce na zama cikakkiyar alƙali, Kawu sai na karɓawa mahaifiya ta haƙƙin ta daga wurin mutumin da tunda na tashi ban taɓa ganin ya yi mata alkhairi ba kullum cikin musguna mata yake.
Ina son haɗuwa da ahalin Mamah sannan ina son haɗuwar ta da ahalin ta, nasan su ma zasu yi farin ciki”
“nayi alƙawari Mamah nah kinda kuwa haɗa ki da ahalin ki shine abu na ƙarshe da zan yi tabbas zan so cimma shi”
Ganin tunanin babu yadda zai kai ta gashi maghrib ta gabato. Tashi tayi ta matso kusan Mamah, Ɗan taɓa ta tayi a hankali,
“mamah lokacin sallah yayi, bari na kawo miki baho kiyi alwalar, ina zaki iya?”
Ɗaukowa baho tayi da ruwa tayi wa Mamah alwala daga nan ta sanya mata hijab a jikin ta ta juyar da ita ta fuskanci alƙibla sannan tace.
“kiyi sallar mamah” duk da raɗaɗin jinya hakan bai sa ta yin farin ciki ba, wai yau Zahrah da kanta take cewa tayi sallah, Zahrah da bata don sallah a da. Alhamdulillah.
Ita ma alwalar tayi tayi sallar ta ta roƙi Allah ya bawa Mamah lafiya. Sauran masa da miyar rana ta ɗauko taci bayan yaci ta ɗauko Quran ɗin ta taci gaba da koyon hadda.
Haddar ta ta koya tana gamawa ta rufe Quran ɗin ta ɗanyi addu'oin ta waɗanda yawanci roƙawa mamah lafiya take wurin Ubangiji.
Lokacin ishà ma da kanta ta taimaka wa Mamah tayi sannan ita ma tayi. Tana idarwa taji sallamar Ammi da kuma Badi'a,amsa musu tayi cikin sassanyar muryar ta.
“Wa alykumussalam, Ammi sannu da zuwa”
“yauwah sannu Zahrah”
“ku zauna manah,”
Zama Ammi tayi bakin bed ɗin kusa da Mamah. Cike da kulawa tace
“ys jikin madinar?”
“da sauƙi ammi”
“Zahrahty ya jikin Mamah? Badi'a ta faɗa fuskar ta ɗauke da damuwa.
“da sauƙi Alhamdulillah”
“Allah ya ƙara sauƙi”
“zahraj tashi ki ɗan zuba mata abincin nan ta ɗan ci ko kaɗan ne ko ta samu ƙarfin jiki” Ammi ta faɗa tana nuna mata basket ɗin da Badi'a ta ajiye gefen ta.
“Ammi ai bata iya cin abincin, ɗazu ma ƙin ci tayi sai Ni na cinye shi da na dawo” ta faɗa tamkar zata yi kuka.
Shikenan zubo ki miƙo Ni zan bata la'alla taci. Zahrah ta zuba abinci ta kawo kusan Ammi ta ajiye, a hankali Ammi ta ɗan taɓa mamar..
“madinah ya ƙarfin jikin?”
Da ƙyar ta amsa “da sauki”
“toh Allah ya ƙara sauƙi, ga abinci ki ɗan tashi ki ci ko zaki ji ƙarfin jikin ki”
Ta faɗa tare da ɗago mamahn. A hankali take feeding ɗin ta, wani abun har da yunwa ta ɗan ci da ɗan yawa kafin ta janye kanta gefe alamun ta ƙoshi.
Bata kwantar da ita ba sai da ta tabbatar abincin ya tsarga.
A nan suka zauna har 10:00pm suka wuce.
Damuwa ta taru tayi wa Zahrah yawa, da ƙyar bacci ya ɗauke ta bayan ta rufo musu ɗakin da addu'a.
______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
﷽
PROLOGUE
𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣2️⃣
Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘
SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________
Kamar daga sama ta jiyo Muryar Mamah na ƙiran sunan ta.
“Zahrah, Zahrah zahrah” ta faɗa tana lalumowa ko zata ji ta. A firgice ta tashi jin kamar mafarki take.
“mamah” ta matso daga da Mamah dake zaune,
“kunna haske” cike da mamaki take kallon Mamah.
“mamah ke kike magana haka, Alhamdulillah Alhamdulillah”
Rufe mata baki tayi sannan ta fara magana ƙasa ƙasa yadda babu wadda zai ji su
“ki kunna haske, zan nuna miki abu ne”
Lalumowa hasken tayi ta kunna sannan ta zuba wa Mamah ido.
Da ƙyar ta miƙe ta nufi wata ƴar adakar ƙarfe dake ɗakin, ɗan murɗa wasu abu dake jiki kamar zobe tayi sannan adakar ta buɗe. Wata haka da ta sha ƙura ta gani ta ɗauko sannan ta rufe adakar.
A hankali take takowa dan kuwa ba wani ƙarfin jikin ta take ji ba.
Zahrah da mamaki yayi kusan kashe ta ga wani tsoro da ya shige ta lokaci ɗaya. Ta ma rasa wane irin tunani zata yi. Ta tuna taji ana cewa idan mutum yan jinyar ajali toh yakan samu sauƙi daf da mutuwar shi. Saurin kawar da wannan tunani tayi jin an dafa kafaɗarta.
“Zahrah!", Ta ambaci sunan cikin raunananniyar murya yayin da Zahrah ta kasa amsawa sai ma wani firgici da ya mamaye ta.
“Zahrah! Ke kaɗai Allah ya bani, kuma bana so ki ci gaba da wannan rayuwar idan aka ce babu Ni. Ina ji a jiki na bazan yi tsawon rai ba, sai dai yanzu naji wani ƙarin guiwa na tunkarar ki da batun ahali na.
Tun ba yau ba kina tunkara ta da maganar ina basarwa saboda yadda nake jin wani mololo ya tare min zuciya da zarar an yi min tambayar. Yau bana jin abun shiyasa nake don sanar da ke Ni wacece, ban ce ki ci gaba da zama cikin gidan nan ba saboda babu rayuwa mai daɗi cikin shi.
Ina da rai ma baki samun kulawa daga wajen kowa sai Ni yin idan babu Ni ban san ya zaki ji ba.
Ammah a matsayi na na mahaifiyar ki kuma mai ƙaunar ki,ko da bayan raina ne bazan zo ki bar cikin gidan nan ba saboda shi ɗin tamkar gidan mahaifin ki yake. Ammah idan kika ji ba zaki iya ba ko kin takura da hakan, ko kuma anci gaba da tauye hakkin ki toh ki nemi ahali na.
Wannan jakar da kike gani mallaki na ne kuma ita ce motar da zata sada ki da dangi na, zan damƙa ta a hannun ki da zarar na sanar da ke labari na, kuma zan so ki adana ta kamar yadda nima na adana ta.”
Ɗan dakata wa Mamah tayi da bayanin tare da ƙanƙame hannun Zahrah cikin nata yayin da hawaye ke zubowa daga cikin idanun ta, ga kuma alamun gajiyawa a tare da ita. Ganin hakan yasa Zahrah share nata hawayen.
Cikin ranta kuwa tunani take
“kamata yayi ace nayi farin ciki da wannan daren, kamata yayi ace naji murnar da ban taɓa ji ba a wannan daren saboda tsantsar tarihin da zai buga cikin rayuwa ta.
Daren da zan samu abun da na daɗe ina fatan samu tun ina ƴar ƙarama ta, abun da tambayar da ke sa mahaifiya ta tayi fushi da ni gashi kuma zata bani shi a yau.
Ammah meh yasa Ni bana jin naji wannan labari da na daɗe ina son ji?, Labarin da zai kasance makullin baƙin ciki na?”
“Tabbas ina don sanin tarihin ki Mamah, ina son sani idan nace bana so toh nayi ƙarya. Ammah Mamah ba a irin wannan lokacin ba. Ina don ki sanar da Ni labarin ki ne a lokacin da in naji zanyi farin ciki, a yanzu baki da lafiya kuma bamu da kowa sai Allah, sai kuma bayin sa Ammi da Abba da ya aiko cikin rayuwar mu.
Zan so ki Dakata da faɗin labarin nan zuwa wani lokaci”
Itama Mamah ɓangaren ta tunani kawai take yi game da rayuwar ta, yarintar ta, tasawar ta i zuwa auren ta da masoyin ta Abdulkarim Kuru. Haihuwar ɗiyar ta Zahrah, da mutuwar ba zata da mijin ta yayi, auren ta da Kawu da kuma irin baƙar izayar da ya gasa mata ita da yarinyar ta.
Shiru shiru babu wanda yayi magana cikin su, Mamah na jiran amsa daga ZAHRAH kan ta fara bata labari yayin da Zahrah ta kurma cikin duniyar tunani.
Mamah da ta gaji da zama ne ta ɗan kishingiɗa, hannun ta dake cikin na Zahrah ne ya zame wannan shine dalilin farkawar su duka biyun daga duniyar da suka faɗa ta tunani.
Bubbuga ƙofar da suka daɗe basu ji anyi ba ya sa suka miƙe tsaye a tare. Har Mamah ta miƙe zata buɗe ƙofar Zahrah tayi saurin dakatar da ita.
“aah Mamah, na san bai wuce Kawu baneh kuma ba zaki buɗe masa ba" bata yi mamakin jin maganar Zahrah ba hakan yasa ta zauna bakin bed Babu musu. Jikin ƙafar ta Zahrah ta zauna tare da kwantar da kan ta kan cinyar Mamah. A hankali ta ɗago ta kalli idon Mamah sannan ta kawar da nata gefe.
“mamah ba haka kawai yasa na tsani Kawu ba sai don rashin nuna ƙaunar shi gare ki a matsayin ki ta iyalin shi. Ba ma wannan ba tunda kika kwanta bai taɓa tako ƙafar sa don ya duba jikin ki ba balle yace yau a kai ki asibiti ko ya karɓi takardar magani yace zai siyo ba bayan kuma Ni da kaina na sanar da shi baki da lafiya.”
Tabbas abun da Zahrah ta faɗa bata ga laifin ta ba ko kaɗan at least ya kamata ko sau ɗaya ace ya zo ya duba ta ɗin.
Gyangyaɗin da Zahrah ta fara ne yasa Mamah cewa ta dawo su kwanta gobe da kammala maganar su. Ba musu Zahrah ta kwanta jikin Mamah nan da nan bacci mai daɗi yayi awun gaba da su. Safiya ta gari.
Ba su suka tashi ba sai da gari ya fara wayewa Mamah ce ta fara tashi ɗauke da addu'ah a bakin ta. A hankali ta sauƙo ta fita, ɗan watsa ruwa tayi a jikin ta ta haɗo da alwala sannan ta yi sallah. Bayan ta isar da Sallah ta yi azkar ɗin ta. Miƙewa tayi don tashin Zahrah tayi arba da jakar nan, a kasalance ta ɗauke ta ta jefa ta cikin wardrobe ɗin kayan ta dake sama can.
Bayan ta tashi Zahrah ta ɗan fara kaɗe ɗakin.
Tana yin Sallah ta gaida Mamah
“ina kwana mamah”
“lafiya zahrah”
“ya kwanan jikin?"
“Alhamdulillah, yi maza ki tashi kiyi wanka kada ki makara"
“toh" tace tana miƙewa, ninke sallayar tayi sannan taje tayo wanka.
Uniform ɗin ta ta manta ba'a goge yake ba, a hanzarce ta shiga gidan Ammi ta goge lokacin Badi'ah ta tashi.
Sanya uniform ɗin ta tayi tana gamawa Mamah ta zubo mata jallof ɗin taliyar da ta musu, ita dai Zahrah mamaki take don rabin ta da cin girkin Mamah tun kwanaki basu fi biyu ba bayan kwantar da ita da aka yi a asibiti yau kuma ta tsiro girki.
Bayan ta ci abincin tana santi ta wanko hannun ta tayi brush daga nan ta zari school bag ɗin ta da kuma hijab ta zura ta fito. A bakin ƙofa suka ci karo da Badi'a ita ma ta shirya tsab”
“har kin shirya kenan, bari na miƙa wa Mamah sai mu wuce" ba tare da ta amsa mata ba tayi waje.
Tana miƙa wa tayi wa Mamah ya jikin ta fito, driver ne ya kai su school sai dai yau Zahrah tamkar ba ita ba, tunani ya addabe ta.
Babu abun da ya tsaya mata a rai irin hirar su ta jiya tare da Mamah.
Hirar da ta tsaya mata cikin zuciyar ta.
“meh Mamah take nufi kenan,idan na fahimta akwai ɓoyayyen al'amari dangane da ita, bana son rasa Mamah don ita ɗin numfashi na ne, ammah cikin maganganun ta na jiya naji zuciya ta na karye wa”
Other heart ɗin ta tace
“haba Zahrah, damah ai yanzu kam kin kai ki san tarihin mamar ki”
“ƙwarai to ammah bana so rada ta ai”
“duk da haka dai ya kamata ki saurare MEH Mamah zata sanar da ke, la'allah ƙarshen zaman ku da azzalumin kawun ki yayi”
“ai kuwa dai, nimah na ga hakan”
Haka tayi ta magana da zuciyar ta har uncle Hashim ya shigo. Dukkan students suka miƙe suna gaida shi, sai dai Zahrah hankalin ta baya ma ajin, bata san wainar da ake toyawa ba. Bai yi mata magana ba ya basu umarnin zama, har ya fara clsss ɗin bata san MEH ake ba sai da Badi'a ta buge ta.
Firgita ta waro ido tana kallon Badi'a.
“ke wai tunanin meh kike yi ne?”
“banu komai”
Ƙasa ƙasa ta harare ta tace
“kina nan kina tunani har uncle Hashim ya shigo kina zauna muka gaida shi kuma kice ba tunanin komai kike yi ba?, U better concentrate” daga haka ta zunguri ƙeyar ta.
Daf da lokacin closing PC ya sa aka kira Maryam, Badi'a da kumah Zahrah zuwa staff room.
“ba komai ne ya sa na kira ki ba sai don na sanar da ku cewa yanzu ba sai anjima ba zaku tafi Jos zaku yi representing school ɗin nan a wani programs so nayi magana da iyayen ku akan tafiyar. Yanzu ku ɗauko school Bags ɗin ku ku ajiye su a nan.
Tare zaku tafi da Academic officer da kuma Hashim. Please Behave well”
Suka haɗa baki suka ce
“ohk sir”
Ɗauko bags ɗin su suka yi suka ajiye. Lokacin Academic officer ya ce su fito. Abun mamaki PC ya tsayar da su.
“ku zo”
Zuwa suka yi ya miƙa musu sabbin uniform da gani goge su aka yi saboda ɗumin dake jiki.
“ku tafi da wannan, ina zaku tafi wajen sai ku sanya.”
Bayan sun amsa suka koma daga nan motar su ta tashi sai Jos.
RACAS FOUNDATION COLLEGE, old airport jos, plateau suka nufa. Ɗan zagayawa A. Officer yayi da su sannan suka koma zuwa destination da aka basu don sai da safe za'a yi competition ɗin.
Abinci mai rai da lafiya yayi order, bags uku ya aiki musu suma suka ɗauki two bags.
Bayan sun ci abinci sun kora da drink suka yi sallah.
Hutawa suka kwanta suka yi, ba su suka tashi ba sai 4:12pm, suna tashi suka watsa ruwa suka maida kayan su sannan suka yi sallah.
Knocking door ɗin aka yi, Badi'a ta buɗe, Academic officer ne yace su zo. Wani ɗan cool down area suka samu suka zauna.
Yayi musu bayani akan programs ɗin da kuma wanda kowa zai yi participating. Daga nan ya ƙara haska musu