Showing 30001 words to 31694 words out of 31694 words
Chapter 11 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete
ya kwashe Zahrah.
★★★★★★★
Tafe take cikin wani baƙin daji mai ɗauke da duhun gaske, babu alamar akwai halitta cikin shi. Ta jima tana tafiya tare da fatan Allah ya haɗa ta da wani wanda zai taimaka mata ta koma gidan kwatsam ta fara jiyo sauti daga can nesa. Yanke shawarar zuwa guriin sautin tayi tare sa fatan Allah yasa mutane ne. The more ta yi tafiya the more sautin ke ƙaruwa.
Tayi doguwar tafiya kafin ta kusanto wurin sautin sai dai alamu sun nuna cewa sautin ba na mutane bane....gurnanin da take ji ne tare da wata mahaukaciyar dariya mai ɗan karen sauti da amo maras daɗi yasa ta ɗan ji tsoro daga ƙarshe kuma ta yanke shawarar ƙarasawa.
Bata kai ga ƙarasawar ba taji ƙasa na wata irin girgiza wanda hakan tayi sanadiyar faɗuwar ta ƙasa, da ta tayi ƙoƙarin tashi sai ta koma saboda girgizar ƙara ƙamari take yi. duk ƙoƙarin ta na tashi tsaye ya gagara hakan yasa ta kwanta tare da runtse idanuwan ta tana miƙa wuya
Wasu munanan halittu ta gani masu munin gaske, kayuwan su manya manyan wanda ke ɗauke da ƙaho biyu, na hagu jibgege na dama kuma ɗan ƙarami. Fuskar su ja jawur da ita ga idon su ɗaɗɗaya ne manya manya marasa daɗin kallo. Baƙin su kuwa ya kai faɗin randa Wanda ke ɗauke da wasu gabza gabza haƙora da suke da launin shuɗi.
Gangar jikin su irin ta mutum ce sak ga kyan fata da suke da shi sai dai bakin su da yake a wangale yana zubar da wani kore da jan jini suke ƙara wangalewa.
Ta riga ta saddaƙar cewa tata ta ƙare hakan yasa ta ƙara runtse idanuwan ta tare da karanto wasu addu'oin tsari. A hankali halittun suka matso daf da ita suka ɗaga ta....basu ajiye ta ba sai cikin wani cage Wanda ke ɗauke da wasu mutane kusan biyar.....ana cikin wannan abu sai ga wata mahaukaciya ta bayyana gaban cage ɗin, jikin ta duƙu duƙu ga wasu kayayyakin ta da suka ji jiki. A hankali mahaukaciyar ta jawo ƙofar cafke ɗin tana motsa bakin kamar mai karanta wani abu.
Tana gama buɗe ƙofar ta jawo su ɗaya bayan ɗaya daga ƙarshe ta janyo Zahrah ta faɗo jikin ta. Bata kai ga gane fuskar waye ba taji kiran sallar asuba, ɗauke da addu'ah a bakin ta tayi miƙa.
Mintuna kamar 10 ta kwashe tana nazarin mafarkin da tayi tare da hasaso ko meh yake nufi.
Kan ta ne ya fara juyawa hakan yasa ta buɗe idanuwan ta da suke lumshe.
A hankali ta shashima gefen ta ta gano ta ina Mamah take sai dai babu kowa gurin.
Ƙafar ta ta sanyo ƙasa yayin da ta ware idanuwan ta.
A hankali ta fita don gabatar da alwala tunanin ta Mamah na banɗaki, ganin ƙofar a buɗe yasa zuciyar ta bugawa sai tayi saurin kawar da abun da zuciyar ta ke shirin shirya mata ta hanyar ɗiban ruwa a buta, sai da ta gama ɗiba ta shiga bayi bayan ta fito tayi alwala ta koma ɗaki don yin Sallah.
Tana idarwa bata iya ko yin azkar ba bacci yayi awun gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai wajen 8:12am sanadin mummunan mafarki da ta ƙara yi na wannan mahaukaciyar. A sukwane ta miƙe tsaye sai dai ƙara kallon gado da tayi sai taga still babu mamah. Zuciyar ta ne tayi wani irin bugu har sai da ta kusa faɗuwa.
A hankali ta duba wurin da Mamah ke sallar asuba ko yaushe taga wayam kuma babu sallaya shimfiɗe. Mamaki ne ya cika ta yau ko ina Mamah ta tafi?.
Bayan ta fito tayi wanka ta dawo still Babu Mamah babu alamar ta hakan yasa ta tsorata da lamarin.
Kaya kawai ta sanya ta nufi gidan su Badi'a ko can Mamah ta nufa sassafe.
Karo suka ci da Abba ya fito daga part ɗin shi, a natse ta kalle shi tare da sunkuyar da kanta ƙasa.
“ina kwana abba”
“lafiya kau Zahran Mamah ya Maman ki?”
Tsoro tambayar ta bata, wane irin ya Mamah bayan kuma nan ta zo. Kawar da abun da zuciyar ta ke saƙawa tayi tare da faɗin
“lafiyar ta ƙalau”
“toh madallah” daga haka ya wuce ita ma Zahrah ta shiga part ɗin Ammi.
Breakfast ta tarar Badi'a da Ammi nayi wanda hakan yasa zuciyar ta yin wani mummunan bugu, a daidai lokacin ta faɗi ƙasa a yashe.
Cike da ruɗewa Ammi da Badi'a suka yi kan Zahrah.
Tunani meh za'a fara yi mata Ammi tayi cikin ruɗu tace
“badi'ah kawo ruwa masu sanyi”
Da gudu Badi'a ta nufi fridge ta ɗauko ruwa.
Har Ammi ta gama yayyafawa Zahrah wannan ruwan babu alamun numfashi a tattare da ita. Kuka Ammi take yi kamar ranta zai fita haka Badi'a, gashi ƙwaƙwalwar ta duk ta toshe ta ma rasa MEH zata yi.
A cikin wannan yanayin Abba ya shigo ganin suna kuka yasa shi ƙarasowa yadda suke da sauri.
“Lafiya kuke kuka haka” kasa magana suka yi hakan yasa ya kai kallon sa ga wurin da idanuwan su ke. Ganin Zahrah da suka gaisa tare cikin mintuna marasa yawa yasa ya matso
“meh ya samu zahrah?" Badi'a da ta shiɗe tace
“Abbah Zahrah ta mutu, shikenan ta mutu kuma babu abun da aka yi mata”
A hankali Abba ya kai hannun shi ya riƙo hannun ta, jin akwai pulse yasa ya ɗago Zahrah da sauri.
“ku biyo baya na”
Cikin hanzari ya fita da Zahrah direct parking. Space ya nufa ya kwantar da ita, Ammi da Badi'a suka shiga.
Kai tsaye Northern Specialist hospital ya nufa da ita. Ba a ɓata lokaci ba aka karɓe ta saboda yanayin da aka zo da ita.
Cikin aƙalla 30minutes aka taro numfashin Zahrah da taimakon doctors da kuma Nurses. Daga nan aka saka mata line na N/A sannan aka yi mata antidepressants injection tuni bacci yayi awun gaba da ita.
Ganin doctors na fitowa yasa Ammi saurin nufar su
“ehm Please ta tashi ko? Zahrah bata mutu ba ko yauwah ku faɗa min meh ke damun zahrah”
Ganin yadda ta bi ta ruɗe yasa doctor murmusawa have
“she's Alright now, ammah tana buƙatar hutu, so zuwa jimawa za'a ɗauke ta daga nan a mayar da ita paediatric medical ward sai ku duba ta”
Jijjiga kai ammi tayi ba tare da ta fahimci dogon bayanin shi ba tunda yace she's alright.
Reception suka koma suka zauna suna ta addu'ar fatan sauƙi wa Zahrah. Sai a lokacin Ammi ta tuna basu bi sun sanar da Mamah ba can tace ba sai an sanar da ita ba kawai saboda kada a ɗaga mata hankali bayan ba cikakkiyar lafiya gare ta ba.
Har wajen azahar shiru hakan yasa Ammi komawa A&E wadda ɗin, karo suka ci da doctor ɗin da yayi mata bayani.
“ehm doctor Bata tashi ba har yanzu?”
“eh yanzu dai a je a nemo mata abun da zata ci zuwa jimawa zata iya farkawa anytime”
“ok” daga nan Ammi suka koma suka yi girki suka dawo.
Har yamma Zahrah bata tashi ba, hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba shine Mamah ta yanke hukuncin sanar da Mamah kada ta ji Zahrah shiru.
Abba na gida kawai ta ƙira shi tace ya aika yaro ya sanar da Mamah Zahrah na asibiti ammah ba sai ta zo ba da an sallamo ta zasu dawo.
Cikin sauri Mamah ta yi picking call ɗin da ke shigowa wayar ta.
“Eh ina ji”
Ta ɗaya ɓangaren kuma ban ji MEH aka ce ba. A zabure ta miƙe tsaye
“ban gane ba.....tooooh ko zaka sa a tambayi amaryar gidan ko tana kwance ba lafiya ne ita ma?.....ohk ina jira”
Daga haka ta dawo ta zauna.
Wasa wasa maghrib tayi kuma Zahrah dai bata farka ba, kuma Abba bai ƙira Ammi ba.
Yanke shawarar barin Badi'a tayi in yaso in Zahrah ta tashi kafin su dawo ma ita tana nan.
Tana isa bayan tayi girki ta nufi gidan Mamah, ɗakin Mamah ta nufa kai tsaye tare da sallama a bakin ta. Jin shiru babu amsa wa tasa ta shiga da sauri tunanin ta ko Mamah na bayan gida ne.
Shiga tayi ta ɗan zauna saboda ta jira ta. Jira shiru shiru Mamah bata fito ba gashi Ammi na son wucewa asibiti. Kai tsaye ta nufi hanyar banɗakin.
“da mutum ne a ciki?”
Sai da Ammi ta maimaita sau biyar ammah shiru ita ma nan da nan zuciyar ta buga wani irin tsoro ya kama ta.
Ganin jiran ba shi da amfani yasa Ammi ta shawarar tambayar baba amarya ko ta ga fitar ta.
Wani kallon banza Baba amarya ta wulla wa Ammi tare da jan tsaki ta koma ɗaki bayan jin ƙudirin Ammi.
Cikin ruɗu Ammi ta fice zuwa gida, ta sanar da abba kafin yace ta wuce babu damuwa wata ƙila Mamah gidan wasu ƴan uwan su ta tafi.
Har lokacin da Ammi ta koma ba'a sauyawa Zahrah waje ba saboda har lokacin bata farka ba.
Allah Sarki ƙauna Badi'a kam kasa cin komai tayi sai kuka ta ke yi
“kiyi haƙuri kiyi wa Zahrah addu'a idan kina kukan babu abun da zai miki sai dai kema ki fara ciwon kai.”
Kai ta gyaɗa tace
“toh mamah”
“oyah zo ki ci abinci” babu musu ta ƙarasa Mamah tayi serving nata, ta ɗauki spoon kenan zata kai loma tace
“Ammi baki bi kin yi wa Mamah magana ba ne?”
“eh tana kan hanya” haka kawai ta faɗa saboda kada ta tayar mata hankali.
Bayan Badi'a ta ci abinci ta ƙara barin reception ta nufi wurin A&E ta tsaya.
Tana cikin tsayuwar Dr. Ya fito. Ganin ɗazu ya ganta tare da Ammi yasa ya nufe ta.
“Baby ina mamar taku?”
“tana can reception” kallon ta yayi yace ta ƙura Maman su.
Da sauri ammi ta biyo bayan Badi'a suka taho.
Ganin irin tashin hankalin da Maman nasu ta shiga yasa Dr. Yin murmushi.
“Yauwah Hajiya ke ce kika kawo wannan yarinyar ko?”
“e...eeeh nice ta farka ne?”
“eh ta farka ammah bata cikin hayyacin ta, so yanzu za'a sauya mata ɗaki sai a bata abinci taci”
“tooh shikenan”
Bayan an sauya wa Zahrah ɗaki zuwa medical ward Ammi da Badi'a suka wuce. So da yake amenity suka kai ta ya sa duk su biyun suka shiga.
Lumshe idanuwan ta suke yayin da fuskar ta tayi pale, sai kamannin ta da Mamah ya ƙara bayyana.
Ƙarasawa wajen ta suka yi suna ambaton sunan ta.
MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA