Showing 18001 words to 21000 words out of 31694 words
Chapter 7 - Babban Gida Takun Farko Hausa Novel Complete
wajen ka ɗin ne kamar zai fi. In yaso in an tashi amfani da shi sai ayi nan gaba"
Abba bai Musa da shawarar Mamah ba haka Ammi. Girman ta kuwa a idon su ya ƙara ƙaruwa. Daga nan suka yi sallama suka wuce gida.
TOH GA FA BABA AMARYA DA KUMA TUGGUN TA GA MAMAH DA ƊIYAR TA
GA KUMA YA ISHAQ SHIMA ASHE YANA NAN.
KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY DON JIN YADDA ZATA KAYA
COMMENTS DIN KU KAWAI NAKE SO SABODA SHINE ƙWARIN GUIWA TA.
DIAMOND LADY CE 💎🤟
Oum Zainab.
______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
﷽
PROLOGUE
𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣0️⃣
Bazan manta da ku ba ƴan uwa na kuma rabin jiki na
Aminatouh Adamu Hassan (Dr. Meenal)
Sa'adatu Adamu Hassan (Shaheedah)
A'ishah Saleh Uthman da kuma
Safiyya Saleh Uthman (Autar Umma)
SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yau daɗi gobe akasin haka. Tun ranar da BABA AMARYA ta dawo daga wurin boka Bulebule komai ya sauya a gidan nan. Cikin sati guda ta fara shimfiɗawa Kawu sarautar mulkin ta a gidan, tana cewa abu har rawar ƙafa yake don yayi mata.
Wannan shine mafarin zancen.
Zaune take akan taburmar da ta shimfiɗa yayin da Kawu ke mata tausa a tsakar gidan.
“mai gida tashi ka ɗaura mana sanwar nan manah don Ni na riga da na gaji”
Da sauri ya miƙe kamar mai cika umarnin mahaifiyar sa ya fara haɗa ice cikin murhu. Ba don komai ta sashi ba sai don kawai haka tayi ra'ayi.
Da ƙyar wutar nan ta kama ammah haka tace ya daure yayi musu girkin nan. Tun bai wuce 11:20am aka fara girkin ba har 1:00pm da ɗori ba a saka shinkafa ba.
Lokacin da Zahrah ta dawo daga school tayi arba da Kawu na girki. Shewa ta buga sannan tayi hanyar ɗakin Mamah tana dariya.
Batayi tsammani ba sai jin Muryar shi tayi yana ƙwalla mata ƙira..
“Zahra'u zahrah'u”.....babu alamun zata tsaya ballantana na ta amsa ta wuce ciki abun ta. Kamar yayi kuka haka ya tasa tukunya da murhu a gaba, gashi babu yadda ya iya tunda gimbiya ce ta bashi girkin.
Ana cikin haka Badi'a tayi sallama da basket ɗin abinci a hannun ta, a hanzarce ya miƙa ya zo gaban ta yana miƙa mata hannu.
“ɗan matsa zan wuce”
“kawo na shiga da shi” da ƙyar Badi'a ta danne dariyar da ta kama ta sannan tace
“gyara na wuce ko sai na yi wa bodyguards ɗina magana” kasancewar bai san ta ba kuma yaga ƴar gayu yasa yayi tunanin da gaske ne. Direct ɗakin Mamah ta miƙa abincin sannan ta fita.
Kawu da ya gama galabaita ga rana, ga zafi ga hayaƙi in Banda zufa babu abun da ke ketowa daga jikin shi. Bana amarya kuwa ta tsare ina bai dafa ba ko ta dafa ba zai ci ba don ba bashi zata yi ba.
“kiyi haƙuri kizo ki amshi girkin nan, Ni babu abunda zan iya wallahi yanzu haka na wahala”
Hararar shi tayi ta gatsina hanci tukun tace
“ita waccar ta ɗakin uban meh take yi a gidan da bazara dafa ba, maza je ka taso ta”
Zungui zungui babu kunya ya ja ƙaton kanshi zuwa ɗakin Mamah. Lokacin kuwa sun zuba fried rice da kuma papper meat da aka kawo daga gidan Ammi suna ci. Yawun Kawu duk ya tsinke ammah ya dake.
“madina ki fito in ji amarya kiyi girki”
Idan gini na magana toh, Mamah ko kallon shi bata yi ba gashi yanzu duk jin zuciyar sa yake yi a mace ba zai ma iya dukan ta ba. Ya fi 10minutes yana jira ko zata fito ammah shiru, hakan yasa ya ja dogon kafar shi ya koma wajen bana amarya.
Marairaice mata fuska yayi
“don Allah gimbiya kiyi haƙuri ki zo ki ƙarasa, gaba ɗaya sun ƙi kula Ni su ma.
(Nace ah su Kawu anyi luƙus kenan”
Harara ta ƙara banka mishi
“toh ita ɗin uwar ka ce da ba zaka ce ta fito ba, koma kace ta fito” haka ya ƙara komawa kamar ɗan ta.
“tace wai ki fito" banza Mamah ta ƙara yi mishi. Babu yadda ya iya ya ƙara dawowa.
Wasa wasa abinci har 3:00pm ba'a zuba shinkafa ba. Da ya gaji kawai ya fice shagon gyaran babur da yake ya zauna Allah ya taimake shi wani ya kawo gyara sannan ya samu ya ci abinci.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, duk shekara sai lashe kyaututtuka masu yawa daga makaranta da kuma wajen makaranta. Yanzu har su Zahrah suka shiga aji uku (jss 3) kwacakwam hankalin su ya koma kan karatun su, gashi Badi'a na shirin yin sauƙa saboda damah can tayi wa Zahrah nisa.
An samu sauyi cikin gidan Kawu sosai don kuwa yanzu Kawu ya zama dolo, babu abun da ya isa yayi sai da umarnin baba amarya. Ya bi ya rame har abun tausayi ammah hakan bai taɓa zuciyar Zahrah ba.
Yaya Ishaq har yau shiru babu shi, sai dai wasu lokutan ya kan kira wani staff ya haɗa shi da Zahrah. Su Zahrah an girma,duk ƙiriniya irin ta Zahrah yanzu babu, ko dan ance zama da maɗaukin kanwa wai shi ke kawo farin Kai. Toh Zahrah ma dai ta sauya. Ga wani irin kyau da take yi yanzu wanda ake kira da ƙyalƙyalin ƴan matanci....ta ko ina Zahrah batada makusa. Idan kyan fuska ne toh Zahrah ƙarshe ce, kana ganin ta kaga fuskar Mamah kamar anyi copy sai dai Mamah da yake wahala ta dafar da ita yasa Zahrah ta fita haske sosai. Uwa uba wani rashin don magana da Zahrah ta ɗauko abun mamaki idan har kaga tana magana toh an taɓo ta ne. Hakan ba ƙaramin ƙara mata kwarjini a idon ƙawayen ta yayi ba don kuwa kowa shakkar ta yake.
Zahrah ce zaune a class yayin da mates ɗin ta suka kewaye ta tana kwatanta musu yadda ake solving wani equation a maths, da ƙyar suka samu suka fitar da amsar. Bayan sun gama ne ta ci gaba da koya musu sauran abubuwan da suka kamata. Aikin su kenan kullum a school yanzu idan sun je saboda an ma daina shiga clsss ɗin su.
A lokacin exams kuwa Zahra ta nutsu ta rubuta abun ta. Bayan an kammala aka sallame su har sai result ya fito za'a neme su don yin registration na senior class, ranar sunyi kuka iya kuka saboda wasu ba a nan zasu ci gaba da karatu ba. Zahrah na ɗaya daga cikin waɗanda suka cire tsammanin dawowa ALMUNAUWARA don ci gaba da karatu duba da sponsor nata baya nan kuma babu alamun zai dawo, kuɗin kuma yafi ƙarfin mahaifiyar ta.
“Dole zan koma government school ne na sani ammah Alhamdulillah for these three good years I've learned a lot”
Da haka ta lallaɓa zuciyar ta tare da fauwalsws Ubangiji komai.
Yanzu iya islamiyya suke zuwa. Zahrah ta maida hankalinta sosai kan karatun addinin ta, wanda ya kawo sauyi mai kyau cikin rayuwar ta.
Rayuwar ta haskaka sosai, a da Zahrah bata iya riƙe bakin ta duk maganar da ta zo mata ko a waye kwaɓa mata take yi ammah yanzu Alhamdulillah an samu great improvement don kuwa a rana maganganun Zahrah ƙirgaggu ne, sanadiyyar islamiyya yanzu Kawu yana cin arziƙin gaisuwa daga gare ta, haka baba amarya ma idan ta ganta takan gaishe ta.
Sana'ar Mamah ta ja baya sakamakon jinya da take yawan yi yanzu sauƙin ta ma suna samun abinci ko da yaushe ga kuma kyakkyawar kulawa daga sabon ahalin su. Jinya abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, an je asibiti abu yaƙi yiwuwa.
Duk san ɗin da za'a yi sai ya nuna normal hankalin Zahrah duk ya tashi. Damuwa ce fal a ranta ga wata dama da ta fara yi.
Fahimtar haka da Ammi tayi yasa ta yanke wata shawara ita da mai gidan ta.
“Ni wallahi Abban Badi'a abun ya ɗaure mun kai, mutum mai lafiya lokaci ɗaya sai jinya, duk da cewa ba abun mamaki baneh kaɗan daga hikimar Ubangiji ammah jinyar Maman Zahrah akwai sa hannu astaghfirullah, a ce duk wani investigation da aka yi sai ya nuna normal bayan kuma gata nan tana jin jiki”
“ni kaina nayi tunanin hakan, ita wannan mata gaskiya tana ganin jarrabawar rayuwa, kiga fa mijin ko sau ɗaya ban taɓa ganin an zo da shi ba”
“wallahi kuwa Ni haushi yake bani daga shi har amaryar tasa mai zubin karuwai. Wallahi haƙƙin Madina da ɗiyarta kaɗai ya ishe shi, da sannu zai fahimci hakan tun anan duniya.
“Allah zai saka musu kam”
“Ammah Ni ina da wata shawara fah, ko za'a gwada ISLAMIC medicine me?"
“shawara Mai kyau sai mu gwada ai.”
Tun da aka fara ISLAMIC medicine ta ɗan fara samun sauƙi, sai dai yanzu ta fara wasu irin surutai musamman ina tana bacci. Wani lokacin Zahrah sai dai ta zauna tayi ta sharar kukan ta daga ƙarshe ta ɗaura da yiwa Mamah addu'a.
Yau da safe Zahrah na zaune gefen Mamah yayin da take bacci kawai taji Muryar Mamah na magana.
“Tabbas na riga na cuci rayuwa ta da na gudu na bar dangi na wanda bana jin har abada zan ƙara ganin su, Alhaji Baba da kuma Hajjaty ina roƙon ku yafe min bana jin zan iso gare ku mutuwa zata riske ni.... Nan da nan jikin Mamah ya ji ƙera da zufa sai wani karkarwa take yi. Addu'a ta tofa mata nan da nan taci gaba da bacci ta.
“Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari game da rayuwar Mamah na, ya Ubangiji kafi kowa sanin ɓoyayyen al'amari da kuma bayyananne, ya Rabb! Ka bawa mahaifiya ta lafiya ka kuma bani ikon haɗa ta da dangin ta” ta ƙarasa hawaye na zubowa daga idanuwan ta.
Kwanci tashi asarar mai rai Mamah ta shafe wata guda tana jinyar da aka gagara gano wace iri ce, a lokacin kuma baba amarya ta fara shiga tana gaishe ta kullum. Ita dai Zahrah bata kawo komai a ranta ba don yanzu babu laifi suna gaisuwar mutunci da BABA AMARYA ɗin.
Ana cikin haka result ɗin su ya fito, a ranar kuwa suka dukufa zuwa school bisa tursasawar Ammi.
“Zahrah ki tashi kije ki shirya a can tare da Badi'a kuje school za'a buɗe muku result” cikin fuskar dake bayyana tsantsar damuwa tace
“Ammi don Allah ki barni na zauna a nan tare da Mamah, Badi'a sai ta duba min"
“Aah Zahrah tashi zaki yi ku tafi, ina nan zan kuka da mamah”
Babu yadda ya iya ta wuce gidan Ammi a can suka shirya suka shiga adaidaita saboda Abba ya tafi Kaduna. Suna isa ganin classmates ɗin su Zahrah ta ɗan ware, ihun murna suka yi da suka hango Zahrah da Badi'a. Da gudu suka rungume su tamkar zasu faɗi ƙasa.
Murya uncle Hashim me ta dakatar da su
“Hey! Are You alright?” waskewa suka yi suka ce
“yes sir”
Yace
“Alright You guys should FOLLOW me to the computer library so that your results will be checked”
Yana tafe suna bin bayan shi har suka iso. Ɗaya bayan ɗaya ake dubawa kuma Alhamdulillah duk duk sun samu abun da ake so na tafiya senior class.
Badi'a ce second to the last, Tana fitowa tayi hugging Zahrah
“best frightful and colourful result”
Tsalle Zahrah tayi
“Alhamdulillah, bari na dubo nawa ki jira ni”
Kamar yadda Badi'a ta fito da gudu haka Zahrah ta fito da gudu
“Awful and marvelous result"
Farin ciki tamkar su yi yaya.
______________★★★_______________
Typing 📲
🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡
(𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠)
★TAKUN FARKO★
[Labari/Rubutawa]
🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈
𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
﷽
PROLOGUE
𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣1️⃣
Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘
SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________
Bayan an duba wa kowa PC ya haɗa musu assembly.
“Good day to you all our graduating junior students, you indeed deserved to be honored because you all perform well an fantastic.”
Tap tap tap sukafara tafi
“The most amazing part of your success is that three students from this school were honored with money 💰.”
Tap tap tap
“I'll like to see Mayam Muhammad on the stage”
M² ta fito a natse,
“the state's board of junior secondary School examination awarded 100k to you for your wonderful performance and this school specifically honored you scholarship in to the senior class.”
Nan da nan ihu ya kacame sai tafi Tap tap tap
A hankali ta koma tana murmushi.
“Badi'ah Kabir Umar, shi also perform wonderfully in this exams the board awarded 300k to you, congratulations Badi'a, and to you also the school management awarded a scholarship to you in to the senior class”
Ihu ta ka ina da ƙyar suka yi shiru.
“The champion, Zahrah Abdulkarim Kuru being the overall best student to write this JSSE in this state at large was awarded the sum total of 500k and sane, management of the school awarded a scholarship to you"
Murna ta ko ina sai da PC ya tsawatar musu suka yi shiru.
“Congratulations to you all, I hope you'll improve and do better next, Maryam, Badi'a, Zahrah see me in my office"
Daga haka kowa ya watse yana farin ciki bayan an raba musu admission letter nasu da deadline na registration ɗin.
Zahrah tafi kowa yin farin ciki ko babu komai Ubangiji ya kawo mata mafita. A office ɗin PC aka ɗauki pictures nasu aka ce su turo iyayen su gobe before a sallame su. Daga haka suka wuce. Abba, Mamah ammi duk sunyi farin ciki.
Alhamdulillah jikin Mamah yayi sauƙi kwanan nan saboda amfani da magungunan ISLAMIC da take yi. Yayin da suka fara sabawa da baba amarya.
Da yake babu registration bana, on their resumption day sassafe suka fice don yanzu Abba ya samar masu driver da zai ke kula da zuwan su da komawar su. Direct old ss1 suka nufa. Around 7:30 kuwa sauran students suka fara zuwa, da yawa sun dawo ammah wasu sun sauya school ne wasu kuma barin gari zasu yi.
Bayan anyi assembly Uncle John who's the only Christian cikin staff ɗin su ya fara shigowa.
“good morning sir”
“morning, sit down”
Bayan sun zauna ya fara yi musu bayani cikin harshen turanci.
“Ina yi muku Barka da shiga ajin senior. Fatan zaku ƙara maida hankula ku ga karatun ku.
Shi wannan aji da kuke gani na senior mataki ne daga cikin matakan rayuwa, idan kika tafka kuskure cikin sa yana iya wargaza ƙaddarar rayuwar ki.
Saboda haka ku nutsu ku san MEH kuke yi”
Nan ya ci gaba da bayani wanda a fakaice career guidance ya Basu. Cike da zumuɗi da farin ciki bayan ficewar Uncle John suka fara magana.
Zainab Sani tace
“Ni fah da kuke gani tun ba yau ba na riga na ware abun da zan karanta nan gaba.
A rayuwa ta ina matuƙar ƙaunar yadda Nurses ke kula da maras lafiya. The way they show their concern, care and love to their patients drove me to like the profession”
Idanuwan su suka zuba mata yayin da ta ci gaba da bayani.
“kun san MEH, yadda suke salwantar da lokacin su don kula da patients, Baku gani doctors zuwa kawai suke na wani lokaci su tafi, ammah Nurses suna yin 8hrs suna kula da patients da zarar wata ta tafi wata zata zo saboda kada abar patient a haka.
Da wannan profession ɗin zaki samu lada da yawa, sai ki samu aljanna sanadiyyar su”
Kowa ya gamsu da bayanin Zainab. Ɗan gyara zama Zahrah tayi tace
“Babban buri na a duniya bai wuce na zama cikakkiyar alƙaki wato judge mai cikakken iko ba. Ina so naga ko yaya mai laifi yake an hukunta shi.
Akwai wani babban rabo a rayuwa ta da yasa nake don ganin duk mai laifi ya karɓi hukunci daidai da laifin shi.”
Shiru kowa yayi yana nazarin Zahrah. Sun daɗe suna ta maganganu game da career nasu. Har lokacin tashi yayi Duk malamin da ya shigo maganar da yake yi musu kenan tare da basu shawarari kan yadda zasu yi karatun su successfully.
Bayan Zahrah ta koma gida ta tarar da jikin Mamah babu daɗi. Ina banda kuka babu abun da take yi tana roƙon Ubangiji da ya bawa Mamah lafiya.
“mamah tah! Ke kaɗai ke gare ni bayan Allah. Don Allah Mamah na ki tashi ko kaɗan bana son rasa ki.”
Cikin bacci taji kukan Zahrah ita ma lokaci ɗaya hankalin ta ya tashi.
Cikin Muryar ciwo ta kamo hannun Zahrah
“Ɗiya ta! Ki sani kowanne rai sai ya ɗanɗani mutuwa, dole ko ban mutu yanzu ba zan mutu nan gaba. Addu'ar ki kawai nake buƙata Zahrah! Ke kaɗai Allah ya bani kuma ina da burin zuwa ga ahali na sai dai na kasa. Amma ke bazan so ki ci gaba da rayuwa tare da wannan maras imanin ba ko da kuwa bayan raina ne.
Yanzu ki tashi ki shirya ki tafi islamiyya"
Maganganun Mamah sunyi matuƙar tasiri a zuciyar Zahrah, gyara mata shimfiɗa tayi ta zuba abinci a plate sannan tayi feeding Mamah. Sai da ta bata ruwa ta tabbatar ya tsirga kafin ta kwantar da ita.
A gaggauce ta samu ta shirya gashi lokaci ya kusa ƙurewa. Sallama tayi wa Mamah ta wuce gidan Ammi.
Ammi kaɗai ta tarar a parlourn zaune tana kallo. Da sallama ta shiga sannan ta zauna jikin ƙafar Ammin.
Cikin Muryar ta mai sanyi tace
“Ammi ina yini”
Murmushi Ammi tayi tana yabawa da nutsuwa irin ta Zahrah wacce lokaci ɗaya ta zo ba tare da tsammani ba tamkar wahayi.
“lafiya