Showing 27001 words to 30000 words out of 36183 words
mu huta damunmu da ake yi ana
bada bayanin mu a kan idona sai ka ji dattawan
unguwar suna cewa ai nan kusa kusa duk ai babu
sauran sa'arta kai kannenta na kusa ma babu duk sun
garna yin aure sai ita kadai.
Na debi littafin nawa na rungume na jawo kofata
na rufe na yiwa babana sallama na fito da nufin in
mun gama maganar da za mu yi sai kawai in wuce na
kuma san ganina tare da litattafan a hannuna zai kara
sashi tafiya da wuri tunda yasan ina da abin yi.
Ina fita waje maimakon in ga Halliru, Mubarak
na gani a tsaye, wani irin lalataccen kallo ya yi min da
ya sanya gabana faduwa cikin zuciyata na yi maza na
ce, ban yafe maka ba zuwa kofar gidanmu da kayi ka
fadar min da gaba.
Shima malamin naki yana nema ya rikide ne ya
Zama saurayinki? Da sauri na daga ido na kalleshi
121
cikin tsananin mamaki abinda ban taba zaton wani zai
yi tunanin hakan ba don babu wata alama da take nuni
da hakan.
Idan kika kuskura na gane da wani abu a
tsakaninki zaki bar karatun naki gaba daya ki koma
Zaman gida in kumakina ganin kamar wasa nake yi to
bari in gane halkan ki gani kina nufin don yana koyar
da ke karatu a da sai kuma a yanzuki rinka kwasar
litattafaikina zuwa wurinshi kuna zama ku biyu?
A kidune nace mishi, ba fa mu biyu bane? Ya yi
maza ya katseni ko ku dubu ne ban yarda ba kar in
sake gani ko jin kin fita daga gida bayan sallar
magariba, na gaya miki.
Kuka na soma yi mishi saboda bakin cikin abinda
yake yi min, takuraw ar ta kai duk inda ta kai, komai
nake yi ya sani ko baya nan nayi in ya dawo zai ji
labari.
Cikin karfin hali na daure zuciya ta na ce mishi,
to wai ni ina ruwanka da ni ne? Ina abinda ya shafeka
da abinda nake yi, kullum sai ka shiga harkata, kullum
sai ka takurawa rayuwa ta.
Ban san dalili ba rannan sai na kasa zuwa wurin
mraja'ar da Malam Yahuza ke yi min, maimakon
washegartnma inje ban i cb a sai kawai na hakura da
muraja' ar na koma maida hankalina sosai a aji wajen
fahimtar dukkan darussan da ake yi mana.
122
Kullum dai burina bai wuce in samu lokaci in
tatawa Mubarak rashin mutuncin da zai sa ya fita
harkata kwata-kwata ba amma in na ganshi sai in kasa
saboda kwarjininshi da yake yi min nauyi a idona.
Gabatowar watan azutin ra:nadan mai girma ya
sa aka shirya mana jarrabawar da a bayanshi muka
samu hutun makaranta har sai bayan salla mu koma,
farin ciki sosai nayi a wannan. Jlokacin a dalilin
jarrabawa ta tayi kyau banda haka zan dan samu
hutun wahalar da nake yi ta zuwa makaranta da kafa
in dawo da kafa, Sannan zan dan fuskanci wani abinda
nake kuma dokin yi shi ne dinki don na dan fara
iyawa har yaya Dija ta gamsu da labarina bayan
dinkin 'ya'yanta dana dade ina yi musu ta hada min
har da nata nayi a dalilin hakan kuma ta ma karbar
min na kawayenta da abokan zamanta.
Ki natsu sosai ki yi musu mai kyau don sai ya
zamo tamkar tallan iyawarki kikayi, nace mata to.
A wannan lokacin hutun makaranta da dokin
dinkin azumi da nake yi ne ya ragemin damuwa ko
bacin ran da na samu kaina a ciki ra turowar da
Halliru ya yi a ka karbe mishi kayanshi, shi ko kayan
na gani ina so kamar yanda wasu suke fada da da ya
kawo gidan mu haka kawai ban san hawa ba ban san
sauka ba wadanda suka kawo kayan suka zo suka ce a
yi hakuri a basu bisa wasu dalilai da suka ce wai su ne
sukayi dalilin in sa auren nashi a wannan lokacin.
123
Yakumbo Halima dai ta ce min wai yayi mata
bayani da cewar ya fasa auren ne a dalilin akwai wani
dodo dake biye da ni mai tsoratar da mutane matukar
kuma ba a tsaya an rabani da wannan dodon ba to
aure na zai yi wuya.
Bayanin 1ashi ya yi tasiri mai karfi a zuciyar
Yakumbo don salati ta rinka yi tana fadin, wai dama
tuni ta dade tana tunanin watakila aljani ne da ni
wanda ya hanan11 yin aure.
Ni kam tattara maganar nayi na ajiye a gefe ban
yarda ba ban kuma karyata ba don ban san komai a
kan irin wedannan al'arauran ba, abu guda daya dana
sani na kuma yarda na tsaya a kan shine gaba daya
mu mutane da kuma aljanu dukkanmu bayi ne na
Ubangiji babu mai ikon cutar da wani a tsakani sai da
abin da Ubangiji ya yarda ya kuma kaddara fil azal
wannan din zai cutu da shi, wannan shi ne bayanin da
kullum malamin mu na tauhidi yake yi mana da sai
kuma na yarda sai na samu natsuwa da kwanciyar
hankalin dana fuskanci al'amurana na dai san kawai
na koyi yin addu'a.
Sai dai kuma tawakkalin da sanin da nayi cewar
babu mai yi ko hanawa sai Ubangiji bai hana zuciyata
kuntata ba a dalilin aure nake so auren kawai nake so,
SO nake in ganni nima a zaune a nawa dakin ina zaune
ina aurena ga Asabe tunda ta yi aurenta tana dakinta
ban sake ganinta ba, kullum kuma sai uwarta ta yada
124
magana a tsakar gida ta ce, yin aure ai rufin asiri ne
Asabe asirinta ya rufu tana can dakinta cikin ntin
asiri, ubangiji ya sanwaka ace yar mutum tayi ta
galantoyi a gaban shi, yana kallonta kowa ya zo ya yi
kamar zai aureta in ya taya ta sallama yaga araha sai
kawai ya yi dani ya tafi. Tin, ta ja tsaki fa ci gaba da
harkokinta.
Cikin zuciyata dai na kan yi mamakin
al'amarinta saboda a farkon abinda ya faru da Asabe
na dauka zata fita banyar irin wadannan abubuwan sai
ya zamo ko a jikinta ba ta ma tuna nata sai dai na
wani dama bai karasa natan lalacewa ba.
Ana cikin haka watan azumin ramadan ya iso
sayaiya sosai Mansur ya yi min, ina zaune a dakina
ina. buda baki mun kai azumi na biyu ina jin baba
Lantana tana cewa babana wai ita din ai rabon wahala
ne ya se ta aurenshi in banda haka ai shima ya san irin
zaurawan da tayi, cikin zuciyata na ce ob oh kowa da
irin yanda babu take zuwa mishi, watni ta kara mishi
natsuwa wani kuma ta yis anadin wargajcwarshi, wata
mai daraja irin' na azumi bai sa ta dan rusunawa
al' amiaranta ba.
Isiyaku ya yi sallama a kofar dakima ya shigo,
anti ina wuni? An sha ruwa lafiya? Na amsa gaisuwar
tashi ina mai kallonshi. Ya yi fes da shi ya yi kyau
kamar in tambayeshi ka samu wani abin yi ne Isiyaku,
sai na yi maza na fasa a dalilin ba wani shiri muke yi
125
ba a yanzu saboda gaba daya al'amuranshi na
Mubarak ne.
Ya karkata ya zaro envelop daga aljihun shi ya
ajiye a gefena, wai gashi in kawo miki. Da sauri na ce
mishi, Isiyaku ashe ban ce maka kar ka sake karbo
wani abu daga wurin mutumin nan ka kawo min ba?
To dauki maza-naza ka tafi mishi da shi ka kuma
gaya nishi inji ni na ce ya fita hanyata ya daina shiga
harkokina in bai sani ba ko bai gane ba to bari ni da
kaina in gaya mishi na tsaneshi, na tsani al'amuranshi,
na kuma tsani duk wani abinda ya shafe shi, in ya
kuskura ya sake aikoka da wani abu wurina to zan
karbi abin in aikawa matarshi don tasan yanda zatayi
da shi, ya daina kula al'amarin.
Wani irin lalataccen kallo Isiyaku ya yi min da ya
yi dalilin da nan take na warware hannu na sheka
mishi mari mai kyau a kumatunshi har sau biyu, ina
wasa da kai ne da zaka yi min irin wannan kallon? Bai
cc min komai ba sa hannu ya yi ya dauki envelop in
ya sa kai ya fita ya bar gidan, ya barni ina huci da
tunanin haka zan rinka yi mishi duk lokacin da ya
kawo min wani sako tunda nace msihi ya daina yaki.
Washegari mun taso daga wurin tafsir nufina in
taff gidan yaya Dija don in yi mata barka da shiga
tamadan mai albarka sai kawai naga Mubarak ya yi
fakin din motarshi kusa da hanyar da muke wucewa
126
bai ii tsoron cincirindon matan da suke wucewa su na
hangenshi ba ko don kar su gayawa matarshi.
Yana ganina zan wuce ya yi maza ya fito daga
cikin motar tashi ya tsareni, nmagana yake yi cikin
natsuwa ta yanda na nesa ba za1 gane bakar magana
yake yi ba.
Malamin naki ne ya koya miki rashin kunya da
rashin mutuncin da kike yiwa mutane ko? Na daggo
ido na kalleshi saboda ambaton malamina da ya yi.
Eh ai kafin kullewarku ke da shi rashin kunyarhi
ba ta kai haka ba, ki mari Isiyaku, gansamemen
saurayi kamar Isiyaku ki mareshi dame kika
girmeshi? Kina nuiin in banda shf din yaro ne mai
mutunci za a yi hakan'? Kina mace ki mari namiji kina
nufin in ina da iko da ke ba zan yi miki hukunci mai
tsanani na ladabtarwa ba? Sakarya kawai sokuwa,
shasha:ha wacce rashin mafadi ya hanata sanin
abinda ya dace da ita.
Wani lalataccen kallo ya yi min gami da jan
mummunan tsaki kafin ya wuce ya tafi ya barni, ance
miki matata irinki ce.
Haushi da takaicin kaina suka hadu suka kamani
kan yanda akayi ya gama gaya nun bakaken
magangnaunshi ya wuce ya tafi ba, tare da na iya ce
mishi koami ba, babu kuma abinda yafi komai kona
min rai irin cewar da ya yi wai matarshi ba irina ba ce,
to wacce iri ce? Me yake nufi da wannan maganar ta
127
shi? Babu irin alkawarin da ban yiwa kaina ba a kan
ba zan sake barinshi ya gayamin magana in kyaleshi
ba amma gashi na kasa gaya mishi komai.
Baba Lantana a wanann lokacin tsula tsiyarta
take yi irin yanda ta ga dama, da yake Asabe mai
imani ce da tayi cikinta sai ta reni abinta ta haif
abinta ba ta je ta zubar da shi ba balle ta je tana
dauka wani zunubin na kisan kai, gashi kuma a
saradin hakas ai ta yi aurenta tanan an goye da danta
tukarballa ta bar wasu a titi suna ta tanbele basu ga
tsuntsu basu ga tarko.
Da bain nata ya tsaya a kaina ni kadai da sauki
yanzu yanzun nan ne zata sa shi a gaba ta sulleshi sai
dai in ba zan leka kofar gida ba ko ka ji tana cewa, to
ni in banda na lissafa naga duk tsiyarka kai da
ya'yanka zan iya cinye wannan daki da nake ciki
tunda dai su din mata ne ai da tuni na dade da rabuwa
da kai in yi tafiyata yaushe zan iya zaman jinya, to ba
zan tafi ba ne in bar kasona a ce rashin bhakuri doon
haka nake zaune daram ina jira sai naga kwal uwar
daka.
Wadannan kalaman da na ji baba Lantanan tana
furtawa wadanda na tabatar ba ta san na ji ta ba su ne
suka yi dalilin da na yi sammaon zuwa gidan yaya
Dija na bata labari.
Shiru tayi tana kallona cikin wani irin yanayi,
Jimawa can sai naji ta ce, i tsorona ma kar ta karasa
128
mana shi ba mu sani ba tunda take mapganar gadon
dan wannan gidan wato ita idonta yana kanshi ta sake
nisawa kafm ta ce, nifa da baba zai yarda ma de wani
auren kawai ya kara.
Da sauri na zaro ido ina kallonte cikin razana,
aure kuma? Shi baba ya ce miki zai fya yin mata biyu
ne? Hankalinta a kwance ta ce min to ba shi kenan ba
in ba zai iya biyun mai zama ta zauna mai tafiya taa
tafi, amma wannan fitina har ina? Daka akwai wata
yarinyar bazawara nan kusa da ma takaba ta gama
tana kuma da' ya'yanta biyu k inga in Akayi sa'a ma
sai ya kara haihuwa ya ma huta da sharrin da take
kulla mishi na baya iya tsinans mata komai, baba ai
ba tsoho bane in ma bakan ne bakin cikin ta ne ya
maidashi hakan, na dai ja bakina nayi shiru ina jinta
tana maganganunta bance mata komai ba.
Rannan ranar wata juma'a da yamna bayan
saukowa daga sallar Juma'a naji babena ya karbi
wasu baki a zaurenshi wadanda na tabbatar iyayen
Mubarak ne wato Alhaji Muhammadu da amininshi
ban san takamaiman abinda ya kawo sun ba na dai
gane su din ne kawai ta dalilin ambaton sunansu da na
ji baban nawa ya yi.
Nayi maza na mike na shigs gida na basu wuri,
can cikin zcuiyata dai ina taunsnin wanene kume
Alhaji Muhammadu? A sanina a unguwarmu baban
Mubarak ake kira haka to amma shi me zai kawoshi
129
gidanau? Yana dai zuwa duba babana daga baya
bayan nan tare da Mubarak to amma wannan ai zai iya
Z8ma makwabtaka ne ko kuma kwadayin alherin da
ake samu wurin gaida mara lafiya.
Ina ganin sanda babana ya shigo gida rike da
tabarmarshi a hannu bai ma tarota inje in hade ba bai
ce min komai ba nima kuma ban tambayeshi ba don
dama can babu irin wannan mu' annaiar a tsakaninmu
don haka sai kawai na ci gaba da harkokina.
Da daddare ina zaune dakina takarduna na
makaranta nake dubawa lokacin da na ji sallama a
cikin zauren gidanmu gabana ya yanke ya fadi saboda
jin da nayi tamkar muryar Mubarak ce da sauri na
mike na fito da ita.
Uhh lalle al'amarin babba ne har cicin zare
kuma yanzu kake shigo mana? Ta yi kwafa ta ce ko
baka yi haka ba ai an kuma hade.
Tsayuwar da baba Lantana ta yi a wurin wai sai
ta ji abinda ya kawoslhi ko zai fadi ya hanani tafiya in
barshi don ba zan 6ata mishi rai a gabanta ba, wucewa
na yi nace mishi muje daga waje mana, don haka
muka fito.
Tun kafin in tambayeshi abinda ya kawo shi
gidanmu ta tsareni dai danuwanshi wai ni me baba
yake nufi da ni ne? Tambayar tashi ta sanyani yi
mishi tambayar wane baba? Da saurinshi cikin wani
irin yanayi ya ce min, babanki mana.
130
Gabana ya yi mummunan faduwa jin yanda ya
ambaci baban nawa, cikin zuciyata na ce, lalle
mutumin nan yau yana jin rashin mutunci amma babu
laifi, na kawar da tunanin nawa na naida hankalina
Wajen sauraron abinda Zai gaya min a kAn baban nawa
wanda na tabbatar ba mai dadi bane.
Na rasa me nayi nish na rasa wane irin laifi na
yi mishi wanda ya wuce gabai yafewa, tun aurena bai
wuce wata uku ba na turo aminin babans ya zo
wurinshi.kan maganar ni da ke bai saurari maganar
ba na koma na sake rokon babane ya zo da kanshi ya
yi mishi magana don ya fi ganin abin da muhimmanci
ya zo ya sameshi bai ji kunyar idonshi ba ya ce mishi
ba zai bani ke ba yau ya sake dawowa saboda na sake
komawa gabanshi na rokeshi ya dawo ya sake
rokonshi to ya sake dawowa shi kuma ya sake cewa
matukar shi ne zai daura miki aure da kanshi to ba zai
daura auren da ni ba, saboda na ci mutuncunshi na
keta mishi haddin yarshi nayi sanadin da sai dake
kuna wulakanta shi ne na ce bari in zo in ji me na yi?
Me nayi miki na haka ni na taba ki ne? Ke baki gaya
mishi babu komai tsakanina da ke ba sharri kawai
matar shi ta kulla mana.
Cikin natsuwa na tambayycshi, to in baka yi
komai ba sai me? Dole ne sai ya baka aurena da za a
je ana ta yi mishi zirga-zirga a gida? Sauran iyaye da
sukayi hukunci a kan ya'yansu haka aka yi musu
131
Naga shima shi ya haifeni ko kuwa don an ganshi
yana saida turmatir sai a ce bai isa ya zartar da hukunci
a kan tashi 'yar ya zaunu ba sai an canza mishi?
Bai nuna bacin rai da jin maganar tawa ba sai ya
ce min, 1yaye suna zartar da hukunci mai tsanani a
kan ya'yansu, Maryam yin hakan ba laifi bane amna
kuma da yawansu sukan ciza ne sai kuma su hura a
mati yawancin lokaci ma suikan taya ya'ya son
abinda sukc so matukar sun gane babu cutuwa a cikin
lamarin, me yasa shi ba zai yi hakan ab? Me ya sa ba
zai tayaki son abinda kike so ba ya baki mijind a kika
rayu kina so?
Na ce, ai abinda nake son yake taya ni shi din ya
san ban taba sonka ba ya kuma san duk wani abinda
ya gudana tsakanina da ka ya faru e a dalilin
kuruciya da kurna kuskure.
To babu laifi, ya fadi hakan cikin wani yanayi
don baka nayi maza na juya da nufin shiga gida sai
naji yayi maza ya ce min to, uan dakata mana ki ji
abinda Zan gaya miki.
Na dan ja na tsaya ba tare dan a waiwaya na
kalleshi ba, sai naji ya ce min, to amma ai shi baba
yana da labarin rabo yana kashe mutane ko?
Gabana ya sake yankewa ya fadi jin da na yi ya
ambaci mutuwà a tsorace kwarai na tarabaye shi, me
kake nufi da wannan maganar?
132
A natse ya ce min, abinda naken ufi kenan ki
buda baki ki yi mishi m agana ki gaya mishi gaskiya
babu komai tsakanina da ke ban taba mishi ke ba, na
ce to in baá haka ba fa?
Ya ce shi kenan sai ki yi ta zama sau goma in z2
a kawo miki kaya sau goman kuma za a zo a karbe.
Gabana ya sake faduwa, kar dar ace Mubarak ne
ya yi dalilin fasa aurena da Halliru? Kar dai a ce
Mubarak ne dodon da Halliru ke gayawa Yakumbo
Halima wanda ita ta dauka dodon dodanni ne ko wani
aljani.
Rasa abinda zan cewa Mubarak nayi in dan ji
saukin abinda ke cin zuciyata don haka sai na ce
mishi, a sanina dai baba na shi ne mahaifina yana da
iko a kaina kamar yanda kowane uba yake iko da
danshi saboda randa ya yis anadin zuwana duniyar
nan babu wanda ya taya shi don haka in bar rabon
wani ya zama sanadinshi to na rantse har abada ba zan
auri wannan din ba sai dai ni ma rabon nashi ya sa
yanda zai yi da ni kuma karka sake kulani.
Ina fadin haka na yi maza na shige cikin gidanmu
na barshi a nan wurin yana tsaye. Ko badan ban i
haushin hana Mubarak aurena da babana yayi ba
saboda tuni ya riga ya fita min a rai bana kallonshi inji
zuciyata ta rayamin abubuwan da ta saba raya mina
game da shi a baya sai dai in ganshi in ji faduwar
133
gaba ko in ganshi in ji haushi da takaicin shi sun
kamani.
A wannan lokacin ne kuma baba Lantana ta fito
da wani irin salo a gidanmu duk wani wanda ya zo
wurinta in suna hira bata kai karshen hirar sai ka ita
tana gaya mishic ewar ita wannan zama da take yi ma
ai ya kusa ya zama haramtaccen zarna, abokin hirar ta
ta ya ce, haramtaccen zama kuma, Lantana sai ta ce eh
to haramtacce mana tunda abinda ake yiwa zaman
yayi karanci ace niji kana kallonshi yana kallonka
shimfidarku daya amma sai ya sahfe kwana da
kwanaki babu komai, babu wani motsi a can babu a
tukubya ma babu ana yin zaman haka ne ai ni yanzu
kiris nake jira don ma dai kawai kar ka tafi ne ya
zama ka tafi ka bar ladanka.
Haba Lantana haba Lantana yanzu ke a yanda
kike din nan sai kin yi korafi kan