Showing 3001 words to 6000 words out of 36183 words

Chapter 2 - Halin Rayuwa Book 3 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

206


Tunda baba Lantana ta gane irin zirga-zirgar da
mutane suke yi wajen zuwa asibiin sai itama ta soma
zuwa kulum ta kan zo ne da tabarmarta ta shimfida a
hanyar da ta san itace tas higowar mutane tana ganin
an zo sai ta tari masu zuwan tayi musu jagora zuwa
inda babana ke kwance in suka gaisheshi suka ba da
abin da zasu bayar tayi amza ia karbe ta saka a cikin
yar fos dinta ta koma kan tabarmarta ta zauna ba
kuma zata sake tasowa ba sai wasu bakin sun zo daga
ni har yaya Dija babu wanda ya daga ido ya kalleta
balle ya ce mata kanzil.
Kwana tara baba ya yi kafin aka sallameshi a
hakan ma matsawar shi ce ta sa aka yi ta saboda
yawan maganar da yake yi bai son zaman asibiti bai
taba zuwa asibiti don kanshi ba sai dai don ya zo duba
mara lafiya, yaya Ibrahim ne ya yi duk wata
dawainiya har da biyan kudin sallamar muka dawo
gida.
Likita ya sallame mu ne bisa dokoki na a kiyaye.
bacin ranshi a kula da abincinshi banda gishiri banda
barkono banda farin magaji banda kanwa banda
yawan cin man gyada.
Tun likita yana bayanin baba Lantana ta somna
fadin, hu un wannan banda bandan ai ya yi yawa.
Yaya Dija ta kalleni cikin natsuwa bayan munje
gidamnu da baba tace min debi kayan da zaki diba mu
tafi nace mata a'a je ki kawai ni zan zauna a gida, da

17

sauri ta sake källona za ki zauna fa kika ce? Nace e,
amma ai kuma kin san gidan ba zai zaunu miki ba a
yanzu a yanda take fusacen nan ina nan ma kina jin
irin maganganun da take furtawa balle kuma ace na
tafi na barki ke kadai.
A hankali na daga ido na kalleta kafin na
tambayeta, to in muka tafi dukanmu muka bar baba a
yanda yake din nan wa zai yi mana jinyarshi? Wa zai
bashi magani? Wa zai kula da abincinshi balle ya
tsaya yaga an tsare dokokin da aka sa mishi? Tace to
kuma haka ne ta bude jakarta ta fito da kudi ta bani
tare da fadin, to rike wannan a hannunki kafin inje
gida in ga abinda zan iya hadawa nace mata to.
Na koma zaman gida tare da baba Lantana da
ya'yanta biyu ga kuma babana a kwance yana jinya
tunda ko fita runfarshi baya iyawa balea yi maganar
kasuwarsu, dan garama dai Sallau don shi kam yayi
mana mutunci kwanakin asibitin baba duka tare da shi
muke kwana.
Duk lokacin da na zo shiga dakin baba Lantana
don yiwa babana wani abu ko bashi magani sai tace
wai bata yarda ba ina shiga ne ina ganar mata sirrinta
shi ba zai sha da kanshi ba sai an bashi kamar wani
dan yaro? An wani tasashi a gaba ana shagwabashi ita bata son gulma da iya yi.

18
Babana kuwa shan maganin yake yi a kan dole
sai na yi ta rarrashi ina bashi hakuri kafin ya yarda ya
sha.
Ganin da nayi takurar ta kai inda ta kai ya sa na
shiga dakin da Sallau ke ciki yana kwance kan
katifarshi na ce mishi, Sallau kawar da katifarka ka
.koma can gefe zan yiwa baba shinfida anan don a
samu saukin mu'anala, cikin sauri ya ce min to, nan
da nan kuma ya mike ya soma yin abinda nace mishin
har ya tayani na shiga dakina na dauko katifar da nake
kwanciya a kai nad awo mishi da ita nan na shinfida
mishi ita naje na samu babana na ce mishi tashi baba
mu koma dakin Sallau don zai fi mana saukin zama
ya ce min to.
Na dawo da baya ina jiran fitowar tashi Sallau ya
leko daga cikin dakin yana tambaya ta Mero wannan
ai katifar gadoski ce nace mishi eh, ya ce to ki maida
ita mana kawai sai ya yi amfani da wannan ni zan
rinka yin shimfidar tabarma ina kwanciya, har zance
mishi a'a ya barta kawai sai baba Lantana ta taso da
saurinta to ai ba tasu bace wannan din da kake neman
gwaninta a kanta tawa ce da kudina na sayeta don
haka ban yarda ba, ta sake kallonshi cikin wani irin
yanayi da takaici yafi komai baiyana a idonta kana
tsoronta ne saboda wancan dan iskan ko? Dama ka
wartsake kayi hidimarka shima yanzu ta kanshi yake

19
yi sakaraí matsoraci bani katifata ka rinkak wanciyar
tabarmar da ka zabarwa kanka.
Na kalleta cikin natsuwa na ce mata, to ki fito
min da wacce take kan gadonki ai wannan tamu ce
tunda ta gadon innarmu ce.
Ta zabura kamar zata ki famin mari saboda hakan
dana gaya mata ban san yanda akayi ba ta fasa ta
kuma bar katifar ta tayi nima naja tawa na mayar kan
gadona.
Dawowar da babana yayi dakin sallau sai ya bani
damar dana rinka kula da shi dama duk wani
ala' marinshi ko wane lokaci ina tare da shi komai
naga ya dace in yi mishi bana jiran sai ya ce a yi
mishi, wanka, wanki, komai a kan lokaci.
Duk wannan abinda yake faruwa baba Lantana
bata cas bata as kan abinda ya shafi rashin lafiyar
mijinta taja ta tsaya kan wai raina mata mukayi ya sa
na zo na kasa na tsare a kanshi don haka itama ta cire
hannunta kan lamarin shi tunda shi dama abinda
ya'yanshi suke so yake bi baya kuma gudun abin
kunya na aikata babban laifi bai ce min komai ba ya
tasani a gaba yana kallona masu ya'ya mza ma sun
hukunta 'ya'yansu amma ni ya yi kamar bai san
abinda na yi ba.
Yanda dama can babu mai ce ma ta komai in tana
maganganunta haka yanzu ma a wannan lokacin ko
wani wadataccen girki batayi sai ta ce wai ba a fita an

20
kawo mata ba me zata girka? Don haka kullum gidan
a bushe yake babu abinci ni dai ina tsare da cikin
babana ba na yarda ya ji yunwa ba na ma zaton ya san
baba Lantana bata girki in dai ba ya lura ya gane
abinda kalamanta 11a tsakar gida suke nufi ban e.
Wurin Isiyaku da ya zo gaida babana da jiki na
samu labarin wai ashe Alhaji Muhammadu baban
Mubarak korarshi yayi daga gidan saboda samuna da
akayi a dakinshi da kuma cin mutuncin da baba
Lantana ta je musu da shi cikin gidan tun yana tsare a
wurin 'yan sandan wai ya aike mishi cewar in ya fito
ya nufi inda ya nufa amma ba gidanshi ba, ya kuma
turo har abokan baban sun zo sun b ashi hakuri yaki
ya hakura ya tsaya kan bai son sake ganin shi a yanzu.
Gabana ya yi mummunan faduwa saboda jin irin
hukuncin da baban Mubarak ya zartar a kanshi bayan
kuma na san matsayin da yake da shi a wurin iyayena
nashi na yi matukar kaduwa, tausayinshi kuma ya
kamani har na rinka ganin tamkar ni naja mshi tunda
ai ni naje wurinshi ba shi ya kirani ba, cikin zuciyata
na ce to abinda baba Lantana ta je kenan tana fadin
masu ya'ya maza ma sun hukuntasu amma nawa
yana kallona saboda abin kunyar da na aikata bai
dameshi ba sai wani lallangabewa yakeyi ina
tarairayarshi wai shi nan ga mai 'ya.
A wannan lokacin ba zan iya zama in kwatanta
halin da nake ciki ba na kunci, takura da kuma bakin

21

ciki a halin dan a samu kaina a ciki, na gane ashe ba
auren Alhaji Nalami kadai bane karshen bakin cikin
rayuwa ko da yake dai ni a wurina ina ganin tamkar
shi ne ya yi min sanadi na shiga duk wani hali da nake
ciki, ban kara sanin irin cikin wani hali na shiga wata
gagarumar fitina ba sai da na ji Asabe tana rera wata
irin waka da na sha jinta a bakin yara ban atba kulawa
na gane abinda suke fadi ba sai ko yau da na ji ta a
wurin Asaben shị ne na gane ashe wai ni aka yiwa
wakar.
A wancan lokacin da ko yawan kula, samari
budurwa take yi yan mata yan uwanta suke rera
mata wakar, mace mai wasa da maza karya nayi
mamakin kaina matuka na kuma ga sakarcina da tun
asali ban gane da ni ake yi ba wai sai da na ji wakar a
bakin Asabe, masu gatama masu ya'ya samari basu
tsallake wannan wulakancin ba balleni da bani da
kowa in banda babana sannan tun can asali damab a
wani farin jini ne da ni ba a tsakanin yan mata da
samarin unguwar iyaka dai tsoron Mubarak ya tserar
da ni daga duk wani wulakanci ko iya shege da za a yi
nufin yi min to yanzu kuwa babu shi kowa kuma ya
san ta kanshi yake yi don kuwa wannan hukunci da
babanshi zai yi ba sannan a yanzu bama maganar
wasa da maza bace mas ala ta an kamo ni ne a dakin
saurayi na kai mishi kaina baba Lantana kuma ta sake
rattaba bayani a gaban kowa a cikin daren da babu

22

siri a cikinshi cewar ba ranar na fara 'zuwajne kwana
a wurinshi ba.
Na yi kuka rannan irin wanda na tababtar ban
atba yi ba a rayuwata nayi bakin ciki.na rasa inda zan
tsoma raina in ji dadi na rinka jin tamkar ina ma dai
imsda jlkon bude kasa in 6uya a cikinta saboda
tsaranin kunya.
Duk inda tozarta ta kai duk inda wulakanci ya kai
duk inda muzantawa ta kai kalmomin da suke cikin
wakar sun kai harma sun wuce gashi saboda
wulakanci da raini sai aka yi anfani da sunana ta
yanda kowa zai gane da ni ake yi amma shi Mubarak
babu nashi sunan a cikinta, na samu kaina cikin wani
yanayi da na rinka ganin tamkar babu wanda ya taba
shiga cikin wannan yanayin sai ni kadai.
Da kyar na ke iya fita waje sai in dolen ta kama
dole ina nufin in zan saiwa babana wani abin in ta
kama hakanma sai na yi ta leke naga mutane sun dan
dauke sannan ne zan ruga da gudu inje shagon kusa
da gidanmu in sayo in dawo saboda yara suna ganina
suke fara rera wakar wasu suna anshi cikin tafi sannu
a hankalima dana lura sai na gane ba waka daya aka
yi min ba kaloli ne daban-daban kara fito da sabbima
suke yi, baki ciki in ya dameni sai inji kamar in gudu
in yi tafiyata in tafi can inda babu wanda ya sanni in
yi zamana sai kuma ince to babana fa, wa zai yi min
jinyarshi? Yaya Dija fa ita me tayi min da zan tafi in

23
barta? Sai in tsinci kaina dayin wani tunanin ince to
ai ina ji ana cewa babu wam dauwamammen abinda
ya ke zuwa ya tabbata, in dai ba ikón ubangiji bane
don haka duka binda ake yi zai wuce in rudi kaina da
cewar da nake yi nayi na wai watarana sai labari ina
fadin hakan kuma zanji zuciyata tana tambayata to
yaushe ne naki wataran zai zo? Wanda ni kaina ban
sani ba ina raye ne zanga wataran ko sai na mutu ban
sani ba tunda ni kam ai kullum al'amurana kara
cabal6alewa suke yi bakin cikina kuma yana kara
karuwa.
Yaya Dija ta zo duba jikin babanmu samuna da
tayi cikin wani irin hali ya yi matukar bat amata rai
saukin abin ma shine da muka san ba ku yi komai ba
amma da ya karbi wanna mahaukaciyar kyautar da
kikayi mishi ai da bamu san iyakacin bala' in da muke
ciki ba a yanzu amma yanzu kina yin aure shi kenan
mijin da ya aurehi da duk wani wanda ya danganceshi
zai ce karya ne sharri kawai aka yi mana mai yin
sakamakon kuma zai yi mana wato da Mubarak ya
taba ni da musibar ta wuce haka kenan bata tsaya ba
ni amsar maganar ba sai ta ce min Umman Mubarak
ta aiko da kayaiyakinki da suke wajenta ciki kuwa har
da wani bakin karfe ta tsareni sosai da idonta kafin ta
buda baki ta tambayeni kin gane abinda hakan ke
nufi? Nace mata eh, bata bar ni ba sai ta ce min me
yake nufi? Cikin natsuwa na ce mata kar in sake shiga

24

gidansu tayi maza ta ce to madalla gara da kika gane
hakan, da ya karbi kyautar da kikayi mishin ma da
irin korar da sukayi mishi kenan koma su yi wadda ta
fita.
Ko yake ko dan Umma bata yiwo min irin
wannan aiken ba nima ba zan sake dosan gidansu da
nufin wata mu'amala ba saboda abin kunyar da ya
faru ga kuma irin abinda hakan ya zamewa Mubarak
amma kuma sai naji tamkar ba ta yi min adalci ba ko
kadan ban ji dadin abinda tayin ba don kuwa ita din
uwa na dauketa duk da da itama na sani don Mubarak
din take yi min duk wani abinda take yi min.
A wannan lokacin sai na rinka iin tamkar tubeni
aka yi sirara aka jefar da ni cikin taron jama'a da bani
da kowa a cikinsu balle wani mai taimako amma
kuma ban yarda na munawa yaya Dija tsananin
damuwata ba don kar in kara mata tata damuwar
tunda har itama marasa atuncin yaran unguwarmu
in suka hangota rera mata wakokin suke yi kasa-kasa
amma ba da karfi ba kamar yanda suke yi min.
Sannu a hankali sai babana ya saau sauki har ya
Soma fita kasuwarshi saboda tababcin da likita ya
bayar na jinin nashi ya sauka amma ba ana nuiin ya
warke ba ne shi jini in ya riga ya soma hawa to ba a
daina sha mishi magani don ko wane loakci zai 1ya
tashi, wannan shi ne bayanin da likitan ya yi mana a
ranar da mukaje ganinshi ni da baban nawa.

25
To Dr. Meke kawo ciwon hawan jini? Na yi
mishi tambayar don in kara sani, sai ya ce min akwai
jinsin mutanen da ke da jini wanda yake da irin
wannan matsalar su ne masu yin ciwon a dalilin sun
gajeshi sannan Wasu yakan sansa a dalilin tsananin
damuwa ko kuma yanayin abincin da ake ci shi yasa
yake de kyau mu rinka kula da abincinmu mu kiyayi
abubuwa marasa amfani irinsu gishiri, barkono,
kanwa da makamantansu, sannan mu rinka yawan
motsa jiki, motsa jiki yana da amfani kwarai ga
lafiyar jikiumu kin gane? Nace mishi eh Dr. Na gode.
Rike wannan bayanin da likita ya yi min da nayi
sai na ejiyewa kaina ya zama ka'ida kullum in baiwa
babana magani kwaya daya da kuma yayi min korafi
kan maganin yana sashi yawan taba ruwa sai na
mayar mishi da shan amganin nashi a lokacin dare
haka nan jin saukin babana baisa na fita hanyar kula
da abin karyawarshi ba ko da kuwa iyakar abinda
nake da shi kenan saboda na iga na gane har da
yunwa cikin rashin alfiyar tashi, ina kuma yawan gaya
mishi cwar baba ka rinka shan timatir in ka gansu
masu kyau kana kuma cin danyar kubewa kar kuma
ka rinka yarda mai kankana ko ayaba yana wuceka
baka saya kaci ba komai kankantarshi ya ce min to.
Baba Lantana dake yawan kasa kunne wajen
sauraron maganarmu ta ce eh 'yan kudin da yake
kawowa wadanda dama ba isar mutane suke yi ba su

26
ne.kike koya mishi yanda zařtinka cinyesu a waje ba
saboda. sharrinki kankana da ayaba kuma maganin me
suke in ba iya shege ba.
Babana ya fara fita kasuwa sai dai abin mamaki
shi ne ashe wai har shima bai tsira daga wakar da ake
reramin din ba in an ganshi sai a yi tayi wasu 'yan
iskan su rinka nunashi suna fadin shi ne mutumin da
aka kama' yarshi a dakin saurayi har a dalilin hakan
mijin da zai aureta ya ce ya fasa auren shi sauranyin
ubanshi ya koreshi a gidan shi amma shi yana tashe
da tashi 'yar a gabanshi sai ma kara sonta da ya yi.
Wasu su ce to ance duk abin da take samowa shi
take ba wa, ai mafi yawancin iyaye yanzu in dai
ya'ya zasu basu kudi to magana ta Kare sai su yi
abinda suka ga dama suna kallo kai amma kuwa to tir,
wato shi yana can yana kici-kici da tashi matar itama
ana can ana kici-kici da ita kenan? Sai a kwashe da
dariya.
Su m a yaran dake cincirindon sayen timatirin
babana har ana layi ba a barsu a baya ba sun daina
yayen su ng suka hanasu ko su suka hana kansu saye
sai su saka sauri hatta rijiyar gidanmu da bata kafewa
wacce kullum baba Lantana ke fada da masu zuwa
diban ruwan cikinta su ma yanzu ba a zuwa diba.
A wannan lokacin kusan kullum sai anyi
kwashen timatir babana ya zama bage tuni sai jarinshi
ya soma rushewa sai mai kawo kwandunan timatir

27
attarugu tattasai albasa alaiyahu kubewa masu yawa
sai ya zamo da kyar ake hada kudin daidai don haka
in tsaya fadin an shiga wani halima a gidanmu na
tsaya bata baki ne kawai.
A wannan lokaci saboda samun wuri Asabe
abinda ta ga dama talke yi min ina kallonta bana cewa
komai sabdoa yanzu yanzun nan ne zata fara rera min
waka in taga fuskata ta canza ta ce ba ni na kar zomon
ba raiayc kawai aka bani, bana tanka mata don nasan
bani da yanda zanyi da ita in karfin dambe ne ta jini
gatan da nake da shi din da yasa ake tsorona babu shi
banma san inda yake ba ga kuma aiken da Ummanshi
ta yi min daga gidansu wanda nasan na nuna karshen
mu'amalata da su ne.
Asabe tana cikin tatamin irin tsiyar da taga dama
ne rannan na farka cikin dare na ganta tana kwarara
amai a cikin wani kwano duk da tsananin tsoratar da
tayi da ganin da nayi mata ban gane abinda hakan ke
nufi ba, na hadaki da girman Ubangiji kar ki gayawa
baba kin ganni ina amai ba zan sake yi miki wakar da
nake yi miki ba.
Naceki yi mana ni ance miki wakar ta dameni
ne? Amai kam ai sai na gaya ma ta na ganki kina y1 a
kwano. Tayi ta bani hakuri mamakinta yayi ta kamani
ko ina ruwana da ita da uwarta da zanje ina cewa na
ganta tana amai oho?

28
Tun daga rannan Asabe ta daina nemana da
tsokana a fita hanyata da abubuwa iri-ii abin sai
mamaki yake ta bariï sai a ranar da yaya Dija ta zo
gida ne ina rakata take tanmbayata nalin da muke ciki
da Aabe na bata labarin abinda ya faru sai naga ta ja
ta tsaya tana kallona cikin natsuwa kafin ta ce min,
akr dai ciki ne da yarinyar nan? Kai haba gashi yau na
ganta ta canza to ita uwar ta ta ba zata ganc ba sai an
gaya mata wacce irin shashashar uwa ceh aka? Shiru
nayi cikin tsananin faduwar gaba, ciki? Na yiwa kaina
tambayar a cikin raina.
Ai baka cima masharranci sai ka yiwa kanka mafi
yawancin lokaci ai abin da ake yiwa dan wani shi
yake samun naka ki ja bakinki ki yi shiru karki
yardaki yi abinda uwar ta ta zata gane tunda ita
mahaukaciya ce nace mata to...
Rannan ina zaune a tsakar gida ina hidimar
wankin kayan babane bayan na gama nawa a yanzu
bana fada da kowa saboda Sallau dai mun dan shirya
da shi tun daga kwanciyar asibitin baba da kuma lura
da nayi naga yana mutuntamin baban nawa, Asabe
kuwa tsoro take ji karmu yi fada in fadi abinda ta
roke ni kar in fada bata san ma ni ko munyi fadan ba
fada zanyi ba tunda yaya Dija ta ce min kar in fada.
Cikina ne ya yi wani irin kuka na tunanin da irin
dadewar da nayi ban bashi wani abu na hatsi ba, na
waiwaya a hankali na kalli Asabe da baba Lantana da

29
suke zaune cikin rana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login