Showing 21001 words to 24000 words out of 36183 words

Chapter 8 - Halin Rayuwa Book 3 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

210

kaina da ka yi
dalilin da na kara zama shashasha sokowa sakarya
waçce ta aikata kuskure a rayuwarta, kuskure kuma
har abada, don haka duk abinda ya faru tsakanina da
kai tun daga farkonsa har zuwa karshensa kus...
Ban kai karsen maganar da zanyi ba sai kawai na
ii kafafuwana sun zurma cikin kwatar dake bayana,
nayi maza na kalleshi cikin tsananin bacin rai nan
take kuma na sake dago idanuwan nawa suka hadu da
na Mubarak dake yi min wani irin kallo, yanayin da
na gani a tare da shi ya tabatar min da cewar ba ji nayi
kama ba shine ya hankadani cikin kwatar da na zurma.
Kar ki sake yin kuskuren kallon idona ki ce za ki
yi min rashin kunya irin wanda kika yi min yau in
kuwa ba ki ji kashedinda na yi miki to za ki gane baki
da wayo, sakarya kawai sokuwa shashasha mara wayo

94
wacce rashinmafadi ya hanata sanin abinda ya dace da ita.
Yana gama fadin hakan ya ja wani mummunan
tsaki ya wuce yayi tafiyarshi ya barni cikin kwatar ko
a jikinshi.
Da kyar na iya zare kafafuwana daga cikin
kwatar takalmana kuwa asararsu nayi don kafafuwan
nawa kadai na iya zarewa, a hakana rinka
diddingisawa na doshi gidan Yakumbo Halima cikin
zuciyata dai ni kadai nasan abinda nake ji game da
Mubarak, na tsaneshi na kishi na rinka jin wani irin
ciwo a zuciyata game da shi, babu abinda ke kai kawo
a zuciyata in banda na tunanin yanda zanyi in dau
fansa a kanshi kan irin wulakancin da ya yi min, da
dai ace so shi ne samu to da na tashi daga wannan
unguwar na koma wata don in yi nesa da shi in dains
ganinshi dan ya daena shiga harkokina.
A haka na shiga gidan Yakumbo Halima, tana
ganina ta kama yin salati, wane irin rashin dabara ne
wannan Mero? In zaki fada kwata sai kuma ki fada da
kafa duka biyu kamar wata yarinya 'yar karama?
Ban iya ce mata komai ba kuka kawai na kama yi
don daman daurewa kawai nayi na hana kaina soma
kukan tun daga waje. Cikin hanzari ta tsame hanunta
daga cikin kullin danwaken da take jefawa da sauri ta
iso inda nake tsaye ina ta faman kuka.

95
Haba Mero haba Maryamu da so don kin shiga
kwata kuma sai ki tsayakina kuka? Ai tsautsayi ne shi
kuwa kin ji ance bai wuce ranar shi ba, bari in kwara
miki ruwa a kafar in wanke miki dagwalon sai ki
shige bandaki ki yi wanka ki canza kayan jinki da
wasu.
Har nayi wanka na fito na gama abinda zanyi
duka na zo wurin Yakumbo Halima na zauna ina
tayata jifan danwakenta idanuwana basu daina zubar
da hawaye ba, na kasa gane dalilin bakaken
maganganunshi musamnman gorin da yayi min kan
fasa aurena da Mansur ya yi sunyi min ciwo da yawa.
Rarrashi, banbaki da wayon da Yakumbo Halima
tayi tayi min ya sani kwashe bayani duka na yi mata.
Dama ashe zancen da nake ji a gari na bar yanzu
baku rabu da juna ba gaskiya ne? Tsuru na yi ina
kallon Yakumbo ashe kuskure nayi da na yi mata
wannan bayanin, ashe da ma kadan take jira da ni, to
kuwa ba zai barki ki yi aure ba kin ji na gaya miki ke
ya hanaki aure ya tsareki a waje a cikin gida kuma
yana tare da matarshi duk tsiyar da yake yi mata
wanda ke sanyata zirga-zirgar yaji tun da dai yana
kusantarta ya biya bukatarshi a tare da ita ai aikin
banza ne karyar iya shege kuma yake yi wanda bai
Son mata ai baya kusantarta indai har da gaske yakeyi
yanzu da ta tafi kwanan nan iyayenta suka aiko a
gayawaAlhaji Muhammadu cewar tana da ciki wata

96

biyu yayi musun cikin? Ba cewa sukayi sun janye
sakin da yayi mata ba sukaje suka dawo da ita
dakinshi kuma suna nan tare su na zamansu ana
tarairayarta ana murna zata haifar m usu da ko ya, shi
ne ke ba za ki yi zuciya ki kama mutuyncin kanki ki
fita harkarshi ba sai ki je kina biye mishi kuna
lalacewa tare... ta kama kuka irin wanda bai
kwatantuwa.
Jikina ya kama 6ari hankalina ya yi mummunan
tashi ganin irin kukan daYakumbon keyi, na rantse
aiki Yakumbo... kan in fadi abinda nake nufin gaya
matan tuni ta rufeni da duka da hannaycnta duka biyu,
rantsuwar karya zaki yi min saboda kin maidani
shashashar uwa to ai ni da yaya Ramatu duk daya
muke uwa daya uba daya muka tasha nono ta bani da
kike nema ki maidani mara mutunci. Tana kuka take
wannan bayanin.
Tuni nima na shiga nawa kukan, ba don dukan da
tayi min din ba sai don bakin cikin al'amarina da
bakni cikin yanda na zamo gaba daya iyayena da
jama'ar gari suka yarda da cewar lalacewa mukeyi ni
da Mubarak, yaya Dija ce kawai na tabbatar ta yarda
da maganar da nayi m ata na babu komai a tsakanina
da shi don ta babans kuwa ba zan iya cewa koami ba
tundaban taba jin ya bude bakinshi ya fadi wata
magana ba balle in san a wane hali ya dauki lamarin.

97
Ban san abinda ta gani ba ko abinda ya faru ba
naga maimakon dukan da take ta kai min da
hannayenta duka biyu ta jawoni jikinta ta kankame da
karfinta kuka mai yawa ta yi kafin daga bisani ta
sakeni, ki yi aure Maryamu ki yi aure abinda kawai
zan gaya miki kenan. Magaiar da ta fara yi kenan
bayan ta gama kukan nata.
Cikin sauri na ce mata to Yakumbo ba tare da na
san wanda zan auran ba sai dai kawai don in kwantar
mata da hankali.
Alkawarin da nayi wa Yakumbo Halima na
cewar zanyr aure ya sans himmatuwa wajen ganin na
fidda mijin aure ko da kuwa wane iri ne babu
maganar tsayawaduba cancanta balle a yi maganar
zabe, aure kawai nake so in yi ko zan samu in fita
daga zargin da ake yi min na akwai wani abinda ke
faruwa tsakanina da Mubarak na lalacewa sannan yin
auren nawa zai zamo dailin da zan bar unguwarmu in
yi nesada ita in daina ganin Mubarak wanda a yanzu
na tabbatarwa kaina da cewar in har akwai wani
mutumin da na tsana a rayuwata a halin da nake ciki
to shi ne na tsani Mubarak, na tsani duk wani abinda
ya shafeshi, na tsani duk wani labari da ya
danganceshi, musamman ma labarin matarshi da cikin
dake gareta wanda kuma ya zamo shi ne labarin baba
Lantana da take wuni tana bayarwa ta rinka fadin
karyar banza karyar wofa, yana kinta yake kwabewa

98

a gabanta? Sai kuma ta ja wani mummunan tsaki ta
ce, ku dai da ya mayar sakarkaru ke da ubanli sai ku
yi tayi ya rinka samunki yana rage gajiyarshi ta rana a kanki tunda haka kuka zaba.
Rabon da in tankawa baba Lantana ko wani nata
wata magana har na manta saboda abinda nake ji yafi
karfin duk wasu maganganun na ta ciwo a raina.
Rannan ina tsaye tare da wani sabon saurayi da
nayi wanda inda ya biye min da ko kwana goma bai yi
da fara zuwa wurina ba ya turo iyayenshi aka daura
mana auren saboda irin karbar da na yi mishi da kuma
za a tsareni a tambayeni dalili na na yin irin wannan
bare-baren a kanshi abu guda da zan iya fadi kawai
shine ba dan unguwarmu ba ne ina son aurenshi ne
kawai don in samu in yi nesa da unguwar in banda
haka babu wani dalili.
Ina tarę da shi muna hira a kofar gidanmu sai
kawai ga Mubarak tamkar daga sama aka jehoshi,
gabana ya yanke ya fadi saboda ganin inda muek
zaune ya tunkaro gauan-gadan nayi maza na kawar da
kaina daga gareshi saboda irin kallon da na lura yana
yiwa wanda muke tare da shi din wanda shima na
gane ya tsargu da Mubarak din.
Yana isowa sai na ji ya ce mishi, malaml afiya na
ganka anan wurin? Da sauri mutumin ya daga ido ya
kalleshi latiya? Ban gane tambayar taka ba, ya zuba
mishi ido cikin natsuwa yana kallonshi, wannanai

99
iyalina ce baka ji abidna ke tsakanina da ita ba ne? Ya
shiga waige-waige hankalinshi a tashe jin da ya yi
Mubarak ya ce mishi ti din iyalinshi ce.
Ai ban san matar aure ce ba ni asanina...
Kan ya karasa bayanin ya yi maza ya ce mishi,
bar nan kawai tun kafin abin ya kai ga ranka ya baci.
Yanzu kuwa in ji mutumin, ko raina b a zai baci
ba ma ai da sanina b za ni wurin iyalin wani ba, ita ta
ha'ince ni ta boye min gaskiya, ya kama hanya ya yi
tafiyarshi, nima na mike na shiga gida na barshi a
wurin ban tsaya jin wata magana tashi ba.
Ina gida akan gadona a kwance ina tunanin
al'amarin cikin zuciyata dai nasan babu mutumin da
yake shiga harkokina yake takuramin yake bata min
rai yake sanyani bakin ciki a rayuwata irin Mubarak
sai daiban san yanda zanyi da shi ba tunari mai
tsanani na shiga ciki har daga karshe na yankewa
kaina hukuncin komawa gaban Yakumbo Halima in
gaya mata abinda ke faruwa don kar ta dauka ban ji
maganar da tayi min na inf ito da miji ba. Na gyara na
yi kwanciyata da tunanin na kaiwa Yakumbo Halima
bayanin abinda Mubarak kc yi min.
Ina kokarin tilasta kaina yin bacci kenan sai na ji
Asabe tana kwalawa sunana kira, cikin irin muryar
tsoro ne ya kanani saboda sanin da nayi cewar ni da
Asabe bama ko ga maciji.

100
Waiyo-waiyo dama dai kawai in mutum in huta
da wannan wahalar. Zumbur nayi na tashi na zauna
saboda jin maganar ta ta, me ya satieki haka Asabe?
A tsorace na yi mata tambayar. Bata tanka min ba,
waiyo-waiyo, abinda kawai take te faman fadi kenan.
Na sauko gareta ina kokarin riketa don in tsaida
murkususun da take yi a kasa cikin yanayi na
tausayawa ina isowa garéta na gane lamarin ba karami
bane, ya kuma wuce duk yanda ake zato don haka
nace mata bari in kira miki baba Lantana don tazo ta
ga halin da kike ciki in yaaso a kaiki asibiti. Tayi
maza ta ce min u'u barta kawai kar ki kira min ita ke
dai kawai ki taikameni ki kaini cikin kankon bola ki
barni a wurin in ma mutuwar zanyi in mutu a can.
Tausayin Asabe ya yi matukar kamani, haba
Asabe daina fadin irin wadannan kalaman kankon
bola a cikin tsohon daren nan ko mahaukaci ai ba zai
dunfari wurin ba, na shiga share mata gumi da majina
da hawayen dake ta dalala.
Ki yafemin abubuwan da na yi tayi miki Mero
satar kayanki da ua rinka yi ina sayarwa da kudinki da
sharrin da na... Kai haba Asabe bar irin wadannan
maganganu ai zanman tare ne.
Ana cikin haka naga Asabe tayi rigingine ta
bankade komai babu sauran kunya a tare da ita, tsoro
ya sake kamani jikina ya dauki rawa cikin muryar
kuka nace mata Asabe, don naga alamar bata cikin

101
haiyacinta, kan in kai kkarshen bayani na hango wani
abu yana shirinf itowa da gudu na nufi kofa na 6alleta
cikin rawar jiki da karkarwa na buga kofar da take ta
baba Lantana da babana, tana jin bugun kofar da nayi
sai na ji ta soma cewa, yauwa ai ga ranar da nake jiran
zuwan nata nan ta zo ranar da asiri zai tonu, ranar da
zaka gane shirunda kake kame bakinka kana yi a kan
komai ba dabara bace, ai tun dazu nake gaya makaa
wannan zirga-zirgar da akeyi ana ziryar bayan gida da
kyar ne in ba nakuda ake yi ba, ni na dade ina fatan
ganin an haifar maka shege a gidan nan, ba dai
kwadayin abin duniya ya sa ka zuba mata ido tana yin
abinda taga dama ba? Yaro ya ki aurenta ya kai gida
amma a waje ya maida ita matarshi? To muje ka karbi
haihuwar da hannunka don kar ka ce sharri aka yi
mata ba a jikinta ya fito ba don haka nuje a yi kornai
a kan idonka, kaga ta inda yalke fita muje mu je.
Ina jin hakan nasan fitowar zasu yi tare don haka
na tsaya a inda ana bude kofar babana zai ganni.
Abin kunya ina jin gadonshi kukeyi malam tunda
ba haka ai nayi ta gudun makashi baka yarda da
shawarat bane yasa baka koreshi ba sai da ya sameka
saboda bai damcka ba, muje nace muje kana ji ana ta
gurnanin nakuda ka ki kayi kuzari sai wani jan kafa
kake yi kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki.
A na bude kofar mukayi ido hudu da babana,
muje m ana kayi wani kerere ka tsaya min a hanya

102
kaki ka bani wuri in fita, abinda haba Lantana ke fadi
kenan daga bayanshi saboda kasa motsin da ya yi a
dalilin ganin da ya yi min a bisa da na tabbatar kuma
shi ne da ni ya gani a cikin wani hali na abidna take
gaya mishi watakila da ya yi faduwar da bai sake
tashi ba don a haka ma tsinkewar da yayi ta kai duk
inda ta kai.
Kurdawa tayi ta bayanshi ta fito saboda ta kasa
hakurin ya matsa ya bata wuri, tana ganina a tsaye
tayi maza ta ja ta tsaya ta yi turus cikin tsananin
kaduwa nan take tsoro ya baiyana a idonta, a'a to
wake zirga-zirgar da gurnanin nakudar da ke fitowa.
Ban ce mata kala ba balle kuma babana da ya
zama tamkar mutum mutumi, to wane irin abu ne
kuma haka mai nakuda tana tsaye kememe, da gani
dai nasan kece kike wannan zirga-zirgar da gurnanin
nakudar inma...
Kan ta karasa maganganun nata masu kama da
sanbatu sai kawai mika jiyo kukan jariri daga cikin
dakin namu.
Ina kallon yanda jiri ya debi baba Lantana ya yi
wuji-wuji da ita kafin ya fyadata da kasa, tayi
faduwar yan bori vato da mazaunanta, tsoro ya
kamani saboda ganin irin faduwar da tayin, sai kawai
na ga ta zabura da iyakacin karfinta ta yanka da gudu
ta nufi cikin dakin namu.

103
Wato da ma shari ne abin? Watp ni za a kawowa
iya shege? Dama da hadin baki ne tsakáninki da m
atsiyacin likitan da yace min kaba ce da ke? Ni za ki
kawowa tsiya? Ni za ki jawa magana? To ai kuwa
yanzu za ki gane wautar ki don kuwa kasheki zanyi
murus har lahira.
Tana fadin hakan mulka jiwo-ibun Asabe da sauri
Sallau ya fito ya fada cikin dakin; ba zaiki kasheta
anan ba baba ba zaki yi mana kisan kai a gida ki jawo
mana wata fitina ba, tunda dai har kin kaita gun likita
ya ce miki kaba ce ai kin san da komai, lokacin baya
ta kawo miki gasassun kaji kina ci kowa ai yana
girban sakamakon abinda yake aikatawa ne.
Da karfi Sallau ya jawo baba Lantana ya fito da
ita waje, tana-kicin kwancewa daga gareshi tana
kurma ihu da iyakacin karfinta, ka sakeni kawai in
hadata ita da shegen dan natain murkushesu kowa ya
huta.
Wannan dai duk kina kokarin jawowa kanki wani
abin magana ne kawai in har kika bari makwabta suka
jiyoki suka gane abinda kike ciki da ma ki yi maza kin
san abinda kike ciki da ita da dan nata kafin gari ya
waye magana ta watsu.
Daga cikin gidan baba Baidu muka jiwo muryar
baba Sumaye tana cewa, kar makwabta su ji na nawa
tunda ni naji? Ai ko ladan cikins hegen da tayi ta
rokarwa ya'yan jama'a sai na baza wannan labarin,

104
barde a gonar wani sunkuru ya rufe naka, ddonki kam
ya' yan jama'a ammakin kasa sawa naki balle ki gano
abinda suke ciki, wai likita ya ce miki kaba ke gareta?
Ta kwashe da dariya kafin ta ce, saboda ya gane
ke din mahaukaciyar uwa ce shi ya sa ya yi miki
hakan, kar kumaki ji da wai ba nan unguwar ba ko a
wani wuri na ji 1abarin an tsinci mataccen jinjiri zan
kai rahotonki don nasan halinki kin kuma furta zaki
kashe uwa da da kat su jawo miki abin kunya, sai
kace in da ana kashewa da ke kin kawo yanzu, ai
yanda kika sa su Jkuka da bakin oiki lokacin da kikayi
naki haka kema za á sa ki ki yi abinda,kukayi ne ai za
a yi muku, shi kuma malam Habu Ubangiji ya yaye
mishi abinda ya sameshi, yauwa duk inda naji an
tsinci mataccen jinjiri nasan kece zan fada na kangon
bola ma da aka gani kwanaki wa ya sani ko ke kika
kaishi? Fitinannun mutane masu jawa mutane annoba
iri-iri.
Baba Sumaye tana rufe baki baba Lantana ta yi
zumbur ta maike da sauri ta sake shigewa cikin dakin
namu inda Asabe da dan jaririnta suke tamkar dai ace
dama kasake tayi tana sauraron bayanin nata ban san
yanda akayi ba sai ganinta muka yi ta fito tana
rungume da dan jariri Asabe tana biye da ita cikin
katon lullubi sun sa kai sun fita sun bar gidan, ganin
sun bar gidan ya sa ni nufin shiga dakin namu wai in
kwanta. Abinda na gani a tsakar dakin ya sani

105
kwallara ihun da na dawo da baya cikin sauri Sallau
ya fito ya leka cikin dakin ya tayani ganina binda na
gani, ya koma ya dauko leda ya sanya shi a ciki ya
kuma. sa omo da izal da tsintsiyar zabori ya wanke
dakin tas zuwa tsakar gida dama bayan gidan baki
daya maimakon karni da kazantar jini ya koma tsabta
da kanshin kayaiyakin da ya yi amfani da su.
Na shiga dakin nayi salla na hau gado na kwanta
cikin jimamin abinda ya faru, akan idona Asabe ta
haihu ta haifi da babu aure ba shiri nake yi da ita da
uwarta ba amma na tausaya mata tare da dan nata, ina
cikin hakan na jiyo muryar baba Lantana tana cewa ba
dai dani kuke yi ba ai za mu sa kafar wando daya ni
da ku, munafukan banza munafukan wofi matsiyatan
mutanen da basu san mutunci ba duk zaluncin
ubanku.
Na yi kasake ina sauraron zage-zagen nata cikin
zuciyata na ce, oh oh wannan mata da jarumtaka take
ko ita da su wa take yi oho.
Ina jinta ta shigadakin da Sallau yake bamuji
komai ba illa iyaka dai na jiumuryarshi yana ce mata
to nan take kuma ya yi waje, nima na fito don in
nemawa babana abin karyawa da kuma maganinshi,
lokacin ne na gane daga tafiyarshi masallaci don
sallar asuba bai sake dawowa gidan ba.
Ina daki a kwance ina sauraron shigowar babana
don ba dabi'arshi bacewucewa kasuwa daga

106
masallaci na ji muryar Salau alamar ya dawo daga
aiken da ta yi mishi na ji shi a fusace yana ce mata,
kin ganta ko mnama kin ganta ko baba kinga halin
Asaben ko? A gabanki bakinta ta ce min Agogo ne
ba?
Gabana ya yi mummunan faduwa cikir raina na
ce Agogo kuma? Ban kai karshen maganar zucin
nawa ba naji Sallau shima yana karasa nashi bayanin
to an je anzo da Agogo ya zo ya zare m ata ido yana
tambayarta' shi kadai ne su sauran me yasa bata
amabci sunansu ha sai shi? Mainakon taja ta tsaya a
kan shi kadai ne sai kawai ta tsorata ta ce wai Alhaji
Nalami ne.
Kiis ya rage in rikito kasa daga kan dan gadon
nawa saboda firgitar da nayi, nayi maza nasa hannu
biyu na dafe kirjina saboda harbawar da ya kama yi,
nayi maza na sake tambayar kaina, Ahlaji Nalami
kuma? Wannan abin mamaki da ban tsorod a yawa
suke, Nalami da Agogo su Asabe take tuihuma da yi
mata ciki, ita kuwa wane batan basira ne ya kaita yin
hakan?
Tsawon lokaci ina tunanin tsakanin biyun wanne
ne dama dama? Agogo dai shi ne mutumin da ya
jagoranci abinda Mubarak ya sa aka yiwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login