Showing 30001 words to 33000 words out of 36183 words
irin wadannan
al'amuran, m utumin da ko lafiya bata isheshi ba, tace
a'a ni ban wuce ba sannan tun a can baya ma da yake
da lafiyar me aka yi ne da za a ce yanzu in hakan ta
faru kar in yi magana?
Yaya Dija na baiwa labarin kalaman nata ita ce ta
faiyacemin abinda take nufi, kasar kullum sai ta tasa
babana a gaba tana yi mishi hirar gidan mijinta na
baya, haushi da takaici ya yi ta kama ni na yanda sau
daya babana ya kasa cewa ya sauwake mata nashi
auren taje ta koma gidan mijin nata na bayan, yawan
134
fadan da take sashi a gaba da yi kIsaa kulium da yi
ya sani bashi shawarar dawo da kwana dakin Sallau
don ya rinka samun wadataccen bacci saboda
mas' alar hawan jininshi, kamar bai ji shawarar tawa
ba daga baya kuma sai naga ya koma dakin.
Wata gomas ha daya cif nayi ina zuwa
makarantar koyon sana'a ta Markas kafin aka yayemu
saboda yarda da aka yi cewar mun iya mu gomas ba
biyar aka yiwa yayen aka kuma yi mana kyautar
dinki saboda gamsuwar da akayi da
kwarewarmu, ko kafin nan kuwa nikam na dan dau
loakci ina taba dinkina a gida a kekcn da yaya Dija ta
saya min don haka dana samu wannan kyautar sai
kekunana suka'zama guda biyu.
Naso kwarai in koma Karkas in sake shiga wani
ajin daga cikin azuzuwan sana'o'in dake wurin in
kara koyon wata sana'ar haikan bai yiwu ba saboda
karatun da nake yi a makarantar asidini mai zurfi,
karatu ne dake bukatar sadaukarwa mai yawa banda
haka kuma ga lalurar babana ta yawan rashin lafiya
don haka sai na hakura.
Tunda aka yayena a wuTin koyon dinki na soma
yin dinkin sosa a gida sai mas'alolin da suka
danganci babu sia yi matukar yi min sauki bana asa
na sabulun wanka ko wanki bana rasa ta yin break a
makaranta wani lokaci ma nakan raka babana asibiti
ne ba tare da na shedawa yaya D1ja ba balle inje ina
135
jiran abinda zata bamu wannan-shi ne abidna yafi
komai faranta min rai na.
Shekaru uku ne yau tun bayan faruwar abinda ya
faru tsakanina da Mubarak cikin shekarun nan kuwa
nayi abubuwa masu yawa wanda kasancewata a yau
ni din kwararriyar tela tace gani a fada a kuma
kwaikwaya, ni din kuma gwanar girki ce saboda na
koma makarantar Markas na sake shiga ajin koyon
girki nau'o'inshi kuma malamaina na Markas irinsu
malama Hindu da Basma wadanda mukayi matukar
shakuwa a dalilin kulawar da suka nuna a kaina sunyi
min taimako mai karfi wanda a daliiinshi na samu
shiga exam center dake kusa da Markas din na samu
rubuta jarrabawar dana samu mallakar takardar shedar
gama karatun secondary indana samu credit guda
hudu da pass biyu saura f9.
A 6angaren da nake ganin kamar na yi nasara
kenan, a daya bangaren kuwa Ina nan kamar yanda
dama nake aure ya gagara babu kurna yanda banyi ba
in yi shi hakan bai yiwi ba, zan iya cewa garama da
da yanzu a lokacin da kuka sanni samarin sukan dan
zo auren ne basa tsayawa a yi saboda wasu dalilai to a
yanzu babu bani da wani wanda zan ce wannan
saurayina ne.
Mutanen unguwarmu tun suna nunani suna yin
bayant a kaina zuciyata tana lissafi ta karyata maganar
136
ta su har na hakura na fita harkarsu ta barsu su fadi
duk abinda suka ga dama.
Tun ban a kama maganar mutane irin su
Yakumbo Halima da suke fadin cikin biyu dai alkwai
abu daya ko dai anyi min sihiri ne ko kuma ma aljani
ne ya aureni ya hanani yin aure har na soma shiga
rudani ina tambayar kaina to menene mas'alata, tuni
dai na daina yin kawaye don na gaji da aurar da su da
akeyi ana barina a wannan lokacin in har ina da wata
kawa to kekena ne da kuma dinkina sai ko kwalliyar
da nakeyi don kuwa ba sai an gaya min ni da kaina na
san mu'amalar da nayi da malamaina na Markas
irinsu Malama Hindu da Basma ya koya mina bubuwa
iri-iri da suka danganci mace kwalliya, kamewa,
mutunta kai, iyaka dai har yanzu hakan baisa na samu
mijin da ya tsaya ya aureni ba su ma kamar yaya Dija
sukan ce min wai lokacin auren nawa ne bai zo ba sai
in yi murmushi kawai in yi shiru cikin zuciyata kuwa
tambayar kaina nake yi ko yaushe ne lokacin oho?
Saboda a wannan lokacin har na gaji na soma
tambayar kain to koma dai ni din ina cikin matan nan
ne da ba a halitt musu mazan auren ba?
Tun ina kin yarda in yi amfani da abubuwan da
Yakumbo Halima take bani in yi amfani da su na farin
jini da wai maganin sihiri da kullum take zargin wai
Mubarak ne ya yi min in yi murmushi in ce mata
Mubarka bai ma yarda da irin wadannan abubuwan ba
137
Yakumbo shi fa dan boko ne ma digiri biyu ne da shi
ya ma sake komawa karatunshi don neman na u
yaushe zai zauna yana irin wadanann abubuwan? Sai
ta ja tsaki bayan ta gallamin uban harara ta ce, ai sai
ki yi dama in kana son mutum ai baka iya ganin
laifnishi, ince mata ba haka bane Yakumbo ai ni
yanzu bana son Mubarak abin da na sani ne kawai
nake gaya miki, ta ce to baki san komai ba incem ata
to na yarda.
A wannan lokacin ta kaima ina zama in yi kuka
ins hare bawayena tun ina yi ni kadai har ta kaima ina
yi a gaban yaya Dija, menene mas'alar da ta hanani
yin aure? Bani da fasali ne? Ta girgiza kai uh uh kina
da shi daidai gwargwado, bani da tsabta ne? Ta sake
cewa uh h kina da ita kin kuma iya kwalliya kina
kuma yi iina da kamun kai da natsuwa gashi kin yi
karatunki kina ma kai tunda har yanzu kina yi to
amma lokacin auren bai zo ba, Maryam mijin naki ne
baizo ba d on haka bani da yanda zai yi sai dai in yi ta
baki hakuri in kuma kara rokon ki ki kara tsare
mutuncinki komai zai wuce har kiga kina bayar da
labarin al'amarin, ni dai nasan duk waenda ya yi dace
da samun babbar mata mai aikairori iri-iri, in yi
murmusbi ince yaya Dija kenan kenan kina dai gaya
min hakan ne kawai don in ji sanyi a raina.
Ita dakanta yaya Dija duk da irin wadannan
kalaman sanyaya zuciyar da take yi min ta sha gaya
138
min cewar rashin aurena ya katse mata baccinta ya
gusar mata da nishadinta ya sanyata ta ji zuciyarta ta
kutata don haka mu yi ta istigfari muna rokon gafarar
Ubangiji, in ce mata to wataran kuma in dan zolayeta
ince mata ba kince zai wuce ba? Ta yi maza ta ce,
kamar yanzu kuwa in har muna raye to zamu sheda
wucewarshi.
Yaya Dija ya ce a wurina da ta zame min uwa ita
nake kallo a matsyain uwa saboda duk abinda take yi
min yi take yi da iyakacin iyawarta tana da ya'ya
maza da mata amma bata hada su da ni ba, na sha jin
matan gidansu suna cewa ai ita wai kanwarta ta fiye
mata kowa tunda ita ita kadai ke gareta ba kuma zata
sake 'yar uwa irinta ba tunda uwar da zata haifar mata
wata bata nan ba wadannan kalaman ne suka sa
zuciyata yarda da yaya Dija bata hadani da kowa ba a
aiyukanta ne a kaina shi yas anima bana wasa da ita
duk abinda tace min to káwai nake cewa bana yi mata
musu.
Ina zaune a dakin ina yankan kayan da nake
nufin dinkawa a wannan satin wanda na ankon wani
biki da za a yi ne a unguwarsu aya Dija aka kawomin
ina yankan cikin natsuwa da kwanciyar hankali
saboda daga ni har dakin nawa tsab muke sai kanshi
muke yi, bana tunanin komai cikin raina aiki na kawai
nake yi sanda Asabe tayi sallama ta shigo cikin dakin,
ashe kina ciki? Nace eh Asabe ki zo ne? Ta ce min,
139
ina kwana? Ina amsawa ina matukar jin tausayinta
gaba daya t a canza ko rigar nono a wannan lokacin
na ganiyar kuruciya bata iya sakawa, tsabtar ta duk ta
kare kullum ka ganta gara jiya da yau ba ita ba ba
'ya'yanta kullum yanzu sai tazo gida kullum kuma da
mas'alar da zaka ji tana fadi baba Lantana tayi tayi ta
daina shiga dakina tana gaisheni ta ki dainawa, ban
sani ba ta canza hali ne ko kuma sule biyun da nake
baiwa ya'yanta in zasu tafi ne ya hanata daina wa
oho?
A wannan lokacin wanda. bai yiwa Asabe sani na
hakika ba ba zai ganta ya ganerta ba ga karni da take
yawo a ciki.
Kin fito daga dakin kanwar uwar taki ne? Ban ji
abinda tace ba naci gaba da aikina ina istigfari kan
yawan damuwar da nake yi a kan rashin aurena, na yi
imani da in yi aure irin wanda sabe tayi gara ma ina
zaune a gida gaban iyayena ckin haiyacina da rufin
asirina, tunda ba cewa akayi in ba a yi auren ba ba za
a samu rahama ba sai dai in ba a yi aikin neman
rahamar ba, ba kuma raina auren Asaben nayi ba yasa
na fadi haka tunda na san darajar aure yawa ne da shi
ko banyi shi ba kuma na karantashi a ganewa kawai a
yanda ka'idar auren yake da bayanin shi da akayi a
tsari irinw anda auren Asabe ka tafiya zai yi wuya
kwarai in har ana samun ladan da ake nema din
kullum a cikin korafi ake a zagi miji a zagi kishiya a
140
gaya mata irnin tsiyar da zataje ta yiwa mijin, ni kuwa
ina zaune gaban iyayena cikin rufin asiri ina addinina
daidai gwargwado ina neman ilimi, ina sana'ata ina
kyautatawa mahaifina gwargwadon iyawa ta, a
wannan loakcin banda sutura da hidimominshi har
runfa nayi: nsihi sabuwa ciki da falo, kayanshi suna
can ciki shi da Sallau suna wuri daya, Salau kuma
yana iyakacin kokarinshi kullum babsn ayaną yi min
addu'a yana samin albarka.
Na karaa kallon al'amarin Asabe da aurenta
wanda da ni aka so a tura cikin wannan wahalar
Ubangiji ya tsarcni, kullum a cikin tashin hankali da
miji ake kishiya kuma ta kamata tayi amta dukan tsiya
ta kaima baba Lantana da kanta tayi damara taje har
gidan Nalami wai zata ramawa Asabe dukan da
matarshi ke yi mata ban san yanda akay ba sai naga
tadawo kaca-kaca da kamar akwal rayuIwar addini a
gidan nasu to da komai ma da sauki to babu.
Daga tsakar gida na soma jiwo wata magana da
ta katsemin maganar zucin da nake yi saboda an fara
daga murya ana yinta sama-sama alamar rayuka sun
fara hassala.
To bakya cewa ya sakeki, ke wacce irin sakarya
ce yaya za a ce miji ne zai auna maka hatsi abincin da
ba zai isheka ba babu kudin cefane babu koami sai
abinda kishiya ta baka, sannan in abincin bai isa ba sai
ace. kai ne ka rasa, wannan wane inn zalinci ne,
141
Sannan in dare yayi ya zo ya fada miki da yunwar da
komai ba dama ki ki yarda da shi, ke ko irin 'yar
tirjiya da yangar nan da mata ke yi a rarashesu a yi
musu abinda suke so baki iya ba.
Ai rufeni da duka yake yi yana ganin alamar zan
yi mishi tawaye sai kawai ya tashi ya zauna ya yi ta
jigbata da duka wai ladan hatsinshi da na wuni ina ci,
baba Lantana tayi shiru kamar yanda Asaben' ma ta
tayata yin shiru, imawa cna na ji ta ja wani
mummunan tsaki da bai da dadin ji kafin daga baya ta
bishi da fadin, kai Nalanni dai tsnanne ne.
Shi ne nace to ko zance ya sake nin ne kawai? Da
saun ta ce ys sakeki mana tun yaushe nake gaya miki
hakan? Ta dan rage nurya kadan ta ce, to amma fa ba
Zai yarda in abr mishi wannan yaron a can ba ya ce
wai zaunana ya ke yi na barin gidan shima zai bari
wannan dai ya yarda nashi ne tunda yana kama da
ya'yanshi amma si wannan ai bai ga ta inda ya
daukoshi ba shi ne nace ko zan kawo miki shi ne
kawai in bar mishi wannan din: wahalar da nake sha
tayi min yawa kajin mafa day ake bani figarsu yana
bani sisi-sisi ina samun na sabulu yanzu ta hanashi
bani ko kwabo wai...
Ni da nake kashc da kunne in ji abinda baba
Lantana zata fadi kan kawo mata dan da Asabe ta ce
Za ta yi sai naji ta hassala ta daka mata tsawa, ke barni
haka da wannan mugun albari naki sakarya kawa
142
shashasha sauna mara zuciya ace mutum bai da wani
aici sai na bayar da mugun labari? Ki dauko yaro ki
kawo min ya zama duk tattakar da ya yi miki a banza
kenan ko me? Wannan yaro ai dole ne ya girmaa
gidanshi ladan sukurkutaki da ya yi ya maida ke wata
yamutsattsiyar tsohuwa, tsinannan mutum kawai.
Na ce oh oh ta kacame tsakanin siriki da sirika,
ina zaune kan kekena ina dinkin kayan dana gama
yankawa zuciyata tana tunaina al'amarina irin kokarin
da baba Lantana tayi na ganin ta sa babana ya baiwa
Alhaji Nalami aurena duk da tafi kowa saninshi da
duk wani al'amarinshi tunda tun a loakcin ta sha gaya
min cewar in dai matar Nalami tana nan a yanda ta
santa ai zata yi mata magani na to gashi abin baiyo
kaina ba sai ya fada a kan yarta nan take na tuna da
karin amganar hausawa da ke cewa wai, mugunta
fitsarin fako, in kayi sai ya dawo maka kanka.
Kwalliya mai kyau nayi a ranar da na yi nufin
kaiwa masu kayan kayansu, doguwar riga na sanya
har Rasa ta farar atamfa da aka yiwa ratsi da kananan
filawowi koraye da bulu, saman rigar na yi shi a
matse yayin da na yiwa tsakiyar yankan umbrella ya
sauka har Kasa, dankwalin yadin' atamfar ne a kaina
na yi dauri mai kyau sosai na sanya yan kunne
kanana na yafa farin gyale madaidaici a-kafadata
yayin da na kawata hannayena da adon awarwarai,
agogo da zobuna biyu na zinari daya kuwa na azurta
143
da aka yava kira mai kyau na shuri takalmana silifas
1masu igiya a baya yan Italy da suka kara kawatamin
kwaliyar tawa, nasa garkamemen kwado na kulle
kofar dakina a dalilin gajiyar da na yi da biyan
mutane atamfofinsu da suke bata don haka nama
canza kofar dakin gaba dayanta.
Na baro gida rike da ledar kayan dinki da kuma
pos a hannuna bayan na gayawa babana inda zani,
yar tafiyar da nayi ba wata mai yawa bace na ja na
tsaya don tarar mashin din da zan hau.
Wat ke me yasa bakya įin magana ne? Sau nawa
nake gaya miki in zaki fita ki daina amfani da turare
ki kuma daina hawa mashin bana so.
Ban kalteshi ba balle in bashi amsa iyaka dai
nasan nayi mamakin ji ko ganinshi a wannan lokacin
tunda nasan ya taf Legos bar kima san da dawowar
tashi ba.
Amma shi baba tsareki da ya yi a gida kike ta
wannan zaman a gabanshi yana ganin kamar ya yi
mishi daidai? Shi bai san kin kai kowane irin munzali
bane, bai san kinas ha'awa ba? Ke ba za ki gaya mishi
kina da mas'ala ba? A muku mukuns anyin nan kin
fito za ki je ki kai akyan da kika dinkawa wasu in kina
gidan aurenki mijinki zai yarda da haka? Gaskiya
na gaji da ganinki a haka yanzu fa Rumasa'u
ya' yanta biyu ne.
144
Maganar ta dak zuciyata a hankali na tunawa
kaina da kullum muka gamu da shi bama rabúwa sai
ya san yanda yayi ya sokamin abkar maganar da ta
tsaya mina raina.
To wai ni ina abinda ya dameka da ni ne? Kaga
ni na damu da kai e? Kaga ina. daga ido ina kallcka
ne balel in san abinda kake ciki? Ina dalilin da kake
nema ka maida mahaifina abokin wasanka, kullum ka
ganni sai ka san abinda ka fada a kanshi.
Ban maidashi abokin wasa ba Mero amma
gaskiya zan gaya miki yana 6ata min rai don me zai
hanani ke? Don...
Na yi maza na katseshi, in ya hanaka ni sai ka
rinka gaya mishi magana a kan ido na wane hurumi
ke gareka na yin hakan? Nace bana sonka nace ka fi ta
harkata nace ina kwai wani mutumin da zance na
tsana a yau to kai ne don me ba za ka yi zuciya ka fi ta
hanyata ba?
Ranshi ya yi amtukar 6aci da kalarman da nayi
mishin, wani irin kallo ya yi min irin wanda shi kadai
ya san abinda yake nufi da kallon, kina ganin kamar
ba za a iya fita harkar taki bane? Kina ganin kamar in
an fita harkar taki wani abu zai faru ne da kike
wannan cika bakin? To ni don na fita harkar ki ma
menene Maryamu? Ai ni ina da mace a gida har da
ya'ya kece kike zaune ke kadai kece kike rayuwa
cikin kewa da kadaici, duk sanyin da ya taso ya kare a
145
kanki kina zaune kan kujerar dinki, ni ai da aurena
sannan karya kikeyi kice bakya sona in bakya sona
me ya hanaki yin aure? Fitar da wani ki aura mana ki
zauna kema a dakinki ki dandani dadi da zumar dake
cikin auren sakarya kawai sokuwa shashsha wacce
babu halin a batawa mutum rai ya gaya mata ta
tausaya mishi, sai ta ce zata bishi da bakar magana
sau dubu nawa yake so in turo mishi mutane kafin ya
yarda ya bani ke? Me nayi mishi a rayuwa i banda
adalci.
Sauri nayi na tari mashin babur na dale kai muka
tafi don kar bakin ciki da dacin da nake ji a zuciyata
ya sa in fara yin kuka a gabanshi.
Zagin da ba a taba yi min ba yi min, yayi min
gorin aure da 'ya'ya da... na kasa karasa bayanin
nawa na shiga yin kuka sosai da sosai, tana ta bani
hakuri, jimawa can kuma sai ta nisa ta ce, nima dai
abin yana damuna ina mamakin yanda baba ya ja ya
tsaya ya ki baiwa Mubarak aurenki bayan nima nayi
iyakacin tunanina ban gano laifin da ya yi mishi ba to
inma ya yi a yafe mishi mana, Umma ma fa kwanaki
tazo gidan nan maganar kuma ce ta kawo ta na kuma
san ba dadi ne ya sa ta yin hakan ba, to ya bashi ke
din mana kawai a huta, zan sake zuwa wajen baba in
sake rokonshi inji..
Kan ta karasa na yi mata wata irin rantsuwa mai
karfi kafin na ce mata, ba zan taba aurenshi ba har
146
abada ba zan taba aurenshi ba bana sonshi bana son
shi ko da sunanshi ne a kusa da ni da in aureshi gara
ma in yi ta za...
Ta dakamin tsawa na kame bakina na bar
maganar na koma yin kuka, tun ina yi ni kadai har
itama ta shiga tayani muka yi tayi sai da muka gaji
muka yi shiru.
Mubarak ya saba zagina ko tsareni ya gaya min
bakaken maganganu iya son ranshi a duk lokacin da
ya turo maganar aurena wajen babana ya ce ba zai
bashi ni din ba, to ni yake tsarewa ya gaya min duk
wani abinda yake son fada, in yi bacin ran in hakura
amma bai taba gayamin maganar da ta daki zuciyata
ta sani bakin cki na yi kuka mai tsanani irin wannan
karon ba.
Na gaji, na gaji, na gaji da iin wulakanci da cin
zarafin da yake yi min a kan aurena don kawai ya ga
bani da auren da ina karkashin inuwar aure ai shima
da bai isa ya yi min irin wadannan abubuwan da yake
yi