Showing 9001 words to 12000 words out of 36183 words
yayi kama ai in ba sake danben
nan aka yi ki ka yi mata dukan tsiya ba to raini kawai
kika kara jawa -kanki a tsakaninku da can da kike
dukanta ma yaya kika kare da wulakancinta balle
yanzu da ta jibgeki ta yi miki irin wannan kayarwar?
Lalle ne na gaya miki daga nan zuwa gobe ki san
abinda kike ciki da ita.
Duk da na ji maganganun baba Lantana banyi
nufin sake yin wani fadan da Asabe ba don nima na fi
ganin tsananin sa'a ce ta sani kada ita, amma da gari
ya waye da safe naje na sayowa babana abin karyawa
zan wuce ta ta sa hannu ta kabe min shi ya kife a kasa
na daga ido na kalleta cikin salati mai karfi naji ta ce
min, wai rama abinda nayi mata jiya tayi inji in da
dadi ai gurin danben da na jata da shi ne na yi dalilin
kifewar abincin ta sai kawai na ji tsoron ya gushemin
ban tsaya tambayarta yaushe aka yi hakan ba sai na
sunkuya na kwashe abinda zan iya kwashewa naje na
ajiyewa kaina na sake daukan wani kwanon naje na
sayo wa babana wani na kawo mishi sai da naji ya
gaya ci na bashi maganinshi ya sha sannan na fito na
shigo dakinmu na kama diro da kayan Asabe ina yin
watsi da su a waje ina fadin in baki rama abinda nayi
miki ta hanyar wulakanta abincin da ubana zai ci ba ai
ba zan kara gane ke baki da uban ba Asabe wanda ya
san darajar ubanshi ai zai san na uban wani don haka
43
yau za ki bar min gidan nawa uban tunda ya rufa mi1k
asiri baki gane haan ab.
Da gudu ta baro wurin baba Lantana da suke tare
ta 20 zata rarume ni nayi maza na juya kanta muka
rincabe da danbe ba a je ko ina ba yauma na raruma
Asabe na dagata sama na fyadata da kasa.
Baba Lantana tana ganin haka ta zabura da gudu
ta dauko itace wai zata bugamin tana fadin na gaji da
danben rashin da kike yi min a gida don haka yau za
ku gamu da ni za ku ji a jikinku kumą ta fara nufowa
da itacen nata nayi maza na kamashi na rike na kalleta
cikin natsuwa na ce mata babu sauran duka a
tsakanina da ke wanda kikayi min a baya ya isa, na
sakar mata itacen ya fadi kasa.
Ta zabura ta nufi dakin da babana yake kwance
tana fadin, ina malam din yake kana jin abinda yake
faruwa amma kayi gum. da bakinka kamar. na yi
maza na katseta ta hanayr gaya mata cewar ya isa
haka kar ki sake zaginshi a gabana kar kumaki nemi
ki daga mishi hankali.
In nayi hakan me zaki yi? Za ki buge ni ne? Ban
ce mata komai ba na wuce na nufi dakinmu.
Sallau ya ce uhun baba kenan ai ba ki yarda ba ne
da kin yarda....kan ya karasa ta sunkuci itacen da tazo
da shi din ta shiga rafka mishi tare da fadin zo ka bar
gidan nan zo ka tafi.
44
Ai babu inda zanje baba in dai ba baba da kanshi
ne ya koren ba ban taba samun inda na zauna lokaci
mai tsawo a rayuwata ba sai da na zo hannunshi in har
kuwa ki na so in atfi to ki kwatantamin inda zan samu
dangin ubana tunda kin ce wai ya mutu su kam in kika
nunamin su to ba zan sake zuwa inda kike ba sai don
gaisuwa amma haka kawai ba za ki kora ni in shiga
duniya ba.
Na fito daga wanka na kalli A sabe na tabbatar
jikinta yayi matukar sanyi kan abinda ya faru
tsakanina da ita jiya da yau nace mata haka a yanda
kike na fama da abinda kike fama da shi kice zaki
buge ni ina budurwa gal a leda? Ai ke ma kin san
Karya kike yi ubana ai ya rufa muku asiri dukan ku.
Daga ita har baba Lantanan babu wacec ta tanka
min iyaka dai na ganta tayi wanka ta shirya ta fita ta
bar gidan ta tafi, nima nas hirya na nufi gidan yaya
Dija na gaya mata halin da jikin babanmu ke ciki sai
dai ban zauna ba na dawo gida.
Ina shigowa na samu baba Lantana tana rabon
abinci nayi maza na kwaso kwanuka guda biyu ance
mata ga nawa ga na babana, tayi kamar ba zata zuba
ba ban san tunanin da tayi ba sai kuma naga ta dan
minmindira mana a zuciyata nace oho na dauka na
tafi na kaiwa babana ya ci ya rage sannan naci, ban
wani dade da dawowa ba sai ga yaya Dija ta iso
babana ya yi ta fada kan zuwan da nayi na gaya mata.
45
Ta ce to baba za ka yi ta ciwo ne ban sani ba? Ya
ce to wannan ciwo da ya riga ya zama jiki ai ba
kullum ya tashi ne za a je a fada ba tunda dai ikitama
ya riga ya yi bayanin shi cewar ba a warkewa shi
abokin tafiya ne, nayi maza na ce a'a baba ba fa haka
ake nufi ba ai kca da hanyar tafiyar shi bai kuma
zama dole don kana da shi a ce shi ne abokin tafiya ba
ai ana jin saukin shi. Ya ce uhun fata dai ai bai wuce
na rokon ubangiji ya bamu sa'a ba rmuka ce amin.
Ta gima abinda zata yi ta fita zata tafi na bita ina
yi mata rakiya ina bata labarin abin da ya faru
tsakanina da su Asabe da uwarta sai dai babu alamar
natsuwartı tana tare da ita saboda yanda na ga tana ta
faman har dewa har tana buga tuntube.
Yanzu nan har yanzu wadannan mayun yaran
basu dain aw adannan wakusn naSu na sharri ba? Na
ce mata ch, tyo amma shi ne kike fita? Na yi
murmush na ce to vaya zanyi? Ai ya zama min dole
in fi ta ta ce haka ze hausawa suka ce wai watan
kwaram daya ne in ya mutu sai na wnai ya kama
amma mu namu watan kwaran din bai zamo guda
daya tunda yau waien kwane sittin ne har da bakwai
har yanzu bai mutu ba, bance mata komai ba shiru
kawai nayi har ta gama maganganunta muka yi
sallama na juyo gida.
Da daddare ina zaune a dakina ni kadai saboda
tunda Asabe ta fita ta bar gida bata sake dawowa ba
46
shirin tafiyarmu asibiti nake yi gobe saboda umarnin
da yaya Dija ta bani kenan ta kuma kawo mana kudin
zuwa asibiti. Ina cikin kammala abubuwan tunda
nasan sai munyi sammako sosai ne zamu iya ganin
likitan a kan lokaci sai ga Sallau ya daga labulen
kofar dakin tare da ya min magana a hankali, sannu
Mero. Na daga kai na kalleshi, yauwa sannu Sallau,
ya ya mai jikin? Na ce mishi da sauki. Ya sake rage
muryar tashi ta kara yin kasa kafin ya ce min da wata
shawara nazo da ita ban sani ba ko zata samu karbuwa a wurinki.
Na ce to shigo màna in ji shawarar, cikin natsuwa
ya shigo ya nemi wuri ya tsuguna kamar wani mai
shirin biyan bukata. Da ka zauna ai kamar zai fi yi
maka dadi, a'a babu damuwa, na ce to shi kenan me
ya faru?
Ya danyi kame-kame kadan kafin ya iya fitowwa
sosai ya yi min bayanin rumfarn an ce ta baba da
kullum in bashi da lafiya ake rufeta babu kowa
tumatirin ciki dama duk wani abinda ake da shi su yi
ta lalacewa tunda ba masu jirar zaman bane shi ne
nace ko zan rinka bude ta ne ina zama a ciki? Sanin
da nayi da gaskiyar magana Sallau din ya fada na
kuma san in ma ban barshi ya bude rufmar ya zauna
ya dan taba abinda ya taba na cikina ba to duk ranar
da aka budeta za a kwashe komai ne a zubar tunda za
su gama lalacewa to da a yi irin wannan asarar kuwa
47
gara ko ba zai baiwa baban koami ba ya bude ya
sayar, nasan shi zai dan samu wani abu don haka sai
na kalleshi na ce mishi, to ai hakan yana da kyau
Sallau gobe da safe sai kaje ka bude tunda shi baba
goben zaije ganin likita, ya ce to Ubangiji ya sa mu
gani lafiya, na ce mishi amin.
Washegari da yamma mun dawo daga asibiti
bayan sallar La'asar a dlailin dogon layin da muka
tarar daga nesa na hango Sallau a cikin rumfar baba
yana tashe da yan timatirin da suka saura muka wuto
shi muka shiga gida sai kusan magariba ya dawo ina
kallonshi bance mishi komai ba baya ga gaisuwar da
muka yiwa juna sai da ya tabbatar baba Lantana ta
shiga dakinta ta kwanta sannan ya turo kofata ya
shigo a hankali gaba daya cinikin da ya yi ya zube
min a gabi.na na zuba ido ina kallo nace a'a ciniki mai
kyau aka yi ne haka Sallau? Ya ce eh an dan taba
kadan, to madalla na fada ina mai sauraron
abyaninshi sai da ya gama na ce mishi, to su
wadannan kudin sai ka rikesu kawai a wurinka ba ka
ce kayan bai karasa karewa ba? Ya ce e, na ce to daga
nan zuwa biiba ya gama jin sauki sai mu ga abinda za
a yi, ya ce min to sai da safc ya fita.
Kwana uku bayan nan baba ya fara bude
rumfarshi bayan ya saro wani sabon timatirin a dalilin
saukin da ya samu ban san yanda akayi ba sai na
ganshi tare da Sallau suna zaune a rumfar tare shi
48
yana can ciki a zaune Sallau yana salalmar masu zuwa
saye, ni ma kasuwar zai tafi sai ya tasashi a gaba su
tafi tare.
Rannan ina kwance a kan dan gadona na bono da
hantsi bayan na yi wanka na shafa man basilin din
babana saboda gaba daya kayan shafana sun kare bani
da komai in banda man wanke baki. Ina cikin tunanin
halin da nake ciki ne sai kawai na ji an kwala sallama,
ina jin sallamar na gane wanda ya yi ta nan take na
shiga lissafin rabonshi da gidan yau zuciyata ta
tunamin kwanaki tara ne cif.
Sallama dai sallama dai, na fa iso na kuma san
ana jina yauwa ita rana ai bata karya sai dai ko uwar
diya ta ji kunya, to ni don kar a ji kunyar ma sai na
mutunta na kara kwanaki har biyu kan alkawarin da
aka yi min din, ga zatona za a biyoni da su har
rumfata a mutunce to da ban gani ba kuwa gani na
taho karbar halali na.
Baba Lantana ta fito daga dakinta dankwalinta a
hannu fuskarta kuma a daure abinda na tabbatar shi ne
bata yi azton zuwan nashi ba a yau don kuwa jiya da
shekaranjiya da ta yi tsammanin zuwan nashi tun
sassafe take barin gidan bata dawowa sai cikin dare.
Ah naso karbar halalina ya yi maganar cikin wani
irin yanayi yana mai kawar da ido daga gareta,
watakila saboda mummunan kallon da ya lura tana yi
mishi.
49
Ai kai baka taba cin halal ba a rayuwarka tund
aga kuruciyarka har kawo ga halin da kake ciki na
tsufa a yanzu.
Duk abin da za ki gayamin dai ba zan tanka miki
don kudi ne dai sai kin bani su ko girma da arziki ko
tsiya tsiya duk wanda kika zaba tunda dai na ma yi
sa'a kawarki bata taimakeki kika samu miji a hannu
ki ka yi mata alkawari kika saba saboda ganin
bukatarki ta biya kika wulakantata kika barta tana
bara bara karuwa karuwa ta yard ain munje kotun zata
bada sheda a kanki kyauta ba sai na biya ba ai da
sauki.
Wacce kawa ke gareni da mukayi haka da ita in
banda sharrinka? Da sauri ya ce mata Delu. Ni da
kaina da babu ruwana a cikin maganar na san baba
Lantana tayi amfani da kawayenta wajen neman
babana a malamansu da kuma taga kamar ta samu
yanda take so ta koresu ta hanyar yi musu wulakanci
ba tare da ta cika musu alkawarin da ta yi musu ba
cikin irin wadannan kawayen nata nata har da Delu.
Jikin baba Lantana ya yi sanyi kwarai da jin
cewar Delu zata bayar da sheda a kanta ta kuma san
sauran ma zasu iya yin hakan koma fiye da haka, to su
je su yi ta bayarwa mana, ya yi murmushi ai fa za su
je.
Takardar fuili nake da ita zan baka kaje ka sa
filin a kasuwa ka sayar ka karbi kudinka, takardar fili
50
kuma? Ya yamutsa fuska ni da na bayar da kudi na
tsaba a hannu sai kuma a ce za a hadani da wata
takardar fili? In filin na arziki ne me yasa ke bak
saida shi kin karbi kudin kin b ani ba? Da kyar Alhaji
Nalami ya yarda baba Lantana ta fito dat akarda ya
karba yanad ubawa tana yi mishi bayani, filin ya kai
shekarauku da saye tun a wancan lokacin kuma jaka
uku na sayeshi zuwa ina ganin zai iya kaiwa jaka
goma in an saida shi a kawomin sauran kudin.
A hankali ya matsa kusa da ita ya ajiye mata
takardar tare da fadin, saidashi da kanki ki bani
kudina kawai abinda nake so kenan shi ne kuma zai
fiye miki rufin asiri a kan wannan neme nemen
maganar da kikeyi da ni ai ke ma kin sani sarai tunda
aka saida gonar mage aka saiwa bera daddaawa to
kuwa tsugu ne ta kare msihi ni za a kawowa iyas hege
filin da aka saya shekara uku bayan ne za a yiwa
wannan bayanin ba ku yi magana a kan irinr agin da
za ki yi a kai ba saboda sanin kullum darajar kasa
raguwa take yi ba karuwa ba sai a ce ana neman kari?
Darajar kasar ce take raguwa a garinku ake yin
hakan ko? Ai sau dubu in kika zage ni nace miki ba
zan rama ba, itama Delu shawarar da ta bani kenan,
ambatar sunan delun yake yi kamar da gangan tamkar
dai ace ya san hakan yana bakanta ran baba Lantana.
Tun yaushe aka daina cin ribar fili saboda yanda
darajarshi take ta faduwa ai kudi a hannu ana juyawa
51
su ne wani abu. Da kyar Nalami ya kar6i filin baba
Lantana a jaka ukaun da ta sayeshi tun shekara uku da
suka wuce ya kuma tasa Sallau a gaba don ya kaishi
inda filin yake yana yi kuma yana yi m ata bayani, yo
to ke in banda tsohuwar sanaiya da mutuncin dake
tsakani zan karbi wannan filin ne a haka? Ai da sai
ince sai masu saye sunje sun gani sunyi mishi kudii
tukuna to babu irin wannan a tsakaninmu. Ya tasa
Sallau a gaba suka fita.
Cikin zuciyata na ce uhm uhn kudin babana ne
da aka yi ta titsiyeshi ana tarawa yau Nalami ya zo ya
karbe su a karin banza. Hausawa suka ce wai, Garin
banza a farau farau din wofi yake karewa.
Ban taba sanin duk wata fitina da nake ciki ko
damuwa ko 6acin rai nafila ne ba sai a ranar da
Isiyaku ya zo min da labarin cewar wai Mubarak zai
yi aure.
Samun kaina na yi rannan cikin wani irin yanayi
da ba zai yiwu in tsaya ma kwatantawa ba, kwana
nayi rannan idona biyu a zaune daram a tsakiyar
gadona, ban kwanta ba balle in samu halin yin
gyangyadin da zai zama dalilin runtsawa.
Mubarak zai yi aure? Maganar dake ta faman kai
kawo kenan a cikin zuciyata wacce kuma ita ce ta
hanani sakat ta hanani jin dadi ta hanani natsuwa ta
hanani zaman lafiya balle in yi maganar kwanciyar
hankali, don saukin abin ma shi ne ni kadai ce a ciki
52
dakin tunda Asabe ta tafi har yau din nan bata dawo
ba, don haka zagewa nayi nayi kuka sosai kuka irin na
bakin ciki da tausayin kai sai da nayi na gaji don
kaina nayi shiru, ina cikin share hawayen nawa ne
naji zuciyata tana gayamin cewar ai kukan dadi kikeyi
a yau da dai ace da kikayi mishi kyautar budurcinki
kyautar wauta da shashanci ya sa ki kikayi ya karba
hakan ta auku a tsakaninku to ya karbi budurcin naki
to da yau kin yi kuka na gaskiya kuka iin na nadama
da bakin cikin rayuwa, nayi kasake ina sauraron
abinda zuciyar tawa take gaya min, lokaci mai tsaho
ina sauraronta kafind aga bisani na yunkura cikin
natsuwa na sauko daga kan agdon nawa na zo na
soma binciken cikin kayana, hotunan da Mubarak
nayi ta cirowa ina yagawa tare da konawa saboda
tabbacin da zuciyata ke bani na shi kenan na rabu da
Mubarak rabuwa kuwa ta har abada.
Na kosa kwarai gari ya waye don in je in
shedawa yaya Dija labarin aurcn Mubarak da naji,
garin ya ki wayewa nisand aren ya kai matukar nisa
duhun daren ma ya kai iyakacin duhu, gani nake
tamkar in naje na gayawa yaya Dija tana da wani
taimako da za ta yi min ko wani amfani da zata yi
min, ko wani amfani da gaya mata zai amfanar da ni,
waiyo waiyo waiyo abinda kawai nake iya ji yana
fitowa daga cikin bakina kenan, saboda tsananin zafin
da zuciyata ke yi, da kyar na samu garin ya waye.
53
Muna hada ido da baba Lantana a tsakark gida ta
saki wani irin lallausan murmushi wanda rabon da in
ganta tana fara'a tun ranar da Nalami ya karbi
takardar filinta ya tafi, muna hada idon sai ta yi dariya
ta ce, anya ashe kema kin ji labarin, ta sake sakin
wani lafiyayyan murmushin kafin ta ce, uhun in dai
da namiji ne ai kuka ba ki ma fara shi ba tukun balle
ke da kika wulakanta jama'a a kanki ai kadan kika
soma gani. Ban tanka mata ba na sa kai na fita gidan
yaya Dija nake nufin zuwa.
Ina fitowa daga gida na kara rudewa na kidime
jikina ya dauki rawa karkar kar, cikin hanzari na juya
da baya don in koma gida, amma saboda tsananin
firgitar da nayi maimakon in shga gidanmu sai na
smau kaina a zauren gidan su baba Sumaye,
tsugunawa nayi a zauren cikin wani irin rudani,
cincirindon mutanen da na hango a kofar gidan nasu
Mubarak ne ya yi matukar razanani tafiya daurin
auren nashi za a yi ko kuwa har sunje sund awo ne?
Ban kara sanin irin rudewar da nayi ba sai da na
ganni durkushe gaban baba Sumaye ina kuka alhalin
ba abinda nayi nufin yi kenan ba.
Za ki yi kuka mana Mero za ki yi kuka kai me
sonki ma ai zai tayaki zubar da hawaye, wadannan
abubuwan da suka faru dole ai ba kananan abubuwa
bane ko ni din nan nayi kuka nayi addu'ar ubangiji ya
jikan Ramatu da rahamarsa sanda akayi bikin Dija da
54
yake tana raye ai ba a yi haka ba shiru akayi komai
aka gama cikin rufin asiri da mutunci su na murn
amuna murna, kema maraicinta ne ya ja miki shi ya sa
bana jin zafinki sosai bacin raina daya ne da kikaje
kika bashi kanki to ga abinda gari ya waya, yanzu
waye a kasa? Waye kuma a wulakance? Babu amfani
in tsaya ina yiwa baba Sumaye bayani kan cewar
banyi abinda ake zargina da aikatawa ba, tunda nasan
ba yarda zata yi ba don haka sai kawai naja bakina
nayi shiru ina sauraron abinda ake gaya min.
Ahmad Mubarak zai yi aure don yana son
daidaitawada m ahaifinshi, yin aure da kuma alkawari
na zai fita daga lamarinki gaba daya su ne ka' idojin
da ya yarda da su kafin shi Alhaji Muhammadu ya
yarda ya yafe mishi laifuffulkan da ya yi mishi, kema
kuma don baki da mai taimakon kuruciyarki ya doraki
a kan hanyar da