Showing 18001 words to 21000 words out of 36183 words
da ni da Mansur uka hadu a wuri daya.
Ya ya Dai Maryam? Yaya jikin baba? Na amsa mishi
da sauki, 'yan maanganu kadan mukayi hirar tamu ba
ta yi wani nisa ba watakila don bamu saki jiki ba
tamkar dai ace muna jin kunyar juna.
Takardar naira ashrin guda biyu ya. miko min
wato naira arba' in ko ince fam ashirin, hannu biyu na
saka na karba tare da yi mishi godiya, bai tsaya jin
wata magana ba ya ce min, zan tafi sai na dan huta na
fito za ki ganni, na ce mishi to.
Yana tafiya na dauki takardar naira ashirin guda
daya na nufi shago don yi mana sayaiya, babu wani
abin da ban saya ba na kayaiyakin amfani har man
shafawa da na dade bani da shi na saya, sai dai
81
maimakon 10-0-6 da Mubarak ya koya min shafawa
sai na koma man shafawa na kamfanin shield don dai
in samu in kara fitar da duk wani tunanin shi daga
cikin zuciyata.
Na shigo gida na kama wankin babana cikin
kuzari na gama nayi nawa nayi mana guga na adana
mana kayanmu na gama ba tare da gajiyar aikin ta
dameni ba can cikin zuciyata nace kai babu tana cikin
mas'alolin da ke addabar rayuwar dan adam matukar
dai shi din mai lafiya ne.
Kudin da na samu wurin Mansir sai suka
wattsakar da ni na samu kuzari mai yawa a tare da ni,
nayi duk wani abinda ya dace, ranar asibitin babana
ya zo mukaje muka daow na saya mishi magungunan
da aka rubuta ba tare da na jira ko gayawa yaya Dija
ba, sai da na gama komai ne sannan naje na gaya mata yanda aka yi.
Tun daga wannan lokacin da Mansur ya dawo
daga tafiyar da ya yi zuwa Ghana sai gidanmu ya
zamo nan ne wurinshi sai dai in baya nan, tun ina jin
kunya ina nonnokewa saboda al'amuran da na san ya
sani ya ji game da ni har na wattsake muka shiga
harkar soyaiyar na samu natsuwa da kwanciyar
hankalin da na dadeb an samu ba, na murje na yi kyau
saboda nayi sa'a shima man shafawar shield din ya
karbi fata ta.
82
Yaran unguwa sun yi matukar fita harkar yi min
wake-wake sun yi sun gaji sun hakura, dama hausawa
Sunce wai watan wataran din guda daya ne in naka ya
mutu sai kuma na wani ya kama.
Mu'amala ta da Mansur ta yi amntukar sama min
natsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni, har na
samu karfin da na ji zuciyata ta daina faduwa don na
hango Mubarak ko na ji wata magana game da shi, a
wannan lokacin sai naji a shirye nake in har Mansur
ya yi maganar aurena in amince don kuwa na yarda na
sakankance da cewar shi din miji ne da zai kula da
1yalinshi ya samar musu farin ciki da natsuwa da suke
bukatar samu.
Ina zaune a dakina hutawa nakeyi saboda
dawowa ta kenan daga asibiti don yau ma na raka
babana ganin likita saboda gaya min da ya yi cewar
ya yi kwanaki uku cur bai samu yin bacci ba da
daddare, hutawar da nake yi tare da kara tuna
kalmomin da likita ya yi game da jikin nashi sai naji
yaro yana magana a tsakar gida wai anak iran Mero a
waje.
A zuciyata na ce Mansur kenan shi da yace in
shiga gida in huta sai an jima zai zo me kunma ya tuna
ya sashi fasa hakan? Na mike na fito na wuce baba
Lantana tana fadni, o'o shi wacan ya ja jiki wannan
Kuma ya maye gurbi ya samu an bashi wuri ya zama
shi kadai.
83
Ban kalleta ba na yi wucewata na fita, ban ganshi
a zaure ba kamar yanda ya saba shigowa ciki don
haka na leka kofar gidayasan na zo ina lekawa sai
kawai mukayi ido hudu da Mubarak, ya sha kwalliya
cikin kananan kaya ya yi kyau sai dai ban ji faduwar
gaba a tare da ni ba, dadi ya kamani na kara gamsuwa
da kaina.
Yana ganin naja baya ya biyoni cikin zauren,
sunkuyar da kaina nayi don in kaucewa idanuwan da
ya tsareni da su, zuwa nayi in rokeki ki yi min wata
alfarma Maryam.
Na dan yi kokari na daga ido kadan na kalleshi
saboda maganar tashi da yanayin da yayi maganara
ciki, alfarmar me ni kuma zanyi maka? Na rokeki na
kuma sake rokonki ki yi min wannan alfarmar ki fita
hanyar Mansur bana so ina ganinki tare da shi.
Cikin natsuwa hankalina kuma a kwance na buda
bakina na ce mishi, gaskiya ba zan iya ba. Maganar
tawa tayi matukar bashi mamaki saboda abinda na
gani a tare da shi, cikin wani irin yanayi ya
tambayeni, ba za ki iya ba? Shiu nayi ban bashi amnsa
ba, ban kuma sake daga idona na kalleshi ba, saboda
har yanzu ina jin nauyinshi a zuciyata.
Me na yi miki Mero? Me nayi miki haka da kike
nemaki sani bakin ciki? Ai ban cuceki ba, ban
zalunceki ba, ban yi miki wani laifi ba, in kumakina
gani nayi to gaya min shi in abki hakuri Mero, ai in
84
rai ya baci hankali baya bata a kowane hali muke ciki
ko muka samu kanmu, bai kamata ki rufe ido ki kasa
ganin gaskiya tsakanina da ke ba.
Juyawa nayi da nufin shiga gida in barshi a
zauren, ban san yanda akayi ba sai kawai na yi kicibis
da baba Lantana a kusa da bakin zauren watakit da
shigowa zatayi taga abinda muke yi, tana ganin
Mubarak ta shiga salati tana tafa hannu tare da fadin,
yau ga abin da mamaki yau ga abin al'ajabi, yau ga
wata musiba da ta addabeta ta addabi sauran jama'a,
ashe ba iyayenka sun yi maka aure na rufin asiri don
ka fita hanyar wannan yarinyar ku daina lalacewar da
kuke yi ba, haba wannan wane irin al'amari ne shi?
Aure baifi wata shida ba masifar ka ta sa kullum
yarinya tana kan hanyar yin yaji ta tafi a dawo da ita,
ta tafi a dawo da ita, to kar ka ji da wai zan wanke
kafata inje har gidan iyayenka in kara yin kashedi
tunda na san su ma ba son mu'amalarka da ita suke yi
ba tunda ina da labarin komai sai da ka yarda da
sharadir da šuka sanya maka na fita hanyarta sannan
ne suka bar ka ka dawo suka kuma yi maka aure na
rufin asiri wanda a yanzu kake wulakantawa ko da
yake ba haka kawai suka barka ba 'yarta ai babu
abinda ba zata iya ba.
Wuceta nayi na shiga dakina na yi kwanciyata a
kan gadona sai na ganta itama ta dawo na tabbatar
tafiya yayi ya barta.
85
Wunin ranar nan bakin baba Lantana bai huta ba
fadi suke haka kawai basu shirya yarinya ba sun
kunsota sun kawo sun ajiye mishi ba dole su da ita su
yi ta ganin abinda basa so ba, tunda ya riga ya saba da
tsome-tsome ai zama da shi kuma sai an shirya,
Maganar tayi matukar watsuwa ta yanda har
Mansur ma yazo ya sameni hankalinshi a tashe, ranshi
a bace, me ya saura ne tsakaninki da shi kuma? Na
rasa yanda zan yi na rasa abinda zan gaya mishi
saboda bacin ran da na gani a tare da shi, don haka na
kama yi mishi kuka, kuka kuwa mai yawa irin wanda
na kwana biyu ban yi ba.
To menene kuma na kukan hakan? Ya soma yin
maganar a yanayi na sanyin jiki alamar bacin ran da
ya zo da shi din ya kau, to ni me nace miki da kike
wannan kukan? Kinga share hawayen nan ki ji abinda
zan gaya miki, to ai kuma na gane so kawai kikeyi
raina ya baci shi yas akike ta kukan, in ba haka ko ma
menene nace ki yi hakuri ki yi hakuri ina ce shi kenan
zance ya kare.
Kinga tunda abin nan ya zama haka ana nema a
rinka kai kawon maganganu a tsakani to ina ganin
gara kawai a kawo karshen al'amarin gaba daya in
kina dakina da wani wanda ya isa ya zo yana Rananan
maganganu ne a tsakani? Don hakan ni in kin yarda
kawai a shirye nakwe in je in samu babana ya dawo
86
ya sake yin amgana da baban nan gidan a daidaita a
sanya lokacin auren mu kome kika gani.
Lokaci mai tsawo na dauka ban ce mishi komai
ba har ta kaima ya sake tambayata, ba ki ce komai ba
Mero ko kuna da wani tunani ne? Na sunkuyar da
kaina kasa kafin nace mishi, kai ne dai nake ganin
kamar ya kamata ka kara tunani akan maganar tunda
ka sani sarai an fadi maganganu da yawa a kaina har
yanzu ma ba a daina ba tunda ga ma wanda aka je har
gidanku aka fada kwanan nan in...
Ban karasa zancen nawa ba ya yi maza ya
katseni, yanzu ina amfanin wannan maganar da kikeyi
in dai ba so kike sai döle kin sa raina ya baci ba?
Shiru nayi bance mishi komai ba, kar ki sake kawo
min irin wannan maganar bana so.
A hankali cikin natsuwa na ce mishi, to kayi
hakuri. Dadi ya kamashi saboda hakurin da na bashi,
ya dan gyara tsayuwa kafin ya ci gaba da magana, shi
baba yana dawowa zanje in same shi da maganar. Na
ce Ubangiji ya dawo da shi lafīya, yayi maza ya ce
amin Maryam.
Kafin babansu Mansur ya dawo wata irin
lafiyaiyar soyaiya mu ka shiga, ka'ida ne kullum sai
ya zo ko da rana ko da daddare, wataran ya zo ya sake
dawowa, in na ce mishi baka riga ka zo ka dazu ya ce
ai wata magana ya tuna da ya manta dazu da ya zo din
bai gaya mini ta ba.
87
Rannan muna hira ni da shi tattaunawa muke yi
irin ta fahimtarjuna, ra'ayinshi yake fada kan irin
tsarin da yake ganin zan gudanar a gidanshi wanda
hakan yake matukar taimakawa ma'aurata bayan an yi
aure.
Kin fa san 'yan uwane da ni masu yawa ina fata
zaki yi hakurin zamada su. Na yi murmushi na ce,
insha Allahu. Can cikin zuciyata kuwa tunani nake yi
ni da nake rayuwa cikin kewar 'yan uwan miji zasu
isheni har in kasa yin hakuri da su? To kuma ba zan
barki yin aiki ba don kar ki ji ina cewa za ki koma
makaranta don ki samu takardarki ki yi tunanin ko har
da aiki cikin lissafin nawa.
Na yi murmusih na ce nima ban damu da yin aiki
ba amma cikin zuciyata ina sha'awar yin sana'a, da
sauri ya ce wonderful tamkar ace kin shiga
zuciyatakin gani ai ni mai sha'awar taimakon mace
yin sana'a ne, Maryamu ina son ganin matata ta tsaya
da kafafunta tana dogaro da kanta saboda karki samu
damuwa akan wannan wacce irins ana'a kike son yi?
Na ce a'a ban sani ba tukunna ni dai kawai cikin
zuciyata ina son yi amma ban zabi wacce zanyi bal to
ai kin gani ma shi kenan sai in duba in ga abinda zaifi
dacewa da ke ina ganin ma kawai dinki za ki yi domin
shi ya fi bani sha'awa ko kuwa? Na ce mishi to.
Tun ranar da Mubarak ya zo gidanmu ya rokeni
alfarmar fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba
88
ya dauki mataki in ya ganni bei kulani ko yana fara'a
ya hangoni sai ya yi maza ya tsuke fuska, a zuciyata
na ce nima gara irin haka, abu guda daya dai da na
kasa fahimta ko dalilin yin shi shi ne wunin da
Isiyaku yake yi kan dakalin kusa da gidanmu a zaune
bana dai ko amsa gaisuwarshi balle-wani abu ya
hadamu tunda kowa ya san dan gidan Mubarak don
haka na kara kiyaye mu'amala da shi don Mansur ya
kara samun kwanciyar hankali.
Ni da Mansur muka zama bamu da wani fata ko
buri sai na jiran dawowar babanshi daga tafiyar da ya
yi. Mansur dak ullum yake ce min ai kawai kwana
daya zan yi mishi in ya dawo da rana in barshi ya
kwana ya wayi gari kafin inje mishi da maganar. Sai
gashi baban Mansur ya dawo har ya kwana bakwai
babu wani motsi ko yunkuri daga gidan nasu shi da
kanshi ma sai nake ganin shi tamkar a sanyaye yake
ban dai ce mishi komai ba tunda dama can ba ni ce
mai zumudin maganar ba ni yar tawa ce.
Wurin baba Lantana mai yade maganganu a
tsakar gida na samu labarin wai ashe da baban nashi
ya dawo ya kai mishi maganar sai ya ce mishi ba zai
sake takowa ya zo wurin babana kan maganar aurena
ba ya dai zuwanf arko ya kuma isheshi haka don haka
in har auren yake so da gaske to ga 'yan mata nan bila
adadin tun daga na dangi har bare yaje ya duba gida
na mutunci ya zabi yarinya zai tsaya ya aura mishi ita
89
ko da kuwa nawa zai kashe, amma bani ba in ba
rashin hankali irin nashi ba ko iyayen Mubarak da
suka san da dansu na rinka lalacewa ai ba su bar shi
ya aureni ba balle shi.
Wannan bayanin da naji a bakin baba Lantana ba
Raramin dukan zuciyata yayi ba, don kuwan a riga na
Sakankance na saki jiki zuciyata ta riga ta amince da
maganar aurena da Mansur sai dai duk da haka ban
bari yanayin da na sanu kaina a ciki ya baiyana ba
sabdoa na riga na koyi shanye bacin rai ba komai ya
taba zuciyarka sai na kusa da kai ya gane ba, haka nan
6acin ran da na samu bai sa naji haushin iyayen
Mansur ba to balle kuma shi Mansur din da na
tabbatar shima bai ji dadin hukuncin da aka zartar
mishi ba, sai dai ya yi biyaiya kamar yanda kowane
da na kirki yake yiwa iyayenshi biyaiya kan umarni
ko hani da sukayi mishi, bai dai ce min komai ba
nima kuma bance mishi na ji ba sai dai kuma biri yayi
kama da mutum gaba daya ya canza fara'arshi,
kuzarinshi duk sun sauya mainakon zuwa kullum ya
koma yin fashi in yau ya zo gobe ba zai zo ba
watarana ya yi kwanaki na yi kamar in ya zo in rinka
kin fita sai kuma na ga to a na me?
Rannan dai ya gaji shi da kanshi ya zaunar da ni
ya yi min bayanin komai, hakuri mai yawa ya bani ya
kuma rokeni kan kar gaya min gaskiyar da ya yi ya
kawo karshen mutuncni dake tsakaninma, na ce
90
mishi a'a ko kadan ba za a yi haka ba sai dai ma a
kara nima nayi mishi godiya kan alherinshi a gareni.
Ko ban tsaya yin bayani nayi bacin rai ko ban yi
ba an san nayi saboda na riga na so aure na kuma soo
Mansur don haka fadama batawa ne kawai.
Tunda Mubarak ya taso ya zo gidanmu ya rokeni
in fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba na
Tura al'amura sun sauya a tsakanina da shi amma ban
kara sanin irin tsananta da lamarin yayi ba sai a ranar
da nayi shiri da niyyar zuwa gidan Yakumbo Halima
saboda dadewar da nayi banje ba har na samu labarin
korafinta wajen yaya Dija.
'Yar madaidaiciyar kwalliya nayi a dalilin tsala
kwalliyar ta daina burgeni ta daina sanyani nishadin
da ta saba sanyani a baya sai dai kuma bai hana
kwalliyar tawa zamowa mai ban sha' awa ba.
Ina tafiya cikin natsuwa ba tare da na damu da
kallo ko sanin su wa nake wucewa bisa hanya ba har
na kai ga shiga lungund a fi ta daga cikinshi zan bulla
kan layin da gidan su Yakumbo Halima yake.
Kasancewar lungun a matse yake gashi kuma da
.yawan kwata 'yar hanyar da ake bi din ba wata mai
fadi bane ya sani hi hanyar waiwayawa in ga wanda
ke biye da ni yana taku cikin sauri dan in kauce mishi
in bashi hanya ya wuce in har naga alamar akwai
bukatar hakan, abin mamaki Mubarak na gani gabana
ya yi mummunan faduwa bisa dalilin guda biyu dalili
91
na farko shi ne faduwargaban da na saba samu a duk
lokacin da na ganshi ko na ji nmuryarshi wanda
kwanakin baya nakem urnar na rabu da shi to ya sake
dawowa, daliil na biyu kuma shi ne mummunan
kallon da ya tsiri yi min a tsakanin nan ko yana
walwala ya hangoni sai ya yi maza ya daure fuskaw
ani irin daurewa kuma mai tsanani.
Na maida kaina kan hanyada nufin ci gaba da
tafiyata, yayin da wani 6angare na zuciyata yake bani
shawarar in karta kawai da gudu don in samu in yi
nesa da shi tunda ga dukkan alamu zai kamoni saboda
dogon taku: da yake amfani a tafiyar ta shi.
Tsaya mana mu yi magana, na yi kamar ban ji
abinda ya ce ba na ci gaba da tafiyata sai kawai na ji
caraf ya kamo gyalena ya rike, ina yi miki magana
kina ji nakina tafiya.
Raina a bace saboda fusatar da nayi na rike min
gyalena na juya da nufin yi mishi tuni kan hana shi yi
min hakan da na taba yi in da hali ma in yi mishi tuni
cikin tsiwa den kar gobe ya yi tunanin sakewa.
Muna hada ido da shi gabana ya sake faduwa na
yi maza na sunkuyar da kaina kasa saboda wani irin
kallo da yake yi min wanda ban saba da shi ba.
Kina nufin ko saurarona ba ki da lokacin yi da
pake kiranki kina ji na? So nake in tambayeki yaya
naji maganar aurenki da.masoyin naki tayi sanyi
kamar ma babu ita? Sakarya kawai sokuwa mara
92
wayo wacce rashin mafadi ya hanata sanin abinda ya
kamace ta in taso in zo in rokeki ki fita hanyar shi ki
ce min wai ba za ki yi ba? Ai nayi hakan ne don ina
zaton ina da matsayi a wurinki saboda kin yaudareni
kin yi min abinda na yi zaton ni din daban ne a
wurinki sabdoa kin yaudareni kin yi min alheri wanda
na yi zaton bani da abokin gami a wurinki, ashe ba
haka bane to amma kuma na gode shi da akayi mishi
hani a kanki ya hanu.
Gabana sai harbawa cikin sauri yake yi, bakaken
maganganunshi sun yi tsanani da nauyi cikin zuciyata
kokari mai yawa nayi kafin na danne hawayen da ke
shirin zubowa a idanuna na hanasu zuba don kar in yi
kuka a gabanshi don haka najuya da nufin ci gaba da
tafiya, sai naji ya ce, ni babu inda za ki sai kin bani
amsar tambayar da na yi miki.
Cikin natsuwa na bude baki wanda bai ma san
zan bashi amsa ba dan ya san ban cika yin hakan da
shi ba na ce mishi, kayi hakuri ba yaudara ya sani yi
maka hakan ba kuskure ne.
Ya yi maza ya gyara tsayuwa tare da kara tsareni
da idanuwanshi cikin saurarona binda zai kara fitowaa
daga bakin nawa, ni kuwa ban fasa ba na ci gaba da yi
mishi bayani, kuskure na yi nayi maka abinda na yi
makan wanda ya sanyaka yin tunanin kana da matsayi
na daban a wurina da har zaka ganni a masoyina ka
roki alfarmar in fita hanyarshi, ko Mansur ya rabu da
93
ni ba zan zamo wani sabon al'amari a wurina ba don
sunnar magabata ya bi zan kumaci gaba da
girmamashi tare da soyaiyar da muka yi wa juna
saboda mun yi ta mun gama ta ba tare da ta yi min
wani sanadi na wulakanci ko tozarta ba a wurin
jama'a, na kuma gode maka da baka yi amfani da
kuskurena da wautata da sakarcina da sokoncin da na
rayu a ciki a dalilin bani da mafadi ya sani nayi a
kanka ba da ka yi amfani da damar da wadancan
abubuwan suka sanyani na baka a