Showing 15001 words to 18000 words out of 36183 words
shawarar da zan baki ita ce ki fidda shi a
cikin ranki fito da miji kawai ki yi aurennki ga
Mansur.
Na yi maza na katseta ta hanyar fadin kai
Mansur? A'a ni yanzu bana son kowa. Ta sake zuba
min ido saboda Mubarak da iyayenshi sun ki mu shi
ne shima Mansur laifin zai shafeni, ai in ban manta ba
a nan ne mukayi maganar nan da ke cewar da Mansur
din da kuma Mbarak rdukansu daya ne wanda duk
maganar aurent a kama za a yi da shi, to ba za ki samu
mas'ala ba za ki zauna lafiya da shi za kuma ki yi
68
mishi biyaiya domin su dukansu biyun masu alheri ne
babu kuma wanda zai iyakacin lokacinki a kanshi.
Nan take nas oma yi mata kuka saboda jin irin
kalaman da ta tsareni da su na baro gide na zo wajenta
don in huta ita kuma ta zo tana yi min wasu
maganganu da suke karawa zuciyata nauyi.
Assalarmu alaikum, wai ana sallama da Mero a
waje. Sau biyu yayi maganar kafin na takarkare na
daka mishi tsawa wanda watakila tsayar da nayi
misHi'ne ya yi dalilin fusatar yaya Dija tayi maza ta
zabura ta mike tsaye ta ce min, maza tashi ki je kiga
waye mai kiran naki ai don Mubarak ya yi aure ba zai
zamo danin karewar maza a duoiya ba, da ke wata
mai zuciya ce ma da tsayawa kikayi kika fidda mijinki
nan da kwata talatin a yi bikinki ki tafi gidan mijinki
kije ki yi zaman aurcnki kowa ya huta.
Na tashi na fito don ba zan iya yin jayaiya da ita
ba.
Mubarak na gani tsaye a kofar gidan tsaye jikin
motar tashi da ga shi har ita sai wani sheki suke yi
suna daukar ido, ga dukkan alamu dai shi Mugbarak
dadinshi kawai yake ji bai da wata mas'ala a tarc da
shi, wanna shi ne abin da yafi komai bata miu rai
wato ni ce mai damuwa, ni ce a cikin bakin ciki, ni ce
rashin zuciya ya hanani samawa kaina zaman lafiya
da kwanciyar hankali, ina ma dai ace nima halina irin
na yaya Dija ne?... saurayi na yi na katse tunanin
69
nawa saboda ganin ya nufoni zai zo in da nake tsaye,
nayi maza najuya zan shiga gida, caraf naji ya kama
gyalen da nake rataye da shi ya rike, abinda ya yi
dalilin tsayawata.
Kina ganin kamar kin tsayawar da za ki yi ki
saurareni yana da wani abin da zai amfanar da ke ne?
Ni da ke ai muna bukatar fuskantar juna ne don
musan abinda muke ciki.
Kaina a sunkuye saboda nauyin shi da nake ji, muryata tana rawa alamar idanuwana suna shirin zubar
da hawaye na ce mishi, sake min gyalena bana so kar
kuma ka sake yi min haka bana so. Da sauri ya sake
min gyalen nawa, ban tsaya sake sauraron komai ba
na yi maza nas hige cikin gida na barshi nan wurin a
tsaye, maimakon in tsaya wurin yaya Dija tunda har
lokacin tana zaune a inda na barta wucewa nayi naje
can cikin dakinta na hau gadonta na kwanta ina kuka,
na kaska gane dalili, na kasa gane al'amarina, na kasa
fahimtar yanda za a yi in zama jarumar kaina in fita
hanyar Mubarak in daina ganinshi ina jin wani abu
ganie da shi, na zafi ko ciwo ko faduwar gaba a cikin
raina.
Ina kwance ina yin kukan yaya Dija ta shigo ta
sameni, nayi zaton wani fadan zata sake yi min sai na
ji ta ce min, ki yi hakuri Maryamu wani loakci zaozi
da ke da kanki za ki gane ba Mubarak ne mijin da ya
dace da aurenki ba, mijin da baya rarrashima me za a
70
yi da shi ne? Ke kanii kika ce min bai iya ramashiba,
bai iya bada lakuri ba, bai iya fadin naganganun
soyaiya ba, to ai Mansur ya iya wadannan duka yana
kuma sonki domin ko bayan aukuwar wadannan
al'amuran ya zo gidan nan sau biyu yanzu ma don
baya nan ne yasa kika ga shiru, to don me za ki damu
kanki, akan mutanen da suka ki mu? Kin mu fa suka
yi sun kimu ne saboda sun rainarmu in ba haka ba
wane irin wulakanci ne haka su zargi lalacewa
tsakaninki da dansu sannan su barki su aura mishi
wata? Wannan wane irin son kai ne wannan? Wannan
wane irin rashina dalci suka yi mana? Bana sonsu,
bana son dansu, bana son duk wani abin da ya
shafesu.
Tana fadin maganar tana kuka, nima kuma ina
kara jin tsanar Mubarak da iyayerishi da duk wani
abinda ya shafeshi cikin raina.
Assalamu alaikum, wai a gayawa yaya Dija tanna
da bako a waje. Sau biyu yaron yana shigowa yana
fadin irin wann an maganar a tsakar gida, tana jinshi
bata tanka mishi ba.
Yaya Ibrahim ne ya fito daga úakin su yana yi
mata magana, anene bakon na ki da yake wajen?
Mubarak ne kuma bana son ganinshi, Eai yi magana
ba ya fita wajen sai kawai gasu sun shigo tare, falon
yaya Dija ya shigo da shi.
71
Sannu da zuwa Mubarak, ya nuna mishi wuri ta
zauna shima ya zauna suka gaisa sosai har yana
tambayar shi anyi hidima lafiya? Ya amsa lafiya lau
to Ubangiji ya sa alheri a ka hada ya amsa main.
Jin shigowar tashi ya sa yaya Dija ta matsa kusa
da bakin kofar dakin nata ta labe bayan labule suka
gaisa ba tare da sungajuna ba, itarna tayi mishi murnar
auren nashi sai dai ita kam bai amsa addu'ar da tayi
mishi ba, a hankli cikin natsuwa ya soma yn amgana
wanda yake kamar dama ya samu na gaya musu
abinda ke ranshi watakila don ya wanke kanshi.
Mafi yawancin lokaci mutum yana shiga cikin
wani irin al'amari da bai taba zatarwa kanshi ba,
al amuran da suka faru a cikin watannin nan uku
zuwa hudu da suka wuce wadansu irin abubuwa ne da
babu wani abin da zamu ce sai dai mu kara hakuri mu
kara yarda da cewar komai yana tafiya ne bisa tsari da
rubutun kaddarar da take keddara mana komai.
Yaya Ibrahim ya ce, haka ne, sai ya ci gaba da
magana, ni dai gaskiya a Bangarena na shiga wani irin
al 'amarin a kunci da damuwa, gami da bakin ciki da
tsanani irin wanda bana fatan wani wanda ban sanshi
ba ma ya samu kanshi a irin wanonan yanayin, duk
wata fitina ina ganin kanar tana da sauki kwarai in
har ta zamo babu fushin iyaye a ciki.
Da sauri yaya Ibrahim ya ce mishi, kwarai kuwa
fushin iyaye ai musiba ce mai hankali kuma baya
72
yarda ya zauna a irin wannan yanayin domin kullum
fata muke mu rabu da su lafiya suna sanya mana
albarka.
Maganar da yaya Ibrahim ya yi ta zama tamkar
susa ya yi mishi inda yake yi mishi kaikayi, da sauir
ya ce, yauwa na gode da ka fahimce ni ina fata kuma
itama yaya Dija tayi min irin wannan fahimtar halinda
na samu kaina a ciki na fushin da'mahaifina ya yi da
ni shi ne dalilin da ya sanyani karbar auren da suka ba
ni don in samu in fita daga cikin wannan al'amarin
amma ba yana nufin wani abu zai canza " bane
tsakanina da Maryamu.
Cikin natsuwa naji shima yaya Ibrahim ya soma
yin tashi maganar bayan ya yi gyaran murya, to arna
Ahmadin kayi haka ai ina ganin baka kiyayi bacin ran
iyayen irin kiyayewar da ya kamata ka yi mishi ba, ci
gaba da mu'amala da Maryam kaima kasan ba zai
zamo karbabben abu ba a wurinsu domin rabuwa da
ita yana cikin sharadin da suka sanya maka, ina ganin
maimakon ka dage kan ci gaba da mu'amala da ita har
hakan ya sake jawo maka wata mas'alar tsakaninka da
su da rabuwa da ita kawai kayi tunda ai ka riga kayi
aurenka itama ta fidda miji tayi nata, ina ganin
wannan shi ne abidna zai fiye mana sauki domina
I'amura sun riga sun faru marasa dadi masu bata rai
da tayar da hankali, ya kamata ace mu dukan mu mu
kiyaye sake aukuwarsu, don haka ina so in yi amfani
73
da wannan zaman namu in rokeka ka fita hanyar
Mero ka daina bibiyarta ka barta ta samu natsuwa da
kwanciyar hankalin da zata fuskanci al'amarin ta,
kaima ka samu natsuwa tare da iyalinka don ka samu
zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da iyayenka.
To amma yaya Ibrahim kana nufin don na kar6i
auren da iyayena suka yi min sai hakan ya zama
dlailind a ni kuma ba zan yiwa kaina nawa auren ba?
Eh haka zaka iya yiwa kanka, bance ba zaka iya
ba to amma kuma gaskiya ba Mero bace wannanm
atar domin mun riga mun samu labarin komai don
haka ina so in gaya maka cewar na rokeka ka fita
hanyarta kawai. Ya ce to babu laifi na gode. Ya yi
musu sallama ya mike ya fita.
Yana fita daga gidan yaya Ibrahim yakirani din
na zauna cikin ladabi ina sauraronshi, kin ji yanda
muka yi da Ahmad, na ce mishi ch, ya ce to ki fitar da
miji ki yi aure kinji ko baki ji ba? Na ce mishi naji,
zai fitar ko ba zaki fitar ba? Na sake cewa zan fitar.
Ya ji dadin yanayin da na bashi amsa r a ciki, to
Ubangiji ya yi miki albarka, na ce amin.
Ya tashi da nufin fita yana magana, dagan an
zuwa rana itayau ina so in ji bayani wurin Dija, na ce
mishi to.
Da daddare rannan ina kwance kan gadon yaya
Dija yayin da ita kuma take wurin mijinta bacci ne
yaki daukata na rasa abinda ke yi min dadi, cikin
74
raina na sani ni da kaina na gayawa yaya Dija cewar
da Mubarak din da kuma Mansur duk daya ne wanda
duk aka bani zan zauna da shi, amma a yau sai na
kasa jin irin kuzarinda nake tare da shi a wannan
lokacin da nayi wancan maganar, gaba daya dai halin
da nake ciki nayi jarumtakar daina hana kaina yarda
da cewar son Mubarak ne yake haddasa min abubuwa
da nake fama da su na faduwar gaba da kauracewar
bacci a idona, na yarda da cewar bacin rai ne na
wulakanci da tozartawar da aka taru aka yi min.
Washegari da safe ina kicn ina kokarin sallamar
ya'yan yaya Dija su tafi makaranta saboda bata fito
ba a dalilin ta san ina gidan, ina cikin aikina sai kawai
na jiwo muryar matar wan yaya lbrahim tana cewa
wata da ban sheda ta ta muryar ba, lalle ne su hadu su
je wajen uwar mijinsu su kai karar yaya Dija kan
neman da take yi ta jawo ni ta dawo da ni nan gidan
da zama bayan duk abin kunyar da na akata na
jawowa iyayena da yan uwana abin magana, tana
nema sai tayi dalilin da na shafa m usu na bata musu
sunan gidansu, in mu bamu damu da abin kunya abin
magana ba saboda bamu da yawa ba wasu dangi ne da
mu ba ai su nan gidan dole su ji tsoron abin kunya ko
don yawansu.
Ko kadan ban ji dadin maganganun da na ji ba to
amma kuma sai na kudurawa raina kame bakina in yi
shiru ba tare da na gayawa yaya Dija abinda naji ba,
75
iyaka dai kawai in hanzarta barin gidan in koma namu
tun ban haddasam ata wata fitina ba, don nasan in taji
ba zata yarda ba aurenta kuma aure ne da bashi da
wani tarihi na wata fitina mai karfi sai danabin da ba
za a rasa ba, kawai wanda zo mu zauna zo mu saba ke
haddasawa musamman ma kuma da yake kusan a
hade suke da iyaye da 'yan uwa a wuri daya, ginin da
yayi baisa ya yi nesa da su ba don haka ina gama
aiyukan da zanyi mata sai kawai na yi shirina na jira
ta fito nace mata za ni gida, tayi ta tambayata menene
ban ce mata zan kwana biyu ba? Nace mata eh amma
ai na fasa saboda zan bar baba shi kadai a gida.
Ta gallamin harara, baba shi kadai m atarshi fa?
An ce miki zaki yi ta zaman gida ne saboda baba?
Kema zaki yi aurenki.
Nayi dariya kawai na kama hanya na tafi.
A gida ina zaune ne kawai bana komai bana
kuma zuwa ko ina, ba makarantarboko babu ta allo,
bana kuma fita ko ina ko daidai al'amura sun dan lafa
na wakoki da rashe-rashen mutuncin da akayi tayi
min a baya, na dan samu sauki na dan samu saukin
ciwon da zuciyata take yi min a kan Mubarak saboda
na daina yarda ina zama in bata lokaci wajan tunanin
al'amufanshi, ina kuma kiyaye duk wani abin da zai
hadani da shi ko da kuwa hango ni daga nesa tunda
asan har yanzu ban samo maganin faduwar gaban da
76
nake fama da shi ba a duk lokacin da' na hangoshi ko
na ji maganarshi.
A cikin gida dai ni da su baba Lantana muna
cikin wani hali ga babu ga kuma rashin dadin zama
komai a tsaye yake cak, bani da komai nå abin amfani
ba ni kuma da ko kwandala, rabon da in yi rashin irin
wannan har na manta. Watakila tun ban isa komai ba
tunda in ma ban samu an yi min a gida ba to dai bana
rasawa zan samu wurin Mubarak ko Umamnshi, to
yanzu babu su baban nawa kuma ba shi da shi, ta
lafiyar shi ma ake yi bata maganar runfa ba don ma
anyi sa'a Sallau yana matukar taimakawa a kan bude
rumfar babana yana cikin wani hali na rasa karfi mai
yawa a tare da shi, a hakan kumna wai baba Lantana
bata tausaya mishi a bata dai a bata kawai ta sani ko
da kuwa babu abinda take so a baka din kusan kullum
zaka sameshi ne cikin jiri ko ciwon kai, amma hakan
baya hanata zama tayi ta gaya mishi bakaken maganganu ni kam ma sai nake ganin tamkar
karbem ata fili da Alhaji Nalami yayi ba kairamin kara
mata son kudi da neman tashin hankali yayi ba.
Rannan ina jinta ita da Sallau da ya dawo daga
runfa in da ya danyi aiki, bani kudin nan duka nace
maka ka bani su, a'a baba in na baki su dukan gobe
fa? A ci yau a ci gobe ai shine cin rana daya,
kumburin ciki ne. Nace maka ka bani su, ina ce dai
rumfar bata gidanku ba ce? Cikin natsuwa ya ce mata,
77
eh baba bata gidanmu bace amma shi mai rumfar ai
bai nuna min hakan ba don haka zan tattala mishi
abinda yake ciki ko na samu nima in koyi sana'ar
tunda dai ke baki kaini makaranta ba baki kai ni
wajen koyon sana'a ba.
Ina daga kwance ina jinsu ko motsawa banyi ba,
cikin zuciyata na co kunfi kusa in kuka ga dama kuc
inye su duka a yanzu.
Ganewar da nayi Sallau da iyakacin gaskiyarshi
yake mu' amala da baba na yasa nima ko kadan bana
sa mishi ido kan cinikin da yake yi komai yace min
kuma sai ince mishi to, bana dai sake mishi sosai don
haka sai muka koma m u'amala ta matunci kawai da
ganin girmanjuna, a wannan lokacin babu abinda yafi
tsayamin a ai irin in kwanta da daddare in tuna gobe
da safe bani da kudin da zan sayawa babana abin
karyawa gashi a yanzu baba Lantana sai tayi kwana
da
kwanaki bata yi girki ba, wai abinda ake batan
baya isa a yi girki, na kuma san har da daina yarda da
ayi girki aci ni a hanani da na yi ya kara sata daina
yin girkin.
Kan hakı yasa naje na samu Sallau a rumfar baba
na ce' mishi Sallau. Yayi m aza ya taso, anti Mero ai
da kin jirani a gida ma zan zo. Nace e babu damuwa
so nake mu yi magana. Ya ce to, nayi mishi bayanin
da ya kawo kullum in kayi ciniki ka rinka cire kudin
da zaka rinka saro kayan gobe abinda ya saura ka
78
kasashi biyar kai daya baba daya baba Lantana daya
ni daya, dayan kuwa a rinka sakashi cikin bankin
karfe dake cikin rumfar nan, saboda bacin rana, ya ce
min to.
Yana dawowa kuwa da daddare ya zo ya yi min
bayanin abin da aka yi da yanda ya yi kasafinsu.
Yaya Dija tana iyakacin kokarinta a kan mu sai
dai kuma ita din mata ce da bata iya sana'ar komai ba
duk wani abinda kaga tana yi in dai na kudi ne to
daga aljihun mijinta ya fito ko kuma daga abinda ta
iya tattalawa na canjin cefanenta don haka sai na
kudurawa kaina ba zan taba zama bani da abin yi ba,
ba zan zauna bana sana'a ba, ba zan iya zama sai an
bani ba, zan nemi kudi ko don in yi hidimata da ta
babana ba tare dan a tsaya jiran an bani ba sai dai a
sana'ar ban san wacce zan yi ba.
An wayi gari yau tun asuba zuciyata take ta kai
kawo kan al'amarin Asabe wacce na lura tayi matukar
canzawa duk wani abin da za ta yi ta kan yi shi ne ba
a yanayin da ta saba ba, hatta zamanta da tashinta
amma wai har yanzu baba Lantana tana kallonta bata
gane abinda take ciki ba ko kuma ta ganę tayi shiru ne kawai oho.
Tsawon lokaci ina wannan tunanin kafin na yi
maza na kawar da wannan tunanin na koma kan nawa
al'amarins aboda ganewar da nayi cewar in na tsaya
kan nawa mas'alolin ma kawai sun isheni ba sai naje
79
ina shiga harkar da ba tawa ba ce, don haka na koma
lissafin tawa damuwar gaba daya kayan sakawar baba
sun kare sunyi datti bani da ko sabulun da zanyi mishi
wanki, nmaganin da yake sha yana gab da karewa babu
kudin sayen wani ga zuwa asibitin shima ya zo da dai
ace so shine samu to da na samu wani abinda na
rinkayi ina samuz ko da kwaho kwabo ne don in rinka
aiwatar.mana da abubuwanmu ba komai ya taso sai
naje na gayawa yaya Dija ba.
Gari ya waye da safe nayi abubuwan da na saba
yi mana ni da babana na yau da gobe na kai mishi
ruwan wanka na dawo kenan sai ga yaro dan
makwabta ya shigo, anti Mero wai inji Mansur wai ki
zo.
Na daga ido na kalli yaron yanda ya ambaci
sunan Mansur din gatsu bai yi min dadi ba kamar in
yi mishi magana sai na fasa na kame bakina nayi shiru
cikin zuciyata dai na tabbatarwa kaina da cewar
gimamai na gaba yana da dadi.
Gyalena na dauka na yafe jikina na kama hanyar
fita zuciya'a sai faman harbawa take yi don rabon a
kirani inje har na mance da lissafin. Yana tsaye ne
cikin zauren gidanmu kanshin shi ya gauraye ko ina.
Kunyarshi ta yi matukar kamani na kasa sakewa
a gabanshi saboda sanin da nayi ya ji komai yana da
labarin duk kan abubuwan da aka yi tayi har wakokin
da nayi ta fama da su duk nsan ya jisu, amma hakan
80
bai hanashi zuwa wurin yaya Dija ba gashi kuma yau
a gabana, me yake nufi? Yana nufin har yanzu yana
kan bakanshi bai fasa aurena ba kamar yanda yaya
Dija ta gaya min kome?
Kan in kai karshen tunanin nawa sai naj1 ya ce
min, ran yan mata ya dade ina kwana? A kidime
kwarai na nemi wuri na tsuguna, yan mata yake k
irana bayan tun ba yanzu ba na saba jin mutnae masu
zargi suna fadin ai ni din tun ba yau ba na salwantar
da budurcin nawa, yana ganin an tsuguna shima ya
nemi wuri ya tayani tsugunawa.
A tsarge kwarai na soma amsa mishi gaisuwar
tashi tun bayan faruwar al'amuran da suka farun yau
ne ranar farko