Showing 6001 words to 9000 words out of 36183 words

Chapter 3 - Halin Rayuwa Book 3 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

205

wai suna shan hantsi su ma
zazzare idanu suke yi nuna alamar yunwar su ke ii
kamar ni tunda a yanzu duk mun zama daya ni babu
su ma babu, yanda nake kaiwa Azahar ban karya ba
haka su ma suke kaiwa har gara nima yunwa bata cika
gigitani ta fitar da ni cikin haiyacina ba don kuwa da
ana sabo ko wani kawance da ita to da na ce munyi ba
a yi ne kawai yasa ba zan fadi hakan ba amma duk da
haka zan iya cewa na saba jinta haka nan a duk
halinda nake ciki bana rasa wani dan canji kulle a
bakin zanina wanda nake dan tsakura ina baiwa
babana abin karyawa in ayso ni in hakura don bana
yarda ya fita su kuwa nasan da kyar ne in suna da
wani abu.
A wannan lokacin a gidanmu rashin yin girki bai
zamo komai ba tunda baba Lantana tana kin yin girki
da gangan yanzu mai dalili ya sameta, kasuwar
babana ta yi kasa jarinshi ya yi matukar karyewa tun
yana kawo mata dan cinikin da yake yi tana rainawa
tayi watsi da su ko tayi ta zage-zage tana tambayarshi
wadanann me za su yi mata har ta hakura ta zuba ido
don ta gane abin bana kare bane tunda kullum raguwa
yake yi sai da ta kai ma tana tambayama ace mata ta
yi hakuri tayi ta maganganu to yanzu babu kawai
yake cewa ya ja bakinshi ya yi shiru ya barta ta fadi
duk abinda take son fada.

30
A wannan lokacin sai ta zama bata da aiki sai na
fushi ko mita ko ka ji ta tana baiwa Asabe labari irin
zaurawan da suka nemeta wai ta kisu ta auri babana
sai ta yi kwafa ta ja tsaki tace, to rabon wahala ni
kuwa sai in kyalkyale da dariya tayi ta zagina, Asabe
tana kallonta bata tsoma baki nima bana cewa komai
baya ga dariyar can cikin zcuiyata ina kiranta da
sunan da na saba jin Alhaji Nalami yana kiranta wato
Butulu.
Muna cikin wannan zaman ne muka ji an kwada
wata irin sallama a kusa da kofar shigowa gida
gabana yayi mmmunan faduwa arnma kuma nasan na
baba Lantana yafí nawa faduwa saboda yanayin da na
gani a tare da ita tun kafin ta kai ga amsa salalmar
tashi sai gashi ya fado tsakar gidan.
In ce ko da ba za a amsa sallamar tawa ba ne? Ta
soma kame-kame tana rantse-rantsen wai bata ji
salalmar tashi ba nan da nan ta shiga yi mishi oyoyo
tana sannu da zuwa cikin sauri ta shiga ta dauko mishi
shimfida tana yi tana, habawa yaya za a yi inji
sallamarka in ki amsawa to a wanne dalili? Ta gyara
zama, yana fadin a dalilin cuta mana aike tsunma ce.
Na mike na soma tsince kayana da suka soma
bushewa na wuce na nufi dakina cikin zuciyata ina
kokarin danne dariyar rawanin da naga yayi wanda
yafi kama da na waziri aku.

31
Rawani kuma Alhaji ya koma yi? Tayi tambayar
cikin yanayin sakin füska da fara'a, ko an baka wata
yar sarauta ne ban šani ba Alhaji Muhammadu? Ta
sake janshi da watą rahar.
Ya kara tsuke fuska saboda watakila fara'ar tata
ta yi mishi yawa, kinga bana son irin sunayen da kike
kakabg min ni, naje Makka*ne da kike ce min sunana
Muhammądu? Nalami kawai sunana kenans hi na fi
so shi nafi sani.
Ta yi murmushi Alhaji ai sunan mai niyya ne
bana wanda ya je bane, Muhammadu kuwa ai sunan
maza ne menene aibi don an kiraka da shi tunda
Nalami ai ba sunan gaskiya ba ne.
To ni shi nafi so da shi aka yanka min ragon suna
ko sai ace bai yanku ba? Ta ce ya yanku, ya ce to ni
ba ma wannan ne ya kawoni ba. To ka cire rawanin
naka mana ka sha iska. Ya yi maza ya ce na ki din in
cire yaran unguwarku da basu da tarbiya su hangoni
su zo su kara sani ko? Ko da yake an gaya min cewar
ke kika biyasu kika ce musu su kasheni in nazo wurin
daurin auren to ta Allah ba taki ba gani nan daramin
gabanki da raina da lafiyata.
Da sauri ta tambayeshi ni? Insa a kasheka ake
wane dalili? A dalilin dukiyata da kika karba man
tunda ai an gaya min komai ba kudina ni kadan kika
ci ba, tayi murmushi, wanda ya gaya makan bai gaya
32
ma kag gaskiya ba, niikam ai ina nan a kan bakana
tunda dai kaima ka.ganta da idoka tana nan ba...
.Ba ta karasa ba ya ji maza ya ce ma ce a'a bana
so ina? Ai wautar tawa ba ta kai haka ba ai ni kuma
kin, sanni ba a cutata: sau biyu ko da yake dai ke
zatiddawahice ko gamsheka bata kaiki sharri ba wato
in sake dawowa da sunan karbar aure don ki samu su
karasani ko tunda burinki bai gama cika ba a kaina to
naki bana son auren shiga kawai ki fito mirn da abinda
kika sani nawa sauri nake yi.
Ban san yarıda akayi ba naji baba Lantana ta rage
murya, tayi wata magana sai dai kuma shi bai rage
muryar ba wajen bata amsa don haka na gane abinda
ta ce mishi.
Asabe kuma? In zo in auri Asabe to a kan me? Ai
dai kasan ba finta komai tayi ba tunda ita Asabe ma
ga kirji a cike ga mazaunai ga diri ita wannan ai haka
singul take tsawo ne kawai kamar sanda. Ya yi tsaki
ya ce ai duk a banza gara ma singul din ita Asabe in
ita nake so ai 1asan inda zan sanieta bani kudina
akwai.
Ranta ya 6aci da jin maganar tashi cikin yanayin
fusata sai ta ce mishi karfa ka ce zaka yi min
wulakanci ina binka cikin sauki kana sake baki kana
caba min ma gana da wasu labbanka masu kama da
saukan markade nawa ne kudin naka?

33
Ya gyada kai una alamar gamsuwa da jin
maganar ta ta cikin natsuwa ya ce basu da yawa kawo
min su in tafi in bar miki gidanli jaka bakwai ne.
In banda baba Lantana a zaune take sanda ya
ambaci jaka bakwai din nan watakila da ta fadi kasa
warwas saboda tsananin kadirwar da tayi, a'a jaka
dari zaka ce ba jaka bakwai ba in ka tsaya a jaka
balkwai ma ai sharrinka bai kai sharri ba la'anannen
tsoho kawai matsiyaci da ma abidna ya sa ka zo kace
in baka ita kenan don ka samu damar kullamin sharrin
daka dade kana son kullamin? To bani da su ban ma
san su ba. Nan take kuma ta soma rusa wani irin kuka.
Ban yi mamakin ganin gigicewar baba Lantana
kan ambaton kudin da Alhaji Nalami ya yi ba saboda
a wancan loakcin jaka bakwai din ba karamin kudi
bane kudi ne da ake iya siyen gida da su kudi ne da
akc iya biyan aikin haji da su har aje a karbi guzuri
na zunzurutun kudi dalar Amcrica dubu daya a can
kasa mai tsarki, haka nan ko da ban san abinda yake
tsakanin baba Lantana da Albaji Nalami a kan
maganar kudi ba to nasan shi Nalami zaiyi wuya
warai in yana da kudin da suka kai jaka bakwai balle
ya iya bada su saboda bai da kamannin wanda ya
mallaki irin wadannan kudaden.
Yanzu nan banda fam hamsin dinika guda uku da
ka bani ka taba kawo wani abu bayan nan ka bani?
Sai da ya kara juya mata keya kafin ya ce, fam

34
hamsin hamsin sau uku wasa ne? Tunda kika ambanci
wadannan da bakinki ai sauranma zaki fito da su ai
kin yi kokari ni kam ma ai duka nayi za ki ce ban
taba baki komai ba küma in ma iyakar abinda na baki
kenan to zaman nawa sukayi a wurinki? Da a wurina
suke ina ta juya abina da yanza nawa suka zanma?
Sannan dukan tsiya da kiką sa aka yi min fa? A nawa
dukan yake? Nawa kuma na kashe wajen yin jinyar
kaina? Dankwala dankwalan kajin da na rinka
sayowa ina kawo muku kuna ci ke da mijinii da su
lemon gongoni da na kwalaye fa? Su a nawa suke?
Ko kina nufin za ku ci bulus ne? Sannan kwana nawa
nayi ban fita kasuwa ba a dalilin jinayr? Zan dau asara
ne? Ai kema kin san riba nafi ganewa ba na fahimtar
asara.
A fusace ta ce mishi to asara kam sau nawa kayi
ta a rayuwarka? Babbar sana'arka fa daudu ne? Yayi
maza ya ce yaurwa ga kudin kulla sharri da bata suna
ai hada lissafni koami nayi n8 rattaba wuri daya don
haka ki bani kudina tun muna sheda juna dake cikin
mutunci tun bamu kai ga wulakanta juna a bainar
jama'a ba don ba zai zamomin komai ba in kai
maganar gaban alkali in kira masu sheadr zur mu yi
lada da su su je su yi rantsuwa su yi min sheda gaban
alkali ya karfar min kudina in biyasu ke ni na yarda
ma in bar musu kudin duka su cinye zaifi min dadi
akan ace na bar miki su.

35
Fita min daga gida fita tun ban kira yara sun zo
Sun nada maka dukan tsiya ba, tayi maganar cikin
wani yanayi dake kara baiyanar da tsananin bacin
ranta.
Ya yi murmushi to ai gara ki hanzarta yin hakan
kinga inda sai na tafi neman shedar zur kafin in samu
biyan bukata a kotu sai ya zamo ba sai na yi hacan ba
zan samu don hakan zan sake gaya mikiki bani kudina
da na gaya miki jaka bakwai ko kin san tunda na
ambacesu zan karbesu ai kin sanni sarai nima na sanki
ni dake kar ta san kar ne kin san abinda zan iya da,
Wanda ba zan 1ya ba, ya rantse da kwarankwatsa da
aradud a matsattsaku in baki bani kudin nan ba, Ya
gyada kai nuna alamar wani babban abu zai auku ko
yanzu din nan in gaya niki babu fa inda zani sai kin
bani don ba zai zame min komai ba in kwana a kan
gadon da mijinki ke kwanciya irin kuma tsakaninku
bari ma ki gani. Yayi maza yu mike ya nufi hanyar
shiga dakinta itama tayi maza ta sunkuci tabarya taje
gabanshi ta tsaya.
Kasheni kenan za i yi da kika sunkuto wannan
shirgegiyar tabaryar kamar za ki kashe maciji.
Ai gara maciji da kai Nalami ai kai tsohon banza
ne tsohon najadu wanda ya tsuta bai san ya tsufa ba
kullum kai kenan kana riga fuska da jiki da shuri don
na kashcka ai babu abin da zai faru shigowa kayi
cikin gidana wadanda suka sanka kuma sun san

36
mugun iri aka rage shiga dakin ka grni yanzu in ba
nuna maka kai din lalataccen tsoho bane matsiyaci.
Cikin duk zagin da baba Lantaria tayi msihi Da
lura babu abinda yafi tsaya mishi a rai irin cwar da
tayi mishi lalataccen tsoho don abinda yafi nanatawa
kenan, ni ne lalataccen tsohon? Wato ni ne tsohon
kuma ma lalatacce? Yanzu nan ni tsoho ne? Tayi
amza ta ce na banza ma kuwa.
Ganin da yayi ta fara yi mishi cin mutunci irin
wanda bai zata ba ya sa shi hamzarin fara
kudundumarta yana rantse ranste saukin abin ma shi
ne yana jin tsoron daga murya don gani yake tamkar
in yaran unguwa suka gane shi ne zasu shigo su
sameshi anan din sa karasa aikin da suka fara, amma
duk da haka sai da suka kacame suka haura sama suka
sauko sai kuma na ji su suna daidaitawa a kan yanda
zasu y1 su warware lamarin a tsakaninsu ba tare da
wasu sun ji maganar ba da kanshi ya ce ya yi mata
ragin jaka biyu ta nemi biyar ta ajiye mishi amma
babu sauki a haka don kar ta ga ya yi mata sassauci ta
dauka ko tsoro ne yana dai so ne kawai su rabu lafiya
saboda darajar tsohuwar sanaiya ba a san inda za a
sake haduwa ba.
Kai kam bana fita in sake haduwa da kai a ko ina
har abada kuma.
Ya ce to ai shi kenan ni kam ai duk mutumin da
na sani bana yardamu yi rabuwar banza ni dea shi don

37
ban san abin da gobe azta haifar ba a tsakaninmu na
tafi zan dawo bayan wkana. bakwai ina fata in zo in
samu kudina a ajiye. Bai jira amsar ta ba ya sa hannu
ya gyara rawaninshi ya sa kai ya fita ya bar gidan.
Yana fita daga gidan yanayin baba Lantana ya
sake canzawa kana ganinta zaka gane ta tsunduma
cikin wani irin al'amari da ita kadai ta san abinda take
ji maimakon ta ja bikinta ta yi shiru ko don ta huta
gajiyar cacar bakin da sukayi tayi dana Nalmi sai
kuma ta shiga kurme kurmcn asahar da isine tsine
wanda yawanci ni take yiwa.
Wannan tsinannen aure da me ya yi kama? Haka
kawai ni banci nanin ba nanin zata ci ni, jalka biyar?
To jaka biyar ina na ganta/ ta sake rushewa da wani
sabon kukan.
Watakila Sallau ya gaji ne da ji ko ganin abinda
ke taf aruwa ya sa shi buda bakinshi ya ce mata to
wannan abin duka baba ai ke ika jawa kanki in ba
haka ba yaushe ake haka ba fa ke kika haifi yarinyar
nan ba da ya ce ki bashi ita ai sai ki gaya mishi ba taki
bace, amma ba ki yi haka ba sai kika je kina ci mishi
kudinshi kina shirya yanda za a yi a bashi ita ba tare
da kin nemi hadin kan ta ba, ita gaskiya ai guda daya
ce daga kinta kuma ance sai 6ata, mai kwadayi kuma
kowa ya san yana tare da wulakanci yanzu wannan
jaka biyar din....

38
Ban ji karshen zancen ba sai ca ji saukas mari
mai karfi kau, bai sake cewa koami ba haka nan
itama.
Washegari da safe babana ya yi shiri zai fita
kasuwar timatirinshi nima na yi maza ne zo na tareshi
da abin karyawar shi dana shirya misali wanda kunu
ne kawai sai yan kosan da basu da wani yawa a
dalilin ina tattalin kudin da ke wurin nawa saboda sun
kusa karewa ban kuma hango wata hanya ta zuwan
wasu ba sai dai addu'a kawai da nake tayi na neman
rufin asiri wurin Ubangiji.
Yaya nake ganinka wani iri hak baba? Nayi
mishi tambayar saboda yanayin dana gani a tare da shi.
Jikin nawa ne bana jin dadinshi bani da keri ina
kuma ganin wasu abubuwa kamar 'ya'yan sama suka yi min yawo a idona.
Ya'y,an rana suna yawo baba be jinin ne yah au
ba? Shi ne ba zaka gaya min ba zaika kama ita a
haka? Na soma yi mishi kuka sosai, a'a to menene in
na fi tan'? Na kalleshi kafin na ce mishi to baba amma
in kaje kasuwa kaje ka fadi fa? Ai ka bar fitar kawai
ka shiga daki ka yi kwanciyarka in kaji sauki gobe si
ka je. Bai yi magana ba na dauke kwandon tumatirin
nashi naje na adana, ya yi min magana a hankali, to in
na kwanta me za a ci a gidan ne'?

39
Tana daga daki tayi maza, yauwa gara dai kai da
kanka ka yi mata wannan tambayar ta baka amsar.
Nayi kaar ban jita ba-na ce, to in babu abinci a gida
baba sai kaje kana jiri a cikin m utnae kana faduwva
suna kwasokasuna kawoka gida? Lafiyar ka bata fiye
mana komai ba? Na soma uke, saboda yawan ciwon
nashi yana daga min hankali, loakcin da kake da shiai
Ciyar da wanda ya kamaka dama wanda bai kamaka
ba yanzu kuwa da baka da shi sai kowa ya yi hakuri
wanda ba zai yi ba kuma ya san abinda yake ciki.
Ke na ce ke za ki zage ni ne? Na ce ba zan zage
ki ba amma kuma ba zan barki ki tura min uba cikin
halaka ba ina kallo shekara da shekaru ya yi yana
kawowa don yanzu bai kawo ba kuma babu mai
takura mishi, jeka ka kwanta kaji baba? Tayi maza ta
ce, to ba dai dakina ba don ban ga yanda za a yi
namiji ya kwanta mia a gado zankwankwan ba don
takamar zuciyarshi ta mutu. Na sá hannu na bude
dakin Sallau ya shiga, kwanta kan shimfidar shi, cikin
raina na tabbatar da ma can dole ce kawai zata fitar da
shi amma ba dadi yake ji ba.
Yana kwanciya na sake daukan kwano naje na
sayo waina da miya na kawo mishi yaci ya koshi har
ya rage sannan na kawo magani na bashi kamar yanda
likita ya gaya min in tafiyarshi kalau ya sha sau daya
in da alamar motsawar jiki ya sha sau biyu kafin mnu
zo ganinshi, ya kurkure baki ya gyara ya kwanta nima

40
na dawo dakina a cinye masar da ya ragen na wanke
kwanon na kife kafin naci gaba da harkokina.
Ina dakina a kwance ina sauraron farkawar
babana sai na jiwo baba Lantana tana kiran Sallau da
sabe wai suje su karfbi abincisu ta gama girki na tashi
naje na dauki kwano na kai mata a zubawa babana a
nan in kai mishi nashi.
Wani irin lalataccen kallo tayi min kafin ta ce
min yana daga kwancen ne zan rinka yin girki ina
bashi yana kalmasa baki yana lamushewa? Ba ya ce
bashi da lafiya ba mai ciwo yana cin abinci ne? Na
zuba mata ido cikin tsananin mamakin kalaman nata
kafin ince mata komai sai ta ci gaba ai ba nice zan
ciyar miki da shi ba ban yi miki wannan alkawarin ba
duk ran da kika sashi ya kwanta a gida yaki zuwa
kasuwa toni kuma babu shi a abinci na kin ganima
don ki kara sanin banyi dashi ba kin ga barkono ga
farin magi ga gishiri duk a ciki na zuba in kuma ke ce
za ki fake da shi ki ci to banyi niya ba ni ba baiwarki
ba ce in kin kallem kuma za ki gane ni ba matar da za
a mayar baiwa ba ce.
Ban san yanda akayi ba naji bakina ya kama ce
mata, to me kike da shi da za a ce ki ciyar da baba?
Nace mai ciyar da miji in ya rasa ai babbar mata ce
wacce ta san rama alheri da alheri ba mai ci ta goge
baki ba saboda butulci.

41
Ina fadin hakan na ga Asabe ta fito daga
dakinmu da gudu tana tambayata zaki zage ta ne? Tun
kan in amsa baba Lantana ta soma kuka tana fadin to
zagi kam na nawa ai ta riga ta zageni.
Kan in san menene abin yi tuni har Asabe ta
rufeni da duka tana tambayata wannan wane irin raini
ne a gabana za ki zage ta.
Sanin da baba Lantana tayi na kullum mukayi
fadan dambe tsakanina da Asabe ita ke kwarata ya sa
wucewa tas higa dakinta ta barmu muna danben.
Danbe mai tsanani muka fara yi sai dai ba a je ko
ina ba sai ga shi na sunkuceta na fyadata da kasa a
gigice ta kurma ihu mai tsanani wanda ya yi dalilin
fitowar baba Lantana cikin sauri da kyar ta iya
banbareni a kan Asaben tana rabamu ta nufi kan
Sallau ta wankeshi da mari, gigitaccen mari
tambayarshi kana kallo aka yi hakan ina amfanin
zamanka a wurin? Ya ce uhun baba kenan kema ba
kina kallo aka fara ba kika wucekika tafi? Ni na daina
irin wannan abin na daina shigarwa kowa fada ni
dukan su daya ne a wurina dukansu yan uwana ne in
banda rashin kunyar tsiya meke hadani da Asabe da
zanje ina tayata fadan rashin gaskiya.
Tayi ta zage-zage da addu'o'in da ta ga zata iya
yi mishi.
Ina daki ina jinta tana cewa Asabe ke dama baki
shirya fadan ba kika zo kika rarumeta? To dame
42

wannan abinda kikayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login