Showing 33001 words to 36000 words out of 36183 words
min ba don haka ya zame min dole in tsaya in yi
duk wani abin da zanyi don ganin na yi auren saboda
in huta da wannan wulakancin da kuma cin mutuncin
kan haka yasa washegari da sassafe na yi shiri na tafi
gidan Yakumbo Halima wacce ta dade tana kirana
inzo muje wurin malaminta da take ta faman bani
albari.
147
Ina shiga gidan ta fara murmushi, 'yar halal kin
ko ambato yanzun nan nake maganarki a zuciyata. Na
tayata murmushin kafin na tsuguna na sOma gashcta
tana amsawa tana kallona cikin wani irin yanayi dake
baiyanar da jin dadinta.
Kai wannan yarinya da iya kwalliya kike wannan
kuma wane irin dinki ne? Mu ganshi.
Na numa mata ta gansi sosai, to me sunanshi?
Na gyara na koma na zauna cikin natsuwa, kwalliya ta
fa ke kadai take burgewa.
Ta yi maza ta ce wane mutum ai duk wanda ya
kalleki ya san ke din gwanar kwalliya ce Mero ai
rashi aurenki ba yana nufin ke din kina da wani aibu a
tare da ke ba ne a'a lalura ce dake wani aljani ke
gareki wanda yake biye da ke bana baki albarin
abinda wannan maiamin ya gaya min a kanki ba, ai
nace miki ki zo muje wurinshi don ya ce min akwai
abinda zai yi ya rabaki da shi kika fi zuwa.
Na ce to ai gani na zo yau Yakumbo zuwa nayi
don ki kaini inda duk za ki kaini na gaji, na gaji da
wulakancin da Mubarak yake yi min, na kwashe
bayani duka na yi mata.
Maimakon yauma ta nanata maganarta da kullum
take fadi cewar shi ne ya yi min sihirin da na kasa yin
aure sai naga ta yi murmushi kafin ta ee, ja'ira
shagwaba da gata ne suka sashi yin abubuwan da
yake yi su ma iyayen na shi ai sun yi nadamar hanashi
148
aurenki da sukayi yanzu tunda kwanaki ai ance korar
matar tashi ya yi ya ce a barshi kawai ya yi zamashi
shi kadai tunda dai suna kallo an hanashi ke sun kumna
yi ko oho da hakand a akayi saboda su basu damu ba
ai shi ne dalilin da ya sa ita Hajiya Ummulkhairin ta
kama hanya taje gidan Dijan to shi kuma babanki
shima ya kafe akan ba zai basu ke ba.
Na ce wannan ruwansu ne Yakumbo. Ta yi maza
ta ce ruwan su ma mai ma ya kare musu bari in yi
maza in shirya mu tafi tun rana bata yi zafi ba don
akwai 'yar tafiyar kafa da za a taba.
Nace mata to Yakumbo ai ma ni tafiyar kafa ba
mas' alata ba ce na riga na saba da ita, tayi amza ta ce,
aifa na tuna kin yi ta ba kadan sanda kike zuwa wajen
koyon sana' ar nan gashi ya zama tarihi sai amfanin
shi ake ci ko ince muke ci tunda yaushe rabon da
raina ya 6aci a kan dinkuna? Ace jaruntaka babu
dadi? Bari ki gani ins hirya yanzu mu tafi ba ma sai
na tsaya wanka ba tsaka tsami kawai zanyi in mun
dawo in ban ji kuiya ba na yi wankan.
Nan da nan Yakumbo ta shirya muka kama hanyr
fita, gani bata tambaya ba ya sani tambayarta, dama
kin gayawa kawu ne? Ta dan yi murmushi, mu yan
tsofaffini nan da auren mu ya riga ya tsufa yaushe za
ace komai za mu yi sai mun tsaya wani tambaya ai
shima yasan sabgogin iyali yawa ne da su.
149
Shiru nayi na ja bakina na tsuke tunda nasan
babu halin in tsaya ina tambayarta Yakunbo shi aurenn
yana tsufa pe a dalilin masu yinshi sun tsufa?
Bayan mun sauka a mota tafiyar kafa fosai
mukayi a ciki jeji muka wuce wasu rugage muka
mika cikin wani irin surkukin daji Yakumbu damun
san wurin nan haka yake ai da hayar babura muka
dauko a dan kauyen nan da muka wuto.
Hararata tayi, kufa yaran yanzu bakuda wata
jaruntaka wai ke kina so ne ki nuna min kin gaji da
tafiyar kafar da ake yi ko? Na yi murmushi kawai na
yi shiru muka ci gabada tafiya da kyar muka iso wata
mararraba da ta ce min wannan da muke kai yanzu ita
ce mai kaimu gidan nashi nace mata to.
Mun samu yan daidaikun mutane da ke jiran a
sallamesu amma ana sanar da shi isowar Yakunbo
yace a shiga da mu.
Na yi mamakin ganin mutumin da ta ce min shi
ne malamin na zaci ganinshi dattijo amma sai na
ganshi matashi ma'abocin tsabta da natsuwa ga sutura
tamkar dai ba a cikin dajin nan yake zaune ba.
Hajiya barka da zuwa, ya yi maganar cikin murya
mai cike da kamala suka gaisa nima na gaisheshi.
Maryamu ko? Ta yi murmushi ta ce haka aka yi
kuwa malam, idonshi a kaina ya ce, ai mun gani shi
mutum ai kowa da sunanshi yake yawo, gabana ya
fadi jin da nayi ya ce ya gani kar dai irinsu ne kullum
150
malamanmu suke yi mana wa'azi a kansu? Cikin
Zuciyata na ke wannan tunanin.
Ya jawo wani littafi ya bude yana karantawa na
dan samu saukin damuwa a tare da ni ganin littafi
yake karantawa su kuma malamanmu kulum suna yi
mana wa'azin ne akan masu buda kasa suna masu
duba ko bokaye to tunda wannan ba kasa bace littafi
ne kenan ba duba bane yinshi kuma bai zamo laifi ba.
Mas'alar aure ko? Ya yi tambayar ba tare da ya
kalli kowa ba idonshi a kan littafin shi, ta yi maza ta
ce mishi eh malam aure ne damuwar kullum sai
manema sun fito mata gasu gasu kamar za a yi auren
sai kuma a nemesu a rasa sun gudu, tun ina ganin
laifinta ina ganin kamar ita ke korarsu har na daina jin
zafinta na koma tausayi saboda na gane babu
hannunta cikin lamarin.
Ya girgiza kai cikin natsuwa tare da fadin, ai ba
zai bari a aureta ba, wa kenan malam? Ta yi tambayar
tana mai kallonshi. Ya ce mai ita mana ai wani
maketacin aljani ne yake tare da ita shi ya sa babu
halin tayi aure don ba zai bari ba shi yake korar mata
samarin da siddabaru iri-iri suna tare da ita su rinka
ganin ta caccanza musu tanayin launi lauru su ganta
fara su ganta baka su ganta ja su ganta bulu ko kumna
su rinka ganin fuskarta tana rabuwa biyu sai ta koma
ta hade ta sake rabewa ta sake hadewa, to kinga kuwa
ai babu lafiya.
151
Yakumbo tayi maza ta ce, ko kadan cikin sanyin
murya ni da kaina da ba sosai nake yarda da irin
wadannan abubuwan ba jikina bari yake yi jin
bayanin malamin.
To yanzu yaya za a yi kenan malam?
Ya ce eh to da yanda za a yis ai dai kumaaiki ne
babba sai an rabata da shi gaba daya in ba a tsaya an
yi hakan ba ko anyi auren kashe mijin zai yi don haka
sai an yi juriya da jarumtaka.
In dai za a rabata da shi ai duk wani abin da za a
yi ba zai gagara ba malam a gaya mana kawai abin da
za a yi.
Ya ce to babu laifi akwai aiki da za a yi wanda za
a bukaci sadaka mai karfi ko dai shekararrun zakaru
guda bakwai ko kuma rago sannan zata rinka zuwa
nan muna yi mata wani aiki har kwana bakwai in har
komai ya tafi daidai to kafin cikar kwanaki bakwan
din nan mijin da zata aura zai baiyana ana gamawa sai
a daura auren mu kuma in ayzo to shi ne zai biya
ladan aikinmu baku ba.
Nan da nan Yakumbo ta shiga yi mishi godiya
tare da tambayar to wanne ya yi tsakanin rago da
kajin? Ya ce a'a ao na za a hada ba rago yafi sai dai in
babu hali sai a yi da kajin duk daya ne.
Ta ce to bari mu bada kudin ragon nawa ne zai
yi? Ya ce daga fan goma zuwa sha biyar ko ashirinn
duk wanda kika bayar zai yi.
152
Na yi kasake ina tunanin ta inda kudin da ya
ambata zasu fito sai kawai naga Yakumbo ta jawo
lalitarta ta ciro kudi ta kirga fam goma sha biyar cif ta
mika mshi, ya ce zuba nan cikin wannan kwaryar, ta bi
umarnin nashi ta zuba muka yi mishi sallama muka fito.
Babu abinda yafi komai yi min dadi irin cewar da
ya yi kafin a kammala aikin mijina zai baiyana ana
gamawa kuma sai a daura auren shi nne ma wai zai
biyashi kenan nima zan yi aure babu sauran a tareni a
zageni babu sauran a yi min gori, babu sauran a rinka
nunani a unguwa ana fadin babu sauran sa'ata a' yan
matan da ke yavwo a unguwar.
Washegari da safe naje na samu babana a rumfarshi
bayan na kammala shirina na dan zauna kamar zanyi
mishi hira sai da na bari Sallau ya dauki kwanduna ya
nufi kasuwa sai na kalli babana na ce mishi baba yaya
Dija ta aiko ni wurinka wai ince maka akwa wata
yarinyar bazawara mai hankali kusa da su ko za a yi
magana da ita.
Gabana yana faduwa na yi mshi bayanin, sai na ji
ya ce to ina da kudi ne da za a yi min amgana da
bazawara? Sannan da girmana da komai ita mace ace
miki tana son tsoho ne a shekarun. kuruciyarta.
A hankali na ce mishi, baba ai ita yaya Dija ina
ganin kamar sun fahimci juna ita da matar tace min ne
in yi maka magana in ka yarda ta turo maka ita don ka
ganta, a hankali ya ce a'a ni kam ai ba sai na ganta ba in
153
dai ku tayi muku ai shi kenan fitina ce dai kawai ni bana so.
Nace mishi too nayi mishi sallama na tashi na tafi,
can cikin zcuiyata kuwa mamajki nake yi ban taba zaton
haka amsar babana zata zamo ba, na kama hanyar tafiya
wurin malam don karbo alkawarin da akayi duk da wata
zuciyar tana nunamin in fara ganin yaya Dija tukunna
sai kuma naga to bari dai kawai inje can din in yaso in
na dawo sai in biyo ta wurinta in yi mata bayanin yanda
muka yi da babana daga nan kuma taga abin da na karbo wurin malam.
Wajen karfe goma sha dayan safe na isa kauyen
nan inda daga shine muka soma yin tafiyar kara, nayi
tafiyar kafar har na raina kaina sai da na soma kaiwa
matuka wajen gajiya ne ma na tuna ko sunan malamin
da zani wurin nashi ban ji ba balle kuma na kauyen da
zanin, abin ace na bata hanya ban san yanda za a yi inyi
tambayar da zata zamo mai amfani a gareni ba, sa'a
kawai nayi da na ci gaba da tafiya sai kawai na ganni a
mararrabar nan wacce daga ita ne muka dauki hanyar da
ta nufi gidan malam.
Tsayawa nayi cak. na zubawa hanyoin nan ido ina
kallonsu tare da tunanin wacce muka hau ne a ranar? Na
gaji da dubawa na yankewa kaina bari kawai in hau kan
guda daya tunda bajuyawa baya zanyi ba don haka na
kama ta tsakiyar nayi ta tafiya a kanta banga komai ba
banga wata alama da na gani wacce ta karfafaa min
guiwa ba don haka na juyo da baya zuwa inda
154
nararrabar nan take na sake zabar wata hanyar na hau
an nma nayi iyakacin iyawata nayi tafiya sai da na fara
debe tsammani ina cikin tunanin komawa da baya kawai
in koma gida inje in gayawa Yakurmbo Halima cewar
ban gane hanyar ba tazo kawai ta karbar min maganin
da kanta ko ta tasoni a gata mu zo tare kamar yanda tayi
min rannan tunda ni na kasa gane wurin da kaina sai
kawai naga mutum tsaye cif a gabana tamkar daga sama
aka jehoshi, tsoro ya.yi matukar kamani ba tare da ya ce
min komai ba sai naji ya ce min, wuce mu tafi malam ne
ya turoni in kai mishi ke saboda an gaya mishi cewar
kin kauce hanya don haka ya kwatantamin inda zan
sameki shi yasa na yanko ta cikin bishiyoyin can, nabi
hannun nashi da kallo don inga can din da yake magana
akai, wani irin surkukui ne da sunkurun duhun
bishiyoyi da ban taba tunanin dan adam zai iya shigarsu
ba ban iya buda baki na ce mishi komai ba haka nan duk
da tsananin tsoron da nake cikin ba zai yiwu in yi musu
binshi ba tunda ban san inda zan dosa ba.
Tasani kawai yayi a gaba muka kama hanya 'yar
tafiya "yar kankanuwa sai kawai gamu mun isa gidan.
Shiga nan, yana bani umarni nayi maza na shiga sai
ga malam zaune daram a kan buzunshi cikin manyan
kaya ga hularshi a kanshi yayi kwalliya irin wacce ta
dace da shi.
Maryamn da so ya kira sunan nawa yana ma
kallona, ina babar taki? Na isar da gaisuwarta gareshi
bayan na gama gaisheshi ya ce, alheri ya gaieta, ai ga
155
kwaryar da na hangki a ciki can, nayi maza na waiwaya
na kalli kwaryar da ya ce min daga cikin nata ya
hangeni babu komai a ciki in banda ruwa, na sake
juyawa gareshi na kalleshi don jin bayanin da yake yi,
yayin da zuciyata ke ta faman harbawa 6al 6al 6al, daga
nan din ne na kira wanda ya daukokin don kar ki je ki yi
wa mutanen hanayr da kike ta kakkaucewar wani ta'adi
unda su di mafi yawancinsu ba hakuri ne da su ba.
Wani mutum ya ashigo rike da zangarniyar dawa a
hannunshi ya tsuguna ya mikawa malam, bai kalleshi ba
ya ce mishi, kwaya bakwai nake bukata, ya mika mishi
kwaya bakwai din ya fita da zaugarmiyar a hannunshi.
Malam ya jawo wani tsohon kasko fasasshe ya
debo kasa tafin hannunshi uku ya zuba a ciki ya dauki
tulun dake gefenshi ya jika kasar da ruwa ta jiku sannan
ya shuka kwayoyin dawan nan guda bakwai a ciki kan
kace meye wannan sai kawai naga dawar nan da ya
shuka a kan idona ta kamna tsirowa a cikin kaskon, nan
na zuba ido ina kallon abin mamaki wanda ben atôa
ganin kwatankwacin makamancinshi ba, na yi matukar
kokarina wajen 6oye halin da nake ciki na tsoro saboda
ganewar da nayi ina cikin wani babban al'amari,don
haka nayi maza na soma karanto addu'o'i na neman
tsari.
Kina da wani wanda ya dameki ne a yi miki maganinshi? Na'am na amsa ina kallonshi don ban
fahimci abinda maganar tashi take nufi ba, eh abinda
nake nufi kenan in kina da wani wanda ya dameki
156
kawo sunanshi mu gwada miki aikinmu a kanshi ta
hanayar kashe miki shi nan take.
Kalululu, sautin da cikina ya bayar kenan a lokacin
da na ji maganar tashi, da kyar na iya girgiza kaina don
nuna mishi alamar babu, cikin zuiyata kuma tarnbayar
kaina nake yi me yasa malam yake yi min irin
wadannan abubuwan tunda ni ai ba abin da ya kawoni
wurinshi kenan ba, sannan me yasa bai yi ba ranna na
gaban Yakunbo sai yau da ya ganni na zo ni kadai
Kina saurarona? Na yi maza nace mishi eh, ita
babar taki ta yi miki bayani a kan ka'idojin aikinmu ko?
Na girgiza kai nuna alamar a'a, to muna da ka'idojn da
karyasu yake da hatsari kwarai shi yasa muke bayani a
kansu don kar mutum ya jawa kanshi wata fitina da zata
zo ta dameshi ta damu duk wani wanda yake tare da shi,
ba a yin musu da umarnin da ake bayarwa anan ko mai
tsananinshi, sannan ba a yin gardama ko jayaiya domin
nan din Wuri ne da ake mu'amala da nau'o in halittu
guda uku wato jinsi mutane da na aljanu sai kuma
rauhanai don haka ba wurin wargi kika zo ba, yin daya
daga cikin ukun can dana ambata miki ina nufin musu
gardma ko jayaiya sakamckonshi yin hauka ne hauka
kuma irin wacce bata warkewa.
Cikina ya sake bada wani sautin na kulutuiu har ma
ya fi na farkon karfi saboda tsananin tsoro da na samu
kaina a ciki din.
Kin taba ganin aljani ko rauhani? Na yi maza na ce
mishi a'a, to ai za ki ganshi yau din nan. Na ji kamar in
157
zabura in mike in karta da gudu in shige cikin dajin nan
in huta.
Ya gyara zama ya soma yi min bayani, kin san
akwai jinsih mutum da na aljan da raunahni kafin
mala'iku ko? Angi maza na ce eh ba tare da na fahimci
koami ba da yake nufi ba. To mu nan fadar rauhani kika
zo ki gane? Na sake yin karfin halin cewa eb. Ya zuba
min ido yana kallona ban sani ba ko shima ya gane halin
da nake ciki na tsoro ne.
Yanzu kafin rauhanin da zai yi miki aikin ya iso
tunda mum riga mun kirashi yana can yana dawafi ne in
ya gama zai taho, kin taba yin sata? Tambayar tashi ta
zo min a bazata, na yi maza na kalieshi don inji ko
abinda aa jin daidai ne, ya ce eh abinda na tambayeyi
kenan, kin taba yin sata? Na ce mishi a'a, sata ko wacce
iri baki taba ba? Kin san fa ba a karya a nan, in ka riga
ka shigo nan to gaskiya da gaskiya ne kawai, in kayi
karyar ma za su gane ka don baka yi tunani sosai don
kar su kamaki da laifin yin karya.
Na gama tunanin da zanyi sai na ce mishi, sai dai
ko na abinci ko naman miya a wurin matar babana. Ya
yi maza ya ce, a'a ai wanna ba sata bace bari kawai a
gaya musu baki taba sata ba ko da yake ma suna nan
tare da mu suna jinki, ko kina yin karya? Na dan yi
shiru cikin nazari kafin .shima na ce mishi wani loakci
na kan yi amma ba ko da yaushe ba.
Ya gyada kai tare da fadin, to babu laifi ya yi kya,
kina da kiyayewa kenan? Na ce mishi ch, to ai shi kenan
158
sun jiki, tambaya ta karshe ki fa yi hakuri ba daga ni
bane kaidarsu nake bi don haka suke bincike kan
kamewar mutun kafin sù shigar mishi, kin gamsu? Na
ce eh. Kin taba yin ziua? Na girgza kai na nuna alamar
a'a, to ai ma shi kenan aikin naki mai sauki ne tunda
baki da kazanta mai yawa a tare da ke sai ta kananan
zunubai wannan kuwa dukkanmu ne don haka ki
kwantar da hankalinki shi wannan nikin naki mai sauki
ne kwarai an yi irinshi yafi sau nawa anan in dai kin
bada hadin kai ai shi ke nan tsanani wana uku ne zuwa
bakwai magana ta kare don haka bari ya iso ya
sallameki, na riga na ji tasowarshi don haka bari in yi
miki tuni ka'idojinshi banda musu banda gardama
banda jayaiya ba abokin wasanki bane sakamakon yin
hakan hauka ce da babu nagani kin gane ko? Na ce eh,
can cikin zuciyata kuwa addu'o'i nake ta yi na neman
rabuwa da rauhani lafiya.
Ana cikin haka naji wani abu ya fara bayar da wani
sauti na shuuuuuw sai dai ban san daga ina yake fitowa
ba, wata irin iska'mai sanyi ta fara shigowa dakin.
Yauwa gashi nan ya doso mu gashi nan ya dunfaro
gashi nan zuwa kar ki mance da abinda na gaya miki
don ni kaucewa zanyi in baku wuri banda musu banda
jayaiya banda gardama, dif sai kawai naga wutar fitila ta
mutu duhu mai tsanani ya baiyana, na yi matukar tsorata
irin tsoratar da ba zai yiwu in kwatanta ta ba.
A firgice kwarai na shiga furta kalmar Innalillahi
wa inna ilaihi raji'un, shiiiii sautin da ke ta karuwa a
159
cikin dakin kenan sai kuma tsananin sanyin da ya fara
lcadani, na shiga cikin