Showing 12001 words to 15000 words out of 34734 words
sa su yi abin da ba sa ra’ayi. Umma ma ta ce tana bayan ra’ayin Maimartaba.
Hadiza ta samu Turaki a sashensa ta yi masa bayanin yadda suka yi da iyayen su. Ko ba komai hankalinsa ya kwanta tunda sun yarda sun yafe masa, ya sa a ransa wannan karon shi da kansa zai dawo da Kulsumu rayuwarsa. Zai yi amfani da hikimarsa ta Da namiji wajen sabunta rayuwar su, zai nemi soyayyar Kulsumu, ba tare da taimakon kowa ba!!!.
Washegari Hadiza ta koma Kiru gidan mijinta.
Turaki ya kira Batulu sashensa. Batulu sarkin hidima ga Yayanta, tana shigowa niki-niki da tray da ta jero warmers a kai, ta ce, “Yaya Turaki guess what? Yau Burabuskon gero na yi maka da miyar ganye”.
Ya gintse fuska ya ce, “Fatima, in ya shake ni fa?”
Ta tuntsire da dariya ta ce, “Taste it first, bayan haka ma ga lemon abarba a gefe na hada maka, na zuba kankara a ciki sai ka dinga yi kana korawa”.
Ya yi murmushin sa mai aji, he is not in the mood na yin rahar, ya ce, “Na gode Fatima, Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki miji na gari. Zauna magana za mu yi”.
Ta zauna a gefe tana murmushin addu’ar da ya yi mata.
Ya ce, “Fatima game da kawarki ne, ai ke za ki taya ni biko ko? Ba za ki hukunta ni da laifina ba?”
Fatima-Batulu ta fadada murmushinta. Amma sai ta ga ya kamata ta kare wa Kulsumu martabar ta, an ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne. Balle Kulsumunta. Ta ce, “Yaya Turaki ina sonka da Kulsum, amma gaskiya yanzu na fi son ta auri wani daban wanda yake son ta”.
Lumsassun idanunsa ya bude sosai a kan Batulu, ya ce,
“Fatima na taba ce miki bana sonta?”
A zuciyarta hamdala ta ke yi, amma a fili sai ta ce, “Ai ba sai ka fada ba, action speaks louder than voice”.
Wani dan murmushi ya yi, ya dora habarsa a kan hannayensa da ke sarke cikin junansu. Cikin sanyin murya ya ce, “That was then… Fatima ke kanwata ce, ba zan iya gaya miki komai ba, alfarma kawai nake nema daga gare ki ki ba ni goyon baya, ni da ke mu hada gwiwa mu dawo da Kulsum cikin rayuwar mu, duk son da ki ke da ta auri mai sonta ai ba ya ni Fatima. Tunda masu iya magana sun ce, naka sai naka…”.
Batulu ta wani harare shi ta kasan ido, ta ce, “How can I believe kana sonta yanzu Yaya Turaki? Ba don ka faranta wa su Umma ba ne ka ke son dawo da ita? Gaskiya auren soyayya nake son Kulsumu ta sake yi, irin wanda nake fatar wa kaina”.
Turaki ya tsura wa kanwarsa Batulu ido, yana mamaki, ya ce, “Fatima I’m old enough in zaunar da ke ina fada miki abin da ba shi ne a raina ba. Sannan su Umma sun cire hannnsu cikin maganar nan, ke kadai ce support din da ya rage min if you didn’t trust your brother, who will? So ki ke dai in fito fili in ce miki sonta nake yi ba dan kadan ba, don Allah ki taimake ni Batulu”.
A wannan gabar, Batulu ta karaya, ta amince da gaske yake yi. Sai ta ji ba za ta iya gaya masa ma Kulsumu ta bar garin Gaya ba, zuwa inda ita kanta ba ta sani ba. Domin Goggo ba ta fada mata ba. Hajiya Nasara ta nusar da Goggo kada ta gaya wa dangin mijin Kulsumu inda ta ke, domin ta fahimci har gobe Kulsumu na son Turaki, ba abun mamaki ba ne in ya dawo ya nemi kome ta ce ta fasa karatun, tunda an ce ba shi ya sake ta da kansa ba.
Don haka Batulu ba ta san garin da aka tafi da Kulsumu ba, Goggo dai ta ce da su ‘yar Yayarta ce ta tafi da ita birni, ita ko sunan garin ba ta sani ba.
Don haka Batulu ta ja bakinta ta yi shiru, ta ce da shi in ya shirya za ta raka shi biko. Ya ce ai shi a yau yake so su je ba sai gobe ba.
Suna tafe a gefen hanya zuwa gidan Malam Jibo, garin ba wuta sai hasken farin wata. Turaki na yi wa Batulu tambayoyi a kan Kulsumu, Kulsumun da har aure ya hada su bai san komai a kanta ba. A yau ba abin da yake son ji irin zancenta, Batulu ta lura hirar Kulsumu kawai yake son su yi, ko ta yi niyyar share shi ba ta iyawa, domin Ubangiji da ya nufe su da fitowa daga ciki daya shi ya sanya kaunar juna a tsakaninsu.
Ya ji abubuwa masu yawa a kan Kulsumu daga bakin Batulu, wadanda suka kusan fiddo hawaye daga idanunsa.
Ta ce, “Ita Kulsumu ai mai hakuri ce, duk shekarun nan da ka diba ba ka dawo ba, ba ta korafi. She never complain. Tare muke zuwa makaranta mu dawo, babu wanda ya san tana da aure. Rannan ta ce min,
"Batulu Allah ya sa Yayanki lafiya yake, ni dai in yana lafiya zuwa ne kawai ba zai yi ba, to falillahil hamdu, zan ci gaba da jiransa daga nan har gaban abada!. Sai dai in shi ya dawo ya ce ba ya aure na”.
Turaki ya kauda kai sabida hawaye da suka ciko idonsa. Ya ce, “Wallahi Batulu, ban taba kinta ba, ban taba jin tsanarta a zuciyata ba. Kawai aurenta ya yi min wuri kuma ina son in ji ina son mace kafin in aure ta, sai aka yi min aure na gaggawa, sannan ban samu nutsuwa da isasshen lokacin da za mu fahimci juna ba ina tsaka da shirye-shiryen tafiya ta.
Bayan na tafi kullum da tunaninta nake kwana nake tashi. Ban taba kawo wa a raina Maimartaba zai taba tunanin raba auren mu ba ko shekara goma zanyi ban dawo ba. Da ban yi wannan dadewar ban dawo ba. Abin da raina ke gaya min kullum aurenmu na har abada ne, babu abin da zai raba shi, kuma dukkan obstacles din da ke cikinsa da sannu zan shawo kansu.
Zan bai wa kawarki mamaki Batulu, wannan sabon Abubakar ne, ba wanda ta sani a shekarun kuruciyarta ba”.
Batulu ta san duk abin da yake fadi, har zuciyarsa yake nufi. Amma can a kasan ranta ta san ta yi masa nisa, nisan da ba ta san ranar da Allah zai hada su ba, don kuwa Goggo ta ce mata, ita ko sunan garin da ta ke ba ta sani ba.
Daidai lokacin da suka kawo gidan Malam Jibo, ta ce ya tsaya a kofar gida ta fara shiga. Ba ta jima da shiga ba ta fito, ta ce, Goggo ta ce ya shigo. Sabuwar tabarma Goggo ta fiddo ta shimfida masa, ta rasa a wane yanayi ta tsinci kanta. Yau Turaki ne da kansa ya biyo sawun Kulsumunta! Ko ya ya za ta ji in da a ce tana nan?
Ita shaida ce kan cewa har gobe Kulsumu na son mijinta. Ba ta da zabi ne cikin hukuncin da iyayensa suka yanke musu, sannan kawaicinta ba zai bari ka san abin da ke zuciyarta ba.
Muryar Turaki ta yi sanyi a lokacin da yake gayar da Goggo. Ya rasa me ya sa jikinsa ya yi la’asar, watakila hakan na da nasaba da alamun babu giftawar Kulsumu cikin gidan da ya gani.
Goggo ta ce, “Matafiya an dawo kenan? Da fatan an samu nasarar abin da aka je nema?”
Yana cikin amsa mata Baffa ya yi sallama ya shigo gidan. Da tocilan din hannunsa ya haska Turaki amma bai gane shi ba, domin bayan girma da Turaki ya kara ya ajiye kyakkyawan sajen da ba shi da shi a baya. Fatarsa ta wanke ta yi smooth sannan ta kara yin fresh da ita. Ya ce da Goggo,
“Baki muka yi ne? daga ina, ban waye da su ba”.
Batulu ta yi zaraf ta ce, “Baffa Yaya Turaki ne fa”.
Kan Turaki na kasa, ya rasa inda zai sa kansa da kunyar wadannan dattijai.
Baffa ya ce, “Turaki dai? Turakin da na sani? Na Kulsumu?”
Ba zai iya fadin yadda wannan sentence din ya taba zuciyarsa ba (Turakin Kulsumu).
Wasu hawaye marasa dalili suka sake ciko idonsa. Ya gurfana gaban Baffa ya soma ba shi hakuri a bisa laifinsa na kin dawowa gida kamar yadda ya alkawarta wa iyayensa. Sannan ya ce, “Baffa ni da bakina ban saki Kulsumu ba, amma tunda shari’a ce ta raba auren, kuma Kulsumu ta yi min idda na zo da kokon barana ina rokonku ku dawo min da Kulsumu dakinta. Insha Allahu ba zan ba ku kunya ba, zan rike Ummu-Kulsum da soyayya da amana har karshen rayuwarmu.
Baffa Maimartaba da Umma sun ce ba za su sanya baki ku dawo min da Ummukulsum ba, kada su tirsasa ku. Baffa ni a kan-kaina na zo bikon matata, ku yi min uzuri ku karbi hanzarina, ku ba ni dama ko da ita ce alfarma ta karshe da za ku yi min a kan Ummu-kulsum”.
Baffa da Goggo suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su. Batulu ma hawaye ta ke yi, ta ce.
“Baffa don Allah ku yi wa Yaya Turaki alfarma, ni shaida ce a kan cewa yana son Kulsumu, ko da ma can Baffa shi fa ba wai ba ya sonta ba ne, kuruciya ce da kuma karatun nan da ya sa a gaba, don Allah Goggo ki ba wa Baffa hakuri”.
Goggo ta nisa ta ce, “Batulu sarkin manyance, mu ai ba mu yi fushi ba, kuma ba mu muka ce a dawo da Kulsumu ba, hukuncin na Maimartaba ne”.
Batulu ta ce, “To Goggo ku barsu su shirya da kansu. Idan suka shirya kansu Maimartaba sai ya fi kowa farin ciki”.
Baffa ya dubi Turaki, duk sai ya ba shi tausayi, ya ce, “Abubakar, shi sha’ani na tsallake maganar iyaye da ma karshensa nadama. Na ji dadi da ka fahimci ka kuskurewa iyayenka, kuma ka dawo ka nemi afuwarsu. Har kake son gyarawa. Amma zancen nan da nake maka Kulsumu ba ta gidan nan…”.
Da sauri Turaki ya dago lumsassun idanun sa ya dora a kan tsohon, hasken farin wata na kara musu walainiya. Baffa ya karashe zancensa da cewa,
“Kulsumu ba ta garin nan ma bakidaya!”.
Dukkansu babu wanda bai ji nannauyar ajiyar zuciyar da Turaki ya sauke ba. Ya ce,
“Tana ina Baffa? Ko ina ne zan bi ta”.
Da muryar da Batulu ta kasa amincewa cewa tasa ce. Goggo ta yi saurin cewa,
“Ai an ce ma sun bar kasar, ‘yar Yayata ce ta tafi da ita. Ni kuma ban ma rike sunan kasar ba, Baffa ya ma sunan kasar?”
Baffa ya ce, “Ke ba ki rike ba balle ni? Ko Yagwaslabiya ne ko me? Oho!”
Saura kadan Batulu ta yi dariya ganin Goggo da Baffa sun dage suna son tunawa juna kasar da Kulsumu ta tafi, amma an rasa mai tada daya.
Turaki wanda ke jin wani tukuki a ran sa kamar ya hadiyi zuciya ya huta ya ce,
“Babu lambar wayar wadanda suka dauke ta din?”
Goggo ta ce, “Yo mu ina muka ga waya? Suna da waya kuwa, don da ta zo na ga tana magana da ita, amma ban yi azancin karbar lambar ba. Amma Turaki ka kwantar da hankalinka, duk karshen shekara za ta kawo ta gida hutu”.
Turaki ya ce, “Goggo idan ta zo ba na nan fa? Ni din ba mazauni ba ne, a can inda na yi karatu na samu aiki, da ma zuwa na yi in dauke ta mu koma tare”.
Baffa ya ce, “To insha Allahu duk ranar da Allah ya kawo su za a karba maka lambar waya a ajiye. Ko yarinyar nan Batulu za a kira a ba ta”.
Jiki a salube cikin mutuwar jiki da yankewar buri Turaki ya baro gidan su Kulsumu, Batulu ta tausaya masa halin da ta ga ya shiga. Har suka zo gida bai iya ce wa komai ba. Batulu ta kwashe duk abin da ya faru gidan Goggo ta labarta wa Umma. Tana mai tausaya wa halin da dan uwanta ke ciki.
Umma ta yi dan murmushi, ta ce,
“Daga baya ke nan!”.
Daga wannan ba ta kara tofawa ba.
*** *** ***
Washegari Goggo ta kira Hajiya Nasara ta ce, “Nasara jiya sai ga mu da babban bako, mijin Kulsumu daga Turai ya zo biko”.
Hajiya Nasara ta ce, “Ina fatan dai Goggo kin bi shawarata ba ki gaya masa inda ta ke ba?”
Goggo ta ce, “Ai na fahimci abin da ki ke nufi Nasara, cewa muka yi ma ba ta kasar, daga ni har Baffa kuma ko sunan kasar da ku ke ba mu sani ba.
Amma gaskiya Turaki ya ba ni tausayi, sai da na ji kamar in ba shi lambar wayarta, amma na ce bari in fara shawara da ke tukun kada in bata lamari. Amma mai zai hana mu maida mishi matarshi ta yi karatun a dakinta Nasara? Aure fa yana gaba da komai, kuma na san ba za su hana Kulsumu karatu ba”.
A tsanake Hajiya Nasara ta ce, “Goggo, kada ki yi saurin karaya. Mijin Kulsumu yana bukatar a ba shi lokaci ya tantance tsakanin fari da baki a cikin aurensa da Kulsumu. Ma’ana, baki da tabbacin zai maida ta ne don ya faranta wa iyayensa ko don yana sonta. Sannan ita ma Kulsumu akwai bukatar ta kara hankali, wayewa da nutsuwa kafin ta zaba wa kanta hukuncin komawa gidan mijinta ko yin sabon aure.
Goggo ki daure ki ci gaba da ba ni hadin kai tukunna, ki cire tausayin Turaki a ranki. Shi bai tausaya wa jikarki ba ya tafi ya barta shekara da shekaru a dakinsa ba sako babu kulawa? Ni ban yarda yanzu sonta yake ba, na fi yarda da cewa so yake ya gyara tsakaninsa da iyayensa.
Ki kyale Kulsumu na dan lokaci ta kara sanin kanta, ta samu lafiyar jikin ta, ta yi karatunta sannan ta auri mijin da ke son ta ta ke son shi. Ra’ayi da tunanin su ya zo daya. Koda kuwa Turakin ne amma a can gaba. Sannan Turakin nan fa ba shi ne autan maza ba, ba'a ce bayan shi Kulsumu bazata auru ba wai don lalurar ta, kuma duk abin da ki ke hange a tare da shi akwai shi a sauran maza.
Ki fahimce ni Yaya Aishatu, ba nufi na in hana Kulsumu aure ba, amma don Allah ki kara mata lokaci. Na yi miki alkawarin ranar data zama cikakkiyar Nurse zan dawo miki da ita ta zabi mijin aure. Alhamdu lillahi ta samu lafiyarta wadda ya guje ta a kanta bai kamata don ya zo ya marairaice muku tashi daya ku yi saurin amsa masa ba, gara ya san Kulsumu mace ce mai daraja ya kuma san cewa akwai bambanci tsakanin mai lalurar da ya guda da wannan ta yanzu”.
Goggo ta rausayar da kai, ta ce, “Duk na fahimce ki, na kuma yarda da shawarar ki. Sai dai ba mu da hujjar cewa Turaki ya guji Kulsumu ne sabida lalurarta. Sun auri Kulsumu a kan sanin cewa tana da lalurar. Aure ne dai in Allah ya kawo karshensa dan Adam bai da dabara, amma na yarda da hujjojin da ya bayar kwata-kwata ba su da alaka da lalurar ta”.
Hajiya Nasara ta ce, “Shi ke nan. Allah shi ne masanin gaibu, amma maganar komen nan ki manta da ita Goggo, cikin watan nan Kulsumu za ta fara karatunta, ina rokonku don Allah ku manta da Turaki. Can gaba in suna da rabon komawar sa koma idan tana son shi yana sonta cikin nutsuwa da cikakken hankalin su, Allah ya yi wa Kulsumu zabi mafi alkhairi”.
Goggo ta ce, “Amin Nasara, insha Allahu yadda ki ka ce, haka za a yi”.
*** *** ***
Umma ta shiga turakar Maimartaba a daren ranar a matsayinta na mai girki a ranar. Bayan ya gama cin abinci ta ke labarta masa yadda Batulu ta ba ta labarin zuwansu gidan Malam Jibo ita da Turaki, Maimartaba ya gama sauraronta tsaf! Sannan ya yi murmushi ya ce.
“Kin ga hikimar da na yi ta zare hannunmu daga cikin maganar ta fito zahiri ko? Sun dauke ‘yar su zuwa inda za ta samu kwanciyar hankali ta yi karatun da